Showing 126001 words to 129000 words out of 255288 words

Chapter 43 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1353

idon take mata karya ba wani irin tsadaden murmushi taga ni makale a fuskan shi,
Cikin sauri takawar da kanta gefe guda tana mai jin wani nauyin shi,
Kamar ta juya takoma ciki alokacin sai dai ta daure kawai ta, nufi hanyar kitchen din su tankar bata gan shi ba,
Tunda Yusuf yafita wanan lokacin bai dawo gidan ba sun shiga gari da Assalam da sauran abokai,
A cikin shigar kananin kaya yadawo da dare bayan sallah isha,i, tare da Assalam wanda ke dauke da ledar kayan sweet kala,kala,
Ko da yai sallama ya shigo maryam tana cikin shigar wasu English wear sun mata kyau so sai,
Duk da dare ne mutum zaigane cewa ta gyara fuskan ta tsab da kayan makeup,
Ga kamshi dake tashi kamar wace ke sana,ar kayan kamshi,
Muryan ร€nty Dije ce ke cewa maryam don Allah zo ki tafi hakana kin san halin As,ma,u da saurin rufe gida,
Jin muryan Yusuf yana cewa bissimilahi alokacin da zai zauna,
Maryam dake tsaye tana kokarun sa, takalma tace mai,
"Sannu da dawo wa"
A , kasalance yace "Yauwa"
Assalam ke cewa little mummy ina zaki zani nima,
Kai wani irin son yawo ne haka ?
Kadawo ko zama bakayi ba zakace wai zaka,
Assalam kai baka gajiya da yawo ne wai, kazauna taje tadawo ko ita dare yayi don dai ina son takarbo min kayan yau ne,
Dare ya,yi gaskiya bari mu sauke ta kawai inaga zai fi,
Da mamaki maryam tai saurin dagowa don batai tsan,manin haka ba sam
Idan son samune ita gaskiya sam bata son shiga motar shi
Saboda yana jagula mata hankali duk lokacin da tashiga,
" Wai, har hankalina yakwanta inji Anty Dije ta juya gurin maryam tace kin ga ai kin samu sauki
Ai yanzu zan dawo da sun zauna kawai,
A, lokacin ya mike tsaye yadauki Key's din shi da yazube saman center table,
Gadan gadan yanufi kofar fita wahe batare da yai mata magana ba,
Ai, da sauri maryam tamara mai baya don gudun masifar Anty,
Acikin motar shi yake zaune, tun daga nesa zakaji sautin karatun Al,kur,an mai girma yana tashi suratu Fussilat,
Maryam nakara so,wa ta bude motar daniyar shiga,
Amma sai batafa Assalam aciki ba shi da yaja mata wanan tafiyar,
Da sauri ta kara lekawa cikin motar ko zata ganshi a baya saida baya ciki,
Turus tayi tana zazare ido,
Sai ta dan ja baya tana dan zare ido kamar mai jin tsoro
Ganin har ya kuna motar ya sata saurin shiga jiki ba karfi kamar an zare mata lakka,
Ta zauna a hankali tare da cewa ya akayi Assalam bai zo ba kuma,
A hankali yafara tafiya batare da yabata amsa ba ya hau saman titi a hankali,
Gyaran murya yayi a hankali cikin wani irin soft voice yace aike ce karshen fitowa
May yasa baki fito da shi ba ke, ?
Maryam wace tasan gatse ne yau mata, ta juya abinta cikin natsuwa, tana kallon fitilon dake a gefen hanya,
Sai dai kira,an dake tashi a motar take bi a hankali,
Wayar shi ce tai kara alokacin ya dauka yana yar fara,a
Sadiya sorry nadan fitane zuwa wani guri sai dai kila bazan dade ba,
A hankali ya mika hannun shi yana kokari rage karar sautin dake tashi,
Maryam wace taga ya rage saurin tafiyar da yakeyi batasan lokacin da tai yar tsuki mai sauti ba,
Sai,dai jin karar tayi yafito fili wanda sam bataso hakan ba ita,
Ok to kiti hakkuri tunda ina gari aiko zuwa gobe ne zan shigo,
Eh a hanya nake zan kai maryam unguwa ne amma ba dadewa zamuyi ba ai,,,
Tuni maryam kan ta yadauki caji saboda jin kiran sunan ta da akayi a zancen
Bata karasa jin haushi ba sai,da taji ana cewa maryam ce kuma yau baki sani ba ?
Saida su kayi sallama da juna tukun san,nan yadan ci gaba da tukin motar shi,
Maryam yace cikin wani murya da zakace dole akasa shi yin magana alokacin,
Fuska a daure yace may yasa ki kai muna tsuki, pls,?
