Showing 213001 words to 216000 words out of 255288 words

Chapter 72 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1383

wai baki shigo ba,
Jin shiru yasa safiya din cewa hello, muryan maryam kawai ya tabbatar mata ba lafiya,
Cikin kuka maryam tace Safiya baba yadaura min aure yau,
What inji Safiya tace wa maryam cikin daga sautin tambayam ta,
Shehekan kukan da taji maryam din nayi ya tabbatar ma da maganar gaskiya maryam din ke yi,
Duk da dare ya soma a lokacin hakan bai hana Safiya neman izini gurin mahaifiyar ta ba,
Kwatsa sai ganin ta sukayi tayi sallama, a gidan
Lokacin maryam wace ta dunkule a cikin bargo saboda sanyin da takeji ga ruwan sama an lema agarin,wuri ya dauki sanyi,
Anty ce take mamakin ganin safiya ciki dare saboda bata saba,zuwa a wanan lokacin ba,
Amma kuma sai ta nasa cewa ai kila safiya din ta samu labarin abinda ya faru da aminiyar ta,
Bayan sun gaisa ne Anty dije din tace wa safiya sai kikaji labari kwatsam ko,
Ki shiga tana ciki ai don haka safiya, ta shige dakin su maryam din cikin damuwa,
Ganin yadda yaga maryam din a kwance yasa ta karasa gurin ta da,sauri tadan dafa goshin kan ta,
Sai a lokacin maryam din ta bude idon ta ganin safiya ce yasa ta,saurin rungumota zuwa jikin ta,
Nan suka dan yi kukan su suka,share hawayen su saboda kukan bashine mafita ba,

Tun da gari yawaye yake ta faman aiwatar da,duk wasu abubuwan da yake da bukatan yi don ya samu ya koma Abuja ,
Abinda yafi bashi mamaki shine rashin kiran shi da,su KB basu yi duk cikin wanan lokacin shima dai share su yayi ya kama abinda ke agaban shi,
Jirgn yamma yabi zuwa Abuja don haka acikin dare ya isa Abuja,
Driver shi yazo yadauke shi zuwa gida duk da agajiye ya ke bai hana shi daga waya ya kira mahaifin shi ba,
Don yaji lafiyan jikjn shi saboda yakira kafin ya taso akace yana barci ai,
Yanzu da yakira bayan shigan shi gida ko daki bai shiga ba yakira don yaji,
Inda yai sa,a ance yana zaune don haka aka bashi waya don su gaisa da mahaifin na shi,
Maganar farko da Mr Emanuel yayi shi ne, Joseph are you married with a hausa girl,?
Daddy just relax iam coming home tomorrow insha Allah,
Jin haka yasa Mr Emanuel's saurin kashe wayan,
Yusuf wanda yadda mahaifin nashi yai mai ya san cewa a kwai magana agaba,
Saidai yana mai rokon Allah akan duk abinda zai faru Allah yakawo mai sauki,
Daga haka ya haura zuwa sama don ya watsa ma jikin shi ruwa huta,
Daga haka bai kara saukowa kasa ba don yana bukatan hutawa a tare da shi,

