Showing 129001 words to 132000 words out of 255288 words

Chapter 44 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1411

Wayar shi ce yaji tai kiran Sallah alamar kiran ya shigo mai,
A hankali ya isa gurin da ya jona ta acaji ya ciro ta alokacin har ta kusa katsewa ko,
Maryam KG a karubuta a jikin sunan dake kiran nashi,
Furta sunan yayi a fili ya ce Maryam a hankali, kamar ta kusa,
Jira yayi kiran ya katse sai ya kirata, da kan shi don kada ya ci mata kudi,
Tana kokarin kiran shi taji kiranshi yashigo a wayar ta,
Bayan ta dauka sai kuma tai shiru a nata bangaren tana sauraren shi,
Shi ma dai shirun yayi a lokacin don yaji sallamar ta tunda ita tafara kiran shi,
Jin shirun da sukayi yai masu dan yawa ne yasa su yin magana alokaci guda,
Assalamu alaikum yace ita kuma tana cewa hello, duk alokaci guda,
Murmushi yayi wanda taji a nata bangaren kamar a fili yayi shi,
Ina wuni ta kara furtawa a cikin zakakan muryan ta mai kama da busa,
Kwaikwayon tayi da cewa lafia kalau, kamar yadda tai magana,
Kafin tai magana sai ce mata yayi matar lecturer halan yau ya cika maki waya da kudi ne dai,
Don naga yau an,kirani kai tsaye,
Murmushi kawai tayi don ta san cewa tsokana ce kawi yake mata,
Katse shi ta da cewa Ya Yusuf sai kuma naga kaya wai kace abani,
Ya ce eh maryam don dake naga kayan sun dace shiyasa nace kawai abar maki kuyi anko da budurwar Jibrin
Shiru tayi kamar baza tai magana ba sai kuma ta tuna cewa yin maganar ta zai jawo mata fada gurin Anty,
Sai kawi tace to nagode ya Yusuf amma dai da naga kamar doguwar budurwar ka ka sayawa su,
Wani irin malalacin dariya yayi yace sai kuma ga rashin da,cewar su da ita
Sai da yar budurwar mr lecturer suka dace kawai shi yasa na ce abarwa matan malam su tayi wa malam kwalliya yasha kallo
Ko yar kauna ta ?
Wani irin abu taji ya tokare ta a zuciya
Tace to zuciyar ta yana nufin cewa A, A ba zai iya saya min bane ko may ?
Kawai sai taji tamayar mai da kayan shi tace batason ta gode kawai,ya bar su,
Amma sai taji muryan shi a cikin sasautawa ya na cewa maryam,
Kayan sallah ki na aiko maki da su saboda kayan da na sayawa sadiya naji ance sunyi waya
Shi yasa nace wa Anty tabawa little sister dina kayan ta na sallah su,kuma idan zan zo zan shigo masu da nasu,
Kinga saura shoes da bags ke nan ko ?
Kamar ya,na ganin ta takada mai kai alamar eh,
Yace size din ki zaki fada mun kin ga zai fi idan kuma da akwai wani abin kina iya fada min sai a hado maki da shi,
Kwata kwata maryam bata so wani abu daga gurin Yusuf ba ,
Amma ya ta iya tun da gashi ya,dage har da cewa yasan ,
Ya,san bai isa sai mata abu ba saboda tana da dubun su
To amma yanzu tunda sun shirya yana son ta nuna mai cewa ta hucu kabar kayan zai nuna mai alaman hakan
Tambayar ta yakara yi in akwai wani abin da zai sayo mata in zai zo,
Ba komai ta furta a,hankali kamar mai shirin yin kuka a lokacin,
Sai yaji tabashi wani irin tausayi irin yadda tai mai magana a cikin damuwa,,,
A hankali tai mai sai da safe ta kashe wayan ta ba tare da ta kara furta wani kalma ba, a,kai ba, ta,katse wayar,
Lumshe idon shi yayi alokacin kamar mai jin barci tare da fadawa saman gado ta baya,,
Haka ya kwana da tausayin maryam a cikin ran shi wanda bai san dalilin hakan ba
Ita ko maryam ba yadda ta iya saboda har taji Anty na fadar irin dinkin da za taiwa kayan,

