Showing 57001 words to 60000 words out of 255288 words
Chapter 20 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete
Ejoma,
Haka kawai yaji wanan karon ciwon mahaifin nashi ya,taba mai zuciya, sosai fiye da koyaushe da a,ke bugo mai,
Tunda safe yakama hanya zuciyar shi fam da fargaba tare da zullumi acikin ta don yadda yaji Ruth tana kuka a wayar
Tafiya yakeyi amma hankalishi baya atare dashi sam ji yake tankar ya tashi sama da mota ahida Samuel ne acikin motar,
Samuel wanda ke ganin irin gudun da yayan nashi keyi amma ya kasa magana a,ramshi dai yana addu,an Allah kai su lafiya,
Sun kusa kawo wa kwantagora saboda irin gudun da yake shararawa a saman titin,
Daidai wani kwana baiyi aune ba saiga wata motar irin ta kwasan shanui din nan, a wani kauye, ta debo shanaye zuwa wani kauye
Aiko nan suka jamay motar su Joseph tashi kusan kasar motar,,,,,
Bude idon shi kawai yayi yagan shi a gadon asibiti kwance,
Andaura mai ruwa a hannun damar shi,, ga yan nurse nan na,ta yawo akan shi,
A hankali ya dan kara lunshe idon shi ya mayar dasu ya rufe
Yana kokarin son ya tuna ko a ina yake haka, don yakasa gane ko may ke faruwa dashi, alokacin,
Zubur ya so, mikewa sai,dai ya ji andafe shi da karfi,
Samuel, kawai ya iya furtawa a lokacin muryan Samuel din yaji yana cewa broda iam here,with u,
Daga haka ya lumshe idon shi bai kara sanin inda yake ba kuma,
Kusan duk wanda ke gurin zugun suke,cikin mawuyacin halin damuwa,
Daga KB har jibrin duk sun halarci gurin duk tatare su da yan uwan Joseph din keyi alokacin,
Anty Dije tare da yaran ta da Maryam dake tare da kawar ta SAFIYA, wace tazo yi wa Maryam din yini,
Anty Dije tace su shirya sutafi diban Joseph din a asibiti,
Ba yadda maryam ta iya ,dole suka shiriya, don bin Anty asibitin kamar yadda ta umurce su,
Amma afili cewa tayi wa anty haba ai gaida mara lafiya lada gare shi duk dadai ba musulmi bane shi din,
Sanan kuma aiko don Assalam dole ne in tafi in dibo shi Anty,,,,
Malam A,A masuga sukaiwa magana, yazo kai su,,
A, cikin shiga ta alfarma suke daga su har yaran don daka gansu kaga wayayyun yan birni, daga shigar su kawai zaka gane hakan,
Leda tab da kayan fruit da kuma abinci a wani basket mai kyau, wanda aka dan lulube kulolin da ke ciki da wani kyale mai kyau,
Shiko Mr Emanuel hankalinshi yai mugun tashi yadda yaga yaran gari hausawa suna tazuwa duban dan nashi mara lafiya,
Bai,taba tsan manin cewa jama,ar da ake fadi yanadasu sun kai haka ba sai yanzu,
Don haka tun da yaga Joseph din yadan samu lafiya yabukaci abashi, shi su koma gida adinga zuwa diba shi,,,
Yayi hakane don ya rage yawan masu zuwa ganin shi kin san yadda yare suke da chanfi,
Motar A,A masuga ta Parker a cikin haraban gidan Mr Ema din wanda yasha shuke ,shuken flowers masu kyau,
Sai wani katon kare da suka gani daure da sarka, kaca, yana ganin su ya mike daga kwancen da yake yana wani gurnani, da haushi,
Wa,iyazu,billahi inji Maryam,
Cikin sauri maryam tayo baya inda anty take tana kokarin shige mata,
A,A dake bayan su yai yar murmushi ya ce matsoraci, kada ki kada Anty pls,
Amma jin maganae A,A din baisa ta rage shigewa jikin Antyn ba,
Daidai kofar shiga falon gidan sukaga wani dan dattaijo zaune ya rike wata sanda mzi yar adon kamar kan mutum,
Fuskan shi murtun kamar bai taba dariya ba arayuwar shi,
Cikin ladabi suka gaishe shi har su Assalam yadda yaga su Anty sunyi haka shima yayi,
Duk da shan tokan da Mr Ema yayi yana ganin ladabin su dole jikin shi yai la,asar,
Duk da bai san ko suwaye ba,
A,A ne ke fasa mai cewa sun zo gaida Joseph ne,
Da hannu ya nuna masu kofar wani falo cikin hausar shi tayare mai nuna kasaita,
Yace ku shiga yena ciki,
