Showing 174001 words to 177000 words out of 255288 words
Chapter 59 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete
yasa ta kara tsinkewa,
Alwala tayi da niyar yin sallah idan ta idar sai ta shiga gidan su gurin baba, ta sheda mai,
Da sallamar ta tashigo gidan ta wuce dakin ta direct ta kwabe hijab din ta da sauri kamar yadda kishiyar mama ta ce mata tai saurin mayar da kayan ta gurin da suke,
Buta ta sura zuwa gurin alwala, sallah magrib ba, din kada ta makara,
Tana zaune bayan ta idar fa sallah tana lazimi taji shigowar yar nata,
Daga kofa ta tsaya tana mai tambayar ta da cewa ina ta tafi tun da safe, haka,?
School muka,shiga don yin submit din wani takarda, dake a hannun mu,
Amma maryam shine baza ki fada min ba sai ki bari ina yawon neman ki,
Kiyi hakkuri tace kawai sai anty dije ta juya batare da takara cewa komai ba,,,,,
Sosai wanan karon yai shirin shigowa don yasan cewa lokacin tafiyan Alhazai ya yi Insha Allah,
Shigan dare yaiwa garin a lokacin don haka bawai kowa ne yasan da zuwan shi garin ba,,
Gidan mahaifin shi ne ya nufa kamar yadda baba ya bashi shawara,
Zaune Mr Ema yake yana shan hantsi, safe dake karawa,jiki karfi,
Cikin mamaki yake kallon dan nashi ganin irin yadadda ya kara zama big man
Da gani abin duniya akwai su a gurin sun zaunu dam,
Duk irin yadda ya sha cewa zai dake aduk inda suka hadu da yaron nashi ya gwada mai cewa ya fita batun shi sam,
Zaune yake amma Yusuf din yana zuwa yadan rakwafo zuwa jikin mahaifin nashi kadan,
Bayan shi yadan bubuga yana mai baya yana ce mai welcome my Son,
Ba karamin mamaki Yusuf din yaji ba don jin abinda Dad ya ce mai yau,
Yaushe rabon shi da samun haka daga gare shi har ya manta da lokacin gaskiya,
Hamdala yayi azuciyar shi na samun wanan sassaucin da yayi gurin mahaifin nashi,
Bayan sun gaisa ne yakoma mota ya,dauko mai tsaraban da yazo mai da su,
Daga gidan nasu yakama hanyar zuwa gidan anty dije,
Gittawan motar shi da suka gani ne yasa su gane cewa ya shigo gari a lokacin,
Aminu wanda ke tsaye a kofan wani shago ya ji ana cea cewa
Dan iyamurin nan yashigo kenan kwanan nan akwai harka ke nan,
Cikin sauri Aminu din ya juya don yagan shi wani irin yai mai acikin mota yake zaune,
Binshi yayi da kallon mamaki har ya bace mai da gani, don yasan cewa tunkar shi akan a kan yaron nashi zaiyi wuya sosai,,
Gidan Anty ya yaron nashi daniyar zuwa ya karya zancen dan shi yanzu yana da wuya sosaiduk da yasan cewa bawai ansan da zuwan, n shi bane don haka ba,a yi komai dashi ba, sai dai yasan cewa bazai rasa mutumin shi ba ai watau ,kunu,
Duk da safiyane, Wasu Swiss pure cotton ne saye a ajikin ta masu saukin kudi, ne amma sun karbe ta sun kara fitar mata da kyaunta
Kunnun gyada yau suka dama saboda yaran sunce shi suke son sha, wannan lokacin,
Sallamar shi ce yasa yaran kurma wani irin ihun murna, a lokacin, a
Wanda ya jawo hankalin iyayyen nasu gare su, kowan su sai da yai mamakn ganin shi
Maryam wace tafito daga kitchen dauke da cups a hannun ta ganin Yusuf a tsaye tare da yaran yasa ta tai kamar ta koma baya
Sai kuma tadake takaraso tana mai sannu da zuwa,
Sau guda ya dan kalli gefen da take ya kau da kan shi cikin sauri,
Amma sai yaji gaban shi yai wani irin faduwa saboda ganin yadda ta koma takara yi mai wani fes a fuska,
ZEEE. MAKAWA
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
FUREN JUJI
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
7β£0β£
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI
Dan girman Allah ku tayani addu,a pls ina a cikin damuwa, πππ
IYYA,KA NA, ABBUD,DU WA, I YYAKA NAS,TA,INN,
Kusan maryam ce ta karshe gurin yi mashi sannu da zuwa,
A lokacin tana dauke da cups din kunun yaran guda biyu a hannun ta,
Mikawa ko wani yaro nashi cup din tayi ta juya da niyar komawa kitchen din,
Muryan Yusuf ne wanda ta dade bata ji ba yake cewa,
Maryam da akwai sauran kunnun dan Allah a san min,
Guri guda ta tsaya cak don sauraren a binda yake cewa,
Tana kokarin juyawa ne don ta debo mai, sai, taji muryan Anty Dije a bayan ta tana cewa,
Haba Yusuf azubo maka dai ko badai a san makaba,
Dariya yadan yi mai kama da yake yana cewa to ba, a dama shi da ni ba aikin ga zan rage maku quantity ko?