Sosai alakar mai nisa ta shiga tsakanin Ibrahim da Ejoma wace yanzu duk suna zaune a gidan yusuf ne dakw garin Abuja, a karkashin kulawar shi,
Tun suna kojarin boyewa maigidan nasu Yusuf har takai yanzu basu iya boyewa,
Maman choima da fara ganewa taiwa Ejoma magana acikin ka
,kausar murya cewa ta rabu da Ibrahim din tun Yusuf bai sani ba,
Amma sai Ejoman tace ma mama ai tafi son yasa don ya yanke masu hukunci,
Ran yar tsohuwar bai yi dadi ba sai tafito fili tacewa Ejoma ya zatayi da addin ta idan ta aure shi,
Sai da Ejoma tai yar dariya san nan tacewa mama ai su addinin su bai hana su auren yan addinin mu ba,
Sai,dai matan su ne ba,a yarda su auri mazajen mu ba sam,
Ehye, u see
Inji mama tana mai kada kai tace tana mai ba Ejoma shawarar ta tsaya a ,addinin xa iyayyen ta suka haife ta aciki yafi mata,
Ganin cewa ba,zata iya shawo kan yarinyar ba yasa ta kawar da kanta gefe guda,
Tsayin wani lokaci babu wanda yace wa dan uwa kala a cikin su
Don dai ita Ejoma gaskiya zata iya rabuwa da addinin ta tunda dama tadade tana sha,awar musulunci,
Yin Sallah da sa hijab na burge ta sosai, a rayuwar ta,
Har zuwa lokacin dawowar Yusuf da Ibrahim yayi daga office suna zaune a hakan,
Ibrahim wanda ya fara shigowa dauke da yar brief case din Yusuf a hannun shi,
Ya gaida mama acikin ladabi amma fafir yar tsohuwar taba shi baya taki karba mai sam,
Yana tsaye yana mai mamakin abin da yahana ta karbawa Yusuf yashigo cikin gidan,
Cikin irin takon shi na alfarma ya Wanan tafiyar tashi, guda guda tankar yana tsoron kasa,
Suit ne ajikin shi mai ruwan asshh, colour, hade da wandon shi sai far tie shirt da yasa daga ciki,
Isowar shi falon ne yaji muryan Ibrahim yana cewa mama idan har yai mata ba daidai ba ta yafe mai pls,
Da mamaki Yusuf wanda yadawo a gajiye ya tsaya yana kallon tare da tambayar ko may ke faruwa,
Kafin Ibrahim yai magana mamace tafara magana acikin fada tana cewa
Yusuf ya maida ita gida tunda taga kowan su yana musulunta
Gaskita ita bazata yarda azo da tsufan ta a cuce ta,
Da mamaki Yusuf ya juya inda Ibrahim yake. tsaye don karin haske, ga maganar,
Kafin wani yace wani abin Ejoma tafi daga ciki tana cewa ,
Brother zan koma ga addinin ku saboda wanda nake tare da shi yanzu dan addinin ku ne ,
Cikin mamaki Yusuf ke kallon Ejoma wace ke mai bayani a lokacim,
Cikin mamaki yake nunata da yatsar shi ya na cewa Ejoma ke, ke, ke,
Yace nasani sani cewa warana zaki gane hanyar gaskiya insha Allah,
Gashiko yau da kanki kin dawo saboda ra,ayin ki,
Baki sake da mamaki mama ke kallon su duk ta kawo iya wuya, saboda haushi,
Ciki tashige tana ta faman fada kamar wace akaiwa wani abu
Karin bayani sosai Ejoma keyi mashi ta yadda zai fahince ta
Sai ga mama da jakar kayan ta tana ta fada cewa wai a kwai evil din dake cutar su agurin,
Da kyat Yusuf ya samu takoma don ko shi saida yace mata akwai yan rituals a waje sanan ta yarda ta koma,

