Showing 246001 words to 249000 words out of 255288 words

Chapter 83 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1351

taci ga ba da basu labarin akan yadda tasamu kan jibrin yagigice a lokaci guda duk da mahaifin shi yace kada yayi wanan aure amma ido rufe yace sai yayi,,,,,,

Musalin karfe biyar na yamma suna zaune a falon su na kasa
Maryam ta sayi da wani dogon riga english wear,
Ringan yadan fitar mata da dan suran jikin ta don har dan matashin cikin ta yadan fito
Yau saboda ta sauko, kasa,Pipkin ne, ya matsawa maryam sai ta,zo su yi game,
Wayan tai yai kara ta dauka don ta diba, wa ANTYNA tagani an rubuta baro,baro,
Mamaki ya kamata,saboda ganin kiran wace tadade tana mamakin rashin kiran ta,
Anty tafadi a,lokacin da ta dauki receive din wayan nata,
Maryam ya kuke ya mai gidan naki, saida maryam ta lumshe idon ta saboda wani farin cikin da ya ziyarci zuciyar ta, don yau taji dadin sautin muryan yar na ta,
A lokacin Yusuf ya karaso falon cikin shigar shadda assh mai haske,
Ganin yadda maryam take waya acikin jin dadi yasa shi mamakin koda wa take wanan wayan,
Cikin dan murmushi yaga tana miko mai wayan, cikin jin dadi,
Karba yayi yasa a kunen shi ya mai yin sallama cikin tatausar harshe,
Muryan anty yaji tana mai sheri ce mai baban baby,
Sun gaisa da murna dajin dadin adduan shi yakarbu na ,
Yamikawa maryam din sundayi hira take fadawa anty cewa ai anbata bed rest ne yanzu haka
A nan Anty taima maryam din warning akan don Allah ta kula da kan ta sosai,
Dadi sosai maryam taji na kula ta da yar uwan ta tayi yau din,
Abinda tunzuwan ta Abuja aure bata samu ba daga gare ta,
Duk irin wahalan da maryam ta taso aciki bata taba nuna gajiyan ta ba,
Wai sai yanzu ne yar uwan nata zata bata baya,
Dadi sosai ya rufe Maryam din bayan sun gama waya har Safiya saida tai mamaki,
Nan tace nikan nasan cewa da akwai abinda yafaru da farko kin ko ga yadda ranan Anty ta rufe ido ta zazaga min masifa cewa wai ai taji
Dake dani mun hada kai sai munga bayan auren ta
Saboda ina son auren mijin ta na saki a hanyar cuta mata,
Kuma kince wai duk tazo gurin ki bidan abu bayan bautan da tai tasaki agidan ta sai kin mata wulakanci,
Don yanzu kinfi karfin ta, babu abinda zata iya gwada maki arayuwa,
Daga maryam har Yusuf saida sukaji wanan maganar acikin ranan su,
Maryam kan hawaye ne yadan zubo mata saboda bacin rai,
Yusuf wanda ke shirin fita mai gadin shi yashigo yana ce wa ogan nashi yanada bako awaje,
Umar sultan ne yazo gidan motar shi kawai zai isawa mutun shi wani ne
Sun gaisa dashi inda yaiwa maryam text zai shigo da bako yanzu,
Da sauri suka hau saman stari koda suka shigo basu afalon sai Pipkin kawai,
Abin sha da motsa baki aka kawo wa Sultan din yana cine yanaba Yusuf labarin bayan rabon su,
Bai boye ba yace kuma yana ganin cewa alakar su zai tashi don dai shi kaunar matar shi da yagani yake so,
Dariya Yusuf yai mai yake cewa ai baza ta iya zana dashiba da matar shi baturiya,
Nan yake fadawa Yusuf matarshi ta yi accident ta rasu tabarshi da yarinya yar shekara uku,
Yusuf yaji tausayin shi sosai inda yai mai gaisuwa mutuwan matar,
Umar yake fadawa, Yusuf cewa mahaifin shi da yan uwan shi yanzu sun sa shi agaba sai yadawo gida yai aure,,,,,,,,,,


ZEEEE MAKAWA YELWA

🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
9⃣8⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI,

ADADE A,NAYI SAI GASKIYA πŸ‘πŸ‘πŸ‘
GODIYA DA YABO SUN TABBATA GA ALLAH UBANGIJI SUBBAHANAHU WATA,ALA,
KARIN GODIYA DA YABO GA SHUGABAN HALLITA ANNABI MOHAMMAD S,A,W,,
ALLAH MUNGODE MA DAKA TARAMU A WANNAN GIDAN MAI ALBARKA NA TSAWON SHEKARU BIYU CIF CIF YAU, πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘
KOMAI AKA GINA AKAN GASKIYA GASKIYA CE TAKIN SHI TABBAS GROUP DIN MARYAM SALISU MAIDALA GROUP MAI ALBARKA ACIKIN GROUP DIN HAUSA,,,

