Showing 3001 words to 6000 words out of 255288 words

Chapter 2 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1335

Jinkarar bude kofar da akayi a lokacin ya dan waiga don ganin wanda ya shigo cikin falon a lokacin,
Inok ne ya shigo wani abokin shi ne da suke yawan mu,amula indan yana Lagos da shi,
Inok yazo inda yake suka yar lalai hannu cikin nuna kulawa,
Inok yana kaiwa zaune yace wa Joseph kai aboki nai muna sabon kamu fa,
Duk da nasan cewa kaiba dan wanan harkan bane , nasan cewa wanan karon zaka kamu sosai indan har kaga cik din nan,,,
Kwantar da bayan shi yayi a saman kujera yadan waigo inda Inok ke zaune yana murmushi ya ce nagode da gudun mawarka amma kasani cewa ni wanan harkan bata a gabana yanzun haka,
Indadai wani business ne kasamo muna danafi kowa farin ciki da kai yau,
Baki bude Inok ke kallon Joseph yana mamakin irin halinshi na ko in kula ga mata,
Gashi dai yaro matashi mai jini ajika aman ba ruwan shi da harkan mata,,
Sai cewa yayi wai kai joe wani irin guy ne kodai matane baka so sai maza,
Cikin mamaki Joseph ya kalleshi alamar mamaki karara a fuskan shi yace
God forbid bad things,,,,,
Me, Joseph doing such bad habit in my life never,,,,
Daga haka yamike tsaye ya haye sama abinshi ya ma kulle kofar dakin shi yabar Inok zaune a falon
Ido kawai Inok ya bishi dashi har zuwa lokacin da Joseph yabugo kofar dakin da karfi
Inok ya mike tsaye yana mai watsar da hannuwar shi alamar haka take gare shi,
Sai da Joseph ya tabbatar da cewa Inok yabar gidan sannan ya fito ya dauki makullin motar shi yabar gidan cikin kunar rai,
Direct inda suke shan whisky ya nufa can ya zauna yadan sha kadan sanan yabar gurin zuwa gidan wani kawun shi da yake son ziyara da dadewa,
A can gidan yakai dare tare da uncle Sam, inda suka dan taba hira gamay da halin da family su ke ciki,
Kafin atafi saida yaiwa babban dan uncle sam , alkawrin samun aiki,
Sai bayan yadawo kamar da kwana uku ne yakira nobar wayan jibrin da yabashi ranan da suka hadu ,,,
Sun kai wani dan lokaci suna hira cikin mutunci inda suke ta hiran classmates din su,, da kuma irin gidajen da suke zuwa idan antashi makaranta,
Sunyi dariya sosai idan sun tuna da wani abu da sukayi ada suna yara,,,,,,,
A haka sukyi ban kwana da junar su har zuwa wani lokaci,,,,,,,,,
Kwance yake yana barci a saman tangamay may gadon shi,
Karar wayace ta katse mai barcin dayakeyi , a hankali ya diba kowaye yakirashi cikin dare haja,
Monday yagani rubuce, acikin muryan barci ya dauki wayan ya kara a nunen shi yace,
Hello, a bangaren Monday ya ansa da cewa hello sir,
Anan Monday ke sheda mai cewa wai motar man su guda da aki loading zuwa westnorth ta samu matsala a hanya har mai ya tsiyaye,
Awani dan kauye kuma sunyi iya kokarin su su tasarya abin ya gagara shiyasa ya bgo mai wayar,,
Mikewa yayi zaune daga kwanciyar da yayi batare da yaba monday ansa ba ya kashe, wayar,shi,
Wurin window dakin shi yanufa tsaye yake yana kallon hasken fitilun da yadan haska duhun dare, kamar yadda taurari suke haska sama,
A fill ya furta Monday, I will delling with u, soon, gurin fridge ya wuce yadauko ruban ruwan sanyi ya kwakwade shi dukka, lokaci guda ya cillar da robon kasa,,,,
A ranan barci rabi da rabi yayi don zuciyar shi na kuna ga irin rainin hankalin dasu Monday ke yi mashi,
Don kashi na uku kenan suna mai wanan hasarar da kuma wawaso,
Tunda safe ya shirya tafiya zuwa arewa batare da sanin kowa ba,
Sai da yai nisa yai wa KB waya, yana msi tambayar shi idan har bai komai yana son ya raka shi wani uguwa,
A suleja suka hadu, suka kama hanyar zuwa inda minday yace sun samu matsala,
Har zuwa adamawa babu tanker motar dasuka hadu da ita a saman hanya, da zasu dawo kuma suka kara bi ta wani sabon hanya da akai masu kwatance
Still a nan ma basuga komai ba, sai mota guda suka fani kuma ba ta company su bace ,
