Showing 30001 words to 33000 words out of 255288 words

Chapter 11 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1343

kasha,,
Bayan fitar su waje ne Joseph din ke cewa jibrin yanzu may ake ciki akan zancen,
Nan dai Jibrin ya sheda mai cewa kotu tace mutumin yabiya shi nan zuwa karshen shekara,
Joseph yace har lokacin ba,atafi aikin ba ke nan,
Jibrin yace kai haba har wasu na shirin zuwa ma alokacin ,,
Kai haba impossible inji Joseph gaskiya asan yadda za,ayi musamu baba su tagi wanan shekaran,
Jibrin yace yaya zamu man tunda duk dan abi da ke ga baba shine ya hada yabiya masu
Joseph dake kokarin bude mota yace ma jibrin a ina zamu samu kujerar, ne,
Mamaki karara a fuskan jibrin yace kai bafa maganar wasa bane man kudin mutum uku baba ya bita fa,
Joseph yace and so what,
Indai har zamu samu ai sai su tafi,
Murna jibrin zaiyi ko kuma may
Saidai kuma a zuciyar shi ya na tunanen in har mahaifin su zai yarda da zuwa makka da kudin Joseph,
Don haka ba bata lokaci suka shiga cigiyar kujerar makka
Saida kyat suka samu a wani local government kusa da kwantagora magama local government,
Saidai an masu karin kudi sosai akai amma haka ya juye madu yabiya, don dai kwai yadda yake jin kada a wuce baban jibrin bai samu zuwa aiki hajji ba kamar yadda ysi niyya,,,
Maganar nazuwa gurin baba aikuwa baba yace sam badashi za,ayi awanan aikin ba,
Ina zai tafi aikin hajji da kudin kafiri,
Da tambaya dakomai malamai sukace ya halatta su tafi tunda shi yaga dama yabasu kudin shi kyauta,,
,,,

