Showing 144001 words to 147000 words out of 255288 words

Chapter 49 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1395

fesar da iska Yusuf yayi da bakin shi don abin da yaji,
Shi a,zaton shi Maryam basu tare da wanan guy din,
Kanta ta maryam gefe cike da jin nauyi yadda yaron yai magana,
Sai yanzu ta tuna cew tabar wayan ta a daki tun dazu tasan yakira lalayin ta bai shiga ba,
Yaron zai kara sallama Anty Dije tai tsuki cikin tsawa tace wa yaro kai katafi dan Allah taji pls,
Kamar may rada yadan kalli inda take yana nu mata kayan da yaci abinci
Wani irin haushin maganar shi taji don tasan zai jagula mata al,amarin ta,
Dakin tatakoma ta gyara kimtsawa alokacin yana zaune da Anty suna zancen uren,
Cikkin shigar wani jan dogon riga ta material, anyi mata wani dinki mai shara,shara,
Sai kamshi ke tashi a duk inda ta gilma saboda yadda ta daba shi a jikkn ta kamar da gaiyya
Fitar maryam ba ai wani dade ba Yusuf yafito a kasalance,
Hango su yayi zaune a cikin mota saida maryam kamar kullun kafar ta a waje yake ganganjikin ta aciki,wani irin haushi guy din ya bashi yau amma bai san ko may yasa ba,
Maryam dake a cikin mota ta hango fitowar Yusuf din daga cikin gidan
Full light ya sakar masu yana kallon yadda maryam take kokarin kare hasken motar da hannun ta
Wani irin ashar A,A ya afka mai da ita wanda har sai da maryam tace, haba malam wanan zagi haka kamar yaro,
Kallon ta yayi cikin nuna zargi yace,
Maryam ku, kuka dauki wanan dan IBO da wani muhinmanci,
IBO ne fa ba wata tsiya ba, ni wallahi zanyi maganin shi idan har ya shiga gona ta,
Hannu Maryam tadaga mai abin da bata taba yi mai ba
Tace shi IBO ba musulumi ba ne?
Damay mutun ke nunawa agurin Allah da al,umma ban da Islama,
Shi wanan da kake nu cewa IBO ne naga yafi wasu dubun hauwa( tauhidi)
Ashe ke nan da ibo da bahaushe da bayerabe kai dama kowani irin kabila
Mafi karfin imani shine mai rin jaye ga alumma bawai yare ba,
Yadda kake ganin shi IBO anan haka acan kasar su suke ganin ka bahaushe kai ma
Kallon ta kawai yake galala don yadda ta zake take kare Yusuf yau a gaban shi abin ya bashi mamaki,
Sai dai duk maganar da ta fada babu wanda ba gaskiya ba daga cikki
Hiran nasu daga karshe haka suka watse ba wani kwakawaran zance sai debet akan IBO da hausawa
Ida ita maryam ta dage da cewa kabila bashine abin suka ga mutun wanda yake musullumi ba,
Dane a lokacin da ake da karancin addini ake irin wanan maganar,

Washe gari Yusuf bai shigo gidan ba sai kusan shadayan rana,
Sanin yana gari maryam bata zama da kananin kaya agida kamar yadda idan mijin Antyn idan yana gari bata wani damuwa da gyaran jikinta,
Yauma dai wasu zanin tamfane masu ruwan powder sai wa su flowers da akai masu masu ruwan milk,
Zaune take a gaban tebur tana cin abinci a cikin natsuwa kamar ko , yaushe,
Yakai wani lokaci agurin tsaye yana kallon yadda take komai nata a natse
Sam bata da hayani ko wani rawan kai irin na yan matan da yake yawan gani,
Ita dai gatan ako da yaushe sai umurnin da akaba ta arayuwan ta duk, da irin, halin miskilancin da ke gare ta kafin a saba da ita,
Alamar tsayuwar mutum a kanta taji da kuma kamshi da bawai na irin turaren da yasaba sawa bane yau a jukin shi,
Saye yake da wata yar farar tee-shirt, mai wani dan flower ja agaban rigar daidai saman aljihun gaba,
Wani wando ne baki kamar Jens a wanan yadi yana wani dan walkiya,
Cikin dan rudewa ko razana da ganin shi a tsaye tayi
Saboda azaton ta har yazo ya karya ya wuce ko
Sai idon ta ya hango mata abin karin sa a gefe aje,
Don sam yau kin fitowa tayi tai kwanciyar ta kawai, abinta, adaki sai da ta ga cewa rana yayi shine ta fito,
Da yar murmushin shi ya karaso har inda take zaune,
Ina kwana ta tare shi dashi yayin da yazo gab da ita,