Kiran monday yayi yace ya fada mai daidai inda motar tasamu matsala gashi a cikin North,
Cikin rudani Monday yace what, You mean you are in North now yace mai of,course,
Jin yadda monday ke in,inniya yasa shi kashe wayar shi,,,,,,,,,


ZEEEEE MAKAWA,,,,,,,,,,,,,,,
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJ
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
3⃣
BY
ZAINAB IDRIS MAKAWA
🐎HUGUMA GROUP🐎

Assalamu Alaikum yan uwa dan Allah kuyi hakuri don ina sane da sunan da yakamata in sa wa , wanan novel din sai dai a gaskiya ina ganin kamar akwai wace ta riga tayi novel da wanan sunan, ( FUREN KAN JUJI)
Hakan yasa na can za wa nawa suna namaida shi FUREN JUJI dafatan zakuyi maneji dashi hakana,,, nagode,,,,,,,,

Sai musalin shadayan dare suka isa cikin garin kwantagora,
Gidan su KB ya wuce direct don ya sauke shi, tare da tsarabar da sukayo ma yan gidan su KB din,
Tsarabar doya ce da manja,don saida buth ya cika fam,
Acikin daren ya wuce zuwa gidan su dake can uguwar sabon gari,
Duk da dare yayi amma yasamu yan gidan su sun dawo daga church suna kokarin cin abinci,
Cikin murna da farin ciki suke tariyan shi, shiko ya na dan buga masu kafada ahankali,
Inda mahaifin shi yake zaune saman dogon kujerar dake falon gidan nasu da gashi sai yar singilati da gajeren wando,
Sai abin fitar da ke a hannunshi yanadan fifitawa a hankali,
Daidai satin kafan uban yadan duka inda uban yadan dafa mai kai ya na cewa you are welcome, ba,,,,
Joseph Why d, you like to travel in d night ?
Sai kuma yaci gaba da fadin cikin har shen IBO,
Dan Allah ka daina tafiyan dare saboda hanya da bai da kyau so sai,
Murmushi kawai Joseph yayi yana cewa ba abin da zai faru by god grace,,,
Kayan shi yasa aka shogo dasu inda uban ya kalli kayan yace
Dat means u are going to stay long, ba,,,
Yace cikin IBO yes dad akwai abinda zamuyi ni da abokaina a nan garin,
wani irin ihu yayi kamar yadda IBO kanyi idan sunji abinda ya taba masu zuciya, yace hyyy Cineke God Woooo,
Joseph Why ,u no dey, hear word,
Nafada ma karabu da yaran hausan nan but still kaki,
Kayi hankali kada su jefa ka a cikin wahala watara na,
Kokarin shiga ciki yakeyi alokacin yace, nothing will happen Dad,
Daga haka yai shigewar shi ciki ruwa ya watsawa jikin shi, sanan yafito ,
Saman kujerar dake falon ya, zauna gurin zaman mutum daya,
Duk da agajiye yake sai kuma yunwar da yake ji, tuwon teba da miyar egusi, aka aje mai a gaban shi,,,,,,,,,

Sai musalin shadayan rana yafito cikin shigar suit farare sol sai yar kwalar shirt din cikine kawai pink colour,
Yar jakar da yashigo da ita ya bude yadauko rapan yan dari bibiyu dana dubu guda guda yasa a cikin aljihun shi,
Wayan shi ya dauka yana latsa nobar KB yace
Hello KB kana gida ne yace mai eh ai na kira wayar ka yana akashe,
Yace ko zan samu kunu da kosai a gidan ku pls,
Saida KB yai yar dariya sannan yace mai baran diba ko akwai, shi, a ciki don na shanye nawako,
Daga haka suka kashe wayar su, inda KB yashiga ciki gurin mahaifiyar shi yana tambayar ta ko akwai kunu,
Cikin mamaki umma ke tambayar Kabiru may zaiyi da kuna bayan wanda akasa mai,
Yace mata Joseph ne ya bugo min waya yana son kunu da kosai,
Ikon Allah tace shi,wanan yaron har yanzu yana cin irin abincin mu,
Ba bata lokaci ummah ta hasa wutar dama kunu inda taba kabirun kudi yaje ko za,a samu kosai,
Saidai sunyi kicibis da Joseph din a kofar gida yana Parker motar shi,
Tare sukaje gurin sayen kosai ba,a samu ba don haka suka dawo gida,
Ummah tasan halin Joseph tun suna yara, kuli,kulin suga ta aje mai tare da sugari ,
Bakaramin murna yayi ba don yace rabon shi da kuli,kuli tun a wancan lokacin,
Abin yaba ummah mamaki gani andawo mata da jug bakomai dik an shaye, kunun,
Koda ta bude kwanon kulikuli sai kudi tagani aciki yan dubu dubu har guda goma,