ZEEEE MAKAWA
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
1⃣4⃣

ZAINAB IDRIS MA KAWA


Wanan tafiyan na mahaifan Jibrin da Joseph ya ba kudin zuwa Saudiya ya jawo muhawa sosai a cikin gari,
Har takai wa yanda basu san shi ba yanzu sun fara samun labarin shi,,,
Dashi akai komai har zuwa rakiyan su airport a Minna inda zasu tashi, zuwa kasa mai tsarki ,,
Wanan abin yabawa Joseph mamaki sosai don tun a nan sun fara ibada
Daga can ya wuce zuwa Abuja gurin zancen business din da suke so sufara jonawa,
Wanan tafiyar tankar tafiyar don jibrin a kayin don itace samuwar aikin jibrin din,,,
Anbashi In charge na supplying din duk wani shinkafa da mangyada da za,a shigo dashi daga wata kasa,
Zuwa kasar arewa da kewayen ta, kamar su Cameron da Chadi, Niger
Bakaramin sa,an samun wanan nasar yayi ba don mutane da dama sunyi ta korafi akai,
Wanan abin yaiwa mutane da yawa dadi saboda jibrin mutum ne mai tsimakon nakasa da,shi sosai,
Lokacin tafiyan su Joseph da kakar shi yayi kawai sai ji Mr Ema yayi cewa Joseph yafita tare da ita, zuwa Jerusalem,,,
Wanan fitar mutane kauyen suka,dinga mamakin cewa tunda ita witch ce yaya zata iya zuwa can wurin bauta,
Wanan tafiyar ta daure wa Joseph kai sosai saboda abinda yagani a can ya banbamta da yadda suke gudanar da tasu,addinin a nan,,,,,
Saboda sai yaga cewa ai duk kusan al,adun da akeyi acan kamar al,adan musuluman Nigeria ce da sauran duniya,
Hatta da alwala indan bakayi ba ba,za,a bari kashiga cikin massallacin ba,
Abubuwa da dama yagani a can sai kuma yaga cewa ai har da musulumai daga wasu kasashe suna zuwa yin bauta a cikin wanan masallacin mai tsohon tarihi watau masallacin, BAITI,MUKADIS,,,,
Ya dawo gida zuciyar sa fam da tunane kalala, acikin sa,
Kakan shi mai suna Ciyoma, tun acan tadinga wani irin kuka na farin ciki tana mai samai albarka,
Addu,an gamawa da lafiya da duniya yadinga mai aciki tasako zancen da ake mata zargi dashi tana mai cewa,
Tagode Allah da jikanta ya zama abin kwatance a cikin jamar su, har yafidda ita daga zargin mutane, cikin wani irin magana kamar waka,
Joseph dake zaune yana kallon ta a cikin dan gurin shan iska da suka tsaya a wani airport,
Yana saye da wani katuwar rigar sanyi,a jikin shi yataso daga inda yake zaune tun fara maganar ta,
Ya rugumay ta ajikin shi don maganganu da take fadi sun ratsa mai zuciya sosai a lokacin
Tunanen mahaifiyar shi wace a yanzu bata da rai ya fara ji dama ace tana da rayuwa ne da yanzu suna tare da ita a wanan gurin,
Saboda yasha tayawa mahaifinshi cewa suzo wanan gurin ziyara amma sai Mr Ema din yace bai son abin wahala shi,
Wasu hawaye masu dumu suka silalo mai daga ido zuwa kasar fuskan shi,
Yanajin mutuwar uwar su kamar yanzu ne abin yafaru mata mai hakkuri da sanin ya kamata
Don yana da wayon shi irin yadda mahaifin shi yadinga wahal da ita a lokacin zaman su,
Jin hawayen Joseph na diga mata a wuyar ta ya sa yar tsohuwar dagawa daga cikin jikin shi ta dubi fuskan shi,
Ta ce Joseph my child don cry pls,
Kara rike kakan tashi yayi saboda yadda yake ji a zuciyar shi ba dadi
Sun kai wani lokaci a haka sanan nan ya ja ta da kyar zuwa wurin da kayan su yake gefen wasu kujeru da aka tanadar wa matafiya,,
Sun iso gida Nigeria cikin farin ciki da walwala a zukatan su saboda, sun tafi inda kowani dan addin Christian ke burin zuwa,,,
Ta Abuja suka,sauka don haka yasa wani abokin shi ya kwaso su, daga airport,
Zuwa gidan shi da yake sauka a Abuja,indan yazo,
Sai da ya huta san nan ya kira KB yana sheda mai cewa sun dawo shi da kakar shi,
Kwanan su biyu abokanan shi suna ta zuwa yi mai barka da dawo wa,
Tun wanan tafiyar tasu josepy yasa wa ranshi cewa ba,zai kara barin wanan yar tsohuwar kakanshi cikin wahala ba saboda tana bukatar hutu a rayuwar ta yanzu,,
Kwantagora suka nufa daga Abuja inda tsohuwa ciyoma bata so hakan ba don dai ita taso ne takoma gida,
Don yanzu bata son wani alaka ya hada ta da mahaifin su Joseph tunda ya iya rabata da 'ya'yan diyar ta,
Inbadon Allah ya bata jika mai albarka ba wanda yasan darajan ta,

Sai bayan tafiyar Joseph Jerusalem ne labari ya iso ga mahaifin shi irin tai makon da yai wa jibrin again,
Abinda takai shi har da hawan jinin shi ya tashi mai dama ko yan uwan Ema IBO sun san shi mutum ne wanda baya son taimakawa na kasa dashi,
Cikin dare suka isa don tun a hanya sukai waya da Samuel nan Samuel yake sheda mai abinda yafaru
A cike da rashin son taimakon da mahaifin shi baison yana yi ya iso fam a zuciyar shi,,,
Murna sosai yan uwan shi sukayi daganin kakar su wace tun suna kanana so sai rabon da su ganta
Mr Ema yana dawo Church gurin service din dare yai arraba wanan tsohuwar duk shi ba wai wani girmuwar shi tayi ba sosai
Nan da nan anurin fuskan shi ta gushe mai sai da kyat ya iya controlling din zuciyar shi,,
A nuse Joseph yafito daga dakin shi don zuwa tariyan baban shi,
A fusace ya ke karba mai inda yafara mai sababi na rashin bin umurnin shi da Joseph din baiyi,
Yace saboda kaga yanzu kana cin gashin kan ka shiyasa ban isa in sa ma doka kabi ba,
Kafada min may hujjan ka na taimakawa yaran hausawa kuma musullumai,
Joseph har in bazaka daina hurda da wa yan, nan mutanen ba ina warning dinka kadaina shigowa kwantagora pls,,,
Joseph wanda kan shi ke duke tunda mahaifin nashi ya fara fada yadago a hankali ya fara magana acikin natsuwar nan tashi yace
Dole in taimaka masu baba saboda sun min abinda yafi haka alokacin da nake bukatar hakan,
Rai bace Mr Ema yadaga kai cikin mamakin kalamin dan nashi yace,
Kana nufin cewa ba,zaka iya rabuwa dasu ba ke nan,
Shiru yayi mai wanan karon yana dai sararon shi kawai,
Barin falon yayi saboda yasan cewa yanzu wani ,zafi ba ,zai lankwasa Joseph din ba,