Tafiya take cikin sauri saboda tana son komawa gida da wuri yau,
Gurin bus stop take kokarin zuwa kozata samu motar da zai kai ta cikin gari da wuri,
Horn taji anayi a bayan ta batare da ta waiga don ganin mai shi ba don bata tsan mani cewa ita akewa horn din ba,
Saida, taji muryan shi yana cewa Maryam bakya ji ne halan,
Sai a lokacin maryam ta juya ta san cewa da ita yake,
A hankali ya samu guri ya Parker motar shi kamar ta wuce sai dai ta daure kawai ta nufi gurin shi,
A hankali ta gaishe shi cikin girmamawa kamar kullun,
Ya amsa mata acikin husky voice din shi
Yatare ta da cewa maryam wai guduna kikeyi ne yanzu ko may,
Don yanzu sai ki shigo cikin school din nan batare da kin je guri na ba,
May nai maki halan kike min wanan judgment din pls,?
Daidai lokacin da ta bude motar tashi ga ta zauna da kyau tadan kalle shi da dauraren fuska tace,
Haka dai kagani malam amma ni may zai sa in ma haka kawai,
Motar yaja suka bar gurin tare da ci gaba da lalashin ta,
Nan yake sheda matacewa yasan ta na fushi dashi don tana gani kamar yaki maida hankali ne a kan zancen su,
Yace ya turawa mahaifiyar shi da wani kawun shi don yaje akai karshen zance,
Maryam dai batace mai komai ba banda cewa da tayi Allah ya kyauta kawai.
A kofar gidan su ya aje ta tare da kara bata hakkurin cewa insha Allah komai zai zama daidai,
Sai a lokavin maryam tadan sauko daga fushin da tayi dashi saboda yana yawan sa mahaifinta na fada da ita da Anty cewa sun mai dashi bi nan,
Rana akeyi ga kuma alamar hadari da ya rufe ko ina giragizai suna yawo alamar ruwa zai iya zuwa ranan,
Tasamu Anty ta rage duk wani aiki da zasuyi a yinin ranan,
Tana zaune tana kallon tv ita da Abubakar wanda ke ta wasan shi shi kadai, a tsakar falon su,
A gajiye ta fada saman kujera tana mai cewa wayyo Allah na wash ,
Har kun dawo inji Anty tana kokarin mikewa tadauki Abubakar din ita maryam,
Ganin yadda take fara,a yau batare da tashige watsa ruwa kamar yadda tasaba ba indan ta dawo yasa Anty gane cewa tana cikin farin ciki yau din,
Tambayar ta yi dacewa halal A, A ya sauke ki naji horn din motar shi, ?
Maryam wace ta dan dakatar da wasan da takewa yaton don jin tambayar da yar ta tai mata,
A hankali tare da sauke yaron dake hannun nata ta amsa da fadin cewa eh a hankali,
Nan take fuskan Anty ya canza ta nuna wa maryam din bacin ranta sosai,
Nan ta shiga yi mata fada akan cewa gaskiya ita zata fadawa baba don yafidda ita daga cikin wa yan da yake zargi,
Maryan cikin marairaicewar murya tace anty kwanan nan zai turo Insha Allah,
Harara anty ta watsa mata irin na ke kika sani din nan,,,,



ZEEE MAKAWA
[3/24, 2:21 PM] 0mmer Farouk: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
5⃣5⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
Jin,jina gare ku ko yau yan uwa masoya novel din furen juji,
Tsayawa rubuta sunan ku zai ci muna time shiya sa nake rubutawa a jam,i gabadaya,
Nagode kwarai da irin kainar da kuke gwada min har kullun,
Allah ubangiji ya karawa,Annabi daraja Allah ka,taimaki musulmi duk inda yake,πŸ‘πŸ‘πŸ‘


Dole yatafi garin kwantagora ya samu Abdulsamad akan zancen Ibrahim da Ejoma,
Don haka yafara shiri matsalar shiguda yanzu shine yadda zai yi handling din maman Choima,
Idan son samu ne cikin wanan week din ya shiga garin,
Sai dai kuma ga aiki yai mai yawa,sosai yanzu da wuya yasamu zuwa cikin,wanan satin,
Zaune yake ya mai,da hankalin shi ga computer shi inda yake ta shigar da wasu sakon,nen masu mahinmanci,
Wayar shi ce tai kara ya mika hannu guda a hankali ya dauko wayar dake aje saman tebur din nashi gefe guda,
Jibrin KG yaga an,rubuta saida yadan sake murmushi yace ya dai man ?
Yace wallahi tun dazu naso inzo office din ka amma aiki ya hanani yau muna entered din kayan da suka shigo cikin wanan satin,
Sai kuma Jibrin din ya canza topic da cewa ga kuma tafiya ta, taso muna,
Kaida wa in ji Yusuf yake tambayar Jibrin din ?
Sai da Jibrin yai yar dariya sanan yace dakai mana ,
Tunda shi KB dama already yana can tun jiya,
Yusuf tace look Jibrin ina son shiga KG so,sai amma aiyuka sun min yawa ,
Dole sai zuwa satin sama koda zan tafi din yanzu,
Jibrin yace zancen baby din nan ce na gurina ya taso shine suka kirani wai inzo zasu sa lokaci,
Yusuf yace wa safiya ?
Ya amsa da cewa ita fa, kaga zamu iya zuwa mu ga su uncle di na akan zance Sadiya dayani
Don ina ga haka zai fi muna sauki da zuwan da zamuyi har sau biyu a cikin lokaci guda,
Shiru yayi kamar mai nazari wani abu yana sauraron Jibrin din,
Ko ya kagani ne man ? Jibrin ya,tambayi Yusuf din
Don haka bayan kwana biyu suka shirya zuwa garin kwantagora ,
Mota uku kawai sukai tafiya da su wanan karon basu zo da mutane da yawa ba,
Badon komai ba sai ganin dayayi cewa yanzu an rage kawo mai hari daga church din su,
Sai da suka kusa kawo wa sanan Yusuf yabugowa anty Dije waya yana sanar da ita cewa zai shigo gari yau insha Allah,
Idan har yana cikin mota yafi bukatar yai tukin mota da kan shi
Gashi kuma da masifar gudu a saman titi sai hankali wanda ke ciki, tare da shi ya tashi,,,