Zama Anty Dije tayi suka fara gaisawa yayin da maryam ta nufi kitchen kawai,
Tafe take dauke da tire da jug din kunu sai kuma wani giran ruwa mara sanyi da ta azo a sama,
Saboda shi da kan,shi ne yai mata bayanin cewa
Idan mutun yasha kunu mai zafi ko tea baya shan ruwan masu sanyi don gudun kamuw da cancer ciki,
Hakan yasa indai abu mai zafi zata kawo mai sai dai ta dauko ruwan da ba, sa a fridge ba,
A gaban shi ta aje tire din wanda dukawar ta yai daidai da juyowan shi, da sauri ya kau da kan shi gefe guda,
Saboda shakan numfashin juna da sukayi, inda turaren ta yadaki hancin shi,
Itama dai maryam daurewa tayi saboda mayattacen turaren shi mai dafe wa mutun a hanci idan ya shaka,
Duk taji kamahi shi har yabar gari da kusan yan kwanaki zakaji falon gidan su yana wanan kamshin nashi,
Jiki ba lakka ta juya da niya barin su amma kuma sai anty ke ce mata maryam wainar zamuyi ko an fasa ke nan,
Yusuf wanda ke zuba kunu a ciku. Cup yana jin an anbai waina sai cewa yayi masha Allah har na manta raboda masa,
Yar harara maryam ta watsa mai ta wutsiyar ido tace,
Cikin wata irin narkarkiyar murya Anty da dai mun barshi kawai ayi wani abin,
Daga Anty har Yusuf dariya sukayi saboda sun gane nufin ta,
Anty Dije tace maryam ke muguwa ce ko don kin ji kanina yace yana son ci zaki mai kurulla akai,
Sai kuma jikin maryam din yai sanyi don an gane nufinta,
Sai cewa tayi nifa Anty ba don shi nace haka ba gani nayi dai kamar baza aci bane kawai,
Waye ba zaici ba maryam abin da muka kwana da niyar yin shi sai dai in kece kika fasa ci din,
Maryam ta juya jiki ba kwari ta fada kitchen girkin miya tafara dorawa tukun,
Miyan kaji ne yaji agushi, sosai a cikin shi sai kuma ta dora farfesun kayan cikin rago a dayan murhun, tafara yin hadin masa,,
Sosai masan yai kyau don tunda dare ta jika danyen shinkafa a ruwa bayan ta gama hada miya, sai ta je ta tsamay shinkafan a ruwa tasamu wani roba mai marfi ta sa aciki,
Ta dauko flower da yis da baking powder ta zuba ta dan sa ata rudu danye kadan sai kuma yan gurorin shinkafa kadan,
Almajirin su da ke masu wanke, wanke da yan sauran aiyuka tabawa yakai mata nika,
Kafin ya dawo ta dauko man suya da duk wanin abin da zata bukata na masa a kusa da ita,
Ba,a wani dade ba yaron yadawo daga gurin nika nan maryam ta zauna tafara suyan masan
Yayi fari yai kyau ba tsami ko kadan kuma yafita za kyau,
Sai da tagama soya masan sanan ta koma takan farfesun da take yi na kassan rago,
Kusan lokaci guda ta kammala komai ta ajiye, a cikin kula,
Daki su ta fada tai wanka takara fitowa wata fes da ita, kamar ba itace tai wanan aikin ba
Azaton Yusuf maryam ba zata yi masan ba ne don baiga tana da niyar yi ba don haka ya mike yana cewa Antyn shi,
Shi zai tafi idan ta gama masa zai dawo anjima yaci,
Anty ce take ce mai ai har angama ko tun,dazun ko,
Maryam anty takira don ta zubawa Yusuf masan, kafin ya wuce,
Duk a zaton shi ko wasa sukeyi mai sai kawai yaga shigowan maryam dauke da kulolin abinci,
Mamaki ne yakama shi don ganin har maryam ta canza shigar ta, ashe daga dogon riga ta koma zani da riga yar atamfa, Ghana, din dan dagwas a jikin ta,
Ta durkusa gaban shi tana kokarin aje kulolim abincin, da ta shigo da su,
Idon shi fes a fuskan ta don har ya manta da cewa anty na gurin,
Anty dije tamike tana cewa maryam dan Allah zuba mai ibda leka nan gidan hafsat yanzu zan dawo ,
Yadda anty tabarta a durkushe tana kojarin aje kulun hakan ne ya bashi daman karewa maryam din kallo,
Lumshe idon shi yayu ya koma saman bayan kujeran yadan kara bayan shi,akai,
Kamshi turaren da tasane ya shiga hancin shi sosai ya shake shi ya koma bude idon shi da sauri,
Cikin wani irin murya maryam taji maganar shi a kunnen ta yana cewa acikin lumshe ido kamar na mai jin barci kin yi kyau maryam ,
