Showing 243001 words to 246000 words out of 255288 words

Chapter 82 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1401

ji tayi still barcin bai isheta ba ,
Anty ce tafado mata arai don shi baba yace ya yafe mata tadaina kiranshi idan yaso shida kanshi zaiwa mijin ta magana abata waya,
Anty ta,dauki wayan cikin wani murya wanda maryam din bawai tasan ta dashi bane,
Gaisawa sukayi sama sama batare da tasakewa maryam din ba,
Sai maryam dince ke cewa abata su Assalam su gaisa,
Bayan sun gama wayan ne sai tunanen yadda yanzu yarta ke mata yadamay ta,
Daga gurin ta koma barci abin ta har akai sallah azuhur maryam bata farka ba,
Yusuf yadawo daga massalaci yaganta a kwance shi da kanshi yata da ita,
Ido ya tsura mata kamar mai son ya gane wani abu acikin ta,
Maryam ya kira sunan ta inda ita Maryam din ta ansa mai a hankali,
YUSUF yace wai mai ke samun kine haka naga duk yanzu kin koma wata iri jiki babu kwari,
Sai barci all the time, may yasa hakane wai, ?
Maryam tadan langabe kan ta tace nima ban sani ba uncle haka kawai nake jin ba dadi ko da yaushe,
Gaskiya anjima zakai ki kiga likita don yadiba min ke ko baki da lafiya ne,
Tana kokarin mikewa,zaune ne tace to aini lafiya na kalau uncle,
Gaskiya ban yarda ba inji uncle yace wa maryam din,
Dole ne aduba minke don duk kwanan nan an hana min, samun wanan ni,imar da aka saba bani
Din yanzu kusan manaji kawai nakeyi ban samu ina kashe kishin sha,awata kamar da,,
Kunya ya kama maryam din wace ta boye fuskan ta cikin filin dake kusa da ita,
Kwana biyu maryam taki yarda,su je gurin likata ta dage wai ita lafiyan ta kalau gajiyan tafiyan jirgine ke tambayar ta,
Shiko Yusuf ya kasa barin ta ta huta kullun sai kokarin diban rabon shi yake yi gare ta,
Hakan yasa jikita yai weak sosai har saida takai kwance,
Bashiri dole suka tafi asibiti don adibata, saboda yadda take jin jikin ta,
Awon farko likita yagane cewa cikine a jikin maryam na wata uku,
Gashi kuma saboda rashin samun hutu har cikin shima yana son samun problem,
Yusuf tun agaban doctor ya rungumay maryam cikin hamdala ga ubangijin shi

Mutum na farko da Yusuf din ya fara kira itace Γ€nty Dije tanuwa Yusuf din farincikin ta sosai a fili,
Amma sai dai abinda ya kula dashi bata tambayi lafiyan maryam din ba,
Amma kuma sai bai dauki zancen da muhinmanci ba,
Ita ko maryam safiya ce takira ta sheda mata duk yadda,sukayi da likita da bed rest din da aka bata,
Anan sadiya tai wa maryam alkawarin zuwa ta diba ta,
Saboda sanin irin mutanen da maryam din kezaune da su,
Mahaifiyan safiya bata da matsala indai har al,amari na maryam ne,
Aikuwa washe gari safiya tafara shirin tafiya,Abuja inda tayowa maryam din tsaraban kanyan miyan hausawa na gargajiya,
Motar farko tabiyo zuwa Abuja din inda suka iso musalin karfe biyun rana,
Maryam taji dadin wanan ziyaran da aminiyar ta takawo mata,
Ita ko safiya sai kallon mamaki takewa kawar ta ga kuma irin daulan da Allah yaba ta,
Gaskiya Allah miskaraziratin ne, ga bayin shi,
Kamar ba maryam wace ke ta aikin wahala agidan yar uwar taba,
Gashi duk wahalan nan da tasha don Allah yaba maryam din gurin zama mai kyau gashi kuma Anty tafara kushewa,
Yusuf yadawo daga gurin aikin yasa mu maryam tare da,abokiyar ta,suna hiran su gwanin sha,awa,
Nan ya zauna tare dasu ya gaisa da Safiya din, inda yake tambayan ta labarin mutanen kwantagora,
Yaso ya tambaye ta zancen Jibrin amma sai fasa saboda ko shi bai son ya tuna da maganar ,
Maryam daga inda take kwace suka hada ido da Yusuf yai mata,wani irin kashe ido
Wanda ita kadaice tasan ma,anan wanan kashe idon ,
Kafadar ta tadaga mai alamar a,a yakara dan langabe kai maryam tai mai da nuni da Safiya wace tabada baya tana kallon TV,
Ya juya yana fara tafiya jiki ba kwari yadan juyo yana cewa ai na manta gobe zamu yi baki daga Niger state,,,,,


