Showing 78001 words to 81000 words out of 255288 words
Chapter 27 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete
irin ihu sukeyi suna cewa please brother don't do that for us woo,
Gida ya rude da wani iri sabon kuwa kamar an masu mutuwa,
Har masu zuwa tambayar wasun su suka fara,ihu da kuka na bidan taimako, daga Jesus,
Shiko Yusuf yana barin gidan su gidan su Jibrin ya fara zuwa
Inda yasamu mahaifin shi ya sheda mai da kanshi saboda girmamawa,
Don yanzu yasan cewa sunyi mashi halarci sosai don basu kyamace shi ba alokacin da yake abin kyama agare su,
Baba yaji dadi kwarai xa wanan karamcin da Yusuf, yai masa, don jin dadi har da hawaye yayi don farinciki,
Yana murna adduan shi takarbu ke nan don a saudiya yai ta mai addu,an Allah ya nufe shi da komawa cikin islama ,
Saboda kyawawan halaiyan shi da yake yi tankar ba dan, Ahalal,Kittabu ba,
Nan Baba ya kara lurar dashi kyawawan hanyoyi acikin al,umma ,
Daga gidan mahaifan jibrin bai tsaya ko ina ba sai gidan Anty Dije ya nufa, sai dai kafin ya isa can saida ya tsaya yai masu tsaraba mai yawa, tukun, kamar yadda yasa ba,
Maryam duk kwanakin nan bata jin dadin jikin ta,tana fama da mura, har takai bata je makaranta ba yau, alhamis,
A,A daga school ya zo diba lafiyar ta don ya san cewa maryam batason magani ko allura
Shine ya sayo mata wasu maganin da ke maganin murah,
Tsaye suke a kofar gidan su, A,A yana rike da marfin kofar motar shi kafar shi guda yana ta cikin mota,
Maryam wace ke tsaye,sanyi da farin hijabin ta,
Idonta da suka dan yi ja saboda murah datake fama dashi, suna dan lunshe,
Suna facing din juna ita da A,A din sai dai dagani ita Maryam din tana nuna yar kunya take ji,
Tun,daga nesa ya hango su a tsaye ya kuma gane cewa itace a gurin tare da A,A,
Saboda yasan cewa suna tare, dashi, dadewa sai dai shi sam guy din bai kwanta mashi ba arai,
Don siffan wayewar shi tayi yawa, sosai yafi karfin wayewar yarinyar, aganin shi,
Alokacin da ya tsayar da motar shi dan nisa kadan da ga inda suke tsaye
Bai,fito ba amma dai kamshin shi,turaren shi ya isar da sakon cewa shine a,gurin
Yadan jima zaune acikin motar shi yana wani abinda sudake ta waje ba su sani ba saidai rabin hankalin shi A,A din yana gurin Yusuf din,
A,A a zuciyar shi mamakin irin yadda Joseph karamin matashi dashi yake shiga irin wa yan nan motocin haka masu mugun tsada,
Maryam ce ta,katse mai tunanen shi da cewa, Kuji wanan yazo ke nan zai damu mutane kwana biyu yahana mu hutu,
Haba dai ai yanzu kudashi kun zama daya don irin shakuwar shi da gidan nan yai nisa,
Kam wallahi kan bamu zama daya ba taya zaka hada mu da arne wanda bai sallah,
Kawai dai yana zuwa ne don yaran nan sune abokan hiran shi,
Kina da sauran fahinta maryam ai zuwa yake yi kawai don gari su dauka cewa yana hurda da musulmai bawai yana kin su ba,
Amma wanan ai irin mishon din,nan ne bat da musulmi,
Kagan shi kamar na Allah amma cikin zuciyar shi baya kaunar musulmi ko kadan,
A daidai wanan lokacin Yusuf yafito daga cikin motar, shi , direct inda A,A ya ke tsaye ya nufa yana mai mika mai hannu yana cewa Assalamu, Alaikum,
Gabadayan su saida sukaji wani irin don jin furucin shi na yau,
Saboda sam ba su sancewa Christian suna sallama irin ta muslumai ba,
Saida maryam tadan nisa tukun tare da jan dogon numfashi,,
Cikin mutunci Yusuf yagaida A,A, wanda ke da sauran mama a makale a fuskan shi,
San nan Yusuf yadan waigo inda maryam take tsaye rakube a jikin bango,
A,hankali ta furta sannu da zuwa, saboda wani kwarji da taga yai mata a ido,
Yusuf din yakalle ta suka hada ido sai, tai saurin sunkuyar da kai kasa,
Wani irin juyowa AA yayi wanda bai, masan lokacin da yai hakan ba da wani irin mamaki ya kara baiyyana a fuskan shi,
Daga Yusuf har Maryam wace kanta na ,a,duke, lokacin ba wanda yasan yana yi,
