Showing 234001 words to 237000 words out of 255288 words
Chapter 79 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete
Ya lumshe idon shi ya bude su a lokaci guda ya dan furzar da iska waje,
Zan sa a bincikar min dalili insha Allah,,,,,,,,
ZEEE MAKAWA YELWA
[5/5, 9:13 PM] +234 703 055 6607: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
9⃣3⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI
ADDU,AN NAKE NEMA AGURIN KU, DA FATAN ZAKU TAYANI ROKON ALLAH
JUMMA,AT MUBARAK YAN UWA RAMADAN MUBARAK👏👏👏👏
Yadda Yusuf yaga,cewa hankalin maryam ya kwanta da zancen da yai mata,
Bayan shi maryam tabi da kallo ta re da sauke ajiyan zuciya,
Mikewa tayi zuwa gurin window dakin, tana kallon furannin dake haraban gidan,
Zuciyar ta na cigaba da harbo mata maganganun da Jibrin ya yi daren jiya,
Abinda ya faru abayane yazo mata sabo fill yadda yai ta magiya akan tai ma safiya din magana,
Don irin yadda Jibrin din ya rude da akan samun yardan safiya taso shi a lokacin da yafara son ta,
To may yafaru haka a tsakanin don dai tasan cewa kowan su na son dan uwan shi,
Innalillahi wa,inna ilaihi raji'un"
Maryam tai saurin ambato wanan kalman a sarari gami da rintse idon ta, don dai tasan da akwai matsala
Idan ko hakane Jibrin din yaci amanar aminiyar nata ke nan, don dai itace silar hada su ,
Tana cikin wanan tunanen ne tsaye a bakin window taji muryan Pipkin a kusa da,ita,
Murmushin dole maryam ta kirkiro tace cikin turanci Pipkin ina nani batai maka wanka ba,
Hannun yaron takama zuwa dakin shi inda taimai wanka ta shirya shi,
Abinci taba shi yaron ya bude cikin shi yaci sosai ya kwashi abin cin,
Maman Choima fitowan ta ke nan daga daki a falo tasamay su maryam din na gogewa Pipkin bakin shi,
Wani irin ya tsune fuska tayi tawani kau da kai gefe guda,
Maryam ta mike a cikin girmamawa tace a mama ina kwana a harshen turanci,
Kamar bazata ansa ba sai can ta ansa da cewa lafiya kawai daga haka tafara kokarin hada abin kari, da kanta,
Ganin Pipkin yana wasan shi yasa maryam mikewa zuwa dakin ta,
Wayan ta ne dauko don takira Safiya, kira guda ga na biyu safiyan ta daga wayan kamar wace ke jiran wayan,
Cikin tsokana suka fara magana, a,a mutanen Abuja ai da har nayi fushi.
Haba dai inji maryam safiya tace amarci tun yanzu ya hana zumunci kullun na kira waya akashe,
Murmushi maryam din tayi tana yar dariya ciki ciki, itace tafara kau da zancen sherin da Safiyan ke mata da cewa,
Ya su mama da sauran mutanen gida Safiya tace wallahi suna nan lafiya kalau,
Wai ko kin san wani abu, inji safiya take tambayar maryam,
Nan da nan gaban maryam din yafadi dam don tana zaton maganar su da Jibrin ne zata fada mata,
Safiya tace na je Kamfanin Bobi gurin mama,
Cikin wani irin ihu maryam tace ke safiya dan Allah dai Safiyan ta ansa da fadar wallahi ko,
Kwana na biyu a can wani irin dadi ne ya lulube maryam din takara jin son aminiyar nata,
O, o safiya nagode kwarai, wallahi, da sauri safiya tace may na godiya aciki ina nima uwatace mama din,
Murmushi maryam ta yi har safyan taji hakan a wayan ta,
Nan dai safiya taiwa maryam labarin irin dadin da taji gurin mama din,
Anty Dije fa inji maryam tana tambayan safiya ,
Safiya taba da ansa a takaice da cewa ban je ba maryam,
Cikin mamaki tace saboda may Safiya cikin sauri safiyan tace dalilina ne kawai bada wani ba,
Haba dai safiya Anty n nawa zaki ki zuwa gidan ta akan may,
Ke ya maigidan ki da mutanen ku duk suna lafiya ko safiya din ke tambaya tana son a wuce zancen Anty Dijen,
Amma sai maryam din tace gaskiya nai mamaki kwarai da jin hakan safiya,
Maryam ke bazaki gane komai ba don haka mubar zancen don. Allah ki ce ina gaida uncle don Allah,
Dakata Safiya inji maryam din tace wai ya zancen ku da Jibrin ne don naji shiru ba wani zance akai,
Shiru safiya din tayi can kuma sai ta dan nisa tace maryam kibar zancen Jibrin pls,
Saboda may safiya maryam din tai mata takaitacen tambaya ?