Cikin sauri ta,ce amayar mai da kudin shi, badon yabata wani abu ba tai mai shi,
Koda yaron yaje saiga Joseph ya shigo rike da kudin a hannun shi,
Salama yayi kamar musulumi har ummah ta amsa mai sai da ta daga kai sai taga ashe Joseph, ne,
Tai saurin yin astangafullah a cikin zuciyar, ta, nan da na ta hada fuskan ta, ta tare shi da cewa haba Yusif don nadama ma kunu zaka bani kudi saboda may zakai mun haka,
Saida yadan sha fa kan shi tukun sannan yqi yar murmushi
Yace haba Ummah aiko baki bani kunu ba zan baki wanan kudin,
Nabakine don neman albarka a wurin ku ba wai don abinda kin min ba,,,,
Shiru Ummah tayi saboda maganar ta kashe ma ta jiki so sai,
Sai bude baki tayi tana mai cewa Allah yai ma albarka Yusuf Allah ya karkato ka kagane hanyar gaskiya,
Murmushi kawai yayi batare da yace mata komai ba,
Hannu yasa a aljihu ya ciro yan dari bibiyu ya ba sauran mutanen gidan,
Har zai fita saiga baban su kabiru ya shigo, gidan da alamar kasuwa yafito don kayan cefane ya sayo a cikin leda,,,
Shima sun gaisa yabashi nashi Alherin, daga nan suka fita,
A wanan ranan sun sha yawo da KB don duk gida jen da yake zuwa lokacin yana karami saida KB ya kai shi yai masu alheri,
A karshe suka je gidan wata kawar maman shi da ta mutu,
Matar a,na ce da ita salama, irin matan nan ne masu sana,ar Manja a cikin gida
Hakan yasa tasaba da maman su Joseph din, sosai har yakai zata ita daukan man ja ko da jarka nawa take so,
Sai sabo mai karfi ya shiga tsakanin su sosai,
Har zuwa lokacin da maman su Joseph tasamu accident a hanyar ta na dawo wa daga kasar su bukin chrismatic,
Har bayan rasuwan maman sukan je wurin Salama mai manja,
Saida yabar kasar ne wanan alakar ta mutu tsakanin Salme da su,
Yau kwatsam saiga shi yace KB ya raka shi gurinta,
A bayan Neper gidan Salame yake,
Gidan yana nan kusan yadda yasan shi bai wani can za ba,
Sunyi sallama akace masu wasuke nema sai KB yace ace gurin salama suka zo,
Mamaki salama tayi don jin ance wasu samari biyu ne da wata katuwar mota,
Don ita a iya saninta bata da wani mai irin wanan motar,
Balle yazo gurinta, tadauko tsohon hijab dinta ta saka akan ta cikin dan sarsarfa ta isa kofar gidan,
Salama nan kamar yadda yasan ta saidai tadan kara manyata sosai fiye da ,dai,
Yana mai, murmushi lokacin da ya hangota ita ko ,sai kallon mamaki take masu don har KB din bata gane ba,
Tana isowa inda suke duk suka dan duka suna mata ina wuni, cikin ladabi,
Ta, amsa masu tana cewa daga ina fa samari, kodai wani kuke bida, ne,
Dariya suka dan yi KB ne yace mama Salama baki gane mu bane har da ni,
Tadan kada kai tace gaskiya kan ban gane kuba,
Cikin hausar shi da ke nuna cewa ba pure bace sosai yace,
Mama kin manta da Dan ki yaron mama Ebele, Yusuf Joseph,,,
Cikin mamaki ta kama bakin ta tana cewa ,a,a,a dan gidan mama Ebele mai man ja kai ne,
Allah sarki ina ka shigr haka duk wanan dadewan haka,
Nazata ai munyi bye da kai kenan kabar wanan garin
Don nasha tambaya ana ce min kana kasar waje, kaje karo ilimi, can,,,
Tace barin samo maku abin zama ko, har suna hada baki gurin cewa a,a barshi kawai mama,
To barin kawo maku ruwan sha ko shimadai sukace tabar shi ,
Sunzo kawai ne su gaishe ta,
Sai takama sa masu albarka tana godiya ga karamcin da sukai mata na tunawa da ita bayan wani loakaci,
Kudi ya mikawa KB yace yabata, amma tayi hakkuri zai dawo badadewa ba ,,,
Saida kudin yabata tsoro don a gsskiya ta dade rabontq da kudi masu yawa hakan ga,
Taitayi mai addu,a tana sa mai albarka da fatan gamawa da duniya lafiya,
Nan yaga wasu yan tsofi maza guda biyu saman wani tabarma ya basu, dubu guda guda,
Har ya bace sunayi mai addu,a da fatan alheri suna kuma tambayar kowaye,
Salama ta fada madu cewa dan waje Ema mai manjane tsohuwar kasuwa,
Tsohon guda yace Allahu akabar ashe FUREN KAN JUJI ne shi, gashi yaron kirki amma ba jinsin kwarai,.