ZEEE MAKAWA YELWA

🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
9⃣7⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI


YA ALLLAH KA KARAWA ANNABI DARAJJA KA KARAWA MUSULUNCI DARAJA πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘

Tun lokacin da Yusuf ya buga mata waya akan zancen, cikin maryam sai ta,shiga tunane,
Shin maganar da Umma da, Yashe suka fada mata akan maryam gaskiya,ne kuwa,
To in ma har gaskiyane ai shi Yusuf mai yai mata da har zata hada dashi a cikin maganar,
Ita kan ta maryam din har yau bataga wani alaman daga gare ta ba,
Don dai duk yadda,take nuna mata cewa tagane may sukayi
Bai hanata kusan kullun bugo mata waya ba ta gaishe ta,
Uwale ce ta kara kwada sallama Anty dijen zaune a falo,
Firgigit Dije tai ajiyan zuciya tadawo daganin ga aminiyar ta uwale,
Wani irin tunane kike yi haka Dije ?
Uwale ce ke tambayar ta cikin mamaki don son jin ansa,
Numfashi ta sauke da nauyi cikin da nuna damuwa a fuskan ta ,
Tace ke dai Uwale bari kawai wallahi wani magana ne ke damuna,
Subbahanallahi inji uwale ijin maganar da sauki dai,
Ke ba wani magana bane sai maganan maryam
May yasamu maryam din cikin tashin hankali uwale ke tambaya,
Bari kedai Uwale wai ashe maryam da kawar ta safiya ni sukaje yiwa asiri kwanaki har tai wanan ciwo din,
" Ke, Dije cikin zaro idanu Uwale tace haka nan,
Yanzu wani mara tsoron Allah ne ke son hadaki da yar uwan ki,
Yarinyar da ba tafita ko ina ko yaushe tana gida abinta,
Nima dai shi nagani Uwale,
Bayau ba tun da maryam din tai aure da kwana biyu naji maganan wallahi,
Uwale Umma mahaifiyana itace tazo tasamay tare da Yashe, wai maryam da kawar ta safiya sun ji gidan wani malami wai ai masu aiki a kaina ita maryam din ta samu miji wanda yafini,ita kuma safiya wai baban yaran nan take so,
Innalillahi wa,ina alaihim raji,un,
Dije ina ilimin ki da tunanen ki suka tafi dahar ki ka yarda da waman zancen da bai da kai baida gindi,
Wanan ma ai zancen shirmay ne koda ace maryam ba yar uwar ki bace ta jini ai zaman da ku kayi yawuce irin wanan cuntan,
Amma gaskiya dije baki tunane jiyadda yarinya ta dauke tankar mahaifiyar ta,
Anty dije tafadi cikin wani irin murya tace Uwale tunan da nakeyi ke nan ida hakane Maryam tana min hassada ai da baza ta ciga ba da mai dani tankar mahaifiyar ta ba,
Ki di fa hatta kayan lefen da wai miji yahado mata daga waje da suka fita saida tace akawo min in yi duk yadda ya dace,,
So,sai Uwale,ta kara fahintar da Dijen akan cewa Umma tana son ne kawai ta rabu su da maryam din,
Uwale tai mata tuni a kan sunan da zata raka ta gobe a kan wuri,
Bayan fitar uwale ne bada wani dadewa ba umma ta shigo gidan,
Bayan sun gaisa ne Anty Dije tana mamakin yadda yanzu umma ke yawan zuwa gidan ta,
Cikin zanin ta tafito da,wani bakin leda tana kokarin budewa tana leken hanya,
Zuviyan Anty dije yasa mata tsoro sosai akan mahaifiyar nata,
Wanan dan kwallaban ruwan ciki akeso ya taba jikin maryam din,
Wanan garin kuma hayaki zakiyi ki dinga kiran sunan maryam da mijin ta,
Kine cewa su rabu har abada,
Gaban anty yaba da dammm maganar uwale ne yafado mata arai,
Data ce idan maryam bata da alhakin ta duk sherin da taiwa yarinyar zai iya dawowa akanta,
Con n rawan murya Anty Dije tace umma, in raba sufa kikace,
Umma tace to sai may don kin raba su dije ?
Yanzun ke inba rashin wayon ki ba har ace diyar kishiyana wace batakai ko ki diri ba balle ma,ana wai tafiku sa,an daki,
Innalillahi umma maryam fa tankar diyar ki take don may zamuyi mata haka ?
Dakuwa taiwa diyan nata tace wai ke yaushe zakiyi wayo ne dije,
Tun farko sam banso a ce kin dauki wanan yarinya tazauna agurin ki ba,
Gashi yanzu sanadin zamanta gidan yasa har wanan yaron ya gan ta ya aura,
Da yake ubanku muna fukine shi don yaga gurin ci yadauki yar shi yabayar,
Anty, dije taji wani iri a cikin ran ta yadda mahaifiyar ta, da kan ta kewa mahaifin ta wanan mumunar fahinta,
Sanan Umma din takara da cewa,kitabbatar da cewa kin yi duk yadda malam yace,
To Umma inji Anty dije tadan ja ledan kayan zuwa gefen kujera,,
Umma ta mike tsaye tana gyara daurin zanin ta tace tashi ki duba idan kuna da shimkafa ki debo min,
Ita dai Anty ta mike tsaye zuwa samo ledan da zata zuba masu,
Bayan tafiyan umma Anty dije ta zube a gurin cikin tashi hankali da nadama,,,,

Maryam ta gama gyaran jikin ta tadan juya gurin da Safiya take tsaye ta na, gyaran gadon da suka kwanta,
Maryam tace Safiya ban san ko may ke faruwa a tsakani na da Anty na ba, ?
Murmushi safiya tayi a lokacin da take gyara filon gadon,
Abinda Anty Dije da kannen ta suka rufe ido sukai mata yafado mata arai,
Idon ta dan runtse ta dan hade wasu miyau takaici dataji sun zo mata,
Amma a fili sai ta daure ta furtawa maryam din cewa ,
Maryam akwai matsala a tsakanin ki da Anty ban,dai fada maki wanan labarin bane,
Amma gaskiya an shiga tsakanin ku ke da yar uwan ki,
Do min maryam naje gaida Anty bayan ku wuce da kwana biyu, don in kwaso kayana agidan, sai kuma ta ce,
"Hmmmm, kawai tace ta girgiza kanta don bazata iya fadin maganar cin fuskan da Anty tafada mata ba, a lokacin,
Zaune maryam takai don ta fahinci akwai abinda yafaru a tsakani safiya da yar uwan ta har ita kanta zancen ya shafe ta, ke nan
Gaban maryam ya yanke yakara faduwa don tana tsoron ko may za,a ce tafadawa yar uwan nata, da har tai saurin dauka haka,,,

Yusuf ya fahinci cewa akwai matsala a tsakanin maryam da yar uwan ta, Anty dije,
Amma tunda ba bata fada mai komai ba akai don haka ya share zancen kamar bai san da maganar ba,
Sai,dai gaskiya yasan cewa a yadda yasan Anty dije bawai zata iya jure maganar ba,har ta bawa kaunar nata baya ba, haka,

Bakaramin dadi Yusuf yaji ba saboda irin yadda yaga Safiya tare da yan aikin su sun hadawa bakin shi abinci,
Suleiman ne, ya zo wanan, matashin da Yusuf ya tai maka da shawara a kasan Dubai,
Yasamu cigaba sosai ga harkan don har yana shirin komawa kara saro wasu kayan, a karo na biyu,
Sanar,ar kayan na electronic bakaramin sana,a bane, wurin samun ci gaba,
Tare yazo da wani kawunshi saboda su ma Yusuf godiya taimakom da yai mai, har gida,
Sun zowa maryam da tsaraba masu yawa da kuma kyautan turare da agogo wa , maigidan, na ta,
Bayan tafiyan su ne maryam da,safiya suka bude kayan suna kallo, suna yaba irin wanan kyautan na bajin ta,
A cikin kayan maryam ta dauki atamfa guda da takalman su, tace zatabawa Ruth, ne , sauran kuma gaba daya tabawa Safiya su,
Mamaki kwarai ya kama safiya din wanan irin kayan maryam zatace ta bar mata su duka,
Maryam ta ce haba Safiya komai ma zan iya maki a duniya saboda irin gudun mawar da ki kai min a duniya, nima,
Safiyar kin fa sadaukar da farin cikin ki a kai na kin dauki yan uwana da iyayyena tankar naki,
Banda abinda zan ce sai dai in maki fatan alheri yadda kikai min kema Allah yai maki,