Maryam don Allah mubar wanan zance kawai dai na gode wa Allah da ba wani abinda ya shiga tsakani na dashi,
Subbahanallah inji maryam abin har yakai cen amma ban sani ba Safiya,
Maryam sanin baida wani amfani ne shiyasa ban fada maki ba tun farko ,
Ikon Allah safiya fada min tsakani da Allah may ya hada ku ?
Maryam bawaini zance bane mai tsawo matsalan a,kankine kawai
Ido waje maryam ta kara tambaya cikin daga murya tace matsala tafa kika ce safiya,
Nashiga uku ni maryam tace cikin karayan murya may nayi har zan shiga tsakanin ku haka ?
A takaice Safiya tace wai kin aurewa yar uwan shi saurayi har kuma da sheri kukai mata,
Nan dai tafara ba maryam labari kamar haka,
Watarana yazo gurina rai bace bai wani dade dazuwa ba a ka kirashi ga waya,
Bayan ya daukane na fahince da mace yake magana
Inda naji yana cewa wai aidama don haka ita dije duk ta asirce Yusuf din don ta hamdamay komai nashi,
Hakan bai mata ba shine yanzu take kokarin hada Yusuf da kaunar ta,
Haka sukai ta zancen har zuwa lokacin da suka gama,
Bayan sungama ne nake ce mai may yafaru ne wai, bai boye min bayake shedazmin cewa wai ai kuna nan kuna tawa Yusuf kule,kule akan ya aure ki,
Nan nake sheda mai cewa ke baki ko ra,ayin wanan hadin
Yace wai inji wa ya fada min wai harda kazafi kukayiwa cousin sister shi cewa tana maki asiri,
Safiya tace nan da nan rai na ya baci wallahi maryam nadinga mai nasiha akan shiga maganar mata,
Sama sama muke dashi saiga zancen auren ku da Yusuf andaura shine yace wai ai har da ni a cikkin kulle,kullen da akayi,
Wai ai sai ya rama wa ita sadiyan abinda Yusuf yai mai,
Wai shima da yake tubabbe mara asali har zai, wa mutane rainin wayo,
Ita ko sai tace mai aiko baida asali yana da abinda ke nemo asali ai don ko acikin rashin asalin suke bin shi har suna cin arzikin shi,
Kawai kin san may hannu yadaga yakai min mari a fuska,
Tun wanan ranan muka samu matsala yanzu naji ance wai shi zai auri Sadiyan ai,
Maryam tace, O Allah ni maryam yanzu sakaiytan da Jibrin zai muna ke nan,
Aikuwa wallahi shi yai hasara insha Allah indai don ya rabu dake ne zai auri sadiya yaje ganin kamar yai maki bakin cikine,
Ke maryam ni wallahi nama fita zancen kinji nabarwa Allah zabi akai,
Allah yai muna mafi alheri inji maryam din tafada rai a bace ,
Sun dauki lokaci suna tataunawa akai har maryam din ta fahinci cewa ba komai ai safiya din ta hakkura,
Yinin ranan haka maryam din ta wuni rai a bace tana tunanen zancen Jibrin din,.
