Showing 39001 words to 42000 words out of 255288 words
Chapter 14 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete
din shi yanayi yana gyaran dan farin glass din da ke man,ne a fuskan shi,
Saidai a cikin zuciyar shi maganganun yariyar dazu ke mai yawo a kwakwalwan shi, yana jin muryanta tana fadin ,,,,
Allah yabashi dama saidai shi yana amfani da wanan baiwar yana cutar, da,diyan mutane dashi,
Yau ko karyawa ban tsaya nayi ba saboda kawai in,samu shiga kafin time din shi yayi sai,dai abin hawa yaban matsala saboda, minti biyu, kawai kacal, na kara
Shine ka gan,ni ana ya hanani shiga, saboda daukar alhaki
A cewar wanan yarinyar da ke ta fadamai magana tsakani da Allah
Kai ya girgiza da yakai nan yana mai furzar da wani irin iska daga bakin shi,
A gaskiya wanan maganan ta soki zuciyar shi don dan abu kadan kejawa mutun matsalal rayuwa,
Shi baiyiwa mutane uzurin matsalal suba taya shi Allah zai sa wani yai mai nashi watarana,
Idan ma har bai yi nasiha ba sai wani yazo yayi don komai dadewan ka a wuri dole watara bakai, bane a gurin,,,
Ire,iren wanan tunanen yadinga yi a zuciyar shi yanayi yana kallon agogon dake daure a dogon hannun shi,
Dan tsaki yaja don rashin ganin yarinyar batazo ba balle ya karasa jin korafin jama,a akan shi,,,
Maryam ko wace sai kusan uku na rana tasamu kan ta sai a lokacin ta tuna cewa ,wani yabata appointment dazu da safe,
Bashiri cikin sauri tajuya zuwa block din da aikai mata kwatance,
A hankali ta kwankwasa kofar office din yana zaune hankalishi naga aikin da yake idon kafe da farin glass din dake idon shi,
Batare da yadago kai ba yake cewa mai kwan kwasawar come, in, batare da yadaga kai ba still
Da sallama abakinta ta shigo office din wani irin sanyi da kuma kamshi, turaren maza na Minkaeel, ne , ya,daki hancin
Sai da yaji muryan mace ce yadan dago kai yaga kowace,ce har zai maida kanshi ga abinda yakeyi
Ido biyu sukayi da maryam wace ke cikin shigar doguwar jallabiya sai dankwalin da ta yane fuskanta da shi,
Wanda iya round din fuskantà kawai zaka iya gani ,duk sauran jikin ta a rufe yake lif,
A hankali cikin dishasshiyar murya take gaishe shi cikin ladabi,
System din dake gaban shi yadan rufe kadan ya na mai fuskantar ta,
Cikin kujeru biyu dake office din suna fuskantar wanda yake zaune ya nuna mata,
Malam kayi hakkuri pls sai yanzu muka , fito, daga lectures,
Cak taji numfashin ta ya tsaya daidai lokacin da tai tozali da wani dan prem dake kafe a gaban tebur din shi
An rubuta da wani ruwan gold cikin wani sallo A,A MASUGA,,,,
ZEEE MAKAWA,,,,
[2/20, 10:24 PM] ‪+234 806 595 8685‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
1⃣8⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA,
A,A masuga ido ya kura mata batare da ya dauke kan shi ba don ganin irin re,action din da tayi lokacin da idon ta yakai ga prem din,
Murmushi yayi yadan gyara zaman glass din dake idon shi, dai dai lokacin yake ce mata,
A nutse, ya,ce,ya, sunan ki malama,, cikin wata irin tsadadar murya yake magana kamar bai son yi,
Kusan minti uku bata iya cewa komai ba har lokacin
Murmushi yayi shi ya fargar da ita daga dogon tunanen da tafarayi naganin gata a gaban hukumar makarantar an gurfanar davita akan sai takawo shedan cewa A,A masuga mugune,
Kara tambayar ta yqi yana mai cewa ,cewa nayi ya sunan ki ne, ?
