Showing 189001 words to 192000 words out of 255288 words
Chapter 64 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete
Tsab ta karanta halayan shi saboda shi mutum ne wanda keda wata irin baudadiyar ra,ayi,
Idan har ba sanin halinshi kayi ba da wuya ka iya fahintar shi,
Gashi miskili irin na karshe din nan gashi da saurin fushi,
Abu dan kan kani zai bata mai rai amma kuma sai dai yana da saurin saukowa daga fushin
Ga yin alheri a gurin shi tankar zuban habo daga hanci,
Alherin shi irin ta bajintace, sai gurin da mabukaci na gaskiya yake yake yin ta,
Abubuwa da dama maryam ta fahinta daga gare shi alokaci guda,
Ko dan da farko bata damu da yanayin shi bane saboda kyamar da ta dora mai na gaira ba dalili,
Tafiyan shi yazo kusa don haka ji yake yi tankar kada ya koma a wanan lokacin,
Amma kuma yazama mashi dole yakoma din saboda harkokin shi da ke cen,
Dama abinda ya kara tsayar da shi akan binciken da yakeyi a shagon mahaifin shi ne,
Badon rai yaso ba yai sallama da su ya koma Abuja cikin jin wani iri,
Sai bayan tafiyan shi ne Sadiya tasamu labarin cewa ai ya koma,
Duk tasan cewa wanan zuwan da yayi kawai dai hakkuri tai ta yi don ba wani kulawa da ta samu daga gurin Yusuf din sosai,
Jin shi shiru da tayine ya sa tabugowa wa Jibrin tana tambayar shi ko Yusuf din yana garin KG har yanzu,
Amma sai kawai taji cewa wai ai Yusuf din ya koma, ko
Sadiya wace wayar ya kusa sullubewa daga hannun ta saboda kaduwa,
Hankalinta yai mumunar tashi ta kasa zaune ta kasa tsaye,
Jibrin takara kira tana tambar shi ko may ya fahinta akan ta gurin Yusuf
Bai boye mata komai ba ya fayyace mata a kan zancen,
Wani irin mumunar faduwan gaba taji bayan taji cewa wai yasamu wata
Sai yanzu tagane takuma fahici ko may yasa Yusuf duk zancen shi akan anty je ne,
Idan ita kuma anty dijen ashe makircin da take kullawa ke nan,
Don su mallakeshi su hada,shi da maryam din yarinya karama da ita,
Gumi taji yana fito mata don jin wani irin zafin dake fitowa daga cikin ta,
Ji takwyi tankar an watsa mata ruwane a lokacin
Dije kinyi kuskure a rayuwar ki in har kina tunanen zaki iya rabani da Yusuf a lokaci guda,
Dije sai na raba ku da yusuf sai na dasa tsana da gaba a tsakanin ku,
Takai,wa hannunta guda naushi tana cewa daga yau zan fara yaki da duk wani wanda keda hannu acikin wanan maganar,
ZEEE. MAKAWA YELWA
[4/28, 5:36 PM] βͺ+234 902 951 1701β¬: πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
FUREN JUJI
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
7β£6β£
ZAINAB IDRIS MAKAWA,
YAURI
*_Masoyan Yusuf da Maryam ku kwantar da hankalinku kar hawan ruwanku yatashi, abunda nikeso ku gane shine sadiyafa real lover ce_*π
*_Koda yake naga ya'n yusmar team sun fi yawa amma kusani sadyus fa suma sun yunkuro sunce sune masoyan Yusuf na asali domin kuwa su ba hadin iyaye bane_*π
~*SADYUS team#*~
&
~*YUSMAR team#*~
π€
_Alherin Allah ya kasance atare da duk wani masoyin Annabin rahama_ πππ
πall
Sannu a hankali yake saukowa a matakalan jirgi, Saye yake cikin shiga irin ta,su ta mutanen kasar waje,
Sai yar far glass da ya zauna mai a ido dagwas, kamar an auna shi,
Daga inda ya ke ya hango shi yana saukowa a hankali,
Murmushi yayi don ganin abokin nashi wanda yai mai tafiyan bazatan ,
Duk da sun dade basu ga junan su ba kowan su yaga dan uwa ya canza a lokaci guda,
Hugging din juna su kayi,cikin farinciki da jin dadin ganin junan su,