Aisha tayi farin ciki sosai da jin cewa Joseph yana gari don tun cikin dare ya kirata yake sheda mata cewa ya shigo,
Tasan cewa ita kan kakanta ta yanke saka kenan don ba karamin abu take samu gurin shi ba,
Duk dai iyakar ta dashi kawai yan wasan ni kuma ba wani mai yawa ba,
Sosai ta shirya ma wanan zuwan nashi saboxa gana da yan bukatoci akan shi da yawa,
Shiko tunda safe ya fita zuwa wani kauye shida KB don yana gari,
Basu dawo ba sai zuwa dare marance,su ka , iso, garin ,
Bayan yai wanka ya shirya zuwa ganin little friend din shi,
Wanda kusan ko yaushe yana tuna yaron haka kawai son Assalam ya shiga zuciyar shi,,
Tsaraba sosai yakawo ma Anty Dije da yaranta don gaskya saida Anty ta kasa yin godiya,
Ita kanta Anty wasu materials madu kyau da tsada yasako mata ciki tare da dogayen riguna,
Issalam tana gama ganin kayan tace ina na little mummy din mu,
Da sauri Anty Dije tace mata ai nawa tare da natane zamu raba,
Wani inji Maryam dake kokarin bude fridge a lokacin don ta debo kayan miya,
Kai ta girgi,za wa Anty tace a nutse na yafe nikan gaskiya ban so,,
Issalam tazo har inda take gaban fridge tace kina so mana little mummy bake ki,kace mama tasaya maki anko ba,
Hannun yariyar maryam ta hado guri guda tace Issalam nagode ban so nace maki
Anty ce tace ke kyale zata karba ai wasa take yi,
Cikin mamakin maganar anty dije ta dago kai kalle ta, da niyar magana,sai kuma ta shiru kawai don irin kallon ki shiga taitayin ki da anty tai mata,a lokacin,
Assalam ne yace mama don ba,a sayo mata nata bane wai bata so ko,???
Nace maku bana so kawai simply ta fadi a nutse daidai lokacin da take kojarin barin gurin,
A hankali yabita da kallon mamaki saboda sai yanzu yafara fanin tsana karara a cikin idon wanan yarinyar,
Ya rasa dalilin wanan tsanar da yar karamar yarinyar ke mashi haka,?
Bayan tafiyan shi Anty taima Maryam fada sosai har takai maryam din yin kuka don dai ita gaskiya bata ra,ayin wanan mu,amular da su anty keyi da wanan Arnen sam,
Washe gari maryam na tsakar gida zaune da farantin shinkafa akan cinyar ta, tana gyaranwa tana raira kira,ar ta, ahankali,
Joseph yai sallama suka shigo tare da Aisha
Wacce tai kwalliya cikin wasu irin haddadun buje da riga masu kyau,
Kallo guda tai masu ta kau da kai gefe guda don bata son kara daga kai,
A hankali tace masu bata nan amma tace indan kazo ga abinci a falo,
Daga haka bata kara wani zance ba sai kokarin ci gaba da aikin gabanta tayi kawai,
Aisha ce cikin magana kamar rada tace wanan yarinyar na lura bata da kirki wallahi,
Ji yadda takewa mutane magana wani iri kamar tana jin warin su,
Baice mata komai ba asali ma kamar bai jita ba,
KB ne yai sallama sosai irin ta musulunci duk da bawai ta sake mai fuska bane amma dai ta karba mai cikin girmamawa da nuna kula,
Daga inda take tanajin suna hira akan wani guy wanda cikin su yake saidai yanzu mahaifin shi bai bari yana binsu sosai,
Wai yana zuwa aikin a gonar mahaifin shi ko yaushe ,
Joseph ne ke cewa gaskiya Umar na ban tausayi don ranan da na ganshi bazaka ce yataba rike biro ba arayuwan shi,,
KB yace Umar din ai yace zai zo zuwa anjima don yana son ku hadu dashi,

