Showing 90001 words to 93000 words out of 255288 words
Chapter 31 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete
mai,
May zai sa bazakai zaman ka anan ba, kawai ka share kowa,
Don har na fara maka planing din din abin yi don ka kauda zaman banza,
Amma ni naga kawai gara kabar zancen komawar ka yanxu har zuwa wani lokaci zai fi,
Yadan dafashi yana mai cewa ya daure yaba su, dan time tukun kafin ya koma,
Wanan zance na Sonny abin dibawa ne sosai don hakan zai sa su dan fita zancen shi,
Amma kuma baya son yabar harkokin shi na can gida, sam
Don haka yakira KB da Jibrin tare da,wani babban amin nin shi amanar kulawa da harkokin shi in secret,
Bayan wata guda daga can ya wuce saudiya ya gabatar da aikin umurah,
Yaji dafin wanan tafiyar tashi so sai don yakara yin hamdallah da rayuwar shi,
Sosai suke business kamar a gida Nigeria suke, don Sonny mutum ne wanda bai ma natare da shi keta sam,
Ba karamin riba yasamu ba daga wanan zaman da yayi acan
Gashi ya murje yayi kyau yayi dan jikin jin dadi ba mai muni ba saboda yawan exercises,
Alhamdullah Anty Dije ta sauka lafiya,tasamu Da namiji wanda bayan sati akasawa yaro sunan Abubakar Sadiq,
Wanan sunan yaiwa maryam dadi sosai kasancewa suna A,A dinta ke nan,
Sosai akasha buki sai kace sabon haihuwa ne kamar na farko,
Inda Jibrin da KB suma sun zo har gida sun,wa Anty Dije barka
Shi kanshi maigidan wanan haihuwar ba karamin dadin shi yaji ba don ga haihuwa ga samun girma daya yi agurin aikin su,
Kayan goyo sosai yazo wa maijego da jariri da inda har dangin shi suka dan fara tsegumi akai,
Wai ta tare guri taki bari wata ta shigo itama tadan lakaci arziki,
Sai ita da yan uwanta ke cin abin su, ita dai bata biye masu ba sai harko kinta take yi kawai,
Anci ansha sosai agurin kamar yadda yakamata a duk wani taro,
Sai washegarin suna bayan an watse ne baba yazo da kamshi don ganin jariri
Maryam ce ta dauko mashi shi cikin showel, fari kal,
Bayan an gagaisa ne baba yaiwa yaron addu,a tare da yiwa uwa fatan gama shan ruwan zafi lafiya,
Sai dan shiru yabiyo baya, alokacin ne yadan dago kanshi cikin fuskan damuwa yana cewa anty wace ke tsugune gefe guda saman wani dan karamin kujerar mata,
Ya zancen maryam ne wai yaji shiru, dafarko yaji zancen rigirigi yanzu kuma yaji sakwot,
Dije yakamata ku mai da hankali kinsan dai in badon a gurin ku take ba ba,zan barta har takai haka ba ba wani matsayi
Don ni bokon bandauke shi wani abu mai muhunmanci ba ga diya mace,
Har wasu yan uwa na acan gida suna ganin kamar cewa nine ke ra,ayin tayi karatun bokom
Kinsan yadda nike da yan uwa na duk da bawai wani arziki ke gare ni ba amma ganin ina acikin gari har yanzu akwai hassada a tsakani na dasu,
Anty Dije ta dan gyara zaman ta datayi mai kama da tsugun ni ta fuskanci baba da kyau,
Tace baba gaskiya muma bamu so akai war haka batare da wani matsaya ba akai,
Da farko ya nuna muna agaskiya baizo da wasa ba,
Katseta baba yayi da cewa
To aimu,bamuga alamar hakan ba, saurayi yadade tare da budurwa har tsawon wani lokaci amma babu wani magana mai karfi aciki,
Gaskiya Dije idan har bazai wani motsa ba yakamata kufita zancen shi kada kice zaki biye wason ran yariyar nan,
Kodai ba yanzu za ai auren ba to ya motsa ma na asancewa,yana ciki,
Ya turo da manyan shi su shiga cikin harkan hakan zaisa kiwa yasan matsayin sa,
Daga anty har Maryam kansu na duke akasa don jin maganar da baba keyi acikin bacin rai,
Daga haka yamike yana cewa kunji maganata ke nan nafada maku nagaji da surutun mutane haka,har aciin iyayen ku ke Dije ina shan surutu,
Itama Anty Dije mikewa tayi alokacin tana cewa baba yayi hakkuri insha Alkah komai zai zo karshe badadewa ba,
Har baba ya bargidan kan maryam yana kasa aduke, cikin ladabi,
Daren ranan Maryam bata samu yin wani barcin kirki ba kamar yadda tasaba gatada karatun test nan da kwana biyu,
Saboda maganar tazo mata abazata don bata tsanmaci baba zai yi wanan zancen ba,
Washegari haka ta tashi bawani kuzari atare da ita saida Anty taimata magana sannan tadan sake ranta,
A makaranta duk yadda taso taboye wa safiya abin bai yiyu ba,
Don haka safiya sai taji kawai itama bataji dadin ganin aminiyar cikin damu ko yaushe kan zance guda
Gaskiya yau zata fada mata gaskiya cewa ta rabu dashi kawai takama masu zowa son ta da gaskiya,.