Ciki ya shiga direct, saidai yadan tsaya ta kofa kadan ya kwada sallama,
Sabanin da dayake shiga sai yakai ciki yai sallama,
Assalam wanda sun dawo daga school ke nan,yana kwance falo yana home,work,
Zubur ya mike saboda fahintar muryan Yusuf da yayi, ba yau ba, duk inda yaji muryan shi zai sheda shi,
Da gudu ya sheko ya rungumay shi, don farin ciki
Shima din rugumay yaron yayi yana mai jin dadin ganin shi
Anty ta fito da fara,ar ta,cikin ta wanda har ya fito,
Anty Dije tace mun yi fushi da mutanen Abuja ne ko Lagos,
Yai yar murmushi ya shafa guskan shi sai kuma ya kama kan Assalam zuwa kofar falo,
Inda Anty Dije ta bude mai don ya shigo, gaskiya ba laifi hakan yasa yake kara son gidan Anty Dije don tsabatan ta,,
Komai na gidan,ta tsab zaka gan shi bakamar na sauran gidaje ba,
Yusuf da murmushi a fuskan shi yazauna yana mai cewa Anty Dije mun samay ku lafiya,
Nan suka fara hiran zancen maciji da yasa su agaba a ma,aikatar da sukeyi,
Nan dai yafara,ba ta labarin yadda abin yafaru, atakaice, inda Joseph, din yace, gaskiya sun bashi tausayi dayasan suna gurin zai iya sayen gurin yabarshi don su kawai,
Amma saida aka kore su ne yaga yadda suke da yawa kamar tashin hankali,
Maryam wace tunda ta tunkaro shiga gida take jin muryan Yusuf
Cike da jin haushin yadda Anty ke wani nan,nan dashi, take ji,
Da sallama tashigo amma kanta yana gefe cike dajin, haushi, lokacin,
Kamar mai rada yace, don Allah in,ba takura,ki karbi wanan key din ki sa,a kwasowa yara, tsarabar su a bayan mota,
Ganin yadda ta tsaya sanin bata jin dadin jikin ta,
Tace wa yar uwar ta,ta, zaki iya kuwa Maryam, ko kuma kisa wasu yara su kwaso sai a sallamay su,
Sautin murmushin shi taji yana cewa anty aiba wani abu mzi yawa bane bari kawai in,fita in,kwaso,
Dama don naga wanan guy din a kofane shiyasa ban shigo dasu ba,,
Key din da ya mika mata ta duka daniyar karba batare da tai wani magana ba,
Cikin rashin , shikuma ya yunkura yatashi,don ya,tafi ya kwaso kayan don ganin ledar magani da yai a,,hannunta,
Fuskanta da goshin shi suka dan gwauri juna, har sai da tasa yar kara, tadago ta, dube shi amma sai taga idinshi kamar na mai jin barci,
Da sauri ta kawar da kanta daga kallon shi, tana mai dagawa,
Muryan ta narawa, tace mai sorry pls,
Key din dabata daukaba ke nan ta nufi hanyar dakin ta,
Shiko Yusuf kamar bashi ba, ya mike a hankali rike da hannun Assalam, suka fita daga falon,
Kayan da yace bayawa su maryam ke jin anata jibgewa a falon, a ranta tace shine wai bayawa,
Takuma kara cewa wai shi wani irin mutum ne wanda baya jin zafin kashe kudi, ne haja
Dama ace shi musilmi ne da ya more rayuwar shi wallahi,
Muryan shi taji yana cewa anty Dije kiyi hakkuri Anty,
Kafin ya karas fadar abin da zaice sai sallamar wani kanin mijin Anty Dije ya katse mai maganar,
Nan ya fara mai hira irin ta maula suna ta zance irin yanayin da kasa ke ciki a lokacin,
Har wani Ladani mai zakin murya a wani masallaci dake makwabtaka da unguwar su,
Yana kiran sallah azuhur,
Agigon dake daure a hannu shi ya diba sai ya mike zubar yana mai kokarin sance agogon dake a hannun nashi,
Inda Assalam yake ya dan kalla yace mai, dauko muna buta, friend
Da gudu yaron yatafi,batare da wani mamare ba,
Anty Dije wace a lokacintake duke tana kaida kayan da yara suka zube mata akofar falo,
Tai saurin dagowa daga duken da take tadan kalli Joseph wanda ke kojarin tankwafe hannun rigar shi da kyau,
Ba shiri yafara gagauta alwalar shi, batare da yai wa kowa magana ba har yakare,
Duk,kan su suna tsaye soro, suna ganin ikon Allah,
Anty Dije wace cikin mamaki take kallonshi har zuwa yanzu da yake kokarin mikewa ya rikowa Assalam hannu,
Yana yar murmushi yace barin dawo anty kawai saikiji karin bayani,