Murya kasa,kasa ta furta cewa Maryam Abdullahi, Bobbi,
Jin yayi shiru tadan dago kai ta kalli inda yake cikin sauri ta dukar da kanta,
Don shima din ita yake kallo a lokacin,
A,dan kunyace ta furta don Allah kayi hakkuri ban san,,,,,
Hanni yadaga mata yana mai gyaran murya yace
Naji duk bayanin da kikai min dazu akan AA masuga
Maryam wace kan ta ke duke sai a lokacin tadan dago kai takara kallon shi a karo na biyu don jin da tayi tace A,A masuga,
Azuci kuma cewa tayi jidan rainin wayo ko har yanzu yadauka ban gane shine ba yaci gaba da shanmata na ,,
Kamar daga sama taji ya kira sunan ta in full,
Adan tsorace, ta dago kanta, saidai wanan karon fuskan shi a daure take tamau, bakamar dazun ba, daya dan sake ta,
Kai ta mayar kasa don ji takeyi gaban ta yana ba da dammmm,
Yace, naji dadin wanan maganar da kika fada min da don tun da nake ba wanda ya taba fada min cewa abin baidace,ba,
Nikuma azato na hakan taimaka wane ga dalibai, ban yi la,akarin cewa zai iya illikanta rayuwan wasu ba,
Kokuma in ci hakkin wani ta irin hakan da nakeyi ,
Yace kin san may ?
Kai ta dake kasa, ta girgiza mai,,
A hankali yaci gaba da mata yan tambayoyi , saidai wanan karon a kunyace take bashi ansa,
Sallama tai mai gami da bashi hakuri,
Yace haba dai ita taimakon shi, ta tayi tunda har ta iya fada mai gaskiya,,,,
Shiru yadan biyo baya sai shi A,A din ne ya ita cewa muje in kaiki gida don time yayi ko ,
Don kada ki rasa abin hawa,
A ranta tace wake kai ta gida da, da bata dare,
Amma a fili dan murmushi tayi, tana mai cewa da kabar shi ai zan samu bus,
Batare da yai magana ba ya mike tsaye, yana mai hada yan tarkacen shi a cikin yar briefcase din shi,
Maryam tarigashi fitowa yana biye da ita a baya don sai da ya tsaya yadan rufe office din shi,
Amma may suna fita fafir Maryam tace yabar shi kawai bazata shiga ba,
Saida ya nuna mata cewa bai son jayayya, sanan ta daure suka tafi, a cikin motar shi, kirar Peugeot NEW MODEL,,,
Tafe suke ba mai magana acikin su sai dai kidar da ke tashi a motar na siliado,
Sun kusa shiga gari ne yadan joyo inda take yana cewa,
Wani unguwa zamu tafi ne, ?
A hankali Maryam tace furta da ka sauke ni a round about kawai sai in karasa,
Batare da bata amsa ba ko tsaya yace wani unguwa pls, ?
Cikin ,ciki ta furta kwanar kuka,
Kwanar da zai sada shi da unguwar ya karya, daidai kusan uguwar ya ce gidan wa,
Illiyasu costume, kallon ta yakarayi da kyau don jin gidan da take,
Yace ke kaunar matar shine ko, kai ta gyada mai a hankali,
Daidai kofar gidan ya aje ta,
Ya ce toh nagode, maryam da taimakon da kikai min,yau,
In sha Allah zan gyara ga dalibai zaku samay ni masauki da rangwamay,
Kan ta na kasa cike da jin nauyi,
A hankali tace nima nagode malam da fahintar gaskiya da kayi,
Murya cike sa cike da amon murna yace ai ni ban san may zan kara fada kuma,
Ta bude gambun motae a hankali tafita shi kuma a hankali ya fara ribas da motar shi,
A nutse ta rika takawa har zuwa kofar gidan su, inda taga wasu a zaune, saida sun bada baya,
Kallonta yayi a glass din motar har tashige shi kuma ya harba yabar shi yan,
Zuciyar shi fam da tunanen kalaman yarinyar,
Har ta shige gida batare da ta lura da wanda ke wajen gidan nasu ba alokacin,
Shigewar ta yabi bayanta da kallon mamaki a ran shi yana mamakin yau she tagirma haka,
Maryam na shiga gida tasamu Anty Dije, tana aiki, taimata sannu da gida tafada Wanka don ta dan ji dadin jikin ta,
A marairaice maryam ta ke cewa Anty Dije, kamar mai shirin yin kuka
Anty tunda safe banci komai ba tun da na fita gida,
Yar karamar harara Anty ta sakar mata tana cewa, ,oho maki, danace ki tsaya ki karya ba ki ,kikayi ba waike kina dokin zuwa makaranta,