Shikan shi Jibrin yana mamakin yawan shakuwar Yusuf da Anty Dije,
Tunda yaga suna shiga gari, ya karya kwanar unguwar su Anty Dijen,
Saida Jibrin ya kasa daurewa yace wai man nifa har mamakin, kake bani,
Saida yadan juya inda jibrin yake zaune yace namay fa,?
Dariya kuma jibrin din yasa alokacin yana ta girgiza kan shi kawai,
Cak ya tsaya a kofar gidan misalan karfe biyar na yamma,
Yan samarin dake zama gefen gidan duk yamma suka yo kansu gaba dayan su, cikin murna,
Saboda sun san cewa zasu samu abin tabawa ke nan,
Hannu ya mika masu gaba dayan su a cikkn sakin fuska suke ta gaisawa da su,
Wani wanda ya samu kariya a sanadiyar hatsarin mashi yana kokarin taso wa zuwa gurin shi,
Da sauri Yusuf ya nufi inda yake yana cewa malam Aliyu har yanzu kafar nan tana nan ashe, ?
Bayan sundan yi ban hannun sun gaisa matashi wanda Yusuf yakira da malam Ali ya ce ma Yusuf,
Wallahi gani nan dai yanzu wai asibitin kashi na kano nake son zuwa a diba min ita,
Sai,dai kuma abin tafiyar ne sai a hankali wallahi,
Yusuf yace haba, haba dai ai da sai muyi waya ko,
Bari zan gan ka idan na huta ai yanzu shigowar tamu ke nan,

Maryam ce tafito daniyar zuwa nan yar kasuwar bayan kwanar kuka don ta sayo yan abubuwan da suke bukata don yin abinci dashi tunda yace yau zai shigo,
Turus taja tai tsaye don ganin da tai masu akofar gida,
Cikin kasa boye mamakin ta take kallon su
Harara ya saki mata daga inda yake a tsaye yace shine taron da za mu samu ke nan ko, ?
A hankali yake kokarin takowa zuwa cikin gidan nasu,
Gefe maryam ta dan rabe mai don yashige,amma sai yadan kurawa maryam ido wace a ko yaushe cikin kara canza mai take,
Ya na zowa daidai inda take tsaye yasa kafar shi ya take mata yan yatsun kafar ta da takalmin shi,
Wani irin dan sautin kara, ta sake, a lokacin guda da sauri ta daga kai ta dube shi,
Amma sai taga bai ma ko kallon inda take, sai kokarin gyaran kwalar rigar shi yakeyi,
Murya na rawa tace wayyo ya Yusuf katake min kafa fa,
Har zuwa wanan lokacin bai nuna yaji may tace ba,
Sai wani irin zugu take ji a yan ya tsun ta,gashi sai kara matse mata su yake da takalman shi,
Zafi da radadi ke ratsa ta alokacin gashi shi yaki daga kai ya kalli ko da gefen da take tsaye ne,
Wasu hawaye masu dumi suka silalo daga idanun ta,
Takara cewa dan girman Allah ya Yusuf kayi hakuri,
Sai a lokacin dan sasauta mata kadan wani irn ajiyar zuciya ta sake cikin kuka,
Sai da ya hango Jibrin yanufo kofar shigowa gidan yai sauri yadan ja baya kadan,
Yantsun kafar nata, ta kalla sunyi wani irin ja jajir
A hankali ta dafa bangon dake gefen ta, tana bi a hankali cikin dan gyashi,
Nan da nan ya tsuke fuskan shi kamar bashi bane yai mun wanan muguntar,
A lokacin jibrin ya karaso gurin yana cewa an sauke kayan ga mutanen ka nan zasu shigo dashi, yana nufin samarin nan da ke kofar gida,
Sai a lokacin idon shi ya kai ga maryam wace ke kwalla, wahala,
What's going on here man,?
Tankar da dutse yake magana yake magana don ko kallon shi bai yi ba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login