Tunda safe babane ke sallama akofan gida jin muryan shi yasa kowa dake gidan tsinkewa saboda, ansa da akwai abinda ya kawo shi,
Daguda guda suka dinga fitowa har Safiya din wace ta kwana gidan don taya aminiyar ta jamame,
Sun gashe shi a cikin mutunci da kuma girmamawa irin yadda diya kewa iyayen su,
Baba wanda yake tsaye daga kofan shigowa yadan jim
Can ya kalli inda maryam take tsugune cikin zumbulelen hijabi, yace,
Maryam , maryam wace jin an kara kiran sunan ta yauma din tadago takai kallonta gare shi a cikin girmamawa tace Na,am Baba,
Yace Allah yai maki albarka kin ji Allah ya sa wa auren ki Albarka ,
Sai kuma yai shiru can yace ina Dije ?
Anty Dije takarba dacewa Na,am baba
Baba yace ban so ance jiya wanan yarinyar ta kwana gidan nan ba naso ace ta kwana adakin mijin ta,
Gaba dayan su suka dago kai suna kallon mahaifin nasu,
Yace na tuntubi shi malam mudi yace min abari har yaron yazo gari a ji ta bakin shi,
Don haka sai ki zauna da shirin yar uwar taki akan duk ranan da mijin ta yazo zata tare a dakin ta ne
Dafatan kin fahinci abinda nake nufi akan zance na,
Anty Dije ta gyada kan ta tare da cewa eh baba shiru yadan yi yana kallon su yace
Allah yai maku albarka Allah yabaku zuri,a masu albarka,
Daga haka yasa kai zai wuce, sai kuma ya juyo gurin da Anty Dije take yadan juya yace bani son samun wani matsala,
Anjima zandawo don muyi maganar dan abinda za,a sai mata,
Sai a lokacin Anty Dije ta samu bakin magana tun shigowar baba gidan,
Tace to amma baba bisa ga hukuncin da naji ka yanke na cewa da yazo ranan zata tare ,
Sai naga cewa ba,a fa yi wani shiri ba akan tarewan
Don may baza a dan dakata harzuwa lokacin da za a shirya,
Ke inji baba cikjn muryan da har saida ta dan razana yace,
Ni komai nawa na dogora ga Allah wani shirine can,
Abinda Allah ya hore min shi zamu kai mata tayi hakkuri yadda kowa yayi,
Ina fatan kun fahinta da magana na don kadaazo ace min ga kara ka itace,
Daga haka yasa kai ya wuce nan ya barsu a cikin tashin hankali,
Daki maryam ta fada sai kawai ta ji hawaye ya na silalo, mata daga idon ta saboda hukuncin da baba ya yanke a kan ta,
A daki maryam ce da aminiyar ta tana bata shawara akan tayi hakkuri da kaddaran ta,
Shawarwari da dama Safiya din ta dinga ba maryan har taji hankalinta ya dan kwanta,
ร€nty Dije tun da tashirya tafita zuwa gidan wata aminiyar ta da suke siri
Duk da matar ta girmay ta sosai sai amma suna siri da mutunci a tsakanin su,
Saida taima matar bayanin abinda baba yazo masu da shi yau da safe,
Na akan lalai sai dai maryam ta tare duk randa mijin ta yazo garin,
Matar tai dariya tace wa dije wanan ai baika na ta da hankali ba,
Don haka yanzu zan dan fita in je in fara samo hakki bakin daji,
Anty Dije tace kai haba ke da anyi zance saiki maganar akan zancen gyaran harka,
Nizancen abinda zan wa maryam na gyaran gida da dakina ke magana,
Kai, matar ta kada tace aikin banza Dije, ai wanan abin shine babban tsaraba da yadace mugyara yafi wanan kayan banzan da kike zance,
Saboda ai shi kayan daki babu inda sunna yace an halattawa mutun shi ko ?


ZEEE MAKAWA YALWA
[5/3, 10:49 AM] โ€ช+234 706 262 3470โ€ฌ: ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
FUREN JUJI
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
8โƒฃ5โƒฃ

ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI

Bazan iya matawa da ku ba masoya wanan novel din kaunar da shi tankar a gare ni ne nagode nagode nagode Allah yakara rufa asiri a rayuwa,,,,

Maryam wace take zaune tai tagumi da hannun ta guda,
Kallon abinda uwale takawo mata acikin roba takeyi,
Gashi uwale tace sai ta shanye shi duk gaba daya, yau din nan,
Safiyace ta shigo dakin inda idon ta ya hango mata abin kamar yadda aka ba ta,
Isa tayi gurin inda ta jawo wani cup dake gefe, ta debo wanan gumbar ta sa aciki,
Bayan ta gama damawa ta dauko madaran peak milk gwagwani guda ta juye a ciki,
Cikin tamke fuska tamikawa maryam din wace ke zaune a gefe guda,
Maryam da bata da wani option sai na ta karba ahaka takarbi cup din a hannun safiya ta fara kurban a hankali tana dan runtse idon ta,
Wani ruwa maikama da ruwan lalai yana kamshin turare a cikin shi safiya takaiwa maryam din a bathroom,
A ranan kusan sau biyar maryam tai wanka da wanan ruwan hadin ga kuma yakin jiki da safiya din da Anty ke tsare ta sai tayi wa jikin ta,
Jikin ta a cikin kwana guda ya sauya kalla, duk da ta ramay amma sai jikin nata yai wani fresh,
Ruwan kanin fari watau, (glove) cike a wani roba mai marfi shi ma tadinga shan shi,
tare da yin tsarki da shi a wanan yinin,
Anty Dije da kanta sai da taga canji a gurin yar kaunar nata,
Takoma wata fresh sai sheki takeyi jikin ta ya sauya a lokaci guda,
Kwana biyu ga naman yan shilan tantabara da uwale ke daho mata daga gidan ta ace wai ita kadaice zata zauna ta cinye, kashi kawai zata bari,
Abubuwa kala,kala aka dinga yiwa maryam din wanda ya kawo mata sauyi, a jikin ta, ita kanta har muryan ta duk taji ya sauya mata ga wani irin kasala wanda ke sata, barci a kai,kai, ,,,,,

