Showing 6001 words to 9000 words out of 255288 words

Chapter 3 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1337


Kai joe samu wuri ka parker zamuyi magana ne,
Ba musu ya parker motar shi inda Jibrin din ya fara magana cikin fushi kamar fada,
Joseph yaushe ka fara shan giya, don dai iya sani na dakai baka irin wanan dabi,ar sam,
Duk da ku a gare ku ba abin kunya bane, to kasani cewa mu kan agurin mu wani babban al,amarine,
Muddin gari akasan kana wanan dabiar gaskiya dole muma mu rabu dakai don gudun zargi a gare mu,
Saboda jama,a zasu iya fassaramu dakai duk abu guda mukeyi,
Kamar yadda kasan mutanen ka na kyamar zaman mu dakai muma hakana namu mutanen suna ganin mu da rashin sanin ciwon kai,
Abune kawai idan Allah ya hada, babu mai iya hanawa,
Tunda Jibrin yafara magana Joseph yana rike da sitiyarin motar shi amma gaskiya bai tsamani maganar da Jibrin ke ma fushi ba ke nan,
KB ne yakarbe da cewa duk addinan mu ba wanda ya yarda da shangiya balle har mu dauke shi kamar abin ado,
Jibrin yace wai ma yaushe ka fara shan giya ne man
Hannu yadaga masu yace is over pls,
Yai ma motar shi giya suka bar gurin batare da wani ya kara magana ba,
Saidai gabadayan su , sun sancewa shikenan kamar yadda yace is over din yadaina kenan har abada,,,,,





ZEEEE. MAKAWA,,,,,,,,,
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
4⃣
BY
ZAINAB IDRIS MAKAWA

🐎HUGUMA GROUP🐎

Mama Farida & Maman Walid
Kuna raina ko yaushe fatan alheri gare ko kamar yadda kuke min akullun,,,,


Maryam , maryam, wai may kikeyi a ciki ne haka, ?
Ki diba time ki gani yanzu kusan karfe biyar ake bida fa,
Wallahi anty Assalam ne yaki tsaya in shafa mashi mai waishi saidai ya shafa da kan shi,
Anty Dije wace ke kitchen tana kokari dora sanwar marance ,
Itace ta fado dakin a hasale tana kokarin bugun Assalam din wanda ke gefe guda tsaye shi adole bai son anty ta shafa mai manshafi,
Cikin sauri Maryam ta tare, da hannun ta inda anty tasamu hannun maryam din
Maryam na gane cewa har dake cikin shagwaba Assalam wallahi,
Aiku da malam ne idan har kun tafi kun iske an tare get,
A gagauce Maryam ta shirya yaran cikin kayan islamiyar su, ta dauko yar jakarta wace yan mata kewa lakani da wankar gefe, taraya a gefen ta,,,,,
Cikin sauri ta riko hannu Issalam wace ke tsaye tun dazu cikin shirinta tana jiran su tafi,
Murya ta daga daga inda take tana fafin Anty mun tafi sai mundawo,,,,,