Wani makeken falo ne agaban su A,A dake gaba yai yar sallama irin ta kafirai,
Suma sukayi kamar yadda sukaji yayi, suna bin sa a baya, baya,
Wata yar tsohuwa suka gani zaune a falon saman wani tafkekiyar kujera ta alfarma,mai kyau da laushi,, tare da wasu yan mata biyu sai wani dan karamin yaro da sukaji sunan shi wai Jacob,
Yan matan suka amsa masu tare tare da nuna masu kujera su zauna,
Nan suka gaida su cikin mutunci kamar yadda suma suka tare da mutunci,
Maryam sai kallo takeyi tana dan yatsine fuska duk da gidan yai madu bazata
Don kamar ba,acikin kwantagora suke ba, lokacin,
Malam A,A yace madu munzo gaida Joseph ne ko yana ciki,
Yar tsuhuwar nan taiwa yan matan wani yare, na IBO tana mai yamutse fuskan ta,
Sai gudan mai wani dan guntun buje iya cinya tace yana barci pls,
Maryam kallo guda tai masu takauda kanta gefe guda don takaici,
Ejoma ce tace wa Ruth da yaren su haba kibari su shiga mana tunda har kikaga baba yabar su sun shigo,
Ku shiga ciki ta nuna masu hanyar wani dan siririn corridor, tace yana ciki,
Nan suka mike suka shiga inda aka nuna masu, yana gurin,
A lokacin KB da Jibrin duk suna gurin shi atare da shi,
Wani da ga cikin yan uwan Joseph mai hausa badarniya yace kutafi pls yana barci ne,
Maryam ta bata fuska tare da hararan mutumin Ejoma wace ashe tana bayan su tace kabari su shiga baba yabarsu suka shigo
Dan takawa sukayi suka isa inda yake kwance saman wani tafkeken gadon mai cin kusan mutun shidda,
Idon shi a rufe kamar mai barci saidai ba barcin yakeyi ba,
Yana jin duk abin da akeyi,
Kafar shi da hannun shi suna daure da wani bandeji fari kal,
Duk wa yanda ke gurin sunyi zugun ga wani a tsaye da alamar likitane,shi,
Assalam naganin shi yace little mummy kamar Uncle Joe,
A hankali ya bude idon shi don jin muryan Assalam da yayi,
Kallon su yakeyi gaba dayan su da suka shigo dakin, alokacin,
Dan murmushi ya kago a fuskanshi duk da zafin ciwon da yake ji,
A hankali suke gaishe shi fuskan su fal da nuna tausayin sa,
Shima dai da kyat yake karba masu, gaisuwar cikin nuna kulawar shi ,
Yanabinsu daya bayan daya da kallo har idon shi ya sauka,akan maryam
Irin kallon da yai mata yasa A,A dan juyawa don yaga ko itace yakewa wanan kallon,
Saidai yaga Assalam rugumay a jikin Maryam din ,
Wanda alama yanuna yaron yake kallo,
ZEEEE MAKAWA
[2/21, 9:11 AM] ‪+234 806 595 8685‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
2⃣5⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
A cikin cijewa da daurewa ya furta sunan Assalam a hankali,
Yana mai kokarin yi mai alamar da ya karaso gurin shi,
Malam A,A shida KB suka gane mai yake nufi da yaron,
Suka ce Allah wai kazo inji uncle, cikin sauri Assalam yadan make hannun shi alamar bai zuwa, ya shige cikin jikin Maryam wace ke rike dashi tun shigowar su,
Dariya kowa yasawa Assalam din wanda ke gani kamar ba Joseph din daya sani, bane a kwance,
Don ganin irin bandejin da akasa mai fari kal a hannu da kafa,
Ànty Dije tace Assalam baka zuwa gurin uncle yau,
Joseph dake kokarin nuna daurewar shi, da kuma cije bakin shi don ciwon da yake ji,
Ganin irin wanan yanayin da yake ciki ne yasa maryam duk taji tausayin sa ya kamata a,ran,ta,
Bata san lokacin da furta a hankali ba murya kasa,kasa, da Sannu ya jikin,
Da, sauri Anty Dije har A, A, suka waiga ta don jin furucin ta yau akan Joseph wanda arayuwar ta taki jinin shi saboda baya sallah,
A hankali cikin cije bakin sa yadan furta, a hankalo cikin dauri, Thank, 'God,
"Nagode,
Yace cikin murya maiban tausayi, irin ta marasa lafiya
Sai a lokacin jin dakin yayi tsit alokacin maryam ta dan tsargu, da cewa kila ita ake kallo,
