Showing 249001 words to 252000 words out of 255288 words

Chapter 84 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1405

gobe zan dan je wani kauye zan diba shanaye na acan,
Yusuf yadawo gida bayan yai sallah magrib da isha,i,
Yanzu dai yai aure kuma abikan shi na kwantagora sun da samu matsala dasu,
Gida ya koma gurin matar shi da kakan shi da yaron shi Pipkin,
Shima zama yayi yaci abinci kadan sannan yai shirin kwanciya barci,

Washegari tunda safe safiya tana gidan a tare ya kwashesu zuwa gidan anty sun yi addon cikin shiga ta alfarma,
Idan mutum ba ance mai maryam bace ba zai taba gane ta ba,
Irin yadda maryam din ta koma kamar wata baindiya,
Komai nata sai mutum ya kalla daga jikin ta har suturan jikin ta zuwa kafanta,
Sai,dai sun samu anyi wa su anty dije rasuwa a family house din mijin ta,
Gaisawa sukayi sai dai anty taji kunyan ganin safiya, tare da maryam din,
Batai kasa a kafa ta ba safiya hakkuri batare da ta baiyana komaye ba agaban maryam,
Hakkuri kawai taba ta sai safiyan tace ai ya wuce babu komai ko,
Gaba,dayan, su ,su ka shiga family house din don yiwa sarakkan Anty dije gaisuwa,
Waje suke zaune saboda wani irin zafi a cikin dakin,
Mutane ana zaman makoki na gaisuwa ana gulman maryam
Kowa sai mamakin yadda tazama classic a lokaci guda,
Ita ko maryam zafine ya ishe ta alokacin ga Pipkin wanda bai saba ba ya ishe su da cewa su wuce,
Gungun matan da suka shigone ya ja hankalin mutane don hakane al,adan gidan makoki yake yanzu,,
Don yanzu, da anzauna hirane kowani gungu zakaji da irin tasu hiran,
Wa yan nan matan bakowa bane sai iyalin gidan mahaifin Jibrin gaba dayan su,
Daga cikin su har da Sadiya matar Jibrin a cikin su,
Kallo guda Sadiyan taiwa maryam da Safiya saida ta tsorata,
Yadda maryam ta koma alokaci guda ga kyau ga iya dressing gata acikin shiga ta alfarma irin ta matan manya,
Kallon guda da tai mazu tasan sun wuce ajin ta nisa ba kusa ba,
Bayan sun yi gaisuwa gungunmutane suma suka samu guri gefe guda suka sa nasu tabarma,
Kallon kallon aka koma yi da su Sadiya da,su maryam din,
Sadiya wani irin mugun kishine ya rufe mata ido a lokaci guda ,
Daga inda take zaune takarewa maryam wace ta mike don kiran ta da wata mata tayi kakan su illiya don tagan ta,
Sai yau tasan cewa kallon tsoro takewa maryam din ada,
Shiyasa da antashi magana sai tace yar kauye ce ya aura ai,
Yau sai ga bakauya ta girgiza mata imani sai hade miyau Sadiya munafuka take yi,
Maryam din wace cikin ta ya zauna mata dan dagwas tana saye da wani alkyabba saman kayan da tasa wanda ganin shi kawai ya isar ma da sakon shi ga kamshi na tashi,
Jakarta ta balle tabawa tsohuwan nan kyautan kudi, saboda ta dade da sanin tsohuwan,
Dibi duk kayan jikin maryam mafi qualities ne wani irin kishine ya lulube sadiyan da ta tuna cewa da yanzu itace a cikin wanan uban daula,
Gashi su Anty dije da yar uwanta suna ci a garasaba sa,.
Sam ta manta cewa suma halarcin su Allah yai masu sakaiyya da shi haka,
Don kwai a iwa maryam da yar uwar ta cinfuska wasu daga cikin yan gidan su Jibrin din sukace,
Ashe matan dan IBO anzo ne ga kuma karuwa har an samu,
Masha Allah sai dai kan yaran ai dole ace masu jikokin Emanuel ko,?
Sai daga can uwale ta jefo masu ansa da cewa kodai jikokin Hamana za ace masu uban su dai musulmi ne, ko?
Ke yar abi yarima asha kida,
Inji wata tacewa uwale da tabasu ansa,alokacin,
Ganin uwale , zata ita daidai dasu a birkice a gurin yasa Anty dije fadawa wata gwagonsu,
Aiko tsohuwan tafito tadinga masu masifa da cin mutunci,
Tace a she hurda dashi baida kyau, ?
Gashi ko duk kwantagora babu wanda yakai uban ku cin dukiyan dan gida n Ema mai manja,
Don dai da kudin kafiri yatafi makka ko kun manta ne in tuna maku,?
Haba dai gwago Kande daga magana zaki fara irin wanan zancen haka,,
Kada kikawo min diban albarka may yasa yaron ga dan gidan ku baice bai son aikin da yasamo mashi ba,
Bagashi har yanzu ya na cin moriyar shi ba ku ba ai maku gori ba sai ku zakuyiwa mutane
Ai gara da ita auren shi takeyi akanta farkin addinin musulunci ko,
Sai da akazo a,kaja gwago kanden tana ta faman masifa dasu,
Sim sim sukabar gidan cikin jin kunyan irin ta,arnatin da gwago kande tai masu a bainin jama,a,,,,,,,


