Showing 216001 words to 219000 words out of 255288 words

Chapter 73 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1409

anty dijen,
Anty ta kara cewa nasan saboda mugun ciwon kan nan da tayi ya firgita ta shi,
Irin yadda maryam ta firgice ai duk wanda ya gan ta sai ya ji tsoro a lokacin,
Maryam din tayi ciwo ne har haka anty ya tambaya a cikin kulawa,
Nan anty ta kwashe duk yadda abin ya kasan ce ta,bashi labari, har zuwa zancen daurin auren su,
Cikin tambayar da ta gigitashi yace Anty kina nufin cewa maryam a matsayin mata ta take yanzu nan,
Mamakin tambayar da Yusuf yai mata taji saboda tazaci cewa tun farko ya san da zancen,
Cikin mamaki Anty Dije tace kana nufin cewa, baka da labarin daurin Auren ku kaida maryam din,
Hasbunallahi wani,imal wake,el,,,
Sai kuma yai shiru inda yadaga kan shi ya na dan kallon saman silindin dakin bakin shi na motsi, kawai,
Da alamar addu,a ya keyi a lokacin, don haka ido Anty dije tabishi da shi,
Yakara dago kai tankar zaiyi magana amma kuma sai ya kasa,cewa komai yai shiru,
Muryan Anty Dije ne yadawo dashi ga tunanen da ya fara inda yaji tana cewa,
Gashi baba yai alkawarin cewa duk ranan da kazo a wanan ranan maryam zata tare a gidan ka,
Cikin rashin fahintar may hakan da anty dije tace yake nufi ,
Ganin bai fahince ta ba yasa ta cewa maryam din baba yace a yau zata shiga gidan ka,
Cikin sauri Yusuf ya tare ta da cewa haba haba anty,
Kada baba ya ce haka pls
Yabari har muyi styling pls, ?
Murmushi Anty dije tayi ta dan kalle shi tace baka da inda zaka satane Yusuf ,?
Anty amarya ai sai sabon gida ko kamai ma sabo ko
Cikin mamaki anty dije tace ma Yusuf din , kai a ina kake zama ?
Yace a wanan dan gidan nawa mana kinga ai ban yi shi as na mace ba ko ?
Hmmm inji Anty Dije saboda mamaki abinda Yusuf yace a kan gidan da yake a ciki,
Ganin tana mamakin yasa shi cewa a gaskiya ban dauka cewa auren mu da maryam zai zo da wuri ba haka don haka ne ma ban wani dade da sayen fili ba nasa ai mun irin plan din ginan da nake son inwa mata ta ta zauna a ciki,
Sai kuma ya wani irin nisawa bayan yakai karshen maganar ta shi,,,
Shiru sukayi gaba dayan su a lokaci guda,
Kowa da irin abinda yake tunane a cikin zuciyar shi,
Mikewa yayi saboda yatafi gurin mahaifin Jibrin din don yana son ganin shi sosai don jin karin bayani,
Duk da zuciyar shi har gagan jikin shi rawa sukeyi a lokacin saboda duk a rude yake,
Mamaki kawai yakeyi wai maryam ce yau a matsayin matar shi,
Jin abin yakeyi tankar a mafarki, ba wai a fili ba, sai da ya kai kofar fita yadan cewa Anty Dije saida safe don da wuya yadawo anjima
Murmushi tabi bayan shi da saboda ganin irin yadda ya rude a lokaci guda,
Abin mamaki yana fita waje a gurin da yabar su maryam din a zaune ba su gurin daga ita har safiya din,
Yaso kwarai ya kara ganin yarinyar saboda tausayin take bashi ,
Bai tsaya wani mamakin ina suke ba don yasan cewa saboda shi ne, suka boye,

Gidan mahaifin Jibrin din yakoma, inda yaci sa,a wanan karon dattijon yana gida,,
A cikin mutunci da nuna kulawa, dattijon yatari Yusuf din,
Kamar yadda yaran hausawa suke gaida na gaba dasu
Haka,Yusuf din ya durkusa har kasa ya gaida mahaifin jibrin din,
Bayan sun gaisa, ne a cikin walwala, Dattijon ya tambaye shi, gajiyan tafiya,?
Sai Yusuf din ke fadawa mahaifin na jibrin cewa yazo ai dazun bai samay shi a gida ba,
Dattijon ya ce Allah sarki ai nadan zagaya nan bayan layin mune gaida wani makwabcina da yadawo umura,
Yusuf yace shima yana da sha,awan bana ya tafi Umarh din nan insha Allah,
Haka akeso ai, inji dattijon ya ce wa Yusuf din,
Kullun ana son al,uman manzo S,A,W su bazama izuwa gurin ibada kasa mai tsarki,
Saboda kara samun ci gaban musulunci a cikin duniya,
Yakare da cewa Allah yasa, Musulunci ya rinjayi kafirci akoda yaushe,
Yusuf ya karba mai da fadin amin, Ya Allah,,,
Dan shirune ya biyo bayan hiran nasu a lokacin,