Wani kululu taji don ai tambayar raini wayo ne wanan
Amma a fili sai cewa tayi yaushe ?
Murya kasa,kasa irn ta wanda bai son magana da yawa, yace may Sadiya tai maki ki,kai hating din ta dayawa haka, ?
Bakaramin kaduwa magana tasa maryam ba,
Amma sai taga cewa tai shiru kawai shine daidai, yafi tace zata bada amsa,
Maryam pls stop hating me like, dis,
Wani abune ya soke ta akirji da ya furta wanan magana
Murya na rawa tace ni
"Ya Yusuf " ?
Kai ya kada mata alamar eh,
Cikin kwantar da murya tace,
Nashiga uku ta furta a fili,
Azuci kuma tace maganar Anty yau ya tabbata ashe ko shi yasan cewa bana son al,amarin shi,
Kafin wani lokaci hawayen da suka cika mata ido suka zubo,
Are you crying maryam,?
Why ?
Matsowa yayi gab da ita yana mai mika mata hankici don tagoge fuskan ta,
Da sauri maryam tadan ha baya kadan kamar wace taga abin tsoro,
Ki yi hankuri pls ban san cewa maganar zatai maki zafi haka ba ?
Har da zubar da hawayen ki masu mahin manci, da ma,ana,
Cikin hawaye wasu nabin wasu tace may kai min dazan yi hating dinka
Bayan yawaita alherin ka a,garemu ko da yau she,
Murmushi yayi ya ce gaskiya bana jin dadin the way you are treating me,
Haka kawai maryam ta samu kanta da cewa,
Insha Allah bazan sake ba Ya Yusuf,
Fuska daure yace sam bana son ina batawa mutum rai maryam bansan ko may nake maki ba haka, ?
Ki fada min in daina pls,
Wani irin nauyi da kunya ya kamata tace,
Subbahanallah wallahi ni ba abin da kai min,
Ganin sun shigo cikin uguwar da zasune yasa shi cewa ina ne kwanar gidan da zasu tafi ?
To ki share fuskanki pls kada ki shiga tagane cewa kinyi kuka pls, ?
Ba musu maryam ta goge fuska da wanan kyalen da ya bata, ta goge fuskan ta a hankali,
Murya kasa, kasa irin ta mai rada furta, na gode,
Shiru maryam tayi batace komai ba,
Wani dan iska ya furzar daga bakin shi,
Kai maryam ta sadda kasa kawai,
A hankali ta bude motar tafita,
Binta ya,yi da kallo har ta shige gidan,
Sai a lokacin yai yar ajiyar zuciya,
Don yaji yarinyar raba shi mugun tausayi sosai, don bai zaci cewa tana da saukin kai haka ba,
Saboda yazaci cewa zatai mai rashin kunya idan yai mata magana,
Bai wani dadewa ba yaga tafito da wani kumshin kaya, dagani kayan sun mata nauyi tana ja,
Da sauri yafito yakama mata yabude bayan mota yasa mata,
Komawa tayi zuwa cikin gidan sai,dai wanan karon ta dan dade, Inda ta dawo dawasu kayan again,
Sallama taima shi ya dago kan shi ya karba a hankali,
Batai magana ba sai kokarin zaman da take yi shiru sukayi a lokacin da yafara tukin motar,
Kowa da abinda yake sakawa a zuciyar shi gamay da dan uwa,
Wayan shi tai kara inda a zaton maryam take tuhumar ko sadiya ce uwar naci,
Amma sai daga baya tagane da Ibrahim yake wayar don kiran sunan Ibrahim din da ya,yi
Sai dai da yaren su suke magana inda maryam ke ta mamakin yadda yake yare kamar bashi ba,
A falon Anty a,kazube kayan sako ne a ka aiko da su, daga Lagos,
Maryam ce ke fadawa Anty ta yadda Assamau tace kudaden kayan suke,
Yusuf eanda ke saman dining table yana zuba tuwon semovita da miyar kubewa danya,wanda akaiwa miyar stwee daban yaji, gadan manya,manya
Yadda maryam ke bayani acikin sanyi murya ya nuna mai alamar
Har yanzu rayuwar ta ajagule yake da zancen su,
Tun da har taki sake jikin ta har zuwa yanzu,
Kudin kowani kaya take fadawa antyn ta a hankali tana taya ta dubawa
Abincin shi yake ci a hankali kamar hankalishi baya gurin su,
Wayan maryam ce yai kara taciro shi daga cikin poss din ta,
A yadda take magana ko antyn ta dake kusa da ita bawai lalai, ne taji ta ba,
Mikewa tayi zuwa cikin dakin ta, karba wayan ta, dake a hannun ta,
Amma, wanda ke falo zai iya jin maryan ta,kamar tana waya har yanzu,
Sama sama tadunga jin muryan su don yakai wani lokaci agidan yana mata hiran kakar shi,