Agajiye suka shigo garin na kwantagora daga kauyen da suka tafi cigiyar Dawaki da Rakumai wanda suke son suyi wasan Dabah dashi
Direct gida kowan su yatafi, shiko Joseph yana shiga gidan su yatar da ba kowa agidan duk sun tafi gurin bidan kudi,
Yar tsuki yaja azuciya shi yace bidan kudi tun bamuzo duniya ba kulun ana shago ba hutu,
Wanka yayi don yadan ji sanyi a ranshi, bayan ya fito wanka ne yadawo falo ko zai samu wani dan abu yaci,,,,
Saboda hura su KB suka sha a kauyen shi kuma bai iyan shan hura yan zu,
Don koda da yake yaro yana sha bai bashi lafiya,
Don,haka wurin fridge ya nufa ko zai samu dan abin da yaci a ciki,
Giya yagani kala,kala ga sunan, tab acikin fridge din,
Iya dibawan shi bai ga komai dazai danci ba sai giya kawai yagani,
Har ya mika hannu yadauko kwalbar wani whisky da yake yawan sha,
Muryan jibrin yaji yana cewa both religions din mu ba wanda ya yarda da shan giya,
Giya tana zubar da darajan mutum,
Da sauri ya dafarar da kwalbar inda akasane ba cikin fridge ba da ta fashe ko,,
Ya mai da marfin fridge din da karfi ya rufe , yajuya da sauri yabar gidan,
Har yafita sai ya tuna da cewa bai dauko makullin motar shi ba, da handset din shi don haka sai ya koma ciki,
Warin giya yaji yau falon nasu nayi a sakamakon bude fridge din dayayi sai kawai yaji warin na hawa mai kai,,,
Maimakon ya shiga mota sai yafita get din su ya taka da kafa,don yatari mai achaba ya hau,
A hankali yake tafiya har ya kusa shan yar kwanar gidan su sai yaga andanyi taro a gurin
Kamar ance mai yatafi har zai wuce sai kuma ya isa gurin,
Wata matace yagani tana ta rusa kuka ga wasu samari suna ta kokarin yin bico a wani fili,
Matar na fadin wallahi bamu sayar wa kowa da filin mu, ba kudine kawai bamu dashi shiyasa bamu gina komai a ciki ba,
Ya dan tsaye daga baya tana kallon ikon Allah, inda yawancin mutane gurin ke cewa ai fillin na matan ne ita da yatan ta,
Sun gaji fillin nr gurin mijin ta da yarasu, lokacin yaranta suna kanani bata da halin gina filin
Yanzu ko yaranta sundan girma shine tazo dasu don sugyara filin su dan samu wurin zama koda bukkah ne su dan haka saboda gidan haya yana mata wuyan biya,
Sai gashi sun fara aiki kenan wani yazo yace ai yasayi filin a gurin kanin mijinta,
Kuma har ya biya kudi dadewa, don haka subashi wurin shi,
Matar nata kurma ihu tana cewa ta shiga uku babu inda zata ga yara gashi basu da kudin biyan haya
Joseph na tsaye yana jin yadda matar ke gumza kuka duk wanda yazo yaji ba,asi sai dai ya ce Allah ya ktau mai shi ya wuce abin shi,
Duk yunwar da yake ji sai yanemay ta yarasa ,
Takawa yayi har inda mutumin da ke ciwa matar mutunci yake, yai mai sallama yana mai mika mai hannu, don su gaisai,
Bayan sun gaisa ne yake tambayar mutumin ya maganar take ne,
Da kamar bazai bashi ansa ba saidai yadda yaga Joseph din is serious sai ke ce mai
Yar rainin wayo ce sun saida filin su dadewa shine yanzu tazo wai ita zata gyara wa yan marayun ta,
Wazata nuna wa marayu nida tunda nataso banda kowa balle,
Wani irin kallo Joseph yai wa mutumin don jin maganar rashin imanin da yayi,
Hannun shi nazube cikin aljihun,farar wandon shi dayasa ya juya dakyau yana facing din mutumin,
Ya yanzu may kake so kai tunda kaji mutane sun sheda cewa filinta ne ita da yaranta,
Mutumi yace kadaina cewa filin ta fa malam kace filina,
Daidai loacin matar cikin kunar rai tace karya kakeyi muna fukin Allah,
Joseph ya waiga gurinta cikin hausar shi ya ce kai haba kibi a hankali mana mama,
Ya juyo gurin mutmin yace to nawa ne kai ka sayi filin malam,?
Mutumin yadan yi dumm can kuma sai yace wai dubu ashirin da biyar,
Wani mutum dake gefe yace kai malam Bawa, dubu goma sha biyar fa aka sayar ma,
Joseph yadaga masu hannu yace Ok yanzu fadi muji nawa zaka sayar mata ita da yaran ta,
Nan da nan gurin yai tsit ana sauraren su,
Malam Bawa yadan yi tunane can yace in an saye hamsin na sayar in ba asaya ba shikenan ni inada abin yi,
Matar takara sa kururuwa tana cewa Allah ya isar mata ita da yaranta akan mutumin da kuma kanin mijinta,
Nan da nan gurin ya shiga hayaniya kowa na fadin albarkacin bakin shi,
Joseph yakalli mutumin yace mai in bazaka damu ba zan baka dubu talatin yanzu gobe ka turo in karasa maka sauran don ban fito da kudi ba,
Ai ba laifi inji malam Bawa nan da nan mutane suka kama cewa wai kada akara mai ko kwabo abarshi hakana macuci, kawai,
Gurin matar Joseph ya karasa yace mata mama nawa kudin hanyan ku tace mai dubu daya da dari biyar ne wata uku,
Dubu biyar yabata yace taje tabiya haya saura,tasayi abinci suci
Zuwa gobe zai nemay ta, zai san yadda za,ayi,
Yazo zai wuce yaji wani mutun yanawa wasu mutane bayanin cewa Saida Dan kahirin can ya taimaka mata yaba malam bawa kudin shi,
Duk da rashi ya baci murmushi kawai yayi ya tqre mai achaba da hannu ya hau yana cewa kaini Green Land,,,
Ya samu majalissar su KB ta cika anata hira saman wani tabar ma wasu kuma zaune a saman wani benci,
Gefe guda ya samu a saman tabar man yadan kwanta rigingine fuskan shi na kallin titi yana kallon masu wucewa,
In akwai abinda maryam taki jini a rayuwar ta shine idan zasu wuce ta iske wanan majalissar ta cika,
Duk da bata kallon gefen su amma tana tsarguwa don ji takeyi kamar duk ita suke kallo,
Tunda ta tun karo gurin taga sun cika duk sai taji ba dadi aranta don haka sai ta dan kara sauri tana rike da hannun Issalam,
Shiko Assalam na bayan su yana shuka tsiya wai bazai tafi ba don haka suka dan yi gaba suka bat shi,
Saida yakawo dai tsakiyar inda majalissar matasan yake ya yanke jiki yafadi wurin kalle kallen shi,
Aiko ya yanka wani irin ihu kamar wanda aka zare wa rai,
Duk wanda ke gurin saida ya waigo inda yake kwance cikin kasa yana faman kurma ihu,
Wasu daga cikin yan majalisar suna ce mai tashi ma na wani kuma na ce mai dan nema wurin shegen kallo har ka fadi,
Dole Maryam tadawo baya ranta duk a bace,
Joseph dake kwance yana kallon tun gilmawan su maryam har zuwa faduwan yaron wanda yai tuntube ya fafi kasa,
Yataso daga inda yake kwance,yazo inda yaron yake yanata tsala ihu,
Daidai lokacin Maryam ta iso gurin,
Tadaga hannu zata kai wa Assalam duka a baya hakan yai daidai da tarewan da ,Joseph yayi sai ta samu hannun shi,
Wani irin kamshin turaren,THE ne ya daki hancin ta ba shiri ta mike tsaye daga tsugun nin da tayi,
Shikuma Joseph ya dago da yaron daga inda yake kwance cikin kasa, yana dan kakabe mai rigar shi da ta baci da kasa,
Maryam dake tsaye tana ce mai bazakazo muje ba ko sai mun makara,
Joseph yadago faren idon shi yadan kalleta ya ce ki tafi zan kawo shi,
Shiru tayi tana nazarin mutumin kafin tayi kwafa ta wuce tana mai jan hannu Assalam tana gunaguni,
Hannun yaron ya rike suka shiga cikin green land super market, tare can ya fito da yaron dauke da yar leda shake da kayan kwalama,
Inda ya rike mai hannu zuwa inda yqga yara madu irin uniform din su na shiga,
Har bakin get din islamiyar ya aje yaron inda yadan rage tsawo daidai ta yaron yana ce mai to abikina shiga kayi karatu abinka kada kaba kowa chuculate din da da biscuit, kaji,
Yaron yadan kara goge busashen hawayen dake makale a idon shi da bayan hannun shi yace har da anty ko da,Issalam?
kada mai kai Joseph ya yi waban karon alamar ya gaji da rigimar yaron,
Yace mai duk kan su karka ba kowa, daga haka yada ya wuce shiko Assalam nata dago mai hannu,
Yana komawa gurin yaji Inus nacewa wai ina Joe ya tafine, ko dai har yanzu yana gurin rigimamayn yaron nan ne,?
Ganin da sukayi mai dawo wa yasa sukayi shiru,
Isowar shi yayi daidai da zuwan wasu mutane su uku a saman mashi,
Yan tsofine mutun biyu sai wani matashi da yajawo su,
Kowa dake gurin saida yai mamakin mai yakawo tsofin gurin su,
Mai mashin din ne yai ma yan dattawan nuni da Joseph yana cewa gashi nan ai,
Daidai lokacin da mutanen sukayi wa wa yanda suka tarar sallama, cikin daga hannu,
Sai dan shiru ya biyo bayan hakan na wani lokaci,
Shima Joseph mamakin nuna shin da akayi yake yi a lokacin,
Cikin mutanen mutum gufa ya fara bayani kamar haka,
Malam yat uwqr muce tasa may mu da kuka dazun take sheda muna abinda yafaru,
Ai duk wanda ke gurin saida gaban shi ya fadi da jin maganar mutumin
Don su azaton su wani abu ne yafaru, da wata da Joseph din,
Mutumin ya cigaba da cewa shi ne muke tambayar kokai waye sai wanan saurayin yace muna shi yakawo ka nan,
Mu zo ne muyi maka godiya a bissa arin taimakon da kawai hajjo,
Mungode kwarai Joseph yace kai haba baba aida baku taso ba wallahi da kubari kawai ba komai,
Ai taimako yi wa kai ne, ba wani abu ba,
Koda yake zuwan naku nan yai mun da dadi sosai
Ammmm KB zo don Allah KB dake zaune a kusa da inda ya tashi ya zo kusa da yan dattawan,
Joseph yace don Alkah zaka samo masu gina sai a nuna maka filin aja ma matan da yaranta daki hudu da katanga,
Ai sai yan dattawan na kokarin hada baki gurin cewa Allahu Kbar,
Yaro halan kai dan gidan waye agarin nan don ban mu san ka ba
Wani habibu ne yai saurin cewa dan gidan Ema mai manjane tsohuear kasuwa,
Da mamaki suke kallon shi gudan mutumin yace ikon Allah,
Dan gidan Ema kuma tau Allah ya kyauta ,,
Mungode kaji Allah ya haskkaka zuciya, dukbda bai gane nufin su ba yadai ce Ameen,,,
Mutanen da zasu wuce ya basu dubu biyu yace su biya mai achaba,
Sai bayan sun wuce ne yadan yi ma abokan nashi dan bayani breifly,
Daga haka bai kara cewa komai ba,duk maganar da kowa keyi yana ji amma bai tanka ba,
Shi baima so kowa yaji wanan zancen daya yafaru ba in badon
Wa yan nan dattawan da suka zo wai yi mai godiya ba,