ZEEE MAKAWA YALWA
[5/3, 10:53 AM] β€ͺ+234 706 262 3470‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
8⃣6⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA,
YAURI



RAMADDAM KAREEMπŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘




Yusuf yana mai sunkuyar da kan shi a kasa ,
Sai shi daddtijon ne yai gyaran murya inda ya soma magana kamar haka,
Yusuf, kasan cewa yanzu dai duk musulmi na kwarai yakan yadda da kaddara,
Walau, mai kyau ko akasin ta watau mara kyau ke nan abin nufi,
Yusuf din yace hakanane baba dattijon ya ansa da fadin da kyau dan Albarka,
Yaci gaba da cewa ta a bayan ka abubuwa da dama sun faru.
A nan ya zayyane masa yadda sukayi tun daga farko da mahaifin su maryam din har zuwa daurin aure,
Kaga kenan al,amarin ubangiji ba, ai,mai shishigi,
Shiru Yusuf din yayi a lokacin tankar bazai yi magana ba ,
Har dattijo ya zaci cewa ko bai yi naam da zancen auren bane, haka,
Sai kuma yaga cewa ai Yusuf din ya can,canci ai mai wanan irin sakkayan da mahaifin su maryam yai mai,
Don gaskiya Yusuf mutum mai taimako da kyautatawa na kasa da shi,
Gashi ya fitar da jama,a da dama daga cikin kangin talauci kai taimakon shima dai mara adadine,
Amma kuma sai gashi wai mutum butulu ana,son abin hannun shi amma baza a iya hada zuria, da shi ba kamar ba musulmi ba,
To amma kuma gashi wanan bawan Allah yanuna halarcin shi gare shi,
Ya nuwa duniya bai kwadayin abin shi sai dai fatan alheri,
Don ko sadaki shi da kanshi ne ya matsa mai akan abarshi a dubu hamsin ,
Don shi mahaifin yarinyar yanuna, wai dubu ashirin ne, za,a bayar da farko,
Muryan Yusuf din ce ta katse mai tunanen ida acikin murya irin ta mai zubbar da hawaye, yace wa dattijon,
Baba ban da abin da zan furta a gare bayan ince Allah ya sa agama da duniya lafiya,
A cikin sauri dattijon ya ansa da fadin amin amin ya na mai gyara zaman shi,
Sai kuma yadan yi shiru hannun shi yasa ga aljihun shi yana kirgo kudin daga ciki,
Yan dubu guda gudane sababbi fill da su ya aje a gaban baban nasu,
Yace baba ga kudin da kuka bayar na sadiki sai kuma kudin goro da sauran su,
Kai, kai, inji mahaifin Jibrin din ya ce wa Yusuf cikin dan ja da baya kusa da kudin da Yusuf din ya aje, kamar wani wanda yaga abin tsoro,
Haba Yusuf ashe baka dauke ni a matsayin mahaifi ba,
No, no ba haka na bane baba, don Allah kayi hakkuri ka fahince ni,
Haba Yusuf duk abinda zan iya yi,wa Jibrin zan iya maka shi aduniyan nan ,
Sanan malam Abdulsamad shine ya siyo su goro da alawa, wanda aka rabawa mutanen,
Da suka sheda daurin auren naka don dai alhamdullahi mutane da dama sun sheda wanan daurin auren na ku, so sai,,,
Shirun da wurin ya dauka gaba daya shi ya sanya mahaifin Jibrin gane cewa Yusuf kuka yake,
Haba Yusuf ka kara godewa Allah ka da ya kaddare ka da yin wanan auren, cikin mutunci da girmamawa,
Don duk yadda ake halarci mahaifin Yarinyar ya yi gaskiya, saboda duk yadda yadace na gwada inda na fahinci cewa tsakani da Allah ya baka yar shi ba don kwadayin duniya ba,
Yusuf yace wa mahaifin Jibrin din nasan da haka baba,
Don wa yan nan mutane suna daga cikin sahun farko na tallafawa shi ga na, addini nan,
Saboda sam basu kyamace ni ba a rayuwar su, a lokacin danake cikin batar kai, kamar yadda sauran mutane ke nuna min kyama a baya,,
Kiran sallah da ya karade gari alamar magriba ya yi a lokacin shi dan tsaida zancen nasu,
Don haka suka mike kusan lokaci guda don haramar dauro alwala,
Amma sai Yusuf din ya dakatar da dattijon da cewa dazun na tafi gidan ita yar yarin wace ke rikon ta,
Take sheda min cewa wai mahaifin nasu yace, duk ranan da nazo a ranan yariyar zata tare agida na,,
Kai mahaifin Jibrin din ya kada yana cewa hmm malam Abdul zai iya yin fiye da hakan ai,
Don shi mutum ne mai ra,ayin kan shi bai bin ra,ayi al,umma,
To kai yanzu ya kake so a yi ne ?
Kai yadan sosa alamar jin kunya, yace baba naso ne ai mata kamar yadda naga hausawa nawa yaran su a gurin aure don saboda hankalin yarinyar ya dan kwanta,
Indan mun fito daga massallaci zan je gurin shi insha Allah, za a san yadda za,a yi,


Anty Dije wace tun bayan tafiyan Yusuf din duk ta rude saboda sanin halin mahaifin su da tayi, cewa bai magana biyu a rayuwar shi,
Don haka ta dauki waya kamar yadda ya umurce ta, da tayi a duk ranan da Yusuf ya shigo gari,
Bayan sun gaisa ne anty ke sheda mai cewa Yusuf yana gari don har ma yazo gidan ta dazun nan,
Albarka yadinga sa mata don bin umurnin shi da tayi ta sanar dashi a lokaci kamar yadda ya umurce ta din,
Nan yace mata da zaran an fito daga massalaci zai zo gidan nasu amma kafin nan duk wani shiri da ya dace tai wa maryam din ta tabbatar da cewa tayi mata shi,
Tun bayan kashe wayan su da babane sai Anty Dije taji idon ta ya ciciko da hawaye tausayin kaunar ta ya kamata,
Gidan uwale ta shiga inda tai mata bayanin komai kamar yadda mahaifin nasu ya, umurce, ta da, tayi,,
Don haka a,tare da Uwale Anty tashigo gidan a lokacin maryam da Safiya suna tare suna dan hiran su,
Safiya ce ke kokarin jan maryam din da hira don ta kwantar mata da hankali kamar ba komai,
Ganin shigowar su yadan tayar wa maryam da hankali amma da yake ita uwale irin wayyayun matan nan sai cewa tayi ,
Haba maryam may ye haka mijin ki na agari amma zaki zauna a haka ba wani gyara jiki,
Ta juya gurin da Anty Dije take tana cewa haba Hadiza kina kallo ko wani gyara baki mata ba idan ya shigo ya samay ta a haka fa,
Maza tashi ki gyara jikin ki kafin ya dawo ya samayki ba wani gyara,
Maryam ta turo baki gaba saboda jin haushin maganar da Uwale tai mata na cewa wai mijin ta,
Sai taji duk ta wani tsani Yusuf din kwatakwata arayuwar ta,
Amma sai taji Anty na cewa tashi mana maryam ana magana da ke,
Ba bata lokaci maryam ta mike inda uwale taimata nuni da cewa su je makewayi,
Abubuwa na gyaran jiki ta umarci maryam din da tayi a bathroom din ,
Inda uwale ke ta wajen bayin tana umurtan maryam da cewa yi kaza sa kaza gyara kaza har ta kimtsa tafito,
Wasu kayan kamshi ne aka bata tashafa wa jikin ta, inda duk hawaye ya cikawa maryam din ido a lokacin,
Daga matse,matsin ta har zuwa cibiyanta sai da uwale tasa maryam din ta shafe shi da wani dan ruwan mai kamshi acikin wani dan kwalba,
Daga haka kuma Safiya ta gyara mata kanta wanda dama tunda rana tai mata kitso mai kyau kamar sun san da zuwan shi a ranan,
Ita kan ta maryam din tasan cewa jikinta yasamu canji sosai, a irin yadda take jin shi,
Duk yadda zan yi bayani haduwar ta a lokacin mutun ba zai fahinta ba sai dai inda kungane ta a fili,
Sallah Uwale tasa ta gabatar daga magrib har isha,i, ta umurce ta dayi,
Amma ita maryam din duk a lokacin ba ta fahinci komai ba don babu abin da ta kawo a ranta,
Abu guda ne ya tsaya mata arai shine jin haushin yadda suke ta wani rawan jikin shirya mata jiki kamar wata bakuwan Yusuf din,
Bayan yasan ko ya take da tayi ado da batayi ba duk yasa ni,
Amma wai yau shine don ance yazama mijin ta shine suke wa ni rawan jiki Γ  kai,
Gurin da tai sallah take zaune Uwale takara umurtan ta da takara shafawa jikin ta har zuwa kasan ta
Wanan ruwan dan kwalban da ta bata, da farko mai sa ta jin kasala ajikin ta,
Bayan ta gama shafawa kamar yadda Uwale ta umurce, tamika mata kwalban,
Takoma bakin gado tazauna tare da sake wani irin ajiyan zuciya,
Daidai lokacin da Γ€nty ta tashigo dakin dauke da wani dakakken lace a hannun ta,
Mai ruwan sky clour da stones farare ajikin shi suna sa shi shining,