Dukawa yayi gab da ita batare da ya amsa gaisuwar ta ba yace
Saurayinki maryam baida kirki ga fahinta na bai dace yazo har kofan gidan ku ya saki a mota ba, mutane shiya suna ganin ku,
Gaba kura baya karen daji,
Jiya ta yi da A,A yau kuma Yusuf ya,tare ta da zancen A, A din,
Ki kula maryam ke mace ce kada ya bata maki record din ki pls,
Bata son nuna mai maganganun da yai mata sunyi mata tasiri a zuciya ,
Amma afili sai ta dake tace ban ga abin sa ido irin haka ba har zargi na son ya shiga,
Yan mata nawa suke hira a mota wasu ma har gida suke bin namiji amma sai mu da muka zauna akofa za a wani sa muna ido,
Wani ajiyar zuciya ya sauke gami da dan kura mata ido kamar zuwa second minutes,
Mikewa yayi daniyar wucewa amma sai yaji muryan ta a rau,nane tana cewa "Na, Gode"
Da dan mamaki ya waigo ta saidai kanta na kasa tana wasa da spoon din dake a hannun ta,
Dan nazarin ta yayi sai yaji wani irin tausayin ta ya kamashi a take ya juya da niyar barin falon,
Ga abincin ka can fa inji Naimat wace duk basu san cewa ta na gurin ba ashe,
Hannu yadaga mata alamar yagode kawai ya juya yabar falon,
Kallon mamaki da al,ajabi kawai maryam kewa yusuf din
Ita ko Na,imat saida ya fita tasa hannu ta toshe bakin ta tana darita cikki,cikki tace
Wa maryam da gani nasan cewa kin tabo big brother yau,
Maryam tace kawai dai yaso yasa wa kanshi abin da bai shafe shi bane,
Nan dai maryam ke fadawa Na,imat yadda sukayi da shi,
Na,imat tace gaskiya sister ba karya bane don mu yaren mu bamu irin wanan sam,
Kinga kuwa tunda yanzu anzama daya dole ya fada maki gaskiya, saboda yasan cewa zubar da mutunci ne irin haka,
Mamakin jin abinda Naimat tafadi maryam tayi,
Yanzu a she har akwai abi da bahaushe zaiyi ace wai IBO naganin shi a cikin rashi tarbiya,,,,,,,,,,


ZEEE MAKAWA
[3/24, 10:10 PM] Zainab Makawa: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
6⃣0⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA,,,


Kaunar da kuke nu na min yasa har na kasa bakin godiya agare ku,
Fatan Alheri ga duk wance ta fahinci ma,anar wanan sakon da nake isarwa,
Ubangiji Allah ya kara maki ke mai karatawa daraja da,dauka,
Allah yasa mu gama da duniya lafiya baki dayan mu
Allah ubangiji ya taimaki addini musulunci da ma musulman baki daya
Ya Allah karawa Annabi Daraja,πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘



Gudu yake shararawa acikin motar shi hannu shi guda yana, dan shafo fuskan shi dashi a hankali,
Tunane yakeyi wai may ke sa shi damuwa da al,amarin wanan yatiyar ne,
Har raini yana son shiga a tsakanin su don tafara mayar mai da magana mai zafi,
Tsuki yaja yace why tausayi zai ja mai raini a gurin ta,
Zai yi kokari ya killance kan shi daga harkokin ta bazai kara sa mata ido ba,
Tun bayan barin shi gidan bai shigo ba har sai zuwa misalin hudu na yamma,
Lokacin duk sun kare aiyukan da Anty Dije tabar ma,su yi,,,
Saidai fuskan shi kawai zaka kalla kasan bai a cikin good mood yau din, saboda yadda idon shi suka kada sukayi jajir da su,
Kallo guda tai mai tunda ya shigo ta kauda kanta daga ganin shi
A take wani yanayi maikama da zazabi ya sauka mata, sai taji kawai kwanci take so a lokacin,
A kan gado ta zube sannan ta lumshe idanun ta a hankali a sannu take jin yadda zuciyar ta ke bugawa,
Muryam Na,imat ce a kanta tana cewa Maryam lafiya ki ka kwanta by dis hours,
Kwanci bayan dis hours yana kawo wa mutum zazzabi fa,
Ido a lumshe ta ansa mata da fadin lafiya kalau, nadai dan kwanta ne kawai,
Dafata tayi tana cewa to ki tashi wanda kika kwanta don shi shima ya wuce bai tsaya ba tunda yaga jeloup din taliya mukayi,
Cikin wani hanzari tamike zaune dan jin cewa bai ci ba ya wuce,
Tambayar Naimat tayi cikin damu to may zai ci da ya wuce,?