Tun zaman ta da Yusuf sai yau zatace taga fararen hakoran shi a waje,
Nan yabarta cikin mamaki yai saurin wucewa massalaci, abin shi,
Wani irin dariya da ihun jin dadi Anty Dije tasa a lokaci guda
Wanda hakan yasa maryam daje kwance daki tana shirin barci dirowa daga saman gado tayo waje don ga ni komay ke faruwa da yar uwar na ta,
Lafiya Anty, maryam ke tambaya cikin nuna zakuwar ta, da son ji komay yasamu haka na farin ciki,
Maryam Joseph ya musulunta fa da,gaske maryam wace ke tsaye daga nesa kadan da yar nata,
Ai, tsale guda tayi sai gata agaban anry Dije tace kai,fa Anty,
Keda ke daki dani da jamil mukaga mamaki yanzu ai,
Don kinga inda yai alwala yanzu yafita, zuwa sallah,
Allahu Akbar,Allahu,Akbar maryam ta iya furtawa kai don komai ma ya bace mata, alokacin,
Nan suka shiga murna tankar wani dan uwan su ne na jini yasamu wani alheri,
Yakai wani lokaci kafin ya dawo dga massalacin inda yasamu har Anty ta idar da sallah tana zaune tana addu,a,
Saida ta shafa ta waigo inda yake taimai murmushi tace ashe labarin da muke ji da gaskiya ne,
Yace Anty Allah ya nufa kuma likaci yayi, nan yafara ba Anty labarin tun yadda ya kai kanshi massallaci gurin, liman har zuwa yadda sukayi da mahaifin shi,
Ysu din yafada matacewa shi musuluntar shi ba gudu baja da baya
Don Allah yayi abinshi sun dauki lokaci tare da Anty yana bata labarai masu ban tausayi gamay da irin halin rayuwar da ya shiga, da kuma wasu ire, iren yan yaren su da indan suka musulunta irin wahalar da suke sha, don rashi kula daga yan uwan, jinsin isalama,
Cikin canza fuska wace ta sauya zuwa ta ban tsusayi, yace ma Anty Dije,
Matsalata guda yanzu yadda mahaifina zai shiga wani hali, don nasan zai sha wuya gurin yan uwan shi tare da members na su,
Amma idan nadaure nasan cewa komai zai wuce insha Allah
Tare da Assalam suka fita zuwa gidan Abdullsamad,
Nan ya kwashe duk yadda sukayi da mahaifin shi yafada mai,
Dan dattijon yana mai girgiza kai yace sai kayi a,hankali yanzu don duk wani hanya nasamun ka zasuyi kokari suga cewa sun, kawo ma farmaki,
Zasu iya bin duk wani hanya don su,ga cewa sun saka acikin wani hali,
Yusuf wanda ke zaune yana sauraren dattijon yai yar murmushi mai nuna takaici aciki
Dattijon yace yes mahaifinka nasan halin shi, sosai Yusuf zai kawo ma attacks sosai,
Don ban manta irin abinda yai min ba , alokacin da na shahada kamar ka,
Nan yabawa Yusuf labarin duk yadda Mr Ema yaita sa a,na,kaimai attacks,
Sam yusuf baiji dadin wanan labarin ba don a yadda yasan mahaifan nashi atare bai zata, zai iyasa ai ma haka ba,
,
ZEEE MAKAWA
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
FUREN JUJI
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
3โฃ4โฃ
ZAINAB IDRIS MAKAWA,,,
Barkan da jumma,a yan ,uwa Allah ubangiji yasada mu da alherin dake cikin wanan ranar mai albarka,๐๐๐
Maganar da Abdulsamad ya fadawa Yusuf gamay da mahaifin shi ya tsaya mai arai, sosai,
Don haka yasan cewa ko shi bai tsira ba ke nan don mahaifin nashi zai iya yin fiye da haka akan church din nasu,
Don haka ya sa a,zuciyar shi cewa, dole ya dauki duk wani mataki wanda yasan cewa ,za,a iya kawo mai hari akai,
Washe gari ya kasance ranar jumma,a ce, don haka tunda zai fito ya fito da kayan da zai shirya kanshi a ciki
Don barci kawai yakaishi gidan su cikin dare sai dai ya kula da cewa kamar an,masa bincike a dakin,
Murmushi yake yayi shi kadai a cikin dakin, don haka duk wani abin da yake bukata ya hada su guri guda,
Tunda safe da zai fita yakwasa sai gidan, รnty shi Dije itace yakai wa ajiyar kayan shi masu muhinmanci, dake gidan nasu,
Maryam wace ke zaune a lokacin gaban mirrow tana make-up,
Taji muryan shi ya na ta kwada sallama akofar shigowa gidan ,
Haka kawai taji zuciyar ta ya tsinke mata, kamar mai tsoro,