Kamar a mafarki taji wanan maganar don bata taba zaton jin haka gare shi ba,
Sai kuma ya daure fuska tankar bashine yai wanan maganar ba,
Daga kai tayi cikin jin nau,yin shi sai sukayi ido biyu da junan su,
A sanyaye maryam tace mai tana mai bude kulalan waina taje tanbayar shi guda nawa zan sa ma a plate,
Baki ji may nace bane maryam yakara tambayar ta ido a cikin ido,
Hawaye ne ya gan garo daga cikin idon ta zuwa fuskan ta,a hankali,
Saida ya dan lumshe idon shi yadan hade wasu miyau da suka tsaya mai a wuya,
Sanan Yace, haba maryam bana son ganin kin bata wanan kwaliyar da hawayen ki
Fitan hawaye daga idon ki tankar rage wani sanadari ne daga cikin jikin ki,
A sanyaye cikin murya kuka tace uncle kayi hakkuri kai wa baba magana a kai na pls,
Ido ya kura mata a lokacin da take wanan maganar,
Ji yayi tankar ya rungumota ba don komai ba sai wani irin mugun tausayin ta da yake ji a lokacin,
Sai dai a gaskiya bazai iya yiwa mahaifinta musu ba kamar yadda yaga tanayi,
Ita kanta yasan dalilin yin hakan nata bai wuce irin halin da surutun mutane zai jefa ta a ciki bane na yadda da auren shi da zatayi,
Don har yanzu al,umma suna mai daukar bai musulunta ba don basu daina nuna mai kyamar kabilanci ba,
Amma sai kawai ya nuna mata cewa shi din na mijine kuma babbane don hakane ya yi kokarin tursasa wa zuciyar shi son ta har kuma zuwa yanzu din yaji cewa ya kama da son ta din,
Don haka ayanzuma yarinyar tausayi taba shi ta re da jin wani irin mugun sha,awan ta da son ta kamar ranshi zai fita,
Haka kawai wanan ganin da yai mata yadinga jin wanan bakon yanayin a gamay da ita,
Ya dan rintse idon shi na dan wani lokaci sai kuma ya bude su still maryam tana durkushe a idan take ,
Ya mika hannun shi a hankali yadafa hannunta dake a saman kulan dake gaban ta,
Jin hannun shi a saman nata yasa tadan cira kai takai mai kallon ya hakane ?
Ya kalle ta a san yaye don shi da kyat yake bude su, yace
Maryam tun ranan da baba yai muna wanan zancen baikara ce min komai ba a kai,
Amma ke har yanzu kinki bari zukantan mu su zauna lafiya akan zancen
Maryam ta kara runtse idon ta lokacin da taji yace mata hakan ga,din,
Kenan ma ahida ba mahaifin shi ba yai biyayya akan zancen sai itace mace kuma diyar ahaifinta wanda shi yakewa ikirarin yaiwa biyayyan akan maganar shi,baba din,
Zuciyar ta takama mata sake,sake a lokaci guda ta rintse idon ta akaro na barkatai dan tsugunin ta a,gurin,
Wani irin damuwane yashige ta alokaci guda har ta dan dinga jin zazzabi na satan ta,
Kallon ta yayi cikin tausaya mata yace ki tashi maryam kada kafan ki yai ciwo,
A hankali cikin raunan,nan murya tace barin sakama masa a plate tukun,
Ya ce to nagode maryam da kulawar ki insha Allah biyayyan ki bazai zama na banza ba,
Taci gaba da zuba mai miya asaman masan da tasa mai kwara uku,
Ta mika mai tare da jawo cup din ruwa agaban shi tana kuma bude mai kulan ferfesun kassan ragon da tayi,
Hannun shi ne ya dan kara taba nata ida daidai lokacin da take kokarin tashi a gurin, shi kuma zai dauko spoon,
Tsikan jikin ta ne ya tashi yarrra ta zamay a hannkali gami da mikewa don barin gurin,
Kallo Yusuf ya bita dashi har zuwa kofan fita falon da ta nufa,
Kitchen takoma ta gyara sauran kayan da ta watsar gurin hada mai abincin,
Falon ta leka ko yagama sai dai ta sha mamakin ganin ko kwaya biyu bai iya cinyewa ba yana ci a hankali,
Tambayar shi tayi da cewa ko masan bai mai dadi bane a baki ,
Bai amsa mata tambayar taba sai dai bude mata kulan dake agaban shi ya yi sai taga ya cinye fiye da rabin masan,
Mamaki maryam tayi don sam bata san zai iya cin masan ba,, sai gashi yabuge ga cin yawa,
Har zuwa lokacin da ya gama cin abincin anty bata dawo ba,
Dama ya riga yagane plan ne yasa ta fita tabar su,
Tambayar ta ya yi da cewa ke bazaki ci abincin bane, ?
