Showing 15001 words to 18000 words out of 255288 words

Chapter 6 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1344

har Issalam duk bayin inda yake kwala ihun suka nufa,
Wanka su ka samu Anty Dije tana mashi yana ta kokarin kubcewa,
Bayan sun shirya ne suka wuce islamiya saboda sun makara, yau
Allah ya taimake su ba su sami malam babba yadan fita don haka badu sha duka ba,,,

Isowar su Joseph da KB a majalissar su ya yasa gurin yadan kaure da hayaniya cikin dan lokaci kadan,,
Bayan dan gaishe gaishen da ya biyo bayan ne suka samu guri suka zauna
Fira akeyi amma shi Joseph uffan bai ce masu ba sai dai idan anyi abin dariya shima yadara,
Ana cikin hirane daidai lokacin da yan makarantan Isalamiya suka fara tasowa, a lokacin wayar shi tai kara alamar kira yashigo mai,
Aisha ce ya gani baro baro a jikin screen din wayar tashi,
Dan tashi yayi nisa kadan daga ind suke zaune, don ya karba wayan nata,,
Tambayar shi take yi yana ina ne ?
Don tana son ganin shi ne, kafin yabata ansa sai ji yayi an rike shi ta bayan shi,
Da alama kuma dan karamin yaro ne don daidai iya gwiwar shi yaron ya tsaya,
Kafin ya juya lokacin da yaji haka yake cewa Aisha yana zuwa pls,
Waigowa yayi a hankali yana kokarin ganin kowaye yaron,
Wani dan farin yaro yagani ya rike shi tsab yaron na cewa,
Abokina kullun sai na diba ko zan gan ka idan zamu tafi islamiya amma bana ganin ka,
Idan kuma na tsaya sai little, mum ta dinga zagina,
Rage tsawo Joseph din yayi don dai bai fahinci ko may yaron ke tawa bayani ba,
Maryam, dake tsaye gefe iyakar kuluwa ta kai har tafi nan,
Don ji takeyi yau idan ta fara dukan Assalam bazata daina ba tunda har yasa ta tsayawa daidai gurin yan sa idon mutanen nan,
Hannun Assalam Joseph yakama ya hade guri guda yana mai fuskantar yaron,
Kafin yai magana sai muryan maryam suka ji tana cewa Assalam bazaka zo mutafi, ba ko,
So kake dare yai muna a hanya kafin mu isa gida ko,
Nunata da hannu Assalam yayi yana mai cewa dakace kada in basu sweet dina sai da little mum ta ba Issalam tasha,
Joseph dai har yanzu bai fahinci yaron ba don ya manta cewa sun taba haduwa da yaron ,,,
Yace wa Issalam bari ,zan saya ma wani mai yawa amma kaba kowa yasha kada kayi rowa kaji,,
Jibrin dake kallon draman su tun dazu yadan taso daga inda yake saman wani benci yana cewa cikin turancin
Ai yaron da ka taba dauka ne da ya fadi a gurin nan da zasu tafi,makaranta,
Saida yadan yi tuna ne sannan yace ok ok na tuna a haba dai my friend kaine haka kazama big guy,,
Yakara jawo yaron zuwa cikin jikin shi ya rungumay yadan dago kai yana kallon jibrin,,
Yace wanan yaron baya mantuwa pa kadiba bafa yau ba wanan event din ya faru wai ama ace bai manta ba,
Maryam kuka kawai ya rake tayi a lokacin saboda sukuwar da yayi da Assalam,
Cikin zafin nama ta isa inda suke tana kokarin finciko Assalam, din,
Kai Joseph yadaga yana kallonta yana cewa haba barshi mana pls,
Wanan yaro ne fa shi ai baisan komai ba, yana fadin abinda ke a mind din shine fa kawai,
Batare da ta saurari may yake cewa ba tace kazo muje gida kaji wallahi yau sai na ma mugun bugu Assalam,
Jibrin da baiyi magana ba tun dazon ne yake cewa kutafi zan kawo shi gida,
Cikin mamaki ta dago kai tana kallon mai magana don ita a iya sanin ta bata taba ganin jibrin a gidan nasu ba,
Yagane kallon da take mai don haka yace mata ke wanan yaron fa nima yaro na ne kin ji,
Kafin mamakinta ya kai karshe
Taji yana cewa ke ba kaunar matan Isiya Custom bane,
Kai kawai tadan gyada mai alamar eh ita ce, din
Yace to kutafi kawai zan kawo shi,
Still wani irin mugun kallon see u tai ma jibrin din alokacin,
Yace ke nifa yaron gwago laure ne don haka ki wuce kawai,
Jin an ambaci gwago laure yasa maryam fara kama hanya rai bace hannunta rike da Issalam tana ja kiiiiiiii,
Anty tana kokari kauda abincin dare daga dan matsakacin kitchen din ta taga shigowar marya da Issalam a hasale,
Babu Assalam a tare da su hankalinta na kofar hanyar shigow taga shigowar Assalam din,
Kafin yatambaya maryam tace wallahi Anty gaskiya ba zan kara fita da Assalam ba tunda a gaskiya duk zamu wuce sai yabani kunya a hanya harda zuwa rokon fa naji yanayi,
Ido waje Anty Dije tace roko fa maryam ina yake in ci abu kazan shi,,,
Maryam tana kokarin shiga daki tabar Anty Dije a tsaye tsakar gida daidai lokacin da tace ya na can mana,
Idon dayafi na dazun fitowa waje tace can ina Maryam,?