ZEEE MAKAWA YELWA,,,,

[5/11, 3:29 PM] β€ͺ+234 706 582 0685‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
9⃣9⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI

ALLAH ABIN GODIYA
RAMADAN MUBARAKπŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘
FUREN JUJI ,FUREN JUJI ,FUREN JUJI
NASADAUKAR DA SHI GABADAYA GA WAKALE FAMILY, KWANTAGORA ALLAH UBANGIJI YAGAFARTAWA MAGABATAN WANAN GIDAN BAKI DAYAN SU WA YAN DA SUKA RAGE A GIDAN UBANGIJI YASA MASU ALBARKA YA DAUKAKA MASU YASA DUK YAN WANAN FAMILY SU GAMA DA DUNIYA LAFIYA ALLAHUMA AMEENπŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘


Yau, Jumma,a ranan da kowani muslmi mata da maza yara da manya har tsofafi zakaga suna murna,
A ranan zakaga kowa ya ci kwaliya acikin tufafi na alfarma, wasu ma zakaga cewa kamar kwaliyan ranan sallah idi ne ranan gare su don har abinci yakeyi na alfarma domin girmama wanan ranan mai tarin alherori acikin ta watau JUMMA,AT MUBARAK,,

Cikin ikon Allah sai gashi yau wanan ranan mai albarka ya hadewa mutane za,a sallace ta tare da mutanen AHALKITABI,
Suma zasuyi bukin murnan zagayowan haihuwan Annabi isah, atare da mutane,
Hakan yasa duk inda kaga musan man babban gari irin kwantagora zakaga duk garin ya cunkushe da mutane kala kala,
Kowa da abinda ke agaban shi a lokacin ba mai kallon wani,

Hakan ne yasa shima Yusuf yau abin yai mai biyu,
Ga Dad din shi na son ganin iyakarshi akan sai yaje gurin addu,a gashikuma yana son ya samu sahun farko kamar yadda al,adan shi yake,
Maryam tana barci ya shirya tun da safe shida Granny din shi zuwa gidan mahaifin shi,
Shi da kan shi yaja su zuwa Church din ya na zaune batare da ya gabatar da komai nasu ba har zuwa lokacin da suka watse daga morning prayers din,
A can gidan mahaifin shi yabar Granny din shi don su yi celebration dasu,
Yadawo gida yasamu maryam zaune a dining tana breakfast,
Kallon shi tayi cikin mamaki don ganun shirin dake ajikin shi lokacin,
Ba boyo yace mata kin tashi ?
Kai ta kada mai yana kokatin zamane yake ce mata,
Kina barci nawuce in kai su Dad da Granny Church don morning prayers,
Gaban maryam ne yaba da dam lokaci guda,nan take fuskan ta ya sauyawa,
Church uncle ?
Yana kokarin bude kulan abincin dake gaban shi yace eh Church naje,
Hawaye ne masu dumi suka silalo mata a lokaci guda jikin ta yana rawa,
Ganin yanayi da ta shiga yasa shi mikewa zuwa inda take rungumo ta yayi zuwa jikin shi,
Cikin murya mai rauni yace maryam kada ki min mumunan fahin ta pls,
Maryam ashe har zaki iya min mugun fatan komawa hanyar bata,
Magan ganun da yakeyi ne suka dan sa ta tsagaita kukan ta alokacin,
Sai dai ta dago kanta tana kallon shi ido cikin ido yau din kamar wace ke son gane wani abu acikin idon nashi a lokacin,
Maryam bakya son in gama lafiya da mahaifina ne ?
Don na shiga church a tare da su bashi zai sa in koma Christian ba,
Asalima naje don ni da kaina nai mai alkawarin hakan cewa zan zo wanan lokacin,
Badon komai ba saidon na fahinci cewa mahaifina yana son ya kureni ne sosai,
Maganan da yake ta hango gaskiya atare dashi,
Sai da yaga tadan sake yakoma inda yataso yafara zuba abinci,
Sosai yake cin abincin shi hakan ya tabbatar mata da cewa baici komai daga abincin su kenan maganar shi gaskita ce,
Dashi da Pipkin ne suka shirya cikin shiga ta alfarma zuwa sallah jumma,a,
Shadda ce gezenah mai ruwan Assh colour din tazarce kala guda dashi da yaron,
Da hullar a hannu yafito yana kokarin gyarawa maryam tana zaune tana waya da safiya,
Akan zancen abinda yafaru da su jiya gidan karban gaisuwa,
Anan Yusuf din yadan yi picking din zancen ita ko maryam ganin shi yasata dakatar da,wayan tanacewa safiya sai tazo,
Ido Yusuf ya kura mata yana son jin karin bayani daga gare ta,
Duk yadda yaso jin zancen maryam taki fada mai gaskiya,
Bayan tafiyan shi ne Safiya tazo gidan, nan suka zauna tare har dawowan Yusuf daga massalaci,
Bayan sallah la,asar maryam tare da Yusuf din suka shirya cikin kaya na alfarma zuwa gidan mahaifin shi,
Wanan ne rana na farko da maryan ta je gidan surukin na ta tun bayan auren su,
Tsaraban da tazowa Ruth dashi shine ta sa a ledar, don ta kai masu,
Sun sami mahaifin nashi tare da abokan shi a farfajiyan gidan shi ,
Suna ta faman tutila giya suna kekewan dariya kamar wasu kananan yara,
Direct cikin gida maryam da mai gidan nata suka shiga hankali maryam yai mumunar tashi a yadda ta gan su,
Don ji takeyi kamar a ce ahir ta sheka da gudun saboda irin yadda ta tsora ta,
Dafdaf take bin Yusuf din duk inda ya cira kafan shi ta a za nata,
Sun sami kanen Yusuf tare da maman Choima wace ke cikin shiga ta alfar ma,
Gwiwa bibiyu maryam ta rusun na har kasa ta gaida yar tsohuwan,
Ansawa tayi cikin nunawa maryam din farin cikin ganin ta a lokacin,
Yusuf ma gaishe ta yayi tare da ce mata ya celebration ?
Ruth ce tazo ta baya ta rungumay maryam tare da ce mata
My wife so na your face be dis ?
Ruth ki sakeni kawai ai nayi fushi dake ne ki,ka wuce batare da kin dawo munyi sallama ba ko,
Acikin hausan ta mai surkin yare Ruth tace wa maryam din haba dai wifiry, dina kada ki bari ajimu pls,
Ledan da ke a hannu maryam ta mikawa Ruth din tace ga tsaraba na nan ,
A kwai agogo da cliffs da turare kibawa Samuel, nashi ba yawa,
Wani irin ihun murna Ruth ta kwala wanda ihun yai daidai da shigowan mahaifin su,
Cikin ran gaji yake dan dodogara sandar shi amna yadan bugu duk da dai su giya yanzu bata kashe su,,
Da Samuel da Ruth sai murna sukeyi da ihu cikin murna,
Ruth ke cewa I love it, ,
I love dis gift ,
Yusuf sai dadin wanan hikimar da maryam tayi yake ji hikimar da shi sam bai yi tunanen yin haka ba, shi,
Maryam ce ta mike tsam daga gurin da take zaune har zuwa gurin da tsohon ya zauna,
Gwiwan ta biyu a kasa cikin mutunci da girmamawa, tace ,
Ina wuni baba,?
Mun samay ku lafiya, in ji maryam din
Kwalban turare da agogo taciro daga cikin jakar ta ta mikawa Mr Ema din cikin yar jin kunya,
Mamaki yayi sosai na wanan abin da yariyar tai mashi shi d yaran shi,
Inda Yusuf yake ya kalla Yusuf din yadaga mai gira alamar ba ruwan shi,
Cikin dan bubuga sanda batare da ya ce wani abuba yace, yane jiki, naki do, so ki ko,?
Maryam tace naji sauki Alhamdullahi na gode ma Allah,
Jin ta ambaci kalman da ya shafi addini yasa shi saurin murde fuskan shi,
A hankali tadaga tabar gurin inda yadan bita da hararan wutsiyan ido ,
Azuciyar shi ya ce wanan yarinyar muddin tana tare da yaron nan bazata bari yadawo Christian ba,
Kowa sai murnan tsaraban shi yakeyi sai a lokacin Emanuel yaga Pipkin wanda ke zaune gefen maman chioma,
Grandson come here ya mika mai hannu ya nason Pipkin din yazo gurin shi,
Amma sai yaron ya make yaki zuwa gurin Mr Ema din,
Mr Ema yace wa dan shi Yusuf akwai, makarantar missionaries da yake son a kai yaron nan bada dadewa ba saboda ya koyi addini tun yana karami,
No, No Dad don't metion that again,
Kasan cewa yaron nan dan musulmai ne don may za a kai shi missionary school ?
Nan mahaifin nashi yace yana nufin cewa ya rike yaron ke nan a hannun shi ba zai kawo shi asa shi a school ba,
To Yusuf ya san da sanin cewa society tasan da zaman yaron don haka zasu sashi a schools din su,
Don ya zama wani abu a cikin Christianity ya tallafawa na baya,
Idon Yusuf atake suka canza kala yace cikin hassala wa mahaifishi kada ya fara yakawo zancen yaron nan ko watan watarana,
Don yaro dai da uwar shi da uban shi musulmai ne don may za a ce yayi Christianity kuma,
Ganin cewa dan nashi yafi sho points na gaskiya don haka yaja zancen yai shiru,
Maryam hankalin ta ya tashi a lokacin ganin cewa itama fa diyan Yusuf su na da iko da su,
Har sukai sallama da su suka dawo gidan su gab da magrib jikin maryam din ba karfi,
Tunanen duniya da tsoro duk ya damay ta, saboda irin yadda taga yau yafaru a gidan surikin nata
Ajiyan zuciya ta sauke a lokacin da tai tunanen cewa, koda wani abu ya cika da ita baza ta ba da diyan ta ba,
Zuwa wani akida na Christian da taji yana fada,
Kai asalima zatayi kokari ta cushawa diyan ta ra,ayin addinin musulunci ne sosai tun suna yara,