HAPPY TWO YEARS ANNIVERSARY πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚
MARYAM SALISU MAIDALA GROUPπŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘


Maryam cikin ga yadan turo izuwa yanzu duk wani kasala da nauyin jiki da take fama dashi yanzu ta daina jin shi,,
Izuwa yanzu tai wani girma komai najikin ta ya bunkasa gwanin ban sha,awa,
Gata yanzu duk inda jeri mata masu jida kan su suke maryam takai wanan gurin,
Ba komai dama ke karawa mace aji ba na farko shi, ne
Wadatan mijin ta indan har miji nada wadata shine ke sa mace tai saurin murjewa,
Bawai ana nufin wadata mai karfi irin na su Yusuf ba,aa,a
Duk irin wadan tan mai gida idan har mace zata samu agaji daga gare shi zaka ga matar rayuwan ta ya nuna cewa akwai shi,
Nabiyu kuma ita mace musam man matan yanzu zakaga cewa matan na kokarin su fi maza bidan abin rufin asiri,
Wanda hakan wani sabon rayuwane wanda boko yajawo acikin al,umman hausawa,,,,

Ganin cewa maryam ta samu lafiya sosai yasa Yusuf sakin jikin shi yanzu duk inda yake hankalin shi a kwance yake,,
Saidai kam masu kamfani median na cin riba dasu don ko da yaushe suna makale a waya,
Ana faman tambaya may kikeyi Maryam, ? Maryam kinci abin,? Maryam kinyi sallah ko, ?
Maryam bakyajin komai dai ?
Wanan shine aikin idan Yusuf yana gurin aiki ko yai wani tafiya,,,

Bukin chrismas yazo don haka kamar yadda Mr Emanuel ya umurci dan shi da cewa duk Christmas dole yazo gida ayi shi dashi,
Shiri sosai Yusuf keyi amma bai sa maryam a cikin tafiyan ba,
Asalima dai ita bata ko san da zancen zuwan shi bukin ranan haihuwan Isah almasihu ba,,
Wanan akidar haka akasarin iyayen da diyan su suka musulunta suke sawa diyan su wanan dokan,
Ko kuma suce akwai family meeting wandai yai dadidai da wanan lokacin,
Hakan zai sa dole musulman diyan su su zo gare su suyi wanan bukin kusan atare,
Alhamdullahi don ita addinin musulunci addinice mai sauki da fahinta,
Addini bai hana musulmi shiga church halatar bukin su ba,
Hakan ne yabawa Yusuf daman yiwa mahaifi shi wanan biyayyan don dai yasamu su rabu lafiya dashi,,

Waya yake yi da mahaifin shi yana fada mashi irin abubuwan da yake son yaron nashi ya sayo masu,
Ruth wace ke tsaye kusa da baban tana zuba mai ruwa zai sha maganin shi,
Tace cikin daga murya don yaji ta a wayan,
Brother you're coming with your ba,??
Yaji abin da tace sai yai murmushi kawai
Mr Ema ya harari diyar nashi yace wetting she go do if she came,?
Papa we go celebrated examas with her now,,,
Yusuf wanda ke jin su a lokacin idon shi kawai ya iya lumshewa don dai yasan yadace yaje da maryam don duk family su zasu hadu to amma wanan haduwar ta daban ce,
May zaicewa maryam din don zuwa da ita cikin yan uwan shi wani matsalane ,
Gama yadda yasan akidar ta tun tana karama da kyamar masu rashin sallah,
Amma bari dai ya gwada yagani idan har zuwan da ita zai zama alheri,
Bayan kuma yan church din su Mr Emanuel din suna faman gulman shi cewa ,
Bana bazai iya bada kyautan da yake bayarwa ba a shekara saboda dama da karfin dan shine yake wanan abubuwan,
Yanzu gashi danshi yafi karfin shi ya musulun ta har ma ya auri diyan hausawa ,,,
Ita,ko grandmother sai shiri takeyi don har gida akakawo tele ya auna ta, don ai mata din kuno ni,
Maryam dai iyakarta da su ido don ba a fada mata ga abinda ke nan ba,
Christmas din bana yai daidai da ranan jumma,a ne,