Tare da wa yanda yake rokon ta fada kai tsaye kawai, tashige abinta,
Wuf Anty Dije ta bita ciki daidai lokacin da Maryam ta kwabe, hijabinta daga kan ta tace mata tare fa dadan gidan gwago laure suke,
Wani cikin su? Kenan inji Anty Dije
Uhumm nima ban san sunar shi ba inji Maryan,
Hijabin da Maryan ta kwabe ร€nty Dije ta jawo tana kokarin sawa,
Daidai lokacin da sukaji ana sallama alamar shigowa cikin gidan
Karar takalman Assalam ne ya sanar da su cewa tare da mai sallamar yake tafe,
Assalam agaba da gudun shi cikin walwala da zumudin ya bude ledar dakw hannun shi
Anty Dije tai saurin kai mai duka a hannu ya wurgat da ledar ya, koma baya da sauri ya fara kuka,
Jibrin ne yace ma Anty Dije haba dai madam ya zaki buge shi tunda har kin gan mu a tare,
Cikin yar dariyar da batakai cikiba take cewa jibrin wallahi jibrin yaron ga baida dabiar kwarai,
Rokon ku fa yayi,
Nan da nan jibrin yakai kallon shi ga kofar daki inda Maryam take tsaye tun shigowar su,,
Hmm kawai yace yana kojarin komawa ya kamo hannun Assalam din
Bai roke mu ba yadai fada muna cewa wanan time din da aka saya mai sweet saida akaba kaunar shi,
Duk da joe yace kada yaba kowa,
Daga Anty Dije har Maryam duk sai jikin su yai sanyi,
Nan dai jibrin yaba Anty Dije labarin yadda akayi tun ranan farkon haduwar su da Joseph din
Joseph da ke waje tsaye yaga Assalam ya firo yana kuka riko mai hannu yayi yana kokarin lalashin shi,
Daidai lokacin Anty Dije da jibrin suka fito daga cikin gida,
Tana daga ciki kadan suka gaisa da Joseph din tana mai yi mashi godiya,
Yace kai haba ai ba komai bane wanan yaro ne Assalam bai san komai ba,
Jin hausan shi da Anty Dije tayi yasa ta gane cewa ba bahaushe bane shi,
Saidai sam batakawo cewa shi Christian bane, shi,
Joseph yace wa Assalm yai shiru zai sayo mai game da mota wasan yara,,,
Hakan yasa shi komawa cikin gida da sauri don yafada wa little mum da Issalam cewa za,a saya mai mota,,,,,,,

ZEEE MAKAWA
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
FUREN JUJI
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
8โƒฃ
ZAINAB IDRIS MAKAWA



Duk wani members din churching Catholicis suna zaune a gurin meeting din da,suka gaiyaci Mr Emanuel,
Bayan pastor yayi gyaran murya alamar kowa ya yi shiru
Gaisuwa yafara kamar yadda sukeyi idan anyi wanan taron,
Shiru gurin yayi nawani dan lokaci can pastor yakira sunan Mr Emanuel alamar suna da magana dashi ke nan,
Hakan yasa Mr Emanuel ya maida hankalinshi da kyau don jin abinda za,a fada,
Wanan taron munyi shine saboda kai da dan ka,
Kai kawai Mr. Ema yadan kada alamar gam suwa,
Yaron ka alamun sun nuna muna cewa baya son hurda da yan uwan shi Christan
Sai yaran hausawa wanda muna gudun hakan ya jawo muna abin kunya nan gaba ,
Hannu Mr Ema yadaga sama yai wani kyatawa yai round da hannun a kanshi yace
Kai abomination, god forbid,
Ya buga kafarshi a kasa
Yace dat will never happen
Never pastor never,
Nan da nan jikin shi ya dauki rawa yana cewa imba
Never sai kafa da yake kadawa ya tabure fuska dagani duk ran shi a bace yake kamar zai fashe,,,,
Suma wurin sauran mutane sai fadin ra,ayin su sukeyi akan zance,
Wani daga cikin su ne yamike inda yai yar gyaran murya yana cewa yana son cometi su ta diba da kyau tai nazarin ko waye Joseph,,,
Yace shi a nashi halin Joseph ba zai yi haka na ba ,saboda yana da tunane so sai,
Yace ai akwai wa yanda suna da kudi sosai daga cikin su amma idan anyi la,akari ko Church ba su zuwa yanzu,
