Showing 162001 words to 165000 words out of 255288 words
Chapter 55 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete
ta jero masu abin sha da cups saman ture din,
Duk wanda da Yusuf ke yi idon shi sometimes suna gittaiyya akan maryam wace ke sintirin taron baki,
A hankali ta dire mazu shi a gaban su inda ya yunkura zuwa dayan kujeran da ke gefen,
A lokacin shi ma yusuf din yai sallama da wanda yake waya dashi din,
A cikkin wani irin kashe murya Sadiya kewa Yusuf din magana ,
Ganin haka yasa maryam yunkurin tashi don barin gurin,
Shigowan Anty Dije tare da sallama sai yan rakiyan da suka raka ta gurin gyaran gidan suka shigo a gajiye,
Yun,kurawa, yayi don ya gyara zaman shi da kyau don gani shigowar su anty gidan,
Kallo daya Anty tai masu kawai sai ta wani dan fuske fuskan ta tankar bata ji dadin ganin su ba,
Su ma dai ba wai sun sake jiki da ita ba ce a irin yadda su ka gan su,
Gaisawa sukayi sama , sama da su anty dije din tankar ba su so ganin ta ba,
Yusuf ne ke gaida anty a cikkin kulawa da girmamawa inda yake ta faman yi masu sannu da zuwa,
Gaba daya hankalin shi, ya baya gurin da anty dije ke mai bayanin yadda aikin nasu ya kaya,
So sai yaji dadin baya nin da Anty Dije ke mai akan irin yadda aikin ya kaya,
Sadiya ce cikin wani irin sallon murya ta ce D, Yusuf din wanda ke, magana da Anty yadan juyo gurin ta kadan,
Maryam ce tsaye a gefe dauke da ruwan leda tana kokarin rarabawa mutane don su biyar ne suka shigo
Cikin wani marairai ce murya take ce mai muna son mu tafi fa,
Anty ce tai magana wanan karon da cewa haba ku dan dakata in baku, abin buki pls,
Maryam ce tace cikin dan sake fuska tun yanzun nan da shigowar ku har zaku tafi,
Sadiya wace tai tankar bata ji ko may maryam din ke fada ba, ta wani share,kawai,
Saida ya gaji don kanshi ya mike tsaye yana mai cewa Anty Dije sai an jima idan yadawo,
Sai anjima ma da kyat sukewa mutane shi ida suka bi bayan Yusuf din,
Su na shiga mota yadan wuce gidan su Anty batare da ya waigo inda Sadiya take zaune ba yace,
Sadiya may wanan yarinyar ta tare maki ki ke wani share ta haka,
Pls bana son irin haka, Sadiya yace a cikin dakewa,
Caraf Sadiya tace Nafa san ko may wanan yarinyar da yar ta muna fuka suke kullawa a kai na,
Da wani irin karfi ya faka motar shi wanda har yasa karan motar yajawo hankalin mutane,
Ita kan ta sadiyar sai da ta ji tsoron wanan karar amma sai kawai ya dake ya wani matse fuskan shi,ya ce,
Kufita min mota, bata motsaba a inda take sai ma ci gaba da taunar chewing gun da tayi,
Wani irin tsawa yadaka mata saida ta firgita wanan karon yace ku fita, min nace,
Yadda su ka ga fuskan shi ya canza tankar na wani katon zaki yasa su jin tsoron shi,
Murya na rawa ka fara cewa, don Allah yayi hakuri ya karasa da su saboda Allah,
Sai da yai kamar ya dukar da kan shi saboda yadda yake ji a zuciyar shi,
Tankar wani zaki da ya kwana bakwai baici komai ba,
Sunan Allah da kawar sadiya ke ta hada su da shi yasa shi tayar da mota ya hau saman titin a hankali,
Sai da suka danyi nisa ya sauke wani irin ajiyar zuciya batare da yakalle ta ba yace,
Sadiya kinyi babban kuskure na ai,banta รnty Dije da kikayi a gabana
Tun ban aure ki ba kina kokarin rabani da mutanen dake sona da zuciya daya,
Mutane da nake jin su tankar yan uwana na ji,ni wa yan da muka fito ciki daya,
Matar da itace tasa ni gaba a kan ki wai yau itace kike wa, wanan bakar maganar haka,
Cikin rawan murya tace Yusuf don Allah dai kayi hakkuri pls,
Yusuf batare da yai magana ba ya kau da kan shi gefe ya na mai fesar da iskan mai huci da zafi, daga bakin shi,
Bai karasa kofar gidan su ba ya aje ta tana mai magana ya fisgi motar shi ya bar gurin,,,,,,
Kwance take makale da waya a kunen ta daga ita sai wani dan rigar shimi fara mai yar hude, hude,
Zani shaddan da ta sa ne daure a jikin ta sai wani dan yalalon gyale da ta rufe fuskan ta da shi, a lokacin,
NA,IMAT ce zaune daga gyafe tare da Isslam suna kallo a wayar ta.