Don ko a kwanaki wani abokin Jibrin yai masa zancan ta,
Zaune suke a cafeteria su na son dan shan, drinks,
Maryam wace ta dade da lulawa duniyar tunane, ko bata ko san ida suke ba a lokacin,
Safiya tadan mata kyatci da hannu a fuska tadanzabura kamar wace taji tsoro,
Dan ajiyar zuciya ta sake tare da kallon safiya din tana kokarin kako murmushi,
Safiya tadan kai mata harara cikin murde fuskanta,
Wai Maryam mayke damun ki hakane pls,?
Tadan gyara zaman ta,tace bari kawai safiya wallahi ina cikin damuwa,
Tun jiya da baba yazo muna barka haihuwa,,
Dakata Maryam, wallahi ki,yiwa kan,ki fada ki danai irin wanan dogon tunanen kadafa ki jawa kanki matsala ina fada maki kullun,
Akan namijin daba ki tabbatar ko zaku zauna tare zaki halaka kanki,
Tadan kara nisawa tace ,baba yazo jiya yaiwa anty Dije tas akaina,
Maganar baba tajiya yasa nakara sanin cewa, A A ba sona da aure yakeyi ba kawai dai,yana son amfani dani, ne ya nunawa duniya,
Don haka maryam da kullun aitawa yar uwata fada akaina,
Gara kawai in rabuda shi in huta Allah yabani wani yafi min safiya,
Subbahanallahi maryam kada kuyi saurin fadar haka mana,
Nan da nan idonta yakawo hawaye, kamar zatai kuka,
Wallahi safiya hakan yafi min don bazan yarda kullun mahaifina yaita bata ranshi akaina ba,,
Dan shiru sukayi a tsakanin su, nadan wani lokaci
Safiya tace kenan kina nufn duk son dakikewa A,A ya tashi abanza kenan,?
Saida ta share kwalar da ya silalo mata tukun sanan tace,
Gaskiya kan safiya rabuwa dashi zaifi min
Yanzu ke maryam bazaki canza shawara,ba akai,
Ki tunkare shi kiji may yake ciki akai, ?
Maryam ta katse Safiya da cewa ,
Wani, ? Allah ya kyauta min, shi bai mun magana aure, ba nice zan masa,
Kawai dai fita batun shi, zanyi, yafi mun,
A,a maryam sam gaskiya, bai kamata muyiwa A,A haka ba kada mu kasa mashi uzuri pls,
Muzo mu kamashi da laifin daba tashiba shi baima san yayi ba,
Yanzu dai musan yadda zamuyi kafin lokacin don musan mafita
Amma dai kin san bazan iya tun,karanshi da wanan zancen ba,
Kadafa ki manta har yaya illiya yakirashi kan zancen amma sai ya doje kawai,
Shine yanzu kike ganin nizan iya tunkaran shi da wani zance can,
Kenan ma nice mai son ya aureni bashi ba,,
Kai gaskiya duk zancen ya,daure min kai wallahi,
Amma ki barni dashi kawai zan san yadda mukayi dashi,
Sam bazan nuna mashi cewa ma kin san da wanan zancen ba,
Maryam takara goge hawayen da ya kara makale mata tace nagode kwarai safiya da wanan shawarar taki,
Haba maryam kifi karfin haka fa agare ni mayye na wani godiya bayan duk yiwa kaine hakan,
Safiya tace daga gobe zan insha Allah zan tunkare shi,
Shi ko A,A yadauka duk gajiyace tasa maryam rashin shigowa school yau,
Saida wani ke ce mai ai yaganta ta shiga napep zuwa gida yadauka malam din bai shigo bane,
A,A yai mamakin ji cewa Maryam tashigo school ya batare da tai mai waya ko ta iso inda yake ba,
Don haka ba bata lokaci yadauki waya ya kira ta,yanamai tambayar ta ko da gaskakene yau tashigo school din,?
A dakile taba shi amsa da cewa eh, kawai ta kashe wayan ta zuviyar ta na mata kuna, sosai,
Mamaki fam a zuciyar shi don tunda yake da maryam yauce rana ta farko da ta taba mai irin haka,
Wanan abin yai matukar bashi mamaki da daure mai kai alokaci guda don sam bai kawo komai ba sai tunane, may ke faruwa,?