Amma shi in har yana gari yana attending din Church tare da su,,,
Shi a ganin shi rayuwar shi ce hakana ta taimako mutane,
Saboda in sun diba ai yanuna wa yanda ke zaune saman benci tare da su da hannu yace,
Joseph na nin su har gida ya tai maka masu time to time,
Yace ko ba haka bane, sukace gaskiya ne, hakane,
Yace to shi yana ganin cewa wanan halin nashi haka take duk wanda yake tare da shi yana taimaka mai,
Mr Ema dake gefe yatokare hannun shi da sanda hular shi ta gwalmade gefe guda sai kafa kawai yake buga wa a kasa,
Jin jawabin na Mr Okarpo yasa gurin ya kara daukar hayaniya, so sai wanan karon,
Mutane da yawa daga cikin su suka kawo shawaran cewa Joseph yaron kirkine,
Shi yasa yake tare da duk wani wanda tunda suns tare ,,
Don ya na taimakawa hausawa ba shine zai sa a ce yana son yin wani abinda ba daidai ba,
Amma duk da haka su elders zasu kirashi su tsawata mai akan hakan,
Da wanan shawaran taron ya watse kowa na fadar albarkacin bakinshi,,,
Tunda Mr Emanuel yadawo daga gurin meeting din rayuwar shi take bace saboda shi a ganin shi an wa dan shi kullin sheri
Saboda kawai cigaban da ake ganin ya samu,
In bashi ba taya zasu dangata shi da wani akida cen,
Yan uwan shi kaf ba musulumi ko wani akida ta daban,
In ma hakane zaiwa Joseph din fada ya daina shigowa kwantagora gaba daya,
Yana yi yana tula giya a cup yana shan ye wa kamar wanda bai da kimar ciki,,,

Duk wani abinda zata bukata ta shirya shi a cikin dan kit din da tadauka don tafiya,
Batare da ta fadawa koda Amina ba zatai wanan tafiyar da zatayi yau,
Saida ta gama shirin ta tsab sanan ta fita tsakar gida inda, inda inna ke zaune bakin murhun ta na kasa tana gyara wuta ga koko a cikin wani dan roba mai marfi wanda ke nuna abinda ke a robar fili,
Ganin Aisha waje da safen nan yasa inna cewa, wa azubo maki kokon ne ?
Tawani ya mutsa fuska kamar wace akaiwa tayin kashi tace kai haba inna da safen nan haka,
Kujera ta jawo gefen inna ta zauna tana fada ma inna cewa zata kauye gurin kakar su ta dibo ta,
Shiru inna tayi cikin zargi take kallon yar nata wace ke magana cikin matse fuska sai kace aiba uwar ta take zance da ita ba,
Har ta mike uwar tace kwana nawa zakiyi saida takai kofan dakin ta ce batare da ta waigo ba,
Sai lokacin da kuka ganni kawai inna,
Daga haka tashige tadauko dan kit troler din da ta shirya kayan ta aciki,,
Tashan hanyar BCG ta nufa tana zuwa ana cewa Minna Abuja kaduna,
Abuja tace kawai kai tsaye aka karbi dan troler kit din ta a ka nufin motar dake kan layi,,,,
Musalin karfe ukun rana ta isa Abuja, wayar ta taciro takira layin shi,
Kira nabiyu yadaga layin yana mai cewa hlo, cikin wata irin murya ta ke magana kamar ta mai shagwaba,
Joe gani a Dikko fa,
Cikon mamaki yace mata Dikko fa Aisha tace mai eh ,
Kwatancen inda zata sauka, ta, tsaya yai mata, yace zai turo azo adauke ta,
Joseph yayi maki kwarai da jin cewa wai gata a dikko, bayan jiya sukai waya yake ce mata yana Abuja yazo yin wani dan aiki ne ,
Sai gashi kawai yana fitowa daga gurin meeting kiranta ya shigo mai,
Wata mota mai kama da, Box ta faka a gaban ta kau da kai tayi kamar bata gasu ba,
Sai hon da taji yai yawa yadan sata waigawa, driver motar ke ce mata itace Aisha ko ta karba mai ya nuna mata complement card din Joseph
Hskan yasa ta yarda da shi ta shiga motar bayan ya bude bayan motar yasa mata kayan ta ciki,,,