Surprise Sonny ya cewa Yusuf bayan yadan bubuga ma Yusuf din baya,
Hannu rike da juna suka wuce gurin da ake ajiye motoci,
Direct gidan Yusuf suka wuce inda suka samu taro daga kakan Yusuf din wace ke ta farin ciki da gani Sonny din,
Sosai soni ya sake jiki ya kwashi girkin gargajiyan da aikai masu tsab ya zauna ya baje ya kwashi abin shi,
Shima Yusuf yaji dadin wanan irin sake jikin da Sonny din ya yi,
Wani tsadaden hotel aka kama ma Sonny din tare da yan rakiyan shi su uku,
Sai bayan ya hutane ne Yusuf ya samay shi cikin shirin shi,
Yana saye cikin jallabiya fara kal sai wata yar farar hulla da ya aa a kan shi ,
Hannu shi yana rike da wani dan farin tasbaha mai kyau yana ja a hankali,
Sonny wanda a lokacin yana zaune yana game tare da wata yar zukakkan budurwa wace da gani yar kabila ce,
Tun shigowar Yusuf din Sonny ya kalle shi saida yaji gaban shi ya fadi saboda irin yadda yaga Yusuf din ya mai wani irin kwarjini a ido,
Zaka ce wani babban malami ne idan ka gan shi,
Gurin zama Sonny din ya nuna ma Yusuf don ya zauna,
Batare da ya kara ko da second a gurin ba ya juya zuwa wani dan karamin korido dake ta wajen dakin ya tsaya,
Sonny wanda yagane komay Yusuf din ke nufi dole ya sallami yarinyar da suke zaune tare saboda yagane cewa saboda ita ne Yusuf bai karaso gurin ba,
Sun kai wani lokaci, tare suna tataunawa akan har kan business din su,
A nan Sonny yagane cewa Yusuf na, son karin taimako a harkokin shi don bunkasa har kokin shi,
Bai wani ce ma Yusuf din komai ba a lokacin saboda shi kadai ya san may ya nufa a zuciyar shi,
Washegari suka kama hanyan kauyen kakanin Sonny din, do halar ta bukin mutuwan kanin mahaifin Sonny din wanda yarage mai a matsayin dan uwa na kusa dashi,
A zaton Sonny Yusuf bazai harar ci bukin ba amma sai yaga cewa dashi akai komai na bukin bine gawan mutumin,
Bayan sun dawo Abuja da kwana biyu ne suka dan zagaya guraren masana,an tar Yusuf din tare da Sonny,
Daga karshe cikin office din Sonny suka ka baje inda aka kawo masu dan abin ta bawa,
Wayan Yusuf ce tai kara a lokacin, kamar kada ya daga amma sai kuma yakai hannun shi yasauki wayar,
Maryam black, yagani a screen din baro, baro abinda yasa shi dan murmusawa ke nan,
Yai mamaki matuka ganin Maryam ce takira shi, yau da kanta,
Da sallama ya,dauki wayan yana mai dan furzar da iska abakin shi,
Itace ta tare da fadin ina kwana bayan sallamar da Yusuf yai mata,
Ahankali ya ansa a nashi bangaren yana mi lumshe ido don jin dadin muryan ta da yaji,
A daidai lokacin Sonny yadago kai don ya tambaye shi a kan wani takarda dake rike a hannun shi,
Ganin yanayin da Yusuf yake ciki yasa Sonny mamaki saboda bai taba ganin aminin nashi a cikin yanayin shauki ba,
Don da gani ko ba,a fada ma ba kasan cewa ya fada tarkon soyayya ne,
Muryan maryam ce ke cewa uncle Assalam ne yace a kira mashi kai ku gaisa,
Murmushi yayi yadda har taji shi har cikin zuciyar ta,
Wani irin abu taji ya daki, zuciyar ta a lokaci guda kamar an dan tsikare ta,
Bata san lokacin da ta lumshe idon ta ba takai kwance daga inda take zaune bakin gado,
Shima Assalam dake kusa da ita yana jiran ta bashi waya yai magana da uncle din shi,
Binta yayi ya kwanta a gefen ta cikin kashe murya yaron ke fadin little mum bani wayan muyi magana pls,
Dan harara takaiwa yaron don ya barta ta karasa wayan ta, tukun,
Muryan Yusuf din ke ce mata, ke baki da magana dani ke nan ko sai Assalam ne zai ce ki kirani,?