Sai yanzu,ne mutanenn gari suka gane cewa ya shigo garin,
Saboda duk kwana kin da, yayi agarin acikin gidan shi yake zaune, bai fita ba don gudu kada a rushe mashi plan din shi,
Wayar shi tai kaa alokacin da yake tuki motar zuwa gidan shi,
MY DAD
Yagani a rubuce yasan a kwai abinda ya faru ke nan tunda Dad yau yakirashi,
Ya dauka da cewa Alo,
Bai ansa mai ba sai magana cikin fada,fada ya keyiwa dan nashi,
Yace suna son kudin church don an,kawo masu sabon pastor ,
YUSUF yai mamaki kwarai da jin maganar mahaifin don alama ya nuna cewa har yanzu bawai ya saduda bane ke nan akan zancen shi,
Har yanzu yana mai kallon Christian ke nan ashe, ?
Dad iam not in your religion now,
So don't involved me in any church matters again pls,
Sai kuma ya juya da harshen su na ibo yace indai shi yake bukatar kudi kowani abu zai iya bashi a tsakanin su ,
Mr Ema wanda sam bai yi tsan mani Yusuf zai iya rufe ido yai mai haka ba,
Ahankali yadafa, kujerar da yake tsaye gefen ta yakai zaune,
Yana mai jin wani irin kunar zuciya atare dashi, lokacin,
Kwallar masu zafi ya matse daga idon shi saboda ya san cewa ya yi loosing din Yusuf ke nan har abada,
Shiko yusuf daga inda yake ya rintse idon shi saboda baiji dadin yadda sukayi da Dad din ba sam,
Amma yasan cewa hakan shine kadai hanyar da ta dace ya daina Dangantashi da akidar church,
Maimakon yaje gida sai ya wuce gurin Abdulsamad yafada mai yadda sukayi da mahaifin nashi,
Abdulsamad yace mai, ai da yabashi kudin kawai amatsayin kyauta idan yakai masu su suka sani,
Yace kasan cewa duk lokacin da zasuyi canjin pastor kashin kudi yazo kenan,
Shawarar Abdulsamad yabi inda yaturo mai dubu dari biyu chur washegari,
Shikuma yadauka yakai, church yace ga gudun mawar yusuf nan,
Aisai murna da shewa suna wakoki cewwa yusuf zaidawo soon,




ZEEE. MAKAWA
[3/24, 2:21 PM] 0mmer Farouk: .๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
FUREN JUJI
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
5โƒฃ4โƒฃ
ZAINAB IDRIS MAKAWA

Assalamu Alaikum yan uwa musulumai masoya novel din furen juji,
Nuna kaunar ga novel din shine taimakon kara min karfi cigaba daga gare ku,
Shawaran ku agare ni tankar taki ne mai kara min karfin hafbaka da cigaba
Nagode Nagode Nagode kwarai daga gaske ๐Ÿ‘๐Ÿ‘