Aida kin tambaya ko da abin da yake so ai mai ko,?
Kin san halin brother baya son dogon magana shi yasa kawai na kyale shi,
KB yana gari don haka yana fita ya juya akalar motar shi zuwa gidan,
Wayar shi ce alamar kira ya,shigo mai a lokacin,
MARYAM BLACK,
Yagani a rubuce kamar yadda yai serving din sunan ta,
Cikin hanzari ya mija hannu yadauki wayan adai,dai lokacin da ya tsaida motar shi,kofar gidan KB,
Da sallama yadauki wayan yana cewa maryam ya dai ?
Kafin ta ce wani abu sai tai dan shiru saboda Naimat da ta tsure ta da ido,
A ladabce tace Ya Yusuf baka ci abinci ba kawuce,
Murmushi yayi dan jin dadin kula shi da tayi, yace No bana cin taliya ne yanzu shi yasa
To amma shine bakai magana ba sai aima wani abin,
No, no no ki barshi kawai zan sha drinks ai,
Wani ajiyan zuciya tayi har sai da yaji ta acikin wayar,
Sallama taimai inda yake ce mata yagode cikin wani murya maikama da na tausayi,
Jingine wayan tayi a saman kirjin ta , tana tunanen irin saukin halin Yusuf din,
Yanzu ya shigo fuska murtuk kamar an aiko mai da sakon mutuwa amma sai gashi taji muryan shi kuma yanzu normal,
A gidan KB Yusuf a waje yake tsayawa saboda baya son irin yanayin matar KB din,
Don ita ko maza sunkai nawane zata iya zama acikin su,
Ko kuma takama gittawa a gaban su cikin shigar matsatun kaya,
Shikuma hakan ke sa yana kare idon shi da daukar dumbin zubi,
Duk yadda KB yaso su shiga Yusuf yaki sai da KB din yace mai ai ba kowa sun tafi gidan su gurin bukin aure,,
Ya,samu akwai abinci da aka zubawa KB din shi ya dan ci amma kadan saboda bai ji test din abincin ba, sosai,
A lokacin da yakora ruwan mai sanyi da KB din ya dauko mai acikin fridge
KB din ne yadan dube shi yace wai ya ake ciki ne akan zancen ku da yariyar nan ne,
Ina sa zuwa yanzu har anyi engagement sai kuma na shiru kawai
Man ya kamata fa ka maida hankali ka aje iyali zuwa yanzu,
A je roban ruwan yayi a saman tebur din gaban shi ya ce,
Ai kasan komai a sannu akeyin shi idan time yayi ba,wani bata lokaci ,sai ayi,
KB yace gaskiya ne ba shakka haka maganar take aure dan lokaci ne,
Washegari duk kan su gidan gyaran jiki sosai akai masu,
Daga adon lalle da kuma dilka, sai kuma kitso da aka yarfa ma su gwanin ban sha,awa,
Gaba dayan su sun fito shar da su, duk wanan shirye, shiryan sunan da za,a yi ne na haihuwar kaunar mijin Anty Dije da tayi,
Ita kanta maryam tasan cewa sun yi kyau duk da ita ba ma,abociya son yin kitso bane,
Allah ya tai make su har aka gama masu Yusuf bai shigo ba saboda yar tafiyan da yayi zuwa kauye,
Da sallama ya shigo gidan inda ya fara cin karo da Na,imat wace a yanzu duk ta juye ta zama bahausa sat,
Saida gaban shi ya fadi irin yadda yaga ta koma alokaci guda kai Musulunci ma Rahamace ya furta a cikin ran shi shi kadai,
Anty Dije ce cikin shigar wasu dinkin Senegal's da mijin ta yasayo mata da sallah bara,
Da fara,ar ta a fuskan ta ta shigo falon gurin Yusuf, din tana tambayar inda ya tafi,jiya,
Maryam najin shi daga dakin su amma sai taki fitowa su gaisa,
Duk hiran da suke yi da Anty Dije sai ya tsunci kan shi da rashin jin dadin ganin maryam din kamar ya tambaya ina ta ke sai dai ya daure,
SAFIYA ce ta shigo gidan da sallamar ta Anty Dije wace ke kokarin aje cup din da tasaha kunu a saman tebur ta dago kai tana amsa da yar fara,ar ta a fuskan ta,
Da murmushi makale a fuskan ita Safiya ta zauna saman daya daga cikin kujerar falon suka gaisa,
Sanan take tambayar maryam din