Ganin zuwan safiya maryam ta dan samu sauki
Yusuf yace su shirya ya kai su cikin gari ranan duk sun yi farin ciki da jin zasu fita,
Yusuf Yayi hakane ko hakan zai kara sa maryam din ta kara warware, jikin ta,
Shiri na alfarma sukayi daga maryam din har safiyan,
Duk wanda ya gan su sai sun burge mai shi saboda yadda su ka haska,
Wani sabon restaurant da aka bude wanda sai ka isa za a gan ka a gurin,
Su uku a table guda suke zaune abincin da ke gaban su suke ci a cikin natsuwa da jan aji,
Duk lokacin da Safiya ta debi abinci zata kai ga bakin ta
Sai sun hada ido da wanan guy din, dake can gefe guda yana saye da wani glass baki a idon shi,
Maryam kan sau guda takai abincin a bakin ta taji bazata iya ci ba,
Ga nauyin jama,a ga kuma test din abincin bai mata ba a bakin ta,
Yusuf ya hankalta da ita ta kasa cin komai a gurin don haka ya matsa mata akan may zataci a kawo mata,
Amma sai maryam din tace ita Fanta kawai zata iya, sha,
Dariya abin ya bashi tare da tausayin yar matar nashi,
Saboda a duk wanan kayan daulan dake gaban ta bazata ci komai ba daga ciki, wai sai common Fanta,,
Da kanshi ya mike zuwa samo mata Fantan sai a lokacin safiya ke fadawa maryam wanan guy din da ya kureta da kallo, a bayan su,
Dawo wan Yusuf da zaman shi yai dai,dai da zuwan wanan guy din gurin, su,
Kafadan Yusuf din mutumin ya dan dafa ta baya yace, Joseph Emanuel,
Yusuf ya juyo don ganin mai maganan,
Umar sultan ya gani course mate din shi a Oxford,
Umar Sultan Yusuf yace cikin mamaki inda su maryam duk suka bisu da kallo,
Sun dan jima rike da hannun junan suna ta zabga hira,
Sai daga baya Yusuf ya nuna inda su maryam suke ya na cewa,
Meet my wife and her sister
Su maryam din duk sun matse fuskan su don kada yaga daman su, a gurin ,

Da sauri Umar din ya waigo gurin Yusuf ya nuna shi da hannu ya ce,
Kana nufin kai musulmi ne yanzu ko? sai ya kuma kasa tambaya,
Yusuf ya gane may yake nufi, don haka yace mai insha Allah,
Da,sauri Umar din ya jawo Yusuf zuwa jikin shi yana mai ce mai, Alhamdullah congratulation, for be in islam,
Nan sukai exchange din noba yace zai ziyarci Yusuf din,,,,,,
A hanya maryam ke tambayan Yusuf ko waye umar sultan,?
Yusuf yace Umar dan sarautan sokoto ne yana da ilimi sosai na addini dana boko,
Suna shekaran karshe wata baturiya diyar wata mai kudi ta lake mai har sukai aure bada sanin iyayen shiba,
Hakan ne yasa shi tsaya can yafara aiki akasan amma kungan shi mutum ne mai son addini saidai zaman shi acan ya dan sauya shi kadan,
Allah ya kyauta sukace alokaci guda daga haka ba wace takaracewa komai,

Gidan bukin ya cika makil da yan suna daga cikki har da uwale da anty dije,
Suna can wani daki zaune suna hira da mutane,
Wata mace ke tambayar Anty ya labarin su maryam da maigidan ta,?
Lafiya suke inji dije nan matar ke bada labarin fadan da tayi da wasu akan auren maryam da Yusuf,
Sai wata ke cewa ina mamakin mutane da zasuce wai suna kyamar auren mutum musulmi dan uwan su,
Ai da ance yar uguwar yamma zai aura amma wai iyayyenta suka nuna cewa shi furen kan juji ne ba,za su bashi ba,
Bashine akace mahaifinku ya fashe mai wanan takaicin ba ya bashi kaunar ki,,
Kiran sallah da akayi yasa matan dan watsewa a dakin,
Daya daga cikin sune zaune tace idan sun dawo zata tafi,
Fitan sauran matan biyu yasa dayan matan da ta tsaya tace yar uwa ashe kece sister din wanan yarinyar da ake hira,
Zaki iya tunawa kwanaki ankira ana fada maku cewa an ma yarinyar asiri,
Uwale tace kwarai kuwa anyi hakana kuwa, ai matar tace wallahi nice,
Nima Sadiya suka shigo gidana suna hira da kauna ta shine naji,
A gurin kauna ta na samu nobar sister din naki wai zasu kirata su zage ku,
Matar tace hankali duk yatashi a lokacin ina gudun abinda zai samu diyan mutane,
Godiya su Anty su kai wa matar tare bata labarin yadda tai fama da ciwon kai,
Matar tace bagashi tayi auren cin amana ba wai yaron shi mutumin ta aura don tabashi takaici, shima da asiri ta nemo shi,
Gashi tun yanzu ance yasamu kariyan arziki saboda irin shagalin da sukayi da auren,
Nan dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login