Dan Adam abin tsoro ne gaakiya ya za,a ce wai Jibrin ne zai fadawa Yusuf irin wanan zancen haba dai duniya,
Kara jin aminiyar nata tayi azuciyar ta saboda ita safiya ta,sadaukar da soyayyan ta,
Ai yukan da duk ya kamata maryam din tayi na gida alokacin su tagabatar,
Tadan ce bari tadan fita yau tasha iska a kasa don tun ranan da tazo bata taba fita wajen ba,
Ta kofan kitchen din su wanda zai sada mutum da waje maryam din tabi,
A kitchen ta hango markade a wuta amma bataga mai aikin aciki ba,
Tana sa kafan ta a waje ta hango mai girkin nasu ta kware riga tana fitsari a tsaye can bayan flowers din su,
Cikin sauri maryam ta dawo baya cikin rawan jiki gaban ta sai faduwa yakeyi a lokacin,
Saboda ada labari take ji bata tabbatar da cewa haka suke fitsarin su da gaske ba,
Nan take taji zuciyar na tashi don abincin da matar ta taba dafawa taci ji tayi kamar ta jawo shi, yafito,
Dakin ta takoma tana mai jin wani irin juwa na kokarin kwasan ta saboda har falon nasu kazantan shi maryam takama ji,
Zaune take saman gadon ta kafan ta zube daga kasan gadon bata hau dasu sama ba,
Tayi zurfi a cikin tunanen abinda tagani da yadda zata kara tsayawa tayi rayuwa da su acikin gida daya a haka,
Har mai gidan nata, ya dawo maryam bata kula da cewa time din shi na dawowa yayi ba,
Yadan dade a tsaye gurin yana kallon ta hannun shi ya sa yadan gada gab da fuskan ta abinda yasa ta szurin yin ajiyar zuciya,
Ta daga manyan fararen idon ta tadan kalleshi , da ido tace mai sannu da dawo wa uncle,
Tana son tashi zaune, amma sai ya hanata mikewa zaune, din
Ta hanyar dan kwanto mata daga tsayen, murmushi tayi ita ma tare da dan ware hannayen ta,,,
Sosai suka murji junan su a lokacin ba karamin dadi Yusuf din yaji ba ganin ya fara,samun responde daga maryam din wace ada shi kadai ke gidan shi da rawan shi,
Maryam wanka tafada ta gyara jikin ta kafin lokacin sallah ya karaso,
Sai dai kuma bayan komai ya kammala tanemi damuwar da take ciki kan aminiyar ta tarasa,
Jin zuciyar ta takeyi wani wasau dashi bakan dazuba matsala guda yanzu hanyar da zata tun kari Yusuf da zancen masu guntun bujen dake gidan dasunan yan aiki,
Bayan ta idar da sallah a gurin da take zaune take tunanen yadda zata bullo ma wanan zancen na yan aikin masu fitsari a tsaye,
Gashi bata,son ta fadawa kowa sirin gidan ta don irin wanan na a cikin kalman furen juji,
Daga karshe wani shawara yazo mata azuciyan ta don haka ta yanke shawaran tunkarar shi akai,
Saboda ko banza bazata so tazama silar hana cin abincin wani dan adam ba ,,,,,
Falo shi na sama yake zaune bayan ya dawo daga massalaci, kira,a yasa wanda duk inda kake a gidan zaka iya jin sautin,shi,
Cikin wani dongon riga da Yusuf yasayo mata maryam take rigar mai adon duwatsu har kusan kasan shi da wasu hannaye shara,shara tadaura dan kwalin rigan akan ta,
Laptop din shi agaban shi dagani tasan aiki yake acikin shi
Cup ne a hannun ta dauke da milk a cikin shi mai sanyi tasa dan wani marfi ta rufe,
Falon nashi ba kowa ke shigowa cikin shiba in bashi da ita ba yanzu,
Kusan yaune ranan farko da maryam din tafara samun shi a falon saboda ta fahinci cewa guri kamar inda yake samun natsuwa agida,
Tunda ya hango tafe sai yaji ya kasa yin aikin dake agaban shi sai kallon shi ya koma gare ta
Maryam wace tafe take acikin rausaya kamar zata karye don rangwada, amma ita batasan tana yi ba,,,,
Yusuf a zuciya, shi sai hamdallah ya keyiwa Allah daya bashi maryam a matsayin matar shi,
Haban shi ya rike da hannunshi kaman mai mamaki,
Kafafuwan shi suna mike saidai ya harde daya cikin daya,
Isowan maryam gaban shi yai daidai da sauke ajiyan zuciyan shi,
Cup din milk din da takawo mai ta dan aje saman stol din da ke gefen kujerar,
Mastawa tayi gab dashi tasa hannun ta ta cire mai hannun da ya tallabo haban shi dashi
Idon shi ya zubo acikin fuskan ta cikin murya mai sanyi yace mata,
Maryam a kullun na kasance tare dake sai in rasa irin godiyan da zan ma ubangijina da ya mallaka min ke a matsayin matar sunna na,
Kalan shi maryam tayi cikin natsuwa ta sake mai wani irin lalausar murmushi,
Don kokarin ta na isar da maganar da tazo mai dashi,