Tun shigowar su gida, yafara kiran mummy zo kiga kayan da aka sayo min ance inci ni kadai bada kowa ba,
Maryam da ta shigo rike da hannun Issalam ta wani zunburo baki gaba tana cewa wallahi anty in har Assalam na muna haka ni bazan kara zuwa dashi makaranta ba,
Dariya maganar maryam yaba a yayan nata, tace idan baki je dashi ba, ai sai ya zauna dama kece mai daurewa karya ai,
Nan Maryam taba yar ta labarin abin da Assalam yai masu hannu takuma mika mata ledar kayan kwalamar da aka sai mai,
Uwar ta karbe ledan tana cewa aiko bazai sha ko kwara guda daga ciki ba, tunda abin da yayi ke nan,
Anty Dije takarbe ledan ta shiga dashi dakin ta,
Wani sabon kuka yasa yana kokarin turje turje a kasa,
Maryam ce tabi bayan anty da sauri tana fadin dan Allah kiyi hakkuri yaya,
Abashi gobe ba zai kara ba, ai,
Da mamaki anty dije ke kallon Maryam ce ta langabe kai kamar zatai kuka don ankarbe ma Assalam kayan shi,
Sai kace ba ita bace ta kawo karan shi yanzu har tana ikirarin bazata kara fita dashi ba,
Murmushi tayi tana cewa kai Maryam abarki kawai daidai lokacin da maryam din ta karbi ledan a hannu anty,
Ido anty Dije ta bita dashi tana murmushi acikin zuciyar ta tana yaba irin son da yar kaunar nata takeyi wa yaranta,,,,,,,,,,