Dadare yazo gidan su amma sai tace ace mai bata nan kawai haka yasa yakara rudewa,
Washegari Safiya ta samay shi a office din shi yana zaune yana aiki acikin computer tar shi yana saye da riga shirt mai dogon hannu fara,bakin wandon Jean's a jikin shi, sai yar farar glass da ya manna wa idon shi,
Da sallamar ta tashiga office din nashi yana ganin ta yadan yi murmushi yana mata iso data shigo,
Bayan sun gaisa ne safiya ta fara shedawa A,A yadda mahaifin Maryam, yasa ta aga ita da yar ta duk dadewanan nan
Shiru yayi har zuwa lokacin da takare zancen ta da cewa mahaifin maryam ya dibar mata wa,adi,
Hankalin shi a tashe yake batare da yaiwa Safiya magana ba
Itama dai din kallonshi takeyi, don ganin irin reaction din da ya shiga lokaci guda,
Saida yaji ta tana huce da iskan bakinta yadan gyara zaman shi yana cewa,
Safiya, wallahi duk na ma rasa may zan ce dake,
Sai kuma yasoma share zufa duk da sanyin A,C dake office din nashi
Aiko magana zakayi don musan mafita, daga cikin
Yadan ce cikin marairaice murya, wallahi safiya akwai abin da nake planing akaine, shiyasa,
Bawai sharewa nayi ba yadda kuke nufi, ba
Safiya tace malam ba fa wai aure akace kuyi yanzu ba fa
Kawai da ka gabatar da magabatanka suga iyayenta don manya su shiga shiga cikin zancen,
Saida ya kara share, fuskan shi karo na barkatai,
Safiya tace kaga aure sai lokacin da katashi ke nan,
Yace nasan da haka safiya amma abin dibawa anan shine kokari nakeyi ingama abubuwan dake gabana tukun
Su kwantar da hakalin su bawai zan yaudareta bane,o something like dat,
Kawai dai zan samu, illiya idan yazo muyi magana akai,
Safiya tace malam idan har bada magana mai karfi zaka je ba kada katafi pls,
To safiya idan sun min haka basuyi min adalci ba gaskiya
Kallon shi safiya tayi da mamamki,
Tace malam waiko kasan duk maganar da kayi da mahaifiyar ka ranan da kukaje da maryam gaida ita duk a kunen maryam ne
Ido waje yake kallon safiya da mamaki da kaduwar jin zancenta,
Nan dai takwashe komai tafada mai wani rin nauyi da kunyane suka lulube shi lokaci guda,
Safiya takare zancen ta da cewa malam don Allah kada k bawa maryam, baya ka guje ma,ta
Sai kuma sai zuciyar ta yai sanyi tana batun sa kuka,
Tamike tabar office din batare da ta saurare shi ba,,
ZEEE. MAKAWA
[3/7, 1:14 PM] +234 803 381 3188: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
3⃣9⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA,,
Alhamdullah Yusuf ya kammala wani course da yadan kara tsayar da shi kasar Korea,
A harkan business ne dama ya tsaya don kara ita fasaha akan, kasuwanci
Don haka yanzu kimanin watan shi takwas ke nan rabon shi da kasar shi,
Duk abinda yakeyi yanzu hankalinshi yakoma gida Nigeria musan,man kakar shi wace yabar ta kwantagora, tare da Dad din shi,
Saboda yasan cewa babu shiri atsakanin su saboda banbancin churches din su, da suke bi,
Yasan cewa yan church din su Dad basu kaunar mabiya Olumbo,
Sonny ya na hankalce da Yusuf din duk kwanakin nan baya son walwala sosai,
Lafiyayyen abinci tare da abin sha daga yayan icce,aka hada masu a matsayin dinner yau,
Sai da Yusuf ya idar da sallah shi na isha,i tare da,shafa,i da wuturi,
Sanan ya koma yai wanka yafito cikin shirin shi,
Yayi mamaki Kwarai da ya samu Sonny a zaune yana jiran shi,,
Yusuf yadan bashi hakkuri tseda shi da yayi har zuwa wani lokaci,
Cikin daga hannu Sonny wanda,yake saye da wata far coth da wandon shi fari, sai bakar shirt da yasa daga ciki,
Yadan, dago wa Yusuf, hannu alamar ya share ba matsala, kawai,
Nan suka zauna suka fara cin abincin su hankali a kwance,
Saida suka dan dauki lokaci batare dayin wani magana ba sai karar cibin da suke cin abinci kawai kake ji yake tashi,agurin,