Yau tana saye cikin wasu purple din atamfa dinkisu umbrella, yadan matse mata cikin ta ta sama zuwa kasa kuma ya sauko yadan baje iya cinyar ta,
Ta daura dan kwali yai mata kyau ga kamshin turen da ta shafa da kuma body spray, tanayi
Tabaya Yusuf ya rungumota, inda yasa ta sauke ajiyan zuciya,
Wuyan ta yake dan sunsuna a hankali har zuwa kanta,
Maryam ta kwanto da kanta zuwa kafadan shi tana sauke ajiyan zuciya,
Hannun shi yakai saman cikin ta dan wata shidda ya shafa a hankali,
Cikin wani murya mai taushi maryam tace uncle,
Yanzu nake shirin zuwa in hada maka kayan ka da zaka dasu,
Kara jawo ta yayi zuwa cikin jikin shi, sai,dai wanan karon
Juyo ta yayi suna fuskantar junan su yana mai kara kai kanta akirjin shi yace ke kin shirya naki ne maryam, ?
Cikin mamaki da kuma sauri maryam ta dago kan ta tana kallon shi,
Cikin sauri kuma ta dukar da kan ta don har zuwa yanzu akwai nauyi da yar kunya a tsakanin su,
Uncle da ni zaku tafi ne ?
Kai ya kada mata alamar eh,
Kara noke kan ta tayi tasa hannayen ta asaman West din shi,
Habawa uncle shine baka fada min da wuri ba sai yau,
A hankali yaja hannun ta zuwa bakin gado suka zauna,
Yusuf yariko hannun maryam din yace da farko ina ganin kamar ba,zaki iya wanan dogon tafiyan bane,
Sai kuma yanzu naga cewa zan dan dade a can gara kawai in tafi dake don gaskiya bazan iya jure rashin yar matana akusa dani ba,
Kunya yaba ta inda har ta dan rufe fuskan ta da hannun ta,,

Sosai maryam din tafara shirin ta cikin , sauri daga Anty dije da mahaifin ta har matan shi,
Sai kuma mahaifiyan safiya din wace, ita ma an mata na ta kalan tsaraban tare da yaran Anty ta,,,

Tunda maman Choima tagane cewa da maryam za ai tafiyan take wa mutane masifa,
Don dai ita gaskiya wanan yariyar da ko yaushe take a cikin wanan abin da take ganin matan hausawa musulmai na rufe jikin su dashi,,
Sam bata son ganin maryam din a cikin irin wanan yanayin,
Yariya karama ta dinga rufe jikin ta ko a gida take ko a waje, kamar muguwa,
Ga su da yan matan IBO kuma Christian amma Yusuf ya kwaso wanan yarinyar, da bata da ko fara,a,

Yusuf tuki yake a hankali amma hankalin shi na agurin maryam,
Bai yarda ko wani driver ya jasu ba,shine ke jan su da kan shi,
Shida maryam a gaba suke zaune, maman choima da Pipkin, a baya,
Sautin kiraan Sudis ke tashi a motan Yusuf yana bin shi a hankali,
Maryam wace zuwa yanzu har barci ya dauke ta ga kuma sa yin Ac da kamshi tana shaka,
Maryam bata farka ba sai a tagina daidai lokacin da taji an sake express kwalta,
Farka wan ta daga barcin yai daidai da jin aman da tayi,,
A gagauce Yusuf yasamu guri ya parker motae sh,
Maryam wace har ta fara aman a lokacin tafito daga gefen dake sai faman sannu Yusuf ke mata,
Ji yayi alokacin kamar ya kama mata cikin don irin wahalan da yaga tananayi,
Maryam tagama ta dawo saman seat din motar tazauna tana cea wai,O, O Allah,
Subbahanallah inji yusuf cikin rudewa azuciyar shi kuma yana da yasanin zuwa da ita dayayi ,
A rude yake cewa may kike so maryam ko mu tsaya ki hutane, tukun,
Cikin girgiza kai jikin ta bata jin karfin shi ko kadan tace No uncle muje kawai ,
Yusuf baiso ba amma dole tasa shi jan motar a hankali
Ita kanta mama Choima itin yadda taga maryam nayi duk sai taji dan tausayin yarnyar a ranta,
Amma a fili sorry dear kawai take iya cewa, alokacin ganin jikan ta duk ya rude,
Gidan shi ya wuce direct dakowa da komai suna isa yasa maryam tai wanka don taji karfin jikin ta,
Barci tayi mai nauyi sai a lokacin hankalin Yusuf yadan kwanta,