Anty Dije tace barin kira maki ita tana can dakin kusa da kitchen kwance,
Lokacin da Anty ke shirin mikewa ita a lokacin maryam ta shigo falon da murrmushi makale a fuskan ta,
Wani irin mugun shock yaji da yana cewa Naimat ta canza cikin dan lokaci sai ga kuma maryam kamar wata Amaryan wani gwauna,
Da sauri ya kauda idon shi gare ta da ya daga don amsa mata sallamanta,
Safiya ce ta tare ta da cewa ke wanan irin haduwa fa kamar wata, amarya can,
Hararan ta maryam tayi tace ina kwana Ya Yusuf, kamar bai gurin
Amsawa, yayi batare da daga kai ba
Safiya taci gaba da cewa Anty shiya sa Dan iskan ga ya wani leke mata kamar kaska,
Ni wallahi Anty A A din nan Allah yakawo wanda zai kifar da gwaunatin shi a zuciyar maryam,
Dan takaitaccen murmushi Anty Dije tayi tace,
Wanan ai tai nisa Safiya indan kin ce ba shi ba yanzu zaku bata ne,
Cikin daure fuska maryam tace wa safiya, gaskiya ke sai mun hau sama dake tukun ina ga zamuyi daidai,
Ta juya tai hanyar shiga dakin su tana magana kasa,kasa,
Safiya ta juya tana fuskantar Anty Dije tace wallahi, anty bana son zan cen wanan mutumin sam mugune har na karshe,
Nan dai sukai ta zance a kan A, A din har zuwa dan wani lokaci,
Yusuf wanda kan shi ke a duke yana ta faman dadannar wayar shi bai ce masu uffan ba,
Daga karshe rai a bace Anty Dije ke cewa, ai duk abin da zai mata Allah bai bashi ikon cutar da ita,
Maryam tafito cikin shigar wasu kaya kamar les a jikin ta sai dai ba masu nauyi bane su tai wani irin bala,in kyau,
Naimat ce a bayan ta ita cikin shigar wasu kaya da Yusuf ya dinko mata,
A tare zasu tafi gidan kaunar mijin anty dije inda ake suna,
Ga kayan ci da na sha nan kala kala da suka dafa da,soyawa wanda za,a tafi mata dasu,
Ganin yau gidan da taron mata yasa Yusuf mikewa yana ma Anty sallama,
Yusuf don Allah ko yan matan nan ka fara sauke min su a gidan bukin pls,
Daga kai yayi ya dan kalli gefen da suke idon shi caraf a cikin na Maryam,
Da sauri maryam din takawar da kanta gefe guda cikjn sauri,
Amsawa Anty Dije yayi da to badon yaso ba, a haka aka dinga loda kayan da zasu tafi dashi a cikin motar shi,
A hankali suke tafe inda yau kidan turanci ne ke tashi a cikin motar shi, ga sanyi AC da ke ratsa masu jiki a hankali maryam ke bin wakar da ke tashi a cikin motar,, le me love you, ,don't give up , i won't, give up, now, know, know,
Kusan duk wakan suke bi, a motar inda Naimat ta kawar da dan shirun da ya biyo baya,
Tambayar shi tayi ya zancen shi da Sadiya ne wai an gyara kuwa?
Bai bata ansa ba sai ma jefo mata tambayar da yayi cewa tana bukatar tace, tazama cikin su,
Kafin Naimat tai magana. Safiya ce tace mai wai, haryanzu zancen yana nan ashe ?
Naimat tace nafison brother ya samu mata wace zata iya kula da mu yan uwan shi a duk irin halin, yadda muke,
Kin san fa mu a yaren mu mace ce ke kara karfafa zumunci ba namiji ba,,,
Idan munzo gidan shi ba,a tare mu da fuska mai kyau ba ya zamuyi
Kinga ke nan zumunci ya baci saboda ita mace ita ce mai zama gida,
Tunda Naimat tafars magana ba wanda yace mata komai har ta kai aya,
Bayan ya sauke har zai wuce sai Naimat tace dan Allah brother ba dadewa zamuyi ba ,
A,lokacin har su maryam sun fara tafiya, zuwa cikin gidan bukin ,
Safiyane amma kasan cewar haihuwan fari ne gida tab yake da jama,a daga fanin mijin ta har na,ta da abokan arzikin, ta,
Bayan sun gama shigar da kayan da,suka fara zuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login