Yar guntuwa tsuki tayi tace kuma wallahi duk sakkon danayi ban samu lecture din ba anty,
Baki Anty ta tabe mata tace anfada maki ana samu cikin zafi ne,
Aikomay zakayi kayishi a cikin hankali, don rashin cin abinci na iya jawo maki ciwon ulcer,
Falo tadosa don ta zauna ciki ta ci abincin ta tana kallo,
Ganin mutum tayi a zaune yana cin abinci shi a hankali,
Juyawa tayi da sauri da niyar barin falon a lokacin, sai kuma tatuna cewa ba su gaisa ba don haka ta tsaya cikin ladabi tace mai ina wuni,
Da wata irin dasashiyar murya ya amsa mata, a hankali,
Sai ta juya kawai tabar falon ,shiko mamaki yaji kwarai da gaisuwar da yasamu cikin mutunci gare ta yau,,,
Wanan shigowan da su Joseph sukayi tare da abokan ahi shigowa ce ta musam man sukayi
Don bukin sallah da za,ayi inda matasa ke bukatar a bukin hawan dawakai wato Dubba,
Don haka basu samu wani zama ba sosai kamar yadda suka saba,
Don yawan zirga,zirgan da suke yi tsakanin birni da kauye gurin ganin cewa komai ya kammala,
Yau ma kamar kullun sun dauke shi zuwa wani kauye duk da shi kauwaici yake masu don ganin cewa suna kokarin sashi cikin al,umurorin su,
Amma shi gaskiya duk irin wanan abin bawai yadamay shi bane shi harkokin business din shi kawai ke gaban shi,
Amma a zuwa yanzu abin da yake gani gurin su jibrin da KB dama sauran abokan su yana bashi sha,awa sosai ,
Duk masifan da mahaifin shi zaiyi yayi mai sunyi mai preaching kala kala akan ya daina bin diyan musulumai,
Kawo yanzu, Yasa an gyara mai gidan mahaifin shi amayar mai dashi hawa biyu sai kuma katon parking space mai girma da saura guraren da ake samu masu kawata gida,
Amma duk wanan baisa Mr Ema kyale dan nashi ba, da fitinar ya daina tallafawa mutane musanman musullumai,
Yasa ma Joseph din ido ne kawai don yasan cewa Joseph din yanzu ya wuce sanin shi,
Wanan hurda da kuma al,adun da Joseph keyi na hausa baima ma Mr Ema dadi sam,
Yau ma kamar kullun cikin fushi yake wa dan nashi fadan cewa yaran hausawa sun asirce shi ne,
Saboda labarin dayazo mai cewa da gudun mawan Joseph acikin wanan gagarumin bukin da matasa ke ta kokarin hadawa don cigaban masarautar su,,
A fuce yace baya son Joseph ya kara zuwa garin yafi bukatar ya daina zuwa da ace yazo yana hurda dasu haka,
Wanan maganar harta kai Joseph yai yun kurin gina gidan shi inda zai dinga sauka inda yazo,
Sai da baban yaga cewa zaiyi hara sosai ya kuma kara bidan dan nashi sulhu,
Inda ya ke sheda mai cewa hausawa shu,uman mutane ne yana gudun nan gaba ne kada su ja,ra,ayin shi akan wani abu can,
Maryam wace yanzu, haduwar ta, da A,A MASUGA, yazama mata, wani sanadin alheri,
Don kwana biyun nan shi ke, zuwa da kanshi ya diba yagani ko ya karatun ta ke tafiya,
Tun maryam na dari,dari har ta fara dan sake jikin ta dashi suka dan fara sabawa,
Duk wanda yasan Maryam ada yanzu in ya ganta bazai sheda cewa ita bace saboda,
Tazama cikakiyar yar jami,a saidai har yanzu wanan hali nata yana, nan kamar da ba ta yawan kula samari kamar sauran yan mata,
Mutana suna zaton cewa ita, sister din A,A masuga ne,
Saboda yawan ganin da ake masu tare ko kuma yawan kulata da yake yi,,
Kwanan nan gidan Anty Dije cika yake yi sosai sasboda gab suke da fara program din su
Duk may neman Joseph indai yana cikin garin kwantagora a gidan anty dije zai samay shi saboda bai son su samay shi a gidan baban shi don gudun fitina,
Tafe suke tare da A,A masuga,,,,da wani abokin shi,, acikin motar shi sai faman waya yake, yi da alamar da mutanen gidan su yake waya don yadda taji yana bada ansa yasa tagane hakan
Yana gama wayan yai yar ajiyar zuciya tare da shafo sumar kan shi tundaga, fuska, zuwa baya,har kusan wuyan shi,,