Da wutsiyar ido tadan kalli, gefen ta aiko ita dince malam A,A kewa kallon mamaki shida anty,
Kata na a dan sunkuye a kasa ta ce a hankali safiya mudan fita daga waje har su fito,
Tayi hakane don tafitar da wani abu azukatan su,a lokacin,
Yin hakan ko yadan wanke ta ga A,A wanda zuciyar shi tadan rude duk da yasan cewa ba wanan ga Maryam
Don ita yarince mai kishin addainin ta sosai,ba,ata taba hurda arne ba arayuwanta ko ta arziki ne,
Daidai zasu fitane saiga Aisha da Amina cikin shiga irin ta wayayyun yan mata
Dauke da wasu irn manyan ledoji a hannayen su,sai tako sukeyi guda, guda,
Wani irin mugun kamshi duk ta gauraye gidan da maryam ke ta tsandar zama, tun shigowar su,
Joseph yadan so yamike amma san yakasa cikin dauriya yace wa su maryam da safiya, nagode sai anjiman ku,
Aisha tabi su da kallon mamaki don sam bata gane cewa maryam bace
Ita a,zaton ta wasu yan matan shine can sukazo gaishe shi,
Har ta fara masu kallon kunyi kuskure yan mata,
Sai idon ta ya sauka akan Anty Dije wace ke zaune saman wani kujera dake facing din inda Joseph yake tana dauke da Issalam,
Dan dariyar yake tayi don ganin tare da Anty wa yan nan zukazukan yan mata suke,
Nan suka gaisa sama sama da,su suna mai kara tambayar ya jikin shi,
Aisha don nuna kosawa da kuma waye wa sai zare dan gyalen da tayafo saman jikin ta tayi
Tana kokarin zubawa Joseph abincin da suka shigo dashi,
Shikuma daga kwance yai nuni da a,a yana kokarin nuna wanda su Anty Dije sukawo,
Wani iri Aisha taji a lokacin, azuciyar ta tace ya kamata fa tai maganin wanan matar haka wace Joseph ke kulawa tankar yar uwar shi,
Amma afili sai tai wani murmushi, Mr Ema yashigo yana fada cewa bai yarda kowa yakara kawo ma dan shi wani abu ba,
Yanata fada da su Ejoma da Samuel har maman Choima,
Joseph cikin karfin hali ya dan nuna Anty yace she, is my sister I always eat from her when I was in the town,
Da mamaki Mr Ema ya waiga gurin Anty Dije don ganin matar da Joseph yace itace mai bashi abinci,
Kara cika mai ido tayi don sai yaji bai iya cimata mutunci akan yadda yake rufe idon shi yai wa wasu,
Kamar zai yi magana sai kuma ya sa kai kawai yafita, yabar dakin,
Sai a lokacin Assalam yadan rarafa zuwa gurin Joseph ya zauna gap da shi,
Su maryam suna falo zaune ana kallon kallo tsakanin su da mama da Ruth,
Ejoma ce tafi tadanzo inda suke zaune cikin matsuwar su Anty su fito subar wanan gidan maikama da kurkuku,
Jin takon su fitowa yasa saurin mikewa don shirin tafiya,
Ànty tace bazaku shiga kuyi sallama dashi ba,
Kai maryam ta kada mata alamar aa,
Sun danbar gidan maryam tai yar siririyar ajiyar zuciya mai nuna wani alama,
Sai a lokacin A,A yace gaskiya ya na jin jikin sa sosai karfin haline kawai,
Anty tace ai ga yadda ake fafi ba,a sa rai cewa sun fita daga cikin motar,
Maryam da sai yanzu tai magana tace da yamutu a kafiri kenan,
Kai, kai inji anty Dije wacce sam bata son wanan halin na maryam akan wanan mutumin watau, Joseph,
Dalilin wanan accident din na Joseph aka dage bukin KB
Wanda shi KB din da kan shi ya bidi alfatman cewa yana son adan daga bukin don wasu bukatu nashi,
Shiko yana ganin cewa hakan baidace ba ace yana bukin shi ga Joseph a kwance ba lafiya wanan ne dalilin daga bukin da yayi,
Sannu, sannu akwana atashi Allah yaba Joseph sauki,
Tun yana dan iya fita kofar gidan su har yadan fara bin abokai suna kaishi yawo cikin gari,
Yau ma kamar kullun dayake damana ya sauka akasa ruwan sama yafara samuwa,
Hadari aka hada sosai ko ina a gari yayi jajir da alamar akwai iska atafe da wanan hadarin
A lokacin Joseph yana tare da yaya illiya hira wanan hadarin yataso,
Sanin cewa bawai, kafar mai lafiya gare shi ba sosai a lokacin
Hakan yasa shi barin har iskan yadan rage ko agama ruwa,
Iska sosai akayi sai dan yayafin da ya biyo bayan hadarin wanda ba wani ruwa mai yawa akayi ba
Suna fita waje sukaga yadda iska yaiwa mutane barna sosai agari,
Yaya illiya na cewa subbahanallah shi kuma Joseph cikin kidimay wa yace, Allahu Akbar,
Da sauri yaya ya kallo shi da wani irin mamaki, don ji yayi kamar ba shi bane yace hakana,
Sai kuma Jesus crisi muna ciki haka akai wanan iska haka,
Bayan sunyi sallama da yaya illiya, ya kama hanya zuwa gida,
A hankali yake tafiya zuwa gida, a lokacin saboda yana dan lalaba kafar shi ne,
Kusan zuwa unguwar su yaga gidan wani malami da ake cewa,,MUSA, JA, don mutumin fari ne sol, da shi,
Yasan shi tun yana yaro yakuma san gidan shi a cikin uguwar tasu,
Gidan yaga ni duk katagar gidan azube duk mai wucewa yana ganin shi,
Malam musa ja Joseph yagani yayi tagu a saman dakalin kofar gidan shi,
Ga matan shi duk mai wuce wa yana gani sai kuma wani makwabcin malam musa ja,
Shima gidan shi tsohon gina ne sosai don duk haka su ka taso suka ga ginan har yanzu suna dan maneji da abin su,
Har yai kamar ya wuce sai kawai yaji bazai iya ba don haka ya yo ribas baya da motar shi,
Cikin dan dangyasawa ya isa ida mutanen suke tsaye cirko cirko
Ya ce malam yau kuma abinda yafaru ke nan Allah ya sauwaka,
Sukayi mai godiya kula masu da yayi ya juya yana mai jumamay abin
Abin na malam musa da makwabcin shi yafi yawa,
Don su ga zubewar gatanga ga kwanon ginan ya hankade ya kware sama,
Sun dade da mahaifin shi a waje suna maganar wanan irin iskan da tazo wa mutane yau,
Nan Joseph ya ba mahaifin shi labarin makwabtan su, abinda iskan yai masu,
Yayi tsan manin zai ji yace masu koda sorry ne sai kawai yaga ya yi murmushi,
Shiko Joseph duk tausayi su malam musa ja ya kamashi da wanan tunanen ya kwanta,
Saidai sam barci yaki daukar shi saigani irin halin da yaga su malam musa da makwabcin shi aciki yakeyi,
Wayar shi ya lalubo, nobar Hamza yakira,don su KB da,Jibrin ba su gari,
Nan yai mai irin bayanin abin da yake so yai mai tunda safe saboda yanzu dare yayi ko,
Waahe gari hamza ne tare da wasu magina sukayi wa Musa,ja, sallama
Hamza yai masu bayanin cewa wani bawan Allah ne ya ruro shi a gyara masu gida amma yace kada a fadi sunan shi,
Gyara sosai akayi don dakuna hudu akaja wa musa ja, shima makwabcin shi am mai daidai irin da ya rushe,
Aikin cikin yan kwanaki aka gama komai kamar yadda yaso,
Kafin agama aikin Joseph yasamu kira na gagawa yabar gari, zuwa diban depot din su da gwaunati ta bude
Ya koma da kwana biyu saiga su malam musa,ja sun samu labarin cewa, ashe Joseph ne ya taimaka masu daga wurin wani ma,aikatan ginan da sukai masu,
Aiko Mr Emanuel maimakon yai murna saiko ya hau masifa dasu ta inda yake shiga bata nan yake fita ba,
Harda cewa wai hausawa sun yi wa dan shi charming,
In ba hakaba ba ai yu,yu yadinga madu wanan dawainiyar ba haka,
Anan mutanen gari suka san cewa Mr Ema baison irin taimakon da Joseph kewa mutane daga cikin dukiyar shi,
Kowa ya shiga fadin albarkacin bakin shi, akan Joseph, din,
Joseph yasha fada mai tsanani sosai gurin mahaifin shi akan irin taimakon da yakewa hausawa
Karshe yai warning din shi kwarai da gaske akan in har yakarajin haka zai dauki mai mataki mai tsanani,
Bayan sun gama wqyan Joseph din yai yar ajiyar zuciya yana madaga wayan nashi yabishi da kallo
Kamar wayan ce taimai magana hakanan har ta bata mai rai,
YÃ u ta kasance ranan litani,itace ranan da ko bature na tsoran ta,
Cikin sauri Maryam ke komai don gudun makara,
Sai,dai duk saurinta, yau din ta dan makara,
Tun,da ga bakin gate ta hango malam A,A shima kusan a lokacin, yake shigowa, school