Shiri yayi so sai don yasan cewa wanan tafiyan ya na bukatan kudi,
Gashi kuma mai laifi a gurin jama,a da dama bai san yadda zai wanke kanshi ba musan ma yar uwar shi dayake ji da ita Anty dije
Wace rabon da suyi waya da ita tun yana garin kano har zuwa yau bai kara kiran ta ba,
Saboda aiyukan da suka sha mai kai gashi kuma wani sabon magana ya bullo wanda yasan cewa zancen yakai gare ta a yanzu,
Sai kuma mahaifin shi wanda har zancen takaishi ga kwantawa ciwo sai rokon Allah yakeyi, akan Allah yasa ya samu kan mahaifin nashi ,,
Gudu motocin keyi kamar yadda suka saba yi a daji amma shi yau bashi ke tuki ba yazo da mutanen shi don haka, suke jan mota,
Sai lokacin da motar ta doshi garin kamfanin bobi sanan maryam tafadowa Yusuf a rai,
Maryam ya furta a hankali tare da lumshe idon shi da su kayi ma jajir a lokacin saboda stress, da yai mai yawa,
Idon shi ya lumshe a lokacin tare da tunanen abinda ya yanke a tsakanin shi da maryamm din,
Sonny kawai yakai mai can a irin yadda yake jin maryam a rayuwar saboda Yarinya tayi mai a irin yadda yake son mace,,
Komawa yayi yabi lafiyan kujeran motan yana mai lunshe idon shi gami da shafo fuskan shi,
Ba,a dauki wani lokaci mai tsawo ba suka shiga garin kwantagora,
Direct gidan shi suka fara zuwa inda suka dan huta, tukun tare da kokarin neman abinda sukaci,,
Amma banda Yusuf wanda ke jin shi a koshe lokacin baya bukatan cin komai a rayuwar shi,
Driver shi guda wanda yasan gidan su Anty Dije ya umarta da yakai masu tsaraban su kamar yadda ya saba kai masu,
Shi kuma yadauki mota shi kadai yabar gidan ba tare da kowani execute ba,
Gidan mahaifin shi ya nufa kai tsaye ba tare da wani shakkan komai ba,,,,,

Zaune suke a falon su gaba dayan su maryam wace ke rike da wani fresh milk na shanu da uwale takawo mata shi wai ta shanye dukka,
Sallaman da sukaji ne na wani mutun inda, Assalam ya,sheka waje don ya,diba masu kowa ke sallama a lokacin,
Sai gashi da gudun shi yana cewa uncle din shi ya, uncle din shi yazo sai kuma sukaji karan ana,sauke kaya a tsakar gida,
Ba maryam ba har su Anty sai da ga ban su ya fadi , badon komai sai don tunawa,da alkawarin baba na,cewa,duk ranan da Yusuf ya,shigo gari a, ranan maryam zata tare a dakin ta,,
Cup din dake a hannun tane ya ke batun faduwa wanda,safiya tai saurin karban cup din,,
Mikewa,tayi zuwa,dakin su cikin tashin hankali don jikin ta har rawa yake yi, a lokacin,
Sadiya ce ta mara mata baya ganin irin yanayin da aminiyar nata take ciki,
Dafa, mata kafadar ta Safiya tayi tana mai kallon ta,
Maryam ta,dago kan ta a hankali tana kallon safiya din,
Idon ta na silalan hawaye kai safiya ta girgiza mata ta bude baki cikin kariyan murya ta ce,
Ka dakiyi haka pls ki zama mai dauri ga duk jarrabawan da kika gani ga rayuwan ki,
Cikin muryan kuka maryam tacewa safiya amma dai kin ji abinda baba yace ko, ?
Kan,ta ta girgiza cikin kuka tace, wa maryam din ai ba lalai bane maganar baba din yayi tasiri a yau din don shima ai yana da nashi uzurin ko,
Sai a lokacin hankali maryam ya dan kwanta a haka tadan kai kwance ta dunkule guri guda kamar wace ki jin sanyi,
Zuciyar ta fam da tunane da addu,a Allah yasa maganar safiya ya zamo gaskiya,

Bayan ya kashe mota yafito yana rike da yar jakar gift da ya sayowa, mahaifin nashi, a lokacin,
Tundaga kafan shi har kai kallo daya zakai mai kasan cewa Naira ta yi rana agurin,
Tafiyan shi cikin takon kasaita irin na gogaggun matasan yan Abuja ko lagos,
Dan sajen da ya bari wanda yai mai round a fuska yakara fitar mai da kyaun fuskan shi fili,
Duk yadda matasan da ke gidan nasu suna kula da aiyukan gida ,
Sunzo karban ledar dake hannun shi amma sam ya hana ya na mai daga masu hannu alamar subar shi kawai,,
A sama resting chair yasamu Dad din shi ya dan kishingida kamar mai tunane muryan Yusuf yaji daga sama don sam bai tsanmani zuwan shi ba yanzu,
Direct gurin shi ya nufa, nufa yadan rungumo Dad din zuwa jikin shi,
Cikin lumshe idanun shi yace ma dan nashi you are welcome my child,
Tare da dan bubuga mai bayan shi cikin nuna mai kulawan ganin shi,
Kujera dake facing din inda Dad din yake ya nufa nan ya zauna suna facing din juna yadan tura mai ledan gift din da yazo mai da su,
Babu wanda keda alaka da giya ko wani abin maye daga duk cikin kwalaben, drinks din na karin jini ne da gyaran jiki,
A hankali tsohon yadago kai ya kallo dan nashi daga inda yake ya ce,
Joseph da gaskiyane ka auri yarinyar hausawa, kokuwa kana shirin aura ne,
Ba wani tsoro ko fargaba Yusuf din yace, baba da ba hausa da yar IBO duk guda ce fata dai in samu wace hankalin mu yazo daya,
Hannu Mr Emanuel yadaga wa Yusuf din wanda ya fara yiwa mahaifin shi dogon sharfi,
Dan tsohon yace lalai Yusuf yanzu kan nagane cewa kafita cikin mu gaba daya,
Don har gudun auren yar kabila, ka kake yi, yan mata nawa aka kawo min cewa in aura maka amma nace a,a don ina da, ra,ayinka zabi mace da kan ka,
Shiru yayi saboda wani irin bakin ciki da ya taso mai har yaji cewa bazai iya ci gaba da zancen ba,
Shima Yusuf din baiji dadi ba sam irin yadda ya ga rayuwar mahaifin nashi ya baci,
Sun yi shiru nawa ni lokaci don haka Yusuf din ya mike saboda yana da bukatan zuwa gurin mahaifi Jibrin don karin bayani,
Acikin rashin sa,a Yusuf bai samu mahaifin jibrin din a gida ba don haka ya juya motar shi sai zuwa gidan Anty dije,
Yasan cewa yau zai sha fadan rashi kiran su da baiyi ba kwana biyu kuma layin da zasu iya samun shi duk a rufe suke,
Da sallaman shi ya shigo gidan wanda kamshin shi kawai ya isarwa mutun sakon cewa yana a gurin,
Waje suke a zaune saboda garin akwai hadari wanda ke yawo a sararin samaniya tun da rana
Yanzu kuma sai yadan ba garin zafi,zafi da dan lumshi,lumshi,
Masara ce gassasa a ga ban su suke ci yayin da anty take kokarin hada kaya a cikin kitchen, saboda ganin hadarin da tayi,
Ganin shi girshi da sukayi babu wani hanya da zai sa maryam din ta boye mai,
Kallo guda su kai wa juna daga ita har shi kowan su ya kauda kai ga dan uwa,
Kowa da abinda yake sakawa azuciyar shi don ganin dan uwa da sukayi,
Safiya ce da Anty ke mai sannu da zuwa a lokacin sai maryam wace ke ta baya kadan ta mai sannu da zuwan acikin wani irin murya mai karyarwa,
a,ciki, ciki,
May yasa may ta ta ramay haka ?
Amma kuma ga jikin ta yai wani fresh maryam din yaga duk ta canza a lokaci guda,
Ita kuma maryam Yusuf din ne taga yakoma mata wani iri tankar yaune ta fara ganin shi,
A galon su , suke zaune suna gaisawa da Anty Dije wace bata san ko may yasa ba yau kawai ta tsinci kan ta da jin kunyan kanin nata, haka kawai,
Ya dan dago kai yana mata dan murmushin nan tashi ta bajin ta,
Anty Dije wace ala dole take wanan zaman da Yusuf din
Cikin dan dukar da kai tace wa Yusuf din, cikin marai,rai ce war murya,
Yusuf kawai sai kaji yadda zance ya kasan ce daga karshe ko,
Baba ya ya yiwa kowa baza ta don ko ni ban san da zancen auren nan ba sai bayan anyi,
Kasan irin yadda maryam din tai ta fama da jin jiki,
Duk wanan bayanin bata lura da cewa kallon mamaki Yusuf din ke mata a lokacin.
Anty ban fahinci maganar ki ba inji Yusuf din yake tabayar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login