Ga kuma tv dake cikin falon shima aiki yajeyi a lokacin
Sam maryam bataji shigowar Yusuf ba a lokacin saboda hankalin ta da ke gurin wayar tana kokari karkada kafar ta,
Kamshin turaren shine ya daki hancin ta ida ta bude idon ta dake a lumshe ta sauke su a cikin idon shi,
Saye yake da jallabiya mai ruwan toka, a jikin shi,
Sai yar karamar tasbaha da yake dan ja a hannun shi, a hankali,
Cikin yare Naimat ta ke gaishe she shi inda ya ansa mta da kada kai alamar ansawa,
Muryan maryam yaji tana cewa ai ko ba,a gaiyace, kaba kai nagida ne zaka iya zuwa,,
Kanta ta kwantar saman hannun kujerar da take zaune a kai, tana mai ci gaba da wayan ta,
Sam ta manta cewa yar shimi ce kawai a jikin ta a lokacin,
Kujerar da yake facing din ta ne ya zauna fuska babu walwala, a tare da shi,
Fitowar Anty Dije ne daga cikin daki yasa shi dan sake fuska,
Sun gaisa take cewa, ya komawar baki dazun da suka shigo,,
Sai da ya idar da abinda yake karan tawa ya shafa sanan ya cewa anty dije,
Anty wanan yarinyar taban mamaki so sai wallahi,
Baidai fada mata ko may ye ba don bazai iya yin magana ba a lokacin irin yadda yake ji a ran shi,
Dariya maryam ke yi a lokacin don abin da A,A ya fada mata har tana wani dan kyarkyatawa,
Ido ya zuba mata daga inda yake zaune yana mai jefa mata harara,
Da sauri maryam ta kauda kan ta daga gare shi don irin yadda yai mata,
Kanta na kasa cike da jin nauyin shi don tunawa da tayi cewa,, daga ita sai, yar base a jikin ta,
Ta rasa yadda zata mike zuwa cikin dakin su a lokacin,
Duk da ya fahinci cewa tana son tashi zuwa ciki sai ya kawar da kan shi gefe tankar bai ganta ba ma agurin,
Cikin dabara ta mike zuwa cikin dakin su inda ta karasa yin wayan ta,
Har ya gama hiran shi da anty ya bar gidan maryam bata leko wajen falon ba,,,,
Bayan ta gama komai tana kokarin kwantawa barci ne taji wayan tana kara,
A sanin ta dai sunyi waya dazun sosai da A, A din ta sai kuma dan bankin ta da ya kirata around four na marance,
Hannu ta mika ta jawo wayan ta, zuwa fuskanta don ganin kowa ke kiran ta a wanan lokacin,
Uncle Yusuf, tagani a rubuce saman screen din wayar nata,
Sunan ta kara nanatawa a fili don mamakin da ya mamaye zuciyar ta
Da sauri ta dauka don bata san ko may ya sa ya,kirata ba, a daidai wanan lokacin
Assalamu Alaikum tace a lokacin da ta dauki wayar,
Shima a nashi bangaren wani iri yaji a kunnen shi a lokacin da tai wanan salaman,
Shirun da maryam taji yayi ne a lokacin yadan kara sa ta cewa 'Hello"
Ajiyan zuciya taji yayi a lokacin inda ta ji shi yana cewa hello,
Uncle naga kiran kane shine na dauka, murmushi taji yayi yana mai cewa sorry bake ce ,naje kira ba,
Cikin yar muryan nan nata mai kama da sarewa tace ok,
Wallahi har gaba na yafadi ina ce ko nai wani laifin ne akakirani ai min fada,
Fuskan shi kum she da murmushi ya ce, au ke kuma ba kyason kiyi laifi ko,
Tana yar dariya tace to ai kaine uncle ba wai sai mutum yai ma wani lafi ba zaka haushi da fada,
Murmushi mai yar sauti ya sake yace ke maryam bana son sheri yaushe nake maki fada ni,
A hankali tace ai kai baka sani uncle sai dai kabar mutun yana ji a zuciyar shi,
Muryan shi cike da amon dariya yace nagode da wanan kazafin maryam,
Lah tace wallahi ba kazafi bane nai ma sai gaskiya kawai,
Ni ba ruwana ban ce nai ma kazafi ba ai
