Showing 240001 words to 243000 words out of 255288 words
Chapter 81 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete
Don dai Sonny bazai iya musulunci ba gashi ya kasa tsayi a Christianity balle musulunci mai akidoji,
Har hotel din da suka sauka Sonny yakai Yusuf sai dai bai shiga ba don adan buge yake alokacin,
Amma yai alkawarin zai kawo ma su ziyara zuwa gobe indan ya fito,
Washe gari ganin da Sonny yaiwa maryam din sai da ya tsorata sosai,
Don maryam din ga kyau, ga iya dressing ga zubi daganin ta ka ga matar manya ce,
Fatan jikin ta yai mata wani lub lub, tankar irin mantan Pakistan din na dakr cikin daula,
Ga natsuwa da kamala don komai nata a natse takeyin shi ba garaje,
Wanda hakan ke wani kara mata aji da class, a idon mai kallon ta,,
Sonny yai masu murnan auren da sukayi inda ya ba maryam din kyautan wani dan kit da kuma wani dan karami box,
Duk kan su sun san cewa kyautan Sonny ta bajinta ce a ko da yaushe,
Basu kara wasu kwanaki ba masu yawa suka bar kasan zuwa kasar Dubai,
A can zai ga wasu mutanen da yake bukatan ganin su don su karfafa har kan median a Africa,
A kasar Dubai maryam tai mamakin ganin yan Nigeria a can birjit, kamar a kasan su,
Wanda duk harkokin business ne yakai su kasar,
Gashi kusan kowa da matar shi zaka gan shi a gurin wasu kuma matan banzane kawai anje shakatawa, ne kawai,
A gidan wani cin abincine suka hadu da wani matashi dan Nigeria wanda yaje harkan business sai dai bawai ya saba bane,
Shida kanshi mutumin mai suna Suleiman yai wa Yusuf magana,
Anan hira ta balle a tsakanin su inda Suleiman ke ba Yusuf labarin cewa ya shigo ne don yadan fara taba international business ,
Shi mutum Minna ne Niger state yana aiki kuma yana son harkan business,
A nan Yusuf yadinga bawa Suleiman shawarwari akan business
Daga karshe sukayi sharing din nomban su wa junan su,
A wani dare ne Yusuf yai waya da KB inda KB ke sheda ma Yusuf wai Jibrin yai aure
Aure fa inji Yusuf wanda yai tambaya a cikin mamaki ?
KB wanda, yaba Yusuf din ansa cikin dan rudewa ya ce, kwarai kuwa,
Auren ne ba dole sai kasani ba inji KB din don wace ya aura din,
Ba safiya bace ya aura sai a lokacin maryam wace take bayan shi kwance rub da ciki tai magana,
Cikin dan dagowa da ga kwanciyar da take yi ne tace wace baka zata ba dai ya aura,
KB kuma a lokacin ne yake ce mai ai Jibrin Sadiya ce ya aura,
Boye mamakin shi ya yi da cewa masha Allah nai mashi murnan samun wanan karuwan,
Amma shine bai fada min ba sai dai kawai inji bayan bukin,
KB yace sai dai in Allah ya dawo muna dakai lafiya zaka ji ai ,
Bayan sunyi sallama ne Yusuf ya turawa Jibrin da text din taya shi murnanan aure,
Azaton shi zai turo mai da ansa amma sai ya ji shiru ba replay
Sai daga baya ne yake tambayan maryam ko tasan dalilin hakan,
Maryam wace take a zaune a gaban mirrow tana daura dan kwali tace
Ai Safiya ta mahuta wallahi maganar sai ta ba yusuf mamaki,
Maryam nasan cewa kinsan wani abu acikin wanan maganar amma baki fada min ba,
Maimakon tai mai bayani abinda ke faruwa sai ta share da cewa uncle je kai wanka kada bakin mu su samay ka bashiri,
Ya fahinci batason yasan wani abu akai don haka yabar zancen kawai,
Baki sukayi wani mutum dan Nigeria da ke son su hada wanan business din da zasu hada a Dubai din,
Sun sa ranan meeting don haka sun dauki lokaci mai tsawo suna wanan plan din,
Matar chairman din comety din nasu ita takawo shawaran cewa su ma matan su ya kamata su kawo nasu gudun mawan,
Wanan taron da matan suka sa zasu ya jawo wa duk wata mace dake cikin gungiyar samun cigaba sosai,
Kafin lokacin Yusuf wanda yasan cewa matar yarinya ce ba wai ta,waye bane kuma sauran matan sun mahaife ta
Wani dan training school na mata ya kaita, cikin kwana uku maryam tazama wata irin gogagan mace yar bariki,
Ranan taron nasu maryam tare da matar da tai mata training din itace da kanta ta,shirya maryam din,
Daga ciki kwalliya irin ta matan hausawa tayi zani da atamfane jikin ta, wanda yasha dinki irin na Dubai design
Daga,sama ta dora wani irin alkyabba irin mai tsadar gaske din nan,
Daga nisa kasan cewa sai matan manya ko matan manyan sai wace ta isa,
Hular alkyaban yadan rufe mata ko ina daga kan ta,
Zakace ko mayafine ta yafa akanta alokacin don irin yadda yai mat,
Hannun ta an jera zobbunan gold sun cika mata yatsu,
Wuyan ta na saye da gold kiran Dubai ya na daukan ido don tun daga nesa zaka hango shi,
Takalmin kafan ta da yar jakar hannun da ta rika shima abin kallo ne,
Ga wani asirttacen kamshi dake tashi daga jikin ta,
Shi kan shi Yusuf din sai yaga maryam din tashi ta canza mai tankar ba ita bace a gaban shi yau,
Yusuf bai san sanda ya jawo maryam din zuwa jikin shi ba,
Jikin shi narawa ya na kokarin kai bakin shi cikin nata,
Sam ya manta da zancen matar da ke tsaye a gefe tana jiran sallama,
Wayan shi yabawa matar yace tai masu photuna,
Ganin irin yadda ya rude baiko iya boyewa agaban mutane maryam din tace haba uncle
Yace gaskiya maryam wanan matar zata hada min duk wasu abinda nake bukata a lefen ki,
Haba wani lefe kuma duk wanan sayayyan da nasha ni sun isheni Alhamdullahi ko hakan,
Ya maryam tsadar shigar ki ko a yaushe shi mutunci na a idon duniya don za,a san ban tauye maki hakkin ki ba ta ko ina,
Maryam tai dariya tace aiko a haka Alhamdulla don an san baka tauye ni ba
A, a maryam nafison ansan cewa ke din ta daban ce zai fi min ni mutum ne mai son ko yaushe inga matana acikin kwalliya,
Irin yadda maryam tashigo dakin taron ya tayar wa sauran matan da hankali sosai
Don gashi dai itace karama daga cikjn su duk sun haifeta wasu kuma sun girmay ta,
Amma sai gashi ta tsone masu ido shi da kan shi Yusuf yai mata rakiya agurin yana nan nan da yar matar nashi,
Duk gurin suka bisu da kallo sai da yaga gurin da ta zauna yadan duka yai mata magana a kunne wanda yasa maryam din sake dan murmushi da ya kara mata kyau,
Kishin haka yarufe wasu mata daga ciki da suke ganin cewa su wata tsiya ce da farko,,,,,,,
ZEEE MAKAWA YELWA
[5/5, 10:21 PM] +234 703 055 6607: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
9⃣6⃣
Cikin jin dafin samun nasarorin da Yusