Showing 237001 words to 240000 words out of 255288 words

Chapter 80 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1367

jikin juna su,
Tundai maryam din wace ke ta aikin zuba shagwaba don duk Yusuf din ya rude a kan ta,.
Saidai har zuwa yanzu babu shiri sam tsakanin maryam da maman Choima,
Amma duk wanan kiyayyan da grandma take gwadawa maryam ,
Maryam dun sam bata nuna damuwan ta akai don ,
A mma acikin ran ta abin na damun ta sosai saboda dai da mijin tane take daurewa,
Watan maryam uku ke nan yanzu a Abuja tare da auren Yusuf,,
Maryam din ta murje abinta,don tasawa kanta kwanciyar hankali,
Duk zaman da Maryam tayi a,gidan Yusuf bata taba rokon shi komai ba,dai,dai da abin abincin da take amfani dashi, bata cewa akawo, sai dai tayi amfani da,abin da ta gani kawai,
Duk wanan abin Yusuf din yana hankalce da maryam,
Sai mamaki kawai take bashi saboda irin hakkurin ta dakuma juriyan ta,
Takardun fitan su waje yafito inda yadawo dasu daga office,
Maryam bata kusa yau ko da ya dawo tana can kitchen tana aikin,
Sai bayan ta gama hada komai ne ta samay shi a cikin falon shi na sama
Saye take da riga ruwan silba mai dogon hannu,an matse tsakiyan ,
A lokacin yana tsaye yana hada wasu na,urorin wuta, shigowan ta falon da sallaman ta yasa shi saurin dago kai,
Da yar murmushi makale a fuskan shi, ido ya tsura mata har zuwa lokacin da ta karaso gurin nashi,
Ajiyan zuciya ya saukar daidai lokacin da ta karaso gurin nashi,
Ina kika shige tun dazun maryam, nadiba dakin ki bakya cikki,
Kitchen tace mai a takaice, mikewa yayi tsaye yakara inda take,
Hannuta ya riko ya rike a cikin nashi yana cewa,
That's why na hana wanan shiga kitchen din don kada a shiga min time dina,
Yakarashe zancen da lakutar mata hancin kara jawo ta yayi
Inda a tare suka fada saman kujera guda yana rungumay da ita a jikin shi,
May kika dafa mun yau ya tambaye ta cikin matse mata yan yatsun hannun ta,
Cikin girmamawa tace sakwara na yi don grandmother,
Yaji dadin wanan maganan data fadi saboda ya na hankalce da ita akan irin kulawan da takeyi ma ta,
Zai yi magana ke nan sukaji motsi turo kofan falo da karfi saida ta iso tace excuse,.
Kokarin mikewa maryam keyi amma sai taji Yusuf din ya kara matse ta a jikin shi
Muryan shi taji cikin wani irin tsawa yace Get out,
A gigice ta juya baya jikin ta na rawa tan dan rusun nawa tana cewa sorry sir,
Maryam din ya daga a jikin shi inda ya mike rai bace ya bi bayan ta cikin masifa,
Da sauri maryam ta riko hannun shi nan yaja guri guda ya tsaya cak,
Juyowa ya yi da idon shi da suka canza a lokaci guda,
Amma kuma sai ya kasa cewa maryam din komai,
Shiru ne yadan ratsa falon a lokacin maryam ce tai saurin kauda shirun,
Tace uncle don Allah ka kyale ta don ba laifinta bane kila da abinda ya kawo ta,
Muryan shi narawa yace maryam don may mai,aiki zata shigo min har nan bayan tasan cewa dokane agida,
Koda baki nan sam banyarda da mai aiki ta shigo part dina ba tun lokacin danagani littafi,
Zanyi maganin ta don gidan zata bari gaba daya,
Ranshi a bace ya dauki remote din dake gefen shi yana dannawa yace ita dabbace dazata shigo muna daki babu sallama,
Uncle don Allah kayi hakkuri don dai ni iya zamana agidan nan ban taba ganin sun hau saman nan ba,
Dole a kwa dalilin zuwan ta nan din dan ko ba halinsu bane,
Bai, yi magana ba sai idon da ya zuba mata kamar mai nazarin zancen ta,
Sai a lokaci ya duko passports guda biyu ya mika mata,
Sai da tadan juya ta duba cikkin mamaki sanan ta bude
Passports ne na fita kasan waje tare da Visa, kai maryam tadago tana mai kallon mamaki,