Duk da wani irin mugun nauyin shi da kunya da takeyi,
Kai kawai ta iya dan girgiza mai ba tare da tai magana ba,
Mikewa yayi ba tare da yai mata wani magana ba yanufi kofan fita daga falon,
Saida yakai kofan fita batare da ya juyo ba yace mata na gode sai an jima ko?
Inda ya fita yabar ta rakube anan gurin antyn ta tasamay ta tazubar da hawaye,
Kallon ta tayi cikin tausayawa yar uwan nata, tambayar ta takeyi ko may ya faru,
Tana share hawaye take girgiza kai gami da furtawa a hankali da cewa ba komai,
Yasha kwana round about da zai kai shi unguwar sabon gari ,
Sai ji yayi ana kokarin tsaida shi kamar kada ya tsaya saboda a saman hanyane gashi naida security , atare da shi duk da yasan cewa, ba,abinda zai faru da shi acikin garin kwantagora yanzu din,
Guri ya samu yai parking din motar shi a hankali ya sauka saman titin,
Fuskan da yagani sai yake tunanen ko a ina ya san shi,
Gaisuwa sukayi acikin mutunci inda yake tamayan Yusuf din da cewa yazo lafiya?
Lokacin da ya,ke ko karin tambayan shi kowaye shi,
Sai yaji mutumin na fadin kamar baka gane niba,ko ?
Ga kwanaki nai ma waya akan zancen Cikin da Ejoma tayi,
Wani irin kallon mamaki Yusuf ke binshi dashi sai cigaba da fadi mutumin ya yi ,
Ina da tun farko ka fada mincewa duk wanda ya aure ta zaka kashe mai wanan dukiyar aida an aure dani,
YUSUF ke mamaki a zuciyar shi irin yadda wanan mutumin ke maganar shi wani kamar mara hankali,
Yanzu so nake idan da akwai abin da ta haifa har zan karba,
Sai kai min wani dan ihi sani kaga sa in toshe bakin duk wani wanda zai kawo min cikasa ga ala,amari,,,
Zaici gaba Yusuf yadaga mai hannu yanna na cewa ka kai ni koto ina ga zaifi ,
Ya juya kawai abinshi batare da ya ji mai zai ce mai ba ya shige motar shi ya bar gurin,
ZEEE MAKAWA YALWA
[4/10, 6:23 AM] 0mmer Farouk: πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
FUREN JUJI
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
7β£1β£
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI
AL,HAMDDULLILAHI RABBIL AL,LAMIN
ADDU,AN KU AGARENI NAGODE SO,SAI YAN UWA MUSULMI IRIN YADDA NAI TA GANIN SAKON TAYANI FATAN ALHERI, NAGODE MAKU KWARAI DA GASKE, ALLAH UBANGIJI YA BIYA DA ALHERIN SAπ
Tukin mota yake amma zuciyar shi ta na gurin tunanen halin rayuwa irin na Aminu masuga,
Duk da yadda yake daukar kan shi bakon shiga cikin addini
Kamar yadda mutane da dama ke mai wanan fahinta, cewa bai san komai ba akan addini tukun,
Hakan ba zai sa shi yin wani abinda zai kas,kantar da kanshi gamay da addinin shi ba irin haka,
Mutum yasan cewa ya aikata zina amma saboda rashin sanin kaidar sharia har yana ikirarin cewa idan za, a bashi wani dukiya mai tsoka zai iya fitowa fili yai ikirarin cewa shike dan da yai rejecting da farko, saboda kwadayin duniya kawai,
Kan shi ya girgiza don takaici da abin da wanan