Wasa wasa zancen Sadiya da Yusuf sai kara ci gaba yake yi,
Yanzu haka kokarin hada kayan mungani muna so
Da kuma kayan azumi da na sallah sukeyi, shida Anty Dije da Jibrin,
Yau ma kamar kulun a waya,suke zancen wasu materials da ya turo Ibrahim ya kawo mata, a sa acikin kayan,
Ganin kayan da kuma tsadan su yasa Anty Dije cewa Yusuf wa yan nan kayan ai sai a cikin lefe ko,?
Maryam wace ke sawa Abubakar Pampers, alokacin ta ce a to ku dai yi ta sawa in hau,kane abin,
Anty Dije ta manta cewa waya take yi sai tace wa maryam,
Abinda mutun ke so maryam a maida shi yake yi tankar kwai,
Dariya Yusuf ya yi daga cikin wayar yace Maryam ce ko ?
Anty ta bashi amsa da cewa itace ma na,
Yar bakar magana,wai muna sa kaya kamar bamu tunane,
Dariya yakarayi
Ya ce Anty
Ta karba mai yace don Allah duk kayan da Ibrahim yazo da shi jiya kiba maryan su pls,
What's,
Tafadi da karfin Allah ,har hankalin maryam ya dawo gurin ta da sauri ta dago tana kallon yar ta,
Lokaci daya maryam ta juyo tana fuskantar Anty nata, zuciyar ta tab da tambaya,
Ji tayi Anty nacewa Yusuf ban fahinci kalman abarwa Maryam kayan ba ?
Cikin wani irin razana Maryam tace wa Anty saboda may, ?
Sai kuma ta dukar da kanta kasa ta na mai jin kunar ran abin da anty tai mata,
Don may za suyi magana a tsakani su har anty ta daga murya Yusuf yaji su,
Tana gama sawa yaron Pampers din tamike tsam tabar gurin cikin kunar rai,
Da harara anty Dije ta raka ta har tabace mata dagani,
Kwance take rigingine fuskan ta na kallon silin din dakin ,
Sai,dai idon dake tab da hawaye,
A hankali tazauna bakin gadon tana kallon ta cikin jin takaicin irin halin maryam akan Yusuf,
Karan ledar kayan ne maryam taji yata dan dago kai,
Zaune tai kokarin tashi cikin mamaki take kallon yar uwar ta, ?
Mika mata tayi tana cewa Yusuf yace abar maki wanan kayan a matsayin kayan sallah ki namu in zai zo, zai zo da su,
Maryam wace ta bude baki da zumar yin magana sai Anty ta daga mata hannu alamar bata son jin komai,
Tace yai min bayanin cewa kayan sunyi yawa amfada mashi cewa sai za,a kai lefe ake kaiwa da yawa,
Don haka tun wutowar Ibrahim bayan Jibrin ya fada mai shine yai shawaran cewa bari yabar maki a matsayin kayan sallah ki,
Tunda wai rin su Jibrin ya sayawa safiyar shi don haka sai kuyi anko,
Bata san lokacin da tai yar ajiyar zuciya ba, don ta fahinci cewa ba fushi yayi ba ke nan,
Anty ta mike tsaye tana cewa sai ki daina fushi, ki, kirashi dai ki masa godiya don nasan halin ki, da basarwa,
A hankali tace to don har yan zu ba, wai ta gama sakewa bane gaba daya,
Batai saurin kiran shi ba kamar yadda batai saurin bude ledar kayan ba
Kayan suna aje a,gefe guda cikin ledar da akawo su,
Har zuwa yanzu maryam bazata iya cewa ga kalan kayan ba don bata diba ba ko, a,lokacin da Anty Dije take kokarin budewa dazu,
Saida ta tab batar da taga komai don haka ta tuna da ledar don ganin shi da tayi a gefen gado,ajiye,
Ledar ta jawo tafara zaro kayan a hankali, saida ta mike tsaye don ganin irin kayan dake ciki,
Materials ne da Swiss masu tsada har guda biyar a cikin leda kala masu kyau da daukar ido,
Kudin kayan zai kai kusan dubu dari uku da hayi,
Cikkn mamaki ta nufo waje inda Anty take tana goge kayan kitchen din su,
Anty kin ko ga kayan dake cikin ledan nan kuwa ?
Sai da ta juyu suna fuskantar juna take ce mata nagani maryam a shi yabani mamaki wallahi,
Ki diba fa yadda mutum zai maka,wanan irin alherin a lokaci guda,
Ni wallahi halin Yusuf tsoro yake bani mutun bai jin zafin kashe dukiyar shi haka,
Shin kin ma kuwa kira shi kun mai godiya maryam, ?
Wani irin kunya ya lulube maryam agurin cikin jin nauyi ta dukar da kanta tace ,a,a
Amma ko halinki sai ke maryam ban san wanan halin naki ko ina ki ka dauko shi ba wallahi
Ga baba nan ya ta yawon fadae alherin da akai mai ko ina ama ke irin wanan kyautar haka kin kasa kiran mutum ki masa godiya haba dai, haba Maryam,
Tsaki taja ta juya wa maryam din baya taci gaba da aikin ta,
A masife tana cewa idan kin ga dama kada ki kirashi ma maryam,
Haka tajuya takoma daki rungumay da kaya a hannun ta,
Wanka tashiga tagyara jikin ta tsab tai sallah shafa,i da wuturi, tadan kai zuwa tara da wani abu zaune saman sallayan ta,
Ta mike tsam zuwa bakin gadon ta da yasha gyara kamar ba a sama za,a kwanta ba,
Zauna wa tayi a hankali ta mika hannu ta ciro wayan ta saje makale yana caji,
Nobar Yusuf ne ta nema takai wani lokaci ta kurawa sunan ido ita kuma bata kira ba,
Can dai ta daure ta latsa nobar a hankali tare da gyara zaman ta, da kyau,

Yadawo agajiye don har dare yana office yau saboda kayan su da yashigo daga Korea,
Wanka yashiga saboda bai sha,awan cin komai ruwan tea kawai yake ra,ayi yau din
Dan karamin towel ya sa yana tsane run dake a kan,shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login