Ran ta bai so ba amma ba yadda ta iya dole ta karbi kayan ta sa kamar yadda aka umurce ta dayi, don gudun sabawa manyan ta,
Daga bakin kofan sukaji muryan mahaifin su wanda hakan ba karamin haifar masu da kaduwa yayi ba dukkan su,
Nan da nan jikin maryam yadauki rawa kamar wace ke jin sanyi,
Baba kecewa ina Dijen take ne wai ko ba ta gidan ne,
Anty Dije ta karba da cewa ganin baba ya ce to, to , ya kun gama shiri ko, ?
Jiki a sanyaye ta amsa mai da fadin eh baba,
Ido Maryam ta zaro waje don jin abinda mahaifin su ke cewa yar ta,
Fito min da ita kawai maryam ta iyaji a lokacin ,
Wanda hakan yai daidai da wani irin sakin kuka da tayi a lokaci guda,
Na shiga uku Anty inji maryam cikin wani irin murya mai ban tausayi, take fadar haka,
Uwale ne da Safiya wace itama dai kukan take sakewa alokacin don ganin irin halin da aminiyar ta yau ta tsinci kan ta,
Duk da dai tasan cewa aure bautan ubangiji ne amma sai take ganin mahaifin kawar nata bai mata daidai, ba gaskiya,
Anty Dije wace hawayen dake idon ta alokacin suka balle mata itama dai kukan tashiga yi,
Jin kukan mu wiwi da baba ya yi, ya sa shi kiran sunan Anty Dije a hassale,
Wata, ashar ya wulwulo ya durawa gaba dayan su a tsorace, ,
Cikin sauri maryam ta koma jikin bango da gado ta kankamay Safiya wace itama kukan takeyi, a lokacin,
Baba wanda idon shi suka yi jawur a lokacin sai huci yakeyi,
Yakara kiran Anty dije a ciki wani kakausar murya wanda yakara sasu firgita,
Wuf maryam din tayi ta cakumi yar nata ta yadda baza ta iya kufcewa ba a lokacin,
Shiko baba daga waje sai cewa yake yi yo naga kina son raina min hanakali fa,
Anty Dije tace cikin muryan kuka baba ga munan fitowa ai,
Kara kankamay Anty Dije maryam tayi tana wani irin kuka cikin sauti mai ruda wakwalwan mai sauraren ta,
Cikin kukan take cewa ban san may nayi wa baba yake min haka duk cikin diyan shi anty kodai laifin da mahaifiya ta taimai yake ramawa a kaina,
Bakin ta Anty Dije ta rufe da sauri tana cewa maryam kan daya kuwa dakike irin wanan kukan,
Safiya tare da Uwale da anty kowa ya hau bakin shi sai magana suke ba maryam din,
Kai ta girgiza tace may ye na bani hakuri bayan wanda ma ya kawo ni duniya yana bidan kai dani,
Wanan karon bakin nata Anty ta buga da karfi sai da uwale tace mata ta daina dukan ta tabar ta taji da abu guda,
Duk zafin rai ne yasa take wanan maganganu bawai cikin hankali takeyin su ba,
Mahaifin su wanda yake tsaye daga waje yana jin abin da sukeyi a cikin daki yai murmushi mai daci,
Uwale ce tazo gaba da maryam din ta kira sunan ta ahankali tana cewa ki yi hakkuri,
Allaj ya kaddarata naki auren zai zo din haka don Allaj kiyi hakkuri da hukuncin da mahaifin ku ya yanke a kan ki,
Wani abu ta shafa mata mai sanyi a hanni tace Allah yasa gidan zaman ki ne maryam, Allah yasawa auren ki Albarka yabaki zuri,a dayyaba,
Sauran dake dakin suka karba da fadin Ameen ya Allah,
Tabbas maryam tasan cewa babu mafita akanta yau tabar gidan yar uwar na ta ke nan,
Safiya ce tai saurin goge lalin da a,ka shafawa maryam din a hannun ta,
Hannun ta ta diba ashe lalle ne aka shafa mata, shike nan tafaru takare,
Wanan karon kukan zuci ne maryam din keyi don sani ba wani makawa a kan ta, sai gidan Yusuf,
Ba suyi aune ba saga Baba har cikin dakin nata yashigo ya rike hannun, maryam din wace ke kuka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login