Cak taji numfashin ta yana kokarin daukewa don jin muryan Yusuf din datayi yana mata wani sauti a cikin kunuwan ta,
Kara mirginawa tayi zuwa dayan bangaren gadon, gefe guda,
Hello maryam bakya jina ne hlo,
Shiru tayi tana yar dariya kasa,kasa tana wani dan lumshe idon ta,
Ok tunda baki magana sai ki bani Assalam din shi dake son mu gaisa dashi sai mu gaisa,
Ai bata san lokacin da ta mike daga zaune ba tana cewa
Ai ina sauraron ka uncle kawai dai ban san may zance ba ne,
Maganar ta yasa Yusuf dan juyawa da kujerar shi yana wani lumshe idon shi don jin dadi,
Muryan shi cikin wani yanayi da sai ka saurara da kyau zaka gane may yake cewa,
Da may kike cewa idan A,A ya bugo maki waya a lokacin,
Wani irin juyi maryam tayi ta maida idon ta ta rutse su gam tana jin wani irin tukuki a zuciyar ta, a lokaci guda,
Da uncle ya sani da bai kira mata sunan wanan mayaudarin ba a cikin wanan yanayi da take na shauki,
Mikawa Assalam wayan tayi ta juya ta ba da baya tana mai fuskantar bangon dakin,
Hira sukayi sosai da shi da Assalam din har yana kyalkyalawa dariya,
Jin dariyan su da Assalam yasa har ta dan rage jin zafin da take ji da farko,
Bayan Assalam sunyi sallama da Yusuf ne ya ce yabawa little mum waya din,
A hankali yakira sunan ta bayan ta karbi wayan hannun Assalam din
Jin Yusuf din ya kira, sunan ta cikin jan murya da kara harshe,
Murya kasa, kasa yace i miss you maryam wani yarrr maryam ta kara cewa ta lumshe idon ta a hankali,
Fuskan ta kumshe da murmushin jin dadi abin da ya ce mata,
A zuciyar ta ko mamakin jin kalma da wai Yusuf ne ke fada wa ita maryam hakan,
Anya kuwa ba wai kunnuwan tane ke mata karya ba,
A hankali ta bude daradaran idon ta a hankali takai kallon ta ga kofan shigowa dakin su kamar mai kallo idan babu mai ganin ta ko jin may zata ce,
Amma sai kuma taji bakin ta yai nauyi fada mai kwatankwacin kalman da ya fada mata,
Jin da yayi cewa bazata ansa mai ba yashi cewa ok well ina aiki but anjima zan kira inji ansata,
Da haka sukayi sallama da junan su yana mai mata bye,
Yadago kai a hankali bayan yadan kawa wayan kallo kamar mai son ganin wani abu a cikin wayar, gami da sake wani irin lalausar murmushi,
Caraf sukai ido biyu da Aminin nashi da ke zaune gefe yana mai wani, irin kallo cikin kurawa Yusuf din ido,,
Duk da Yusuf din ya dan ji nauyi yadda abokin nashi ya ke kallon shi cikin mamaki,
What's up ya cewa Sonny din cikin daga hannayen shi biyu da kafadan shi,
Nothing's inji shi Sonny din ya mayar mai da martanin ansar shi kai tsaye,
Duk kan su hankalin su ya koma gurin aiyukan da sukeyi ne,
Kafin wani dan lokaci Yusuf din ya furza iska daga bakin shi alokaci guda kuma yai wata yar mika ,
Gabadaya Sonny ya dangware takardan dake a hannun shi ya dago kai cikin mamaki yana cewa,
Whose is the lucky girl ?
Yusuf batare da ya kalle shi ba ya cigaba da aikin dake a gaban shi, kawai,
Har zuwa lokacin da Sonny din ya karaso gurin da yake zaune,
A saman tebur ya zauna gaban Yusuf din, Ahankali ya sa hannun shi ya karbe takardan dake a hannun Yusuf din,
Cikin zolaya yace ma Yusuf wanda yadago kai yana kallon Sonny din ,
Tell me how she look like,?