A hankali yace gaskiya kin min don dai ni na san cewa fada na dake shine a kan hawa mashin ne kawai,
Sai kuma taji ya kwantar da muryan shi a hankali yana magana yana cewa,
Maganar gaskiya maryam bana son in ga mace wace na sani a kan mashi, wallahi duk nakan ji rai,na ya baci so sai,
Balle ke da kike ta daban a guri na maryam don may bazan maki fadar hawan mashin ba,
Inda za,a yarda min in saya maki mota batare da an tunhumi komai ba da wallahi na dade da saya maki,
Wani irin nauyi da kunya ne ya kamata tankar yana kusa da ita alokacin,
Kanta na kasa tana mai kurawa ties din dakin su ido tace ,
Haba dai uncle kamar wata mai wani matsayi a gurin ka ni a su wa da har za,a sai min mota,
Bai yi magana ba amma murmushi yaiwa zancen nata kawai,
Ok wait and see yace, mata a hankali,
Dariya ta yi mai sauti ta cikin ciki ,kaman ya na mai, ganin, ta,inda take kokari ta shigar da maganar, da cewa ai sai dai Anty Sadiyar ka ko Anty Aisha ko,
Sune manyan mata da suka dace da shiga mota a garin nan don a,san suna tare da kai,
Duk da ya fahinci irin maganar da tai mai amma sai ya dake da cewa,
To sai gashi kuma wace bata kai su ba tana kokarin ta riga su shiga ba,
Murya cike da maganar serious yace mata maryam,
A gaskiya bana son kina hawan mashin din nan pls,
Ya na,nata tambayar shi don jin shirun da yayi ta na bangaren,
Yace mata acikin murya mai taushi da Kin ji ?
A hankali ta ansa mai da cewa ,"To" uncle,
Cikin wata murya yace, mata kin yarda bazaki kara hawa bake nan kin amince, ko ?
A hankali takara ansa mai da cewa Eh uncle,
Nagode nagode nagode maryam insha Allah zan yi kokarin ganin kin daina kwata,kwata,
Kamin wanin su ya kara wani magana, maryam ce tai saurin cewa uncle nagode sai anjima kada na damay ka,
Sai ji tayi yace ai idan kece bazan ji damuwa ba maryam
Saboda may uncle maryam ta tambaya a kage,
Saboda kawai kina kaunata, kina sani natsuwa aduk lokacin da nake waya dake,
Baki ta dan tabe, alamar kaji dashi tace ashe kuwa A,A nada gaskiya ako yaushe yake a cikin fushi yace idan ba ya kirani ba baya kan samu relief,
A she ko zai daina jin relief idan yai wasa don dai kwanan nan zanwa kaunata aure
Don shi naga bada gaskiya yakeyi ba ,
Dariya maryam tayi wanda bai masan cewa ta iya irin wanan dariyar ba,
Tace uncle har ka sani babban dariya ka ma dai yi min miji ke nan ko ?
Kanshi ya hirgiza tankar tana ganin shi a gurin yace No but zan dai yi maki soon,
Duk a cikin gwarigwarin hausar shi da yar muryan shi mai daukan hankalin mai sauraro suke zan cen,
Da haka yana jan ta da hira har dare yadan yi basu ankara ba,
Inda duk kan su suka sake suna ta surutu da junar su,
Daga karshe maryam ce tace mai ya kwanta hakanan don yasan gobe yana da baki yan daurin aure,
Bai musa mata ba sukaui sallama da junar su kowa yana mai farin ciki na rashin sanin dalilin haka,
A haka maryam ta kwata da, yar murmushi makale a fuskan ta,,,
Washe gari aka daura auren Naimat da Ibrahim akan kudin sadaki naira dubu hamsin
Jama,a sun karba gaiyyatar da Yusuf tare da Abdullsamad suka kai masu inda suka sheda wanan daurin auren da akayi,
A kofar gidan su Jibbrin wanda mahaifin jibrin din ya zama waliyin amarya Naimat,
Bai wani bidia,a ba sai walimar da maza sukayi a kofar garkan gidan Abdulsamad, din,
Don haka duk yinin ranan Yusuf bai samu shigowa gidan anty dije ba.