Sonny ne yadan dago kai yakalli Yusuf wanda dabi,un cin abincin shi yanzu duk ya canza,ba kamar da ba can, baya,
Murmushi mai sauti Sonny yayi wa Yusuf wanda hakan yasa shu dago kan shi yana mai kallon shi,,
Sai kuma ya daure fuska acikin yar damuwa yace,
Man this your religion is good, and have a nice characters,
Unlike Christianity,
Da sauri Yusuf yadago kai ya kalle shi,
Yace ma Yusuf man see how yo pray everyday,
Bayan yawan sallah da kuke yi a kullun, batare da damuwa da ko kowa ba, alokacin yinta,
Amma su Christian saudaya kawai suke zuwa church a cikin sati, inda wasu ma bawai dole su tafi ba,,
Littafinku mai tsarki muslumai dayawa sun haddace shi a kan su ,
Littafin ku mai tsarki Alkur,an, yana nuna abu guda ne ga kowani irin yare za,a fasssara shi,
Zaku iya shiga kiwani irin massalaci kuyi salkah aduk lokacin da ta riske ku
Ba kamar Christian ba suda da angan ka sai an tambaye ka wani church, kake zuwa a cikin sati,
Idan kafadi wanda ba nasuba, zasu iya bata rai, dakai afili,
Dazaran ance kai musulumi to daidai kake dakowa daga cikin musulmi, kuma a nuna ma so da kauna alokaci guda,
Sai kuma duk abinda ka iyayi dazaran kace Allah shikenan an yarda da zancen ka,kowace iri ce,
Amma su Christian dazaran kace God zaka zama abin zargi ke nan in ma bakai hankali ba sai antara ma taron,mutane,
A bincike ka, wani irin God, kake zance shi god din yan Catholic ne ko god din Anglicans, kona na living faith, kok, shin na deeper, life,
Duk da su ma musulmai suna da wayan nan akidodin a tare da su amma sai kayi nisa sosai a cikin su zaka iya ganewa,
Amma su kan Christian a filli suke nuna nasu,
Zaka iya jin ance maka ai jabun pastor ne wani
Banda musulumai da ko yaya imanin ka yake zasu iya binka sallah, a jam i
Gashi su musulmai aduk lokacin da suke azumin su na watan ramadam mai tsarki, duk duniya zasu sani sanan sauyi zaizo wa kowa daga musulmai har Christian alokacin wanan azumin
Amna baka taba jin wani abu maka mancin haka acikin bautar Christian,
Idan wani abin al,ajabi yafaru musulmai zasu yarda da cewa daga Allah, ne amma su Christian sai su ce wai in Jesus, name, wasu kuma suce karfin shedan ne,
Zaka ga idan mai wa,azin musulumai yana waazi, musulumi koda karamin yaro ne ya kewaye shi yana saurare har zuwa lokacin da za,a tashi koda kuwa mutum nada abin yi alokacin ba zai tafi ko ina ba, ko fitsari azasu yarda su tagiyi ba don kada afadi wani abinda basu ji ba,,
Idan ka lura da musulmi yana girmama pastor afili, badon komai ba sai don sanin cewa shugabane na addini,
Amma,su Christian suna jin haushin limamen musulumai sosai,
Yadda zaka ga musulmai suna girmama shugaban nin su sai kaga su Christian suna kokarin gardama da pastor cin su,
Kai abubuwa da dama nayi searching din su naga akwai bambanci halaiya so sai a tsakani,
Tunda ya fara dogon sharhin shi Yusuf yadakatar da cin abincin da yakeyi yana mai tsura mashi ido,
Acikin zancen Sonny din Yusuf yagano cewa akwai wani magana mai muhin,manci, da Sonny din ke son yi dashi,
Hakan yasa ya tatara hankalin shi gabadaya yana mai sauraren shi,
Yyana kaiwa karshe sai ya kalli Yusuf da kyau ya aje cokalin da ke hannun shi a cikin plate din da yake cin abinci,
Yakara duban Yusuf din sosai, yace a yar fahintar da nayi yanzu Joe nagane cewa muna da banbancin addini sosai ni da kai,
Kaga zancen mu hada harkokin mu kamar yadda muka saba ada bai taso ba ,
Kagane ko?
Yusuf yace,,
Fadi maganar ka kawai ina sauraren ka ai,,
Sonny yadan girgiza kai yana mai cewa don haka na yanke shawara nakuma rubuta komai a rubuce har an sa min hannu, cewa
Nabar maka duk wasu kaddarori da suke a hannun ka saboda nasan cewa kana bukatar taimako yanzu a rayuwar ka so sai,
Nayi hakane don in kareka daga duk wani barazanar da za,a yi kawo maka na cewa zasu iya gurgunta