Yusuf wanda yaso ya daure fuskan shi amma sai ya kasa saboda yadda Sonny ya tsure shi da ido,
Dariya suka kyalkyala a lokaci guda gami da tafa hannayen su cikin na juna,
Sonny yace ma Yusuf din,
You are now in the team,
Nan dai yadinga yiwa Yusuf din yan tambayoyi akan ko wacece wanan yariyar mai sa,a da har ta samu sace zuciyar wanan miskilin matashin maiji da kan shi a kan yan mata shekaru da dama,
Sonny yace yana son yaga how beautiful she is,
Yusuf yai murmushi yadan juya saman kujerar shi sanan ya tsaida idon shi ga Sonny din ya ce,
She is not beautiful as you think,
But she is very religious,
Sonny ya ce cikin zolaya really,
Kai kawai Yusuf ya daga mai alamar eh hakane,
Dariya su kayi wa junan su suka tafa hannayen su a cikin jin dadin kasancewa tare da junan su,
Wata guda,Sonny zai yi a cikin kasar shi kafin ya koma inda yafito yaje kuma zama,
Sallahn Shafa,i da wutir ta gabatar daga inda ta idar da sallah ta ke zaune tana gyara jikin ta a hankali, tai shirin kwanciya barci,
Ta mike a hankali zuwa gurin shimfidar yaran yayan nata ta gyara masu,kwanciyar su inda tabisu daya bayan daya kamar kullun ta tofa masu addu,oin shiga barci,
AC dakin nasu tadan kunna masu don dakin yadan dauki sanyi kafin barci ya kwashe ta,
Da Bissimillah ta hau gadon ta kwanta a hankali,
Wani irin ajiyan zuciya tasaukar saboda sanyin da taji yana,shiga jikin ta, ga kuma wankan da tayi ta dinga jin tankar ancire mata wani nauyi ne ajikin ta,
Idanun ta ta lumshe gami da jawo bargon ta har zuwa wuyan ta,
Ga mamakin ta karar wayan ta ya shiga yi a cikin wanan daren,
Da sauri ta mika hannun ta tadauko wayan da ke aje a side drower din gadon ta,
Yusuf ne don haka tai mamaki jin kiranshi a cikin wanan dare don bai faye kiranta ba bayan goma na dare,
Da wata karamar murya yakira sunan ta, amma sai tai shiru tankar bata a online din,
Yasan cewa tana jin shi ansawa ne kawai aiki a gare ta,
Wanda hakan na daya daga cikin abin dake kara burge Yusuf din akan maryam watau jan aji,
Din haka yaci gaba da tambayar ta cikin muryan shi maikama da an tilasta mai yin magana,
Kusan hiran hakkuri ya bata najin shi datayi shiru kwana biyu,
Wanda aiki sukeyi sosai shi da Sonny dake kara mai fasaha akan harkokin business din shi,
Cike da farin ciki maryam ke sauraren shi a lokacin amma bazata iya baiyana mai hakan ba a fili,
A karshe yake sheda mata cewa Sonny zai shigo kwantagora saboda ya gan ta,
Sai a lokacin Maryam tai magana cikin yar siririyar muryan ta tace ni ?
Ni ?
Da murya kamar wace zatai kuka a lokacin,, dama yasan haka zai faru don sanin halin ta da yayi,
Jin shirun da yai yawa yasa shi cewa Maryam din dare yayi ta kwanta ta huta dama don yaji muryan ta da lafiyan ta yasa yakira ta
Maryam wace taji dafin abin da yace tadan ji kunya ya dan lulubeta tankar ya gurin haka yasa ta kashe wayan cikin sauri ta koma saman filo ta kwanta rigingine tana tunane,,
Shiko Yusuf din yamai da kanshi saman kujera yana mai lunshe idon shi cikin jin wani irin farin ciki, a rayuwan,
A duk lokacin da yake waya da Maryam shikadai yasan irin yanauin da yakan shiga,
Ya kasa fahintar ko may ye dalilin hakan kasancewa ai ba ita kadai bace mace ta farko da yake waya da ita,
Amma sam bai jin wanan yanayi gurin sauran matan da yake waya da su,
Maryam wace tun suna waya da Yusuf take jin alamar call na shigowa wayan ta,
Amma ba dama ta diba don suna saman network ita da Yusuf, a lokacin badu jin ashhh,,
Jin sako ya shigo yasa ta saurin daukar wayan da ta aje abayan filon ta,
Azaton ta mutumin natane ya yo mata text din Nice, dream,
Ga abinda tagani a rubuce kamar haka,
Maryam kin bani mamaki sosai kuma na yardda cewa kudi suna iya canza mutum ko shi waye,
Amma ki sani kinyi babban kuskure a rayuwan ki na zaban da IBO a matsayin gwanin ki,
Duk da nasan badon Allah kike son shi ba saboda dukiyan shi kawai yarki makwadaciya ta saki son shi,
Idon ta rintse don jin irin yadda ya aibanta mata yar uwa,
Zaman ki ustaziya kamila ashe duk na iya baki ne baikai ciki ba,
Idan har da gaske ke ustaziya ce ai abinda ki ka tsayar hujja akaina ba zai zama hujja ba,
Sai dai ki min uzuri da nasiha akai har in daina dama ba sona kikeyi ba kindai yi amfani dani kin cin ma manufar ki kawai na haskaki gari an sanki,
Idon ta takara rintsewa saboda jin wani irin abuda ya tokare mata zuciya,
Bari kiji maryam da ace wanine zaki aura ba furen kan juji ba,
Wanda daga karshe zaki fada cikin dangin arna ki haifa ma arna jikoki,
Innallillahi wa,in na alaihim