A lokacin ya koma yazube kan kujerar da ke kusa da wanda take zaune,
Wata irin ajiyan zuciya ya sauke sanan ya furzar da iska daga bakin shi,
Har zuwa lokacin fuskan shi da sauran fushi a cikin sa,
Kwantawa yayi da bayan shi saman kujera yadan lumshe idon shi, yace,
Am hungry maryam,
Kallon shi tayi cikin yaudar so tace yau da wuri zakaci abinci haka ?
A cike da kasala a muryan shi yace sakwara fa kikai muna yau,
Cikin murmushi tace ai yana dinning yana jiran ka dama,
Mikewa yayi da sauri yace good
Sai ki tashi muje ki bani kafin miyauna ya tsinke ba mussu maryam din tamike tabi bayan shi,
Zuciyar ta fam da mamakin Yusuf yadda ya sake jiki da ita haka suke morewa
Yusuf wanda zai kai awa daya aguri batare yai magana ko guda ba,
Tun daga saman steps suka fara jin kamshin girkin a falon ,
Sundan kara steps ne suka hango yar tsohuwar zaune saman kujeran dining din ale,ale tana kwasan gara abinta,
Tun basu kara saukowa ba,suka ji muryan maman Choima tana cewa,
Cikin yaren su da fada na aika akiraka,kazo muci abinci amma shine don kana tare da,wanan muguwar yarinya ka koro yar aiken nawa,
Da sauri ya kalli maryam don maganar ta ya zama gaskiya ke nan,
Da kai maryam ta nuna mai dacewa su karasa mana,
Abincin da yagani a saman dining din shi ya karasa shi kaguwa da ya zauna, ya fara ci,
Don rabon shi da abinci tun abinda ta bashi da safe ya karya,
Maryam ta gaida mama tare da zuwa kusa don ta zuba ma Yusuf din,
Amma sai maman Choima tace cikin bacin kada maryam ta taba mai abincin da zai ci tabari ya zuba da kan shi,
Dariya maganar taso ta ba maryam din don dai tasan cewa itace tai aikin da hannun ta ai,
Don may za,ace wai yanzu kada ta taba wai ko don kada tasamai cuta,
Juyawa maryam din tayi daniyar barin gurin, ji tayi an riko mata hannu,
Ko bata juyaba tasan cewa Yusuf ne ya riko mata hannun nata,
Cikin yar sakin fuska maryam din tace uncle zan je in hada ma ruwan tea ne,
Ganin cewa ba bacin rai a fuskan nata yasa shi saketa, zuwa kitchen din,
Sam maryam batasan cewa Yusuf yana bayan taba kitchen din kusan a tare suka shiga,
Hawaye take gogewa a hankali da bayan hannun ta batai aune ba sai ji tayi ya riko mata hannun,
Cikin yar razana ta juya da sauri ganin Yusuf ne tai saurin wayancewa da cewa uncle bakaci abincin bane,
Baiyi magana ba sai hannun shi da yakai a fuskanta ya kara goge mata fuskan ta ,
Sannan ya dan jawo tazuwa gaban zinc din yasa ta gaban shi yai kaman ya kwanto mata,
Cikin murya mai kama da rada yace kada ki kuka pls na san cewa grandma bata kyauta maki,
Cikin daga hannu maryam tace haba uncle ai nima grand ma dina ce tunda takace don haka banga abinda zatai min yasani bacin rai ba,
Ni ina dai tunanen gidane kawai,ido ya kura mata har zuwa wani lokaci sai ya sake mata hannun,,
Yusuf bai koma dining din bs falon shi ya wuce abin shi zuciyar shi a cunkushe da bacin rai
Ranan karfe takwas sun shige master bed room shi da maryam wace ganin baici abinci ba tadan mai simply noodle takai mai har part din shi,
Haka rayuwan su taci gaba da tafiya inda maman choima taci gaba da tsangwamawa maryam
Ita ko maryam tana kokarin kauda kanta gare tana kaucewa damuwan mijin ta,
Satin da ya kewayo ne tafiyan su yazu don haka suka shirya tafiyan su ,
Inda maryam ta nunawa uncle cewa ya kamata su je da Pipkin,
Amma fir uncle din yaki sai cewa yayi wanan tafiyan nadaban sai in za suyi wani komawa zasu tafi dashi,
A waya takira Anty n ta dije tana sheda mata zancen tafiyan dije taimata yan nasihohi ta kuma bata wasu yan dabarun zanan aure again,
Haka ma safiya ta dauki lokaci tabawa maryam yan shawar wari ,