Afuwan ba yawa pls,,,,,,,



ZEEEE MAKAWA
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
5⃣
BY
ZAINAB IDRIS MAKAWA
🐎HUGUMA GROUP🐎


Maryam Abdullahi bobi, diyace ga malam Abdullahi bobi,
Asalin , Mahaifin su daga wani kauyen kwantagora suke wanda ake cewa kamfanin bobi,
Su malam Abdullahi yan asalin can ne saida zama yakawo kakanin su a cikin garin kwantagora da a cikin jahar Niger State of Nigeria,
Sana,ar maihafin su shi ne saida kayan masarufi a cikin kasuwa,
Yana da mata biyu inna hussai da maman, tunga,
Saidai da dadewa can ya, auri wata yar uwar shi daga bobi, saidai gaskiya babu so a tsakanin su ,
Don tana da wanda take so a can bobi, don haka ta tada hankalinta bata zauna,, auren bai dauki wani lokaci ba ya mutu,
Ashe akwai rabo a tsakani don haka aka samu cikin maryam,
Bayan haihuwar maryam ne tai wani aure anan cikin kauyen Kampanin Bobi,
Tunda aka haifi maryam sau guda aka taba zuwa da ita gidan mahaifinta,
Duk yarinyar na ran malam Abdullahi amma yasan cewa kawo ta cikin iyalin shi wani sabon fitina ne,
Saboda sun riga sun tsani uwar Maryam har abin ya shafi yarinyar don zuwan da akayi da ita ko kallonta ba wanda yayi,
Sai Dije ce kawai taita nan, nan da maryam din tana nuna kulawar ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login