Gashi tun agida tasha alwashin rike mijin ta da,zuciya daya akarkashin yina nayi bari na bari,
Badon komai ba sai don cikawa mahaifinta burin shi na wanda shi kadai yasan dalilin bata Yusuf a matsayin mijinta
Saman hannun kujerar da yake takai zaune tadan kwanto da jikin ta saman kujerar ,
Ta ce cikin wani murya hmmm uncle ni ban ce nagode ma Allah da ya nufeni da zama matar ka aduniya har nake fatan a lahiran mu ,
Cikin sauri yatare ta da cewa in sha Allah maryam in Allah ya yarda,
Ameen ta ansa mai dashi,
Uncle a yanzu fa kai ne mutum mafi daraja a wurina,
Banda wanda yakai daraja a guna domin aljanna ta tana akarkashin kafan ka ne,
Gashi a sannu ka koyar dani sonka acikin dan lokaci kankani,
Banda wanda nake ji dashi nake son shi face kai mijina uban diya na ayanzu ban damu da duk wani abinda mutane ke cewa akan ka ba,
Tunda maryam ta fara jero maganar ta bata tsaya ba sai da takai karshe, batare da ta tsaya jin may zai ce ba,
Rugumota yayi zuwa cikin jikin shi saboda bai taba tsanmanin jin ko makaman cin wanan maganar daga bakin ta ba,
Sai gashi yau ita maryam ce da kanta take fadamai da bakinta,
Don haka zancen ya shiga zuciyar Yusuf sosai har takai ga ya kasa cewa komai sai binta da lalaba yake yi,
Itako maryam dama abinda take jira kenan taga cewa ta birkita mai lissafin shi kafin ta fara aiwatar da plan din ta
"Maryam! ya fadi sunan nata cikin wani yanayi sai kuma yaja bakin shi yai shiru ya kasa furta ko mai akai,
Wata kila kuma don bai da kalman da zai iya fada ne a lokacin,
Kara noke kanta tayi saman kirjin shi tace I love you uncle Yusuf,
Tare da kai bakinta acikin kunnuwan shi ta furta mai hakan,
Nan da nan jikin Yusuf din yadauki rawa tankar yau yafara sanin maryam din,
Hakan yaba maryam daman yimai wasu abubuwan da bai ma san ta iya ba, saboda takara cusa kanta gare shi kamar yadda kowace mace ke kokarin yi don mallakan mijin ta gare ta,
Lokaci mai tsawo suka dauka ita dashi acikin wani irin yanayi da ba zai yiwu a fade shi ba ,
Sannu a hankali maryam din ta dan fara zamay jikinta a cikin nashi,
Ta koma gefe guda tana kokarin sauke numfashin ta,
Sai a lokacin hankalin su yadan dawo suka tuna da gurin da suke
Cikin sauri maryam din tafara mikewa tsaye tana kokarin gyara gaban riganta da ya bude,
Sannan takai dan zaune saman kujera dake kusa da ita,
Yusuf wanda ke kwance saman floor plat dashi daga shi sai yar tree quiter dake a jikin shi,
Gyaran murya yayi yana miko mata hannu alamar ta daga shi daga kwancen,
Dariya tadan kama mashi don sai a lokacin ta tuna da milk din da takawo mai,
Cup din milk din tadauko tanufo shi dashi inda yake kwance tana cewa tashi ga milk kada yai sanyi baja sha ba,
Idon shi a lumshe lokacin cikin kasala yadan kai zaune yajingina bayan shi ga kujera
Bayan ta mika mai yadan kurba kadan sai ya lumshe idon shi,
Azaton shi madaran ce sahihiyar ta sai da ya kurba yaji bambamci a cikin shi,
Sald milk ne a ka hada wanda ke bada kamshin flavor mai dadi,
Cikin lumshe ido Yusuf yace waya koya maki wanan hadin little Mum ?
Sunan da yakirata yasata dan shiga wani yana saboda ya sa tatuna da abubuwa da dama da suka wuce,
Mai makon tabashi ansa sai cewa tayi hmmm inji Assalam ko ?
Gyara dan zaman ta tayi sanan tace Uncle dama ko ina son in dan roki wata alfarma a gare ka,
Cikin mamaki ya dago kan shi ya kalle ta yace alfarman ke nan maryam,
Don Allah so nakeyi a bude min kitchen dina daban sai in barwa su ukeria wancan din surika abincin su suda sauran masu aiki ,
Sai tai shiru alamar tana jiran jin ansar shi a lokacin,
Shiru yayi yana kallon cup din milk din dake hannun shi kamar mai nazarin wani abu,
Sai dayadan kara kuba milk din sanan yace ko so kike akoresu don banyi zaton zaki iya kai warhaka dasu ba don nasan ki da kyamar mara sallah,
Kunya maganar tashi taba don dai yagano inda maganar ta tadosa amma sai tadake tace ,aaa bana son akore su,kawai dai yamanto bani aiki da kayan su,,,,,,,,,
ZEEE MAKAWA YELWA
[5/5, 9:14 PM] +234 703 055 6607: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
9⃣4⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI
Shakuwa maikarfi ya shiga tsakanin Yusuf da maryam,
Har takai koda yaushe suna manne da