Dan gidan Ema kan ai babu batun musulunta gare shi sam,
Gudun tsohon mai dan magana da sauri sauri yace kasan abin Allah yawai gare, ai,
In har mutum bai mutuba ba,a gama halittasa ba ai,,,,,,
Su kace wanan gaskiyane,
Allah ya taro shi ya gane hanyar gaskiya,,,,,,,
Town holl akayi taron na matasa, tsofin daliban SANI BELLO,nursery _ primary & Secondary school,,,
Inda taron yabada ma,ana sosai ga cigaban da matasa keson kasar su ta samu nan gaba,,,
Bayan wanan taron ne akai ta hotuna tare da exchange din nobar waya a tsakani,
Koda suka bar gurin taron har duhu yafara don haka su KB da sauran friends suka nufi massallaci, daidai lokacin da suke alwala, ne shi kuma,
Motar shi ya shiga yatayar duk kusan wanda ke gurin sai da yatau saya mai azuciya ta kasan cewar Joseph Christian,
Gadai mutun har mutum amma babu alkibilar kwarai a rayuwa,
Shiko yana barin gurin Church ya nufa don ya samu evening preys,,
Mr Emanuel yayi farin cikin ganin motar Joseph a harabar Church din a wanan lokacin da bai tsamani ganin dan nashi ba,
Sunkai kusan goma nadare sanan suka dawo gida, inda nan suka zube a harabar gidan aka kama yan shaye shaye, su nan,,,
Har safe Joseph na abuge don ba karamin giya baban shi ya dirka mai ba daren jiya,
Don kawai jin dadin kasan cewar su tare cikin wanan lokacin,,,,,
Sanmako su KB sukayi zuwa gidan su Joseph saboda sunyi alkawarin yin sanmako zuwa wani kauye can guraren daki takwas,,,,
A irin yanayin da suka samay shi yasa jikin su yan sanyi
Don sam basu zaci cewa yana sha ba, don basu san shi da hakan ba,
Tafiyar tasu dole suka fasa suka barshi nan ya zuba shirmay shi suka tafi abinsu,,
Sai bayan karfe biyu ya farka a lokacin ya walwake sarai, wanka yashiga,
Yana fitowa ya zauna cin abinci , saida ya koshi saboda irin yanayin da yake jin cikin shi kamar duk an kwakware mai kayan ciki,,,,
Sai bayan ya koshi ne, ya tuna da zancen tafiyan su, cikin wani irin zabura yace, Jesus, Christ,,,
Saida kowa ya kallo shi don jin abin da ya ambata,,,
Wayan shi ya lalaba cikin sauri,ya diba yaga ko da , KB yakirashi zancen tafitan su,
Gañin babu called yasa shi saurin mikewa nan yabar abincin da yafara ci yanufi hanyar fita da sauri da dan makullin motar shi a hannu,
A,majalusar su ya samay su sun cika kamar kullun,
Can nesa kadan ya aje motar shi yafito ya kulle ko ina
Hannu ya mika masu don su gaisa da kowa , amma fafir Jibrin yaki mika mai,
Yunus wani bayerabe da ke cikin su yace wa jibrin ana baka hannu fa,,
Jibrin yace ai na gani bazan karba bane kawai, duk wurin saida kowa yai mamakin jin kalaman jibrin din,
Shi kanshi Joseph din abin yadamay shi amna sai kawai yabasar da zan cen yai yar murmushi kawai,
Azuciyar shi yace indan kasan mutum to kada katambayi halinshi koda bayan shekara nawa ne,halin na nan,
Don haka yasan akwai abinda yai wa jibrin ke nan, amma saidai shi a iya sanin sa bai mai komai ba,
Saida , karfe shidda yayi jibri yace kai joe muje ka kaini gida,
Babu musu joe din kamar yadda suke kiran shi idan sun so, shi ne guy name din shi,,,
Tare da KB suka fita su uku, sundan fara tafiya ke nan Jibrin yace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login