Wani gida mai hawa biyu suka shiga gidan bawani fadin fili ke gare shi ba amma ko kafin ka shiga kaima kasan cewa hadaden gida ne,
Da,sallamar ta ta shiga don duk ta rude da gani daular duniya da ta gani,
Jin da tayi yana ce mata hy Aisha,,u are, wel,come,
Daidai lokacin da yake saukowa daga steps din gidan,
Yar murmushi ta sakar mai tana wani nuna kamar alamar jin kunya,
Zuwa yayi inda take tsaye yai dan hugging din ta yana mai ce mata bukin surprise ke nan,
Kujera ya nuna mata ta zauna daidai lokacin mai aikin shi yashigo dauke da trey da drinks a ciki, sai cups guda biyu, a sama,,,
Shi da kan shi Joseph din ya zuba mata drink din a cikin cup dai dai lokacin kuma yake tambayar ta ina kawar ta wanan karon,
Tana karban cup din da yake miko mata ta ce, ba wanda yasan cewa nazo gurin ka fa,
Cikin nuna mamaki yafada cikin yar muryan nan tashi, yace saboda may,
Ta dan daga kafadar ta tace Just,
Tace ban son kowa yasan cewa nazo gurin ka, shi yasa tadan kare zancen acikin yar shagwaba,,,,
Bayan tai wanka ta kimtsa jikin ta wani dan kwalba ta dauko a can kasar handbag din ta,
Wani dan ruwa ne aciki blue kamar ruwan turare ta dan shafa kadan a saman maranta,
Sai kuma saman goshin ta daidai tsakiya ta man,na kadan,
Body spray ta feshe jikin ta da shi mai mugun kam shi na ,
Wani ribon ta dauko daga cikin handbag dinta, tadan feshe shi da kamshi ta daure kanta da shi,,,
Duk da tana da gajiyar tafiya a tare da ita, hakan bai hanata binshi zuwa cikin gari ba,
Sahad store ya nufa da ita inda ya bata damar daukar duk wani abinda take bukata yakuma ce mata kada taji komai,,
Cikin yar kunya take zabar yan abubuwa kamar wace bata so, Joseph na tsaye gefe yana kallon ta,
Ganin zata bata mai lokaci yasa shi kwasan mata abubuwar da mata ke yawan amfani da su,
Kamar su manshafi turare, kayan makeup, sai kuma ya juya yanufi fannin sutura,
Sayayyan alfarma yai mata,a wurin sai turamen zannuwa da ya jido kamar mai hada kayan lefe,
Jin bills din kudin saida ya sa Aisha dan kaduwa amma sai taga kawai ya biya batare da jin darrr ba,
Mamaki fal a zuciyar ta don bata taba zaton koda quarter haka ba, daga kowani irin mutum,
Sai wurin kayan kwalama da suka nufa inda nan ma ba karamin kudi ya kashe mata ba,
Wani Guy dake gefe ya ya matso kusa da inda suke tsaye yana cewa sannun ku da,zuwa ya hanya,
Idan kuna son dinki express ga shagon mu nan zaku samu zuwa gobe insha Allah,
Joseph ya dan kalli inda Aisha taja tai tsaye yana mai tambayar ta tana bukatar dinki, ne, kai ta gyada mai alamar eh
Cikin turamay da suka sayo suka bada guda biyar, dinki, akan dubu Ashirin,
Babata lokaci ya biya guy din sai yabasu nobar da kuma, card wanda zasu zo karba,
Daga haka suka wuce zuwa gida da kaya niki niki,
A,falo suka zube nan mai aikin gidan yakawo masu plate, tare da drinks da su, cultularies,
A hankali take komai don abinda take gani ya wuce tsanmanin ta,,,
A daki guda suka kwanta ita, da Joseph duk yadda Aisha take ganin ita yar bariki ce ta katsewa wa Joseph,
Saida ta kwana da dimbin mamakin irin halin Joseph ,
Duk yadda taso tambayar shi ba fuska saboda bala,in kwarji da yake mata, a idon ta,
Kwanan ta hudu Abuja tare da Joseph iyakar shi da ita romance kawai da nuna concern a kanta,
Kamar yadda ba ta fadawa Amina cewa ta na, Abuja ba shima Joseph, din bai fadawa kowa zancen zuwar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login