Kwance take Yusuf wanda shima nashi kalan tunanen daban ne ya nisa tare da kiran sunan maryam,
Maryam din wace tai lamo saman gado tqnkar mai barci a lokacin,
Tana jin shi amma bata karba mai ba don tasan cewa yasan batai barci ba,
Don yana kallon ta har tai wanka tadan gyara jikin zuwa lokacin da ta hayo gado,
Yakara cewa don yasan tana jin shi ansawa daine batayi
Sai kinyi hakkuri gaskiya kitayani yaki da yan uwana kafin komai ya daidai ta a tsakani na dasu,
Koda yake da wuya ne abin ya daidai ta a tsakanin mu dasu saboda banbancin addini da muke dashi,
Sam ni bazan so ace diyana sun yi oda koyi da wani akida na mutane na ba , face kawai sai wanda ke acikin addin islama kawai,
Babu komai uncle tafafi a raunane, tare da cewa Allah dai yasa suma su gane gaskiya sudawo hannya,
Murmushi yayi na takaici yace hmmm kayya da wuya ne maryam,
Ya mirgino kusa da ita ya rungumota ta baya ya dan shaki kamshim gashin kan ta ,
Maryam ki rike ni amna pls ki rike tankar dan uwanki na jini ki so zurian mu ki basu tarbiya ta yadda ya kamata pls,
Ya matse ta gam a cikin jikin shi kamar wanda za a kwace mai ita a lokacin ,
Daga ita har Yusuf din kuka sukeyi ba maiba wani hakkuri a lokacin,
Maryam dince tai karfin halin dan juyawa ta rungumo Yusuf tace uncle kada ka butulcewa Allah ga irin ni,iman da yai maka,
Badon komai ba sai don yana son ka da alherin shi ya tsamoka daga kafirci zuwa islama,
Idan kace kuka zakai mai ka nuna rashin godiyan ka ke nan agare shi,
Don haka ka daure ma duk wani challenges din da zaka gani a gurin koma waye daga both side,pls,
Shafan shi ta kama yi cikin kokarin mantar da shi bacin ran da yake aciki,

Sai bayan kwana biyu ne maryam taje gidan mahaifin ta don gaida matan uban ta,
Umma naganin irin yadda maryam ta koma a take wani kibiyan bakin ciki ya soki zuciyar ta
Kishin yadda yarinyar tawaye ta goge ta murje a lokaci guda,
Har saida takasa boye bacin ran ta alokacin don duk wanda ke gurin ya fahinci cewa rayuwan ta ya baci,
Safiya ta rako maryam din tazo gaida matan mahaifin ta din,
Tsaraban turamay da kudi dubu hamsin hamsi ta basu, su biyu,
Aiko kamar an kara tunzura umma ne a lokacin don irin yadda ta shiga wani hali,
A ranan bayan wucewan su maryam bayan baba yadawo ne rayuwan shi bai mai dadi ba,
Don masifa da jidali umma tasa mai wai dama don yai arziki da yarinya yadauke ta ya bayar gidan kafirai,
Irin suratan da tayi, wa mahaifin maryam a ranan saida dan dattijon yai kuka agaban iyalin shi,
Yadaga hannu sama yana cewa Ya Allah idan har na,bada wanan yarinyar don akan abinda duniyar ke zargina Ya Allah kai ne sheda akai Allah ka isar wa maryama da mahaifiyar ta,
Dayar matan baba ne tai karfin halin cewa assaha malam ai basai ka tsaya cewa hakana ba,
Don Allah yagani da kanshi kuma yasan dalilin ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login