Cikin dan lokaci jibrin yai suna a cikin gari wurin yan kasuwa da sauran manyan mutane,
Don jibrin mutum ne wanda ya iya business so sai da jama,a,
Ga kuma tausayi da sanin ya kamata, akan harkokin shi,
Musan man dayake yana kara samun taimako daga gurin ubangidan nashi a asarice,
Ta yadda mutane bazasu iyagane cewa business din shi bane,
Saidai su dauka na company ne kawai,
Joseph ya koma gurin wanan matar abokiyar mahaifiyar shi mai manja,
Inda yake sa ana kawo mata kayan masarufi tana sayar wa talkawa cikin sauki,da rahusa,
Ta yadda tallaka ba zai yi mugun wahala ba, sosai wurin samun abinci,
Tuni sunan su ya fara fice ga al,umma tun mutane suna zargin su har aka gane cewa business ne sukeyi tsantsar ta don ci gaban mutane,
Matasa da dama sun samu abin yi yanzu wanda hakan yasa emirate taji dadin zaman Joseph a tare da al,uman su,
Wani abin sha,awa kuma shine idan ya samu labarin cewa a unguwa suna samun matsalar ruwa ko wuta sai yasa sai yasa a tona masu famfon burtsatse ko kuma ya sauke masu transformer,
Ya sayo motoncin noma birjit ya tura kauyo ka mafi kusa don tallafawa,
Dalilin da mutane suka sa mai furen juji ke nan,don dai yanzu yan kwamintin su na chu sunkirashi mitin yafi a kirga amma yaki halarta,,


ZEEEE MAKAWA,,,,
[2/20, 9:21 PM] ‪+234 806 595 8685‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
1⃣5⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

Alhamdullah Allah yakawo yau, maryam sun zana jerabar su ta karshe a girls day secondary school, kwantagora,
Fitowar war,ta kofar class din tai wata ajiyar zuciya gami da fesar da watar iska irin na relief din nan,
A hankali take tafiya zuwa bagin get don tafiya zuwa gida jitayi an jawo ta, Assamau musa ce classmate din ta mai photo ta nuna mata tana da bukar suyi photo,
Fara photon nasu ne wasu yan gidan jodda suka shigo akayi da su
Maryam wace kawo yanzu duk ta kagara ta wuce, gida
Don ta huta saboda duk kwanakin nan bata samun barci don mathematics ce zasu zana karshe,
Gani zasu bata mata lokaci da yawan daukar photona ya sai ta, sa kai kawai zuwa fita daga school compound din,
Wata mota tagani tana jiran wata yariyan batai mamakin haka saboda ga abin hawa na birjit a waje suna jiran yan uwansu wasu kuma samarin su,
Tabbas in ba karya idon ta ke mata ba wanda tagani bakin motar KB ne, don ko ina zata gane shi yanzu don yawan zuwa gidan su da sukeyi ko yau she muddin suna gari,
Kai takar kamar bata gan shi ba sai tafiya takeyi cikin sauri don ta isa gida,
Horn takeji a bayanta kamar kada ta waiga fon tasan cewa ba asaman titi take ba ita,
Sai ganin motar KB tayi gaban ta ya Parker dan zuge glass din motar yayi yana mai dan lekowa ta window motar,
Sai a lokacin tawaiga batare da ta daina tafiya ba,
Ta furta a hankali ina wuni,, dan murmushi ya sakar mata ce little mum babu gaisuwa ,
Dan murmushi tayi wanda ya baiyanar mata da fararen hakora ta da suke a jere ras a cikin dan karamin bakinta,
Tace ai na gashe ka ko, ?
Yace zo muje mana mu saukeki a hanya , gani wata classmate din ta zaune a bayan motar yasata dan kara yin murmushi tace ku tafi kawai ai zan hau achaba yanzu,
Ganin zai kara mata magana yasa ta tsaya badon taso ba don dai kada mutane su samasu ido
Don yanzu ba,a raina sa,ido ga dan karamin abu,
Tana kutsa kanta a cikin motar wani irin sanyi da kamshin wanda bata iya tantance ko motar ce ko kuma masu motar ke wanan uban kamshin haka,
Ga sanyin AC ya hade da kamshi wanda zai iya sa mutum acikin wani yanayi, (A,uzu,bikalamatilllah ,tamattah), tace yayin da take kokarin zama a motar,
KB ne ya juyo a hankali yana mai cewa taufa malama ce injin muka dauko,
Maryam da sai yanzu bayan ta samu natsuwa, ta sheda ko wace su KB suka fara dauka a motar
Wata, fatima Indagi ce yar gidan nufawa asalinsu mutanen garin Bidda ne zama yakawo su kwantagora,
Har suka zama yan gari yanzu don sun san kowa kowa yasan yan gidan su,
Bawai wani shiri sukeyi ko a school da ita ba don haka ko kallon inda take,Maryam batayi ba,
Baka jin komai daga cikin motar sai kida ke tashi ta yadda ko na wajen motar zai iya jin kidar daga waje,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login