Sai a lokacin yadan waiga inda maryam ke zaune hankalinta a titi, tana kallon yadda abin hawa suke ta zirga zirga kasan cewar yamma tayi a lokacin,
Maryam ya furta a kasalance kamar yadda yake kiranta kullun,,
Wanan, kiran shi ya,katse mata kallon titin da take yi tun dazu,
May yafaru naji kin yi shiru, ko , yadan kalle ta na minti guda,
Cikin nuna kulawar sa yace kan ki na ciwo ne, naga kin yi shiru,
Kanta ta girgiza tace a,a babu wani ciwon kai ,
Illa masu son yin bukin nan dake son takurawa rayuwan mu,
Ace bamu da hutu sam a gidan mu in har wanan dan Christian din yana gari,
Baki makam A,A masuga ya tabe yace lalai kam ku samu aiki,
Yace wai may ye alakar shi da ku ne, ma wai da naga ya na zuwa gidan ku duk lokacin da yake gari, gashi shiba musulmi ba ba bahaushe ba,
Batare da tai magana ba tai dan guntun murmushi irin na iya fuska, kawai,
Aiko kamar kar su karasa kofan sai ganin jama,a fam sukayi ana t hayaniya kamar ana wani buki,
Da kyat malam masuga yadan samu ind ya Parker motar shi a gefe don tafita,
Aiko idon jama,an dake gurin ca,aaa akan motar don suga ko waye zai fito cikin motae,
A hankali ta bude marfin motar tare da yin yar guntuwar tsuki wanda duk inda kake zaka ji,ta,,,,
Dan harara malam ya watso mata daga inda yake yana cewa
In bake ba wake gudun taron mutane ?
Batare da tace mai komai ba ta,kauda kai zuwa inda taga su Joseph zaune suna diban wasu takardu a hannayen su,
Diba guda tai masu takauda kai gefe guda cike da jin haushi, don wani iri taji a ranta,ganin yadda yake kokarin shige masu,
Koda A,A masuga ya tsaida mota tafita , ko kallon inda suke bayi ba nan tabi ta gaban su ta wuce kawai abinta batare da ta tsaya gaidasu ba,
Kamar may rada taji ya furta sunan ta a karo na farko ke nan tun sanin tada shi,
Wasu takardu yamika mata na cewa don Allah taba Anty Dije ta aje mai akwai wanda zaizo ya karba a gurin ta,
Kamar ta wuce don ita aganin ta yama raina mata wayo ,
A matsayin shi na kafiri, Arne, zaice zai ai,keta sai kuma fadan Anty ya fado mata a rai
Dole ta tsaya ta mika hannu ya miko mata, cikin rashin ko inkula,
Tana shiga rai a bace ta yi kokarin mikawa anty takardan tai shigewar ciki,
Ana cikin wanan hada,hadar shirin hawan dabar da suke yi wanda mutane sun hana Joseph din tare da mabiyan shi shakat,
Har su maryam dake tare dashi a gida koyau she zakaji ance ana wai sallama da Joseph din,
Ita dai maryam mamaki taje ji na wanan halin da ga mutane na kokari zubar da mutuncin su da Allah yai masu akan kwadai,
Don haka ko tana gida bata yawan zama a waje don gudun damuwar jama,,a
Yau malam A,A bai zo school ba yai tafiya zuwa wurin wani seminar da zasu a kwara state,
Mashi ta tare don komawa gida duk A,A din yace ya hada ta da wani friend nashi ya dinga taimaka mata, zuwa gida,
Amma ita maryam din sai taga cewa bazata iya bin wanan mutumin ba don kawai kariyar mutuncin ta,
Mai,mashin tatara ta hau, duk da tace mai kada,yai gudu da ita, amma kamar zuga shi tayi a lokacin
Haka yakw kokarin wuce motoci da ita a baya makale,
Daidai kwanar sabuwar junction suka hadu da motar yan matasan masu tashe agari,
Cikin wata jar mota haka kallo guda mai jan motar yai mata,ta kauda kai duk ita ma dai taji kunyar yadda take dane bayan mashi, mai mashi nata,gudu da ita,
Kallo mai kamar harara ya watso mata, wanda ita ma din kusan irin kallon ta watsa mai a lokacin, ta mayar mai da martani,
Kai Joseph ta girgiza don in a kwai abin da yai hating she yaga mace a saman mashin ana gudu da ita kamar bata san zafin ta ba,
Bai san har lokacin da yafurta a fili ba yace nonsense,kawai,
A rashi yake tunanen ya furta sai gashi ashe afili ya fadi hakan,
Jibrin dake gefen shi ya kyalkyale da dariya yace kaganeta