A cikin barcin da tayi mai tsawo wanda har ya sata mantawa da inda take a lokacin,
Jitayi kamar muryan safiya akan ta,
Abinda yasa ta bude idon ta a hankali don ta gaskanta hasashen ta,
A gefen gadon taga safiya zaune a cikin damuwa,
A hankali tadan yi kokarin dagowa daga kwanciyan,
Sai alokaci tasan ba ita kadai bace a dakin muryan su Yusuf taji yana cewa ki kwanata mana maryam ki huta pls,
Nan zanbar ki da ita ina son zuwa gidan Daddy na ne,
Inda safiya take maryam tadan kala safiya tace ya jikin maryam,
Murmushi tayi wanan karin mikewa tayi gaba daya ta sauko da kafanta kasa daga gadon,
Yunwa nake ji safiya madyam din tafadi haka a lokacin da takai zaune da kyau bakin gadon,,
Abinci na nan da aka kawo maku daga gidan Anty,
Sosai maryam taci abincin tare da kurban ruwa, masu sanyi,
Yusuf yana tsaye yana jiran grandma don su tafi amma sai tace yabar ta nan kawai,
Don ba inda zata matar shi mai ciki bata da lafiya in ma har church zata sai ya kai ta daga nan din,
Ba karamin dadi Yusuf din yaji ba na wanan karamcin da kakarshi tayi saboda sh,
Godiya Yusuf yai mata sai cewa tsohowan tayi don may zai gode mata akan abinda yazama dole tayi,
Diyan shi jinin tane don haka dole taba da nata taimakon akai,
Muryan Yusuf da su maryam sukaji yadawo ne suke mamaki da murmushin shi ya zauna a bakin gado, inda take yana cewa,
Grandmother tace bazata gidan Dadd ba zata zauna a tare da ke ne ,
Murmushi marym tayi tace haba dai sai dai don kai,
Amma nikan ai garny bata zama don ni, yanuna cikin ta da hannu yace amma kin san kina rike da jinin ta ko?
Murmushi kawai maryam tayi batare da ta bashi ansannkomai ba,
Pipkin ne yashigo dakin cikin murnan ganin safiyan da yayi ,,,, ,
Hannu ta mika mai tana cewa my friend how are you,
Yana kallon ta kaman yana son tuna inda yasan ta acikin haka ya mika mata hannun shi,,,,

Yusuf zaune a gidan mahaifin shi suna gaisawa
Tsaraban su ne ya gabatar mashi dasu duk sai murna suke yi,
Mr Emanuel ne yake tambayar Yusuf ko ina maman Choima ?
A takaice Yusuf yace tana gidan shi
Zata zauna da matana da bata da lafiya saboda wahalan bin hanya da tayi,
Jin haka yasa Mr Emanuel bata fuska azuciyan shi wani hau,shi ne ya kama shi,
Sosai rayuwan shi ya baci don har ya kasa boye bakin cikin shi akai,
Yarinyar ta yarda ta haihu da kaine,?
Tambayar yazo ma Yusuf abazata amma sai ya daure yace wa mahaifin shi,
Addini na badon wani abu ake auren mutum ba munayi ne don Idda sunnan ma aikin Allah Mohammad S,A,W,
Jin haka yasa Mr Emanuel saurin daga wa Yusuf hannu, alamar ya isa hakanan,
Baison jin komai a gamay da addinin Yusuf din don daima kamar yafi Yusuf sanin al,adun musulmai,
Daga gidan mahaifin shi ya wuce gidan mahaifin maryam, saidai bai gida yana gurin da yake sana,ar sai,da icce,,,,
Yusuf har can ya samu surukin nashi gefen titi ya parker motar shi bayan ya kulle motar ya tsallako gurin da baba yake,
Ya kasawa wasu yara icce zai dora su a kai Yusuf ya iso gurin shi ya karbi iccen ya dora yaran,
Sai ya rusunna har kasa yana gaida mahaifin maryam din,
Mutanen dake gefen titin dama wa yanda ke a tsalake duk sukayo masu caaa da ido,
Kowa na kallon yadda mutum mai kudi kuma matashi yakewa malam Audu gaisuwa don ya bashi diya,
Daga can nesa wasu gungun mutane ke cewa inda malam bahaushe ne da bazai yi wanan ladabin ba don yana jin kan shi wani abu,
Sai wata mata ce ke cewa ai da shi yanzu yafi kowa sanin darajan mahaifi,
Don dai su kabila sun san girmama nagaban su balle ma wanda ya baka mata, ka aura,
Bencin dake gefe baba ya nuna mai yazauna amma sai Yusuf din yaki zama sam,
Daga inda yake tsugunne yake fadawa baba da maryam sukazo amma bata da lafiya amai taitayi a hanya kafin su iso,
Baba ya ce ashha asshha da sauki dai ko yadan sosa kai yace ai taji sauki don har taci abin ci,
To Allah ya inganta Allah ya raba lafiya inji baba din ,
Gidan Anty yawuce itama sun gaisa da ita sosai inda sukai ta labaran yaushe rabo aga juna,
Ta tambaye shi jikin maryam yace ai dama stress ne kawai ke ya damay ta don lafiya muka fito gida
Gobe ai zasu shigo nan zata wuni ai insha Allah don

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login