Kasar Italy suka fara sauka inda Yusuf din zai tsaya don wasu harkokin business din shi,
Don haka bai samu wani enough time din zama da yar amaryan tashi ba so sai,
Wanan shiga da ficen da Yusuf yake faman yi a kasar Italy din ya jawo mai gagarumin nasaran samun cigaban ckamfunan shi sosai don sun samu nasar sa hannun jari a,wasu kamfunar kasar,
Ana gobe zasu bar kasar Italy din ne yadawo gida agajiye saboda aikin da suka sha guraren sa hannu,
Rungumay yake da coth din shi a hannu sai hannayen shi da yazube su cikin aljihunshi,
Wanka ya fada inda yafito yasamu maryam din cikin wani dogon riga mai hula,
Abinci tagabatar mai sai yadan tsankwara kadan yace ya koshi don shi yanzu girki inba na maryam bane sai dai yaci kawai,
Kokarin lalabanta yakeyi a lokacin amma sai maryam din tana kokarin zulewa,
Tsayawa yayi da mamaki yana kallon ta sai ce mai tayi ai ya kamata ya huta don taga yagaji ne yau
Cikin mamaki yace maryam karda ace kina nufin bazaki iya daukan dawainiya naba,
No no no kada kizamo min haka pls ban da ra,ayin yin mata biyu kin wadace a rayuwata maryam kidaure da duk wani bukatana, pls,
Indan har kin min haka kin min komai pls kin mai dani dan gata ke nan,
Murmushi maryam din tayi tace cikin yar dariya baka da matsala anan uncle,
Yaji dadin maganar ta don haka yace idan har haka gaskiyane ina son yau atabbatar min da honey moon nazo,
Dariya tayi don ta gane wayon manya yake son yai mata kawai ,
Yau kan ba honey moon tana batun gudu yajawo ta zuwa jikin shi yana dariya
Nan ya nemo bakinta ya manne da nashi a guri daya
Can wata duniyar suka lula aciki irin duniyar da baka gane haske da duhu,
Daga italy suka wuce kasar Hong Kong nan ma dai sun morewa rayuwar su kamar ba gobe, kuma,
Wanan tafiya yasa maryam kara shiga farin ciki wanda yamantar da ita duk wani shakku da damuwa,
Saura kwana biyu subar kasan maryam ta, tashi da zazzabi amma kuma baidauki lokaciba tasamu sauki,
Amma duk da haka saida Yusuf yakaita asibiti don adiba lafiyan ta sun gane gajiyane kawai yadan damay ta,
Sun jima sosai a Hong Kong din don maryam ta watsake sosai kafin subar kasar,
Yusuf cikin wanan tafiyan ne yai ma maryam set, din funitures ga gidajen shi uku na kwantagora Abuja sai Lagos,
Batare da sanin maryam din ba ya turo su gida Nigeria ya sa agyara mata ko ina,
Gurin Sonny yake kokarin zuwa da ita don su dan ganshi amma bazasu dade ba acan don zasu wuce Dubai ne daga can,
Maryam ta zama babban mace ta goge takara wani kyau da haske ga hips da ya wani baje mata abaya,
Kiran ta na "ya mace ya fito tsab ta zama classic lady, yanzu don ko ina zata iya shiga don takai,
Sai dai daga maryam har Yusuf din su na jin dar din zuwa gurin Sonny din,
Amma kuma Yusuf yana da bukatan zuwa kasan don haka dole su tafi garin,


ZEEE MAKAWA YELWA,
[5/5, 10:20 PM] β€ͺ+234 703 055 6607‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
9⃣5⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI

JAMA,ATUL MUSLIMI RAMADAN MUBARAK
πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘


Sun bar kasan Hong Kong cikin jin dadi da,walwala,
Ga wani irun mugun shakuwa da yashiga tsakanin,
Don kowa naji da dan uwar shi sosai,,
Idan Yusuf yana gida tilas maryam tana manne a jikin shi idan kuma yana office ne ko wurin wani business to waya ne akai,akai a tsakanin su,
Hakan yasa farin cikkin su kullun yana karuwa ne akoda yaushe godiya sukewa Allah,
Matsalan maryam yanzu guda ne shine yan uwan Yusuf da suka sasu a gaba,
Duk da ba yaren IBO maryam ke ji ba tana fahintar wasu abu a wasu lokutan,
Saboda basu iya magana cif da yare zalla sai sun jefa English a ciki musan man ma shi dan gogan nata,

Sun sauka South Korea amma sai Yusuf bai sauka a gidan Sonny ba,
A hotel mai kyau da tsada suka,sauka shi da black beauty din shi,
Tun shiga shi kasan yake sa ido ga yar amaryan shi wace a yanzu tazama mai wani wani sashi na rayuwar shi,
Saida ya dan huta kwana biyu sannan ya nemi Sonny din,
Sun yi murna sosai da ganin junar su a wanan lokacin
Duk da Sonny yasan cewa Yusuf bai shangiya amma sai da yai mai tayi shi,
Wani irin harar ya watsa mai tare da daure fuska Yusuf yace kokai ina fatan ka bar wanan akidar very soon
Dariya yadan yi mai kama da yake yadan ka da kan shi alamar da wuya hakan,
Kurba guda ya shanye cup guda ya kara zuba wani ya aje a gaban shi,
Zagayowa Sonny din yayi zuwa gaban Yusuf inda ya hau saman table ya zauna gab da Yusuf din,
Yusuf hankalin shi na ga wani takarda da yake duba na,wani harkan business wanda zai iya kawo gida Nigeria har a samu karuwa,
Muryan Sonny ce ta katse yana tambayar shi labarin garin da Sonny ya kai shi, a Nigeria,
Murmushi Yusuf yadan yi yace suma suna kewan shi ai,
Ina wanan Baby din nawa take yanzu ne ?
Tambayar ta tsayawa Yusuf cak amma ba wani shayi ko wani dari yace mai ta na nan,
Da sauri Sonny din ya dan waiga kamar wanda zai iya ganin maryam din a lokacin,
Sai kuma yakai wa Yusuf dan duka acikin yaren su na IBO yace kafaye tsokana Yusuf,
Yusuf a cikin daure fuska ya ce, ba wasa aciki tare muke yanzu haka da ita,
We haven married six months ago,
What's cikin daga murya Sonny din ke tambaya,
"Yes, of course"
Yusuf ya bashi ansa da hakan,
Cikin mamaki Sonny din yace yanzu kayi aure Man shi banda ko labari ban jiba ko ga,wani,
Takardan dake hannun shi ya dire saman table din yace, You now how my sweet religion is,
Basai munyi wani bidi,a ba zamu iya yin auren mu a cikin mutunci bukata kawai shedu su sheda hakan,
Hannun shi ya tafa raf raf raf sau uku ya ce congratulations,
Sai ya duko kan shi gab da kunnen Yusuf din ya ce,
You are the most lucky man ,
I ever meet in the world,
Maganar Sonny taba wa Yusuf mamaki sosai
Sonny din ya ce gaskiya nai maka murnan samun wanan yariyar a rayuwan ka,
Duk da dai kai ba,wai kadamu da mata bane balle kasan irin abin da na hango ga wanan yarinyar,
Amma yanzu tun da ta na gurin ka ,a sannu zaka gane ko waye ita,
Nagode kawai Yusuf din ya furta cikin kaguwa irin yadda abokin nashi ke santin matar shi a gaban shi haka,
Yusuf ne kau da hiran matar tashi daga bakin Sonny,
Harkar business suke tataunawa akai ta yadda abubuwa za su zo mai da sauki,
Sun dauki dogon lokaci a office din Yusuf din suna tataunawa akai,
Sai lokacin da Yusuf zai wuce ne Sonny yake tambayar shi inda maryam take don yazo su gaisa
Tare da cewa shi a matsayin shi na babban aminin shi zai hadawa Yusuf da maryam yar party na aure don duniya ta sheda,
Mamata boye ta nakeyi don bani son maza yan duniya masu halin dan akuya su sa mata ido,
Hararan shi Sonny din yayi yace kada ka dauke ni haka inda dai baka aure ta da duk yadda zan rabaka da ita zan yi don in more mata,
Kaji mara mutunci inji Yusuf ya harari Sonny din yace ya kamata ace kadaina wanan irin akidar ka samu family hakana pls,,
Murmushi Sonny yayi tare da bubuga kafadar Yusuf din,, yadan girgiza kan shi,
Sai da yaba da baya ya ce zan di ba acikin addini ko zan samu wace tai daidai dani,
Saboda a gaskiya bazan iya shiga addinin ku ba don naga kuna da tsananin bauta har sau nawa kuke bauta in a day,
Abinda Yusuf yariga yasani ne dama Sonny bazai taba musulun ta,
Koda yaso musuluntar aminin nashi ne don yasan idan ya auri maryam zata kokarta a kan shi, don yayi addini,
Sai yazu yake godewa Allah na rashin cutawa yar mutane da bai yi ba dakuma cutawa rayuwan shi kan shi,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login