Zubur ta dan yi ta mike a gaban mirrow saboda ta sheda ko muryan waye, ke sallamar,
Saidai, yau ta tsinci kanta da dan jin nauyin ansa mai sallamar tashi,
Saboda irin yadda tai hating din shi a matsayin shi na Christian a da,
A,ciki ciki ta ansa mai sallamar tashi, kamar wace ke rowar magana,
Dankwalin da tafara daurawa rike a hannun ta tadan leko tawaje don tabashi izinin shigowa ciki,
Saboda Anty Dije tana bayi gurin wanka alokacin,
Ido biyu sukayi dashi, yana saye da wata riga mai hannu iya damtsen hannu, sai wani dan ado da akaiwa hannun rigar kamar kwalar riga ta wuya,
Shima wuyar rigan irin hannun rigar ce akai yi ta,
Sannu da zuwa ta furta acikin muryan ta makama da ta rowa kullun,
Sai kuma can tace tadan shiga wanka yanzu zata fito
Abinda kawai ta iya fada ke nan a darare, kamar mai jin tsoro,,
Fuskan shi a natse kamar kulun yace ba matsala ga wanan pls ki bata ta aje min zan je in dawo,
Sigar da yake maganar shiya sata dan dukar dakai don komai nashi a kasaice yakeyin shi,
A, hankali yatako har, gaban,ta ya mika mata jarka
Wace batasan ko tamaye ba,ita,dai ta karbane kawai,
Har yabar gidan tana tsaye a inda ya barta rike da jarkar da ya miko mata,
Karar rufe kofar shiga gidan ce tasa,
Da sauri ta juya zuwa ciki, sai yanzu ma taji haushin fitar da tayi da tasani ma kawai ta amsa mai ata cikin daki,
Turus tayi a folon ganin, รnty Dije zaune tana shiri abinta acikin natsuwa,
Anty ce tace tomay zance tunda kin ce masa na shiga wanka ko,
Inda take ta nufa da jakar ta aje saman wani kujera tafita batare da tai wani magana ba,
Yusuf kuwa yana barin gidan su Anty, kasuwa yatafi
Abinda yaksi shi kawai shine yasamu shago babba mai kyau yasaya,
Allah yabashi sa,a yasamu shago irin wanda yake so,
Ba bata lokaci akai komai yasa hannu ya biya,
Kafin tabar gurin har cikin IBO dake layin sun sheda wa mahaifin shi cew gashi a kasuwa yana diban shago,
Ganin lokacin sallah jumma,a yana gabatowa shiyasa yai haramar komawa, gidan su Anty
Tafe yake yana shawara a,ranshi cewa gobe zai tafi gurin mahaifinshi,yasanar dashi,
Cewa ya sai ma Abdulsamad shago saboda Allah da Annabi
Saboda duk irin halin kuncin da ya jefa Abdulsamad din saboda akidar addini yasani,
Don haka zai fara sanar dshi cewa sun san mugun halinshi akan wanda duk ya canza addini daga cikin su,
Yasan idan har yafada mai garan dagaran zai samu saukin duk wani kulli da zasuyi mai,
Yana cikin shawarar ne azuciyar shi har ya kawo kofar gidan Anty Dije,
Wanda kawo,war yai dai,dai da lokacin da A,A shima yake kokarin aje motar shi don sauke maryam,
Da ya dauko daga school, don yau jumma,a bata wani dadewa, a school din
Sun,na zaune acikin mota, suna dan taba hira saidai kafarta guda yana a tawaje da sauran jikinta,
Hikimar yin haka gareta shine kare zargin yan unguwa masu sa ido a masu zama da maza cikin mota suna masu suna,
Kallo guda yai masu ya,kauda kai, gefe, guda batare da yakara ba,
Don yarasa komay yasa sam baya son yagan su atare da wanan guy din,
Yasamu Anty ta aje mai abin karyawa a falon ta bayan sun gaisa ta gabatar mai da abin kari, kumallo,
Sai yaji wani irin kara girmamata yashige shi shiyasa yake son al,amarin ta, don tana saurin fahintar shi,
Muryan ta yaji tana cewa, tasan cewa baici komaiba har yazu saidai tana gani abincin yai sanyi ko zuwa yanzu,
Ya zauna ke nan da niyar fara ci maryan tashigo gida cikin takon takalmanta da ke fidda sauti,
Tundaga kofa tai arba dashi cikin sauri takawar da kanta gare ahi adaidai, lokacin da yake kokatin zuba ruwan zafi a cup
Duk da takwaso nata kalar yunwa baisa ta tsaya don ta,karya ba sai shigewar ta tayi kawai aciki
Anty Dije ce tasa mata kira don tasan cewa itama bataci komai ba tau tabar gidan
Alokacin maryam harta cire hijab dinta daga ita sai