Saboda sanin da yayi cewa akwai mata da yawa yan zuwa yinin buki shiko a rayuwar shi baya son yana shiga gurin da taron mata yake,,,,
SEENABU ZEE MAKAWA
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
FUREN JUJI
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
6โฃ7โฃ
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAR YAURI,
Alhamdullahi Rabbil,Alamin
รnty Dije tare da wasu daga cikin yan uwan su ne suka tafi kai amarya gidan ta dake a unguwar GRA,
Motoci kusan biyar ne suka zo don daukar a maryan sanin cewa ba wai tana da wasu mutane da yawa bane a garin,
So sai ko jama,a suka dan taru don zuwa rakiyar amarya gidan ta, da misalin karfe biyar na marancen, jumma,a,
A bin gwanin ban sha,awa saboda irin yadda, mutane sukayi don Anty Dije, kusan duk wace take hurda da ita tazo mata wanan karar na buki,
Amarya Naimat tasha ado a cikkn wasu lace farare kal dinkin buba, sai farin mayafi da kuma wani farin sarka mai daukan ido,sai wasu, fararen takalma a kafarta
Idon ta alamar taci kuka saboda irin yadda sukayi mata wani irin lub, lub da su,
Maryam ce kawai aka bari don tsaron gida tare da kau da sauran kayyayakin amfani da suka bari a waje,
Sam bata san shigowar Yusuf din gidan ba saidai muryan shi da ta ji gab da bayan ta,
Inda ta juya a yar razane cikin dan rudewa saboda rashin sanin mutum na kusa da ita,
Fararen shadda ne a jikin shi dinkin tazar ce har kasa,
Hannayen shi a harde saman kafadar shi inda ya kura mata ido kawai a cikin rashin sakin fuska kamar yadda yake a kullun,
Sai da tayi kokarin saita kan ta,tukun, na san nan ta samu bakin yi, mai gaisuwa,
Ya ansa mata kamar kullun a takaice sai dai na yau yana da dan banbanci da saura,
Gurin fridge ya wuce direct inda ya bude ya,dauko goran ruwan Inuwa water,
Kafa kai yayi batare da ya jira kofi ba, ya kama kwankwada, inda duk ya kwankwade ruwan tas,
Yau she su Anty za su dawo ne maryam wace ke kokarin shiga store din su, dan aje kaya ta ansa mai da cewa,
Anjima kadan shiru yayi ba tare da yakara magana ba ,
Gurin kujera two site ya nufa nan yazube sama yana mai cewa Ya Allah,
Akawo ma abinci ne ta tambaye a cikin dan dari, dari,
No thanks kawai yace mata inda ya maida idon shi ya kara lumshewa,,
Aikin ta taci gaba da yi abin ta batare da takara bi ta kan shi ba,
Yusuf wanda ke kwance tankar mai barci sai dai a zahiri idon shi biyu yana tunanen duniya,
Wayar shi ce tai kara gurin da, yake aje a gefen shi,
A hakali ya mika hannu shi ya dauki wayar sunan Jibrin ya gani,
Dan gyara kwanciyar shi,yayi ya na mai kokarin daukar ,
Tambayar shi Jibrin yake, yi ko yana ina ne haka
Sai da ya ja dan guntun tsuki kafni ya ansa mai wayar shi, tu kun,
A takaice ya bashi ansa da cewa gidan Anty mana ,
Jibrin yai yar dariya kafin yai mai magana, tukun
Da iskanci ai ba na fadama cewa zan dan gudo in huta ba kafin su dawo,
Ansa yabashi da cewa an fa kawo kayan da ya ce akawo mai ga mutumin yana neman shi,
Sai da yadan lumshe idon shi, sannan ya dan sukunyar da kan shi yana mai kallon ties din falon yace,
Ya ce gaskiya Jibrin bazan iya zuwa in duba ba saboda ina hutawa yanzu,
Amma zai iya kuzo nan ai maryam tana gidan sai ta tayaka dubawa, ko,
Jibrin din ya ansa mai da cewa gashi nan zuwa tare da mutumin,
Yusuf din ya ansa mai da cewa ya yi kyau sai kun ka raso ina ciki idan kunzo,
A lokacin ne kuma su Assalam suka shigo gidan daga can cikin gida gurin kakan,nin su,
Ganin yana bukatar hutu yasa maryam kiran yaran zuwa gurin datake,
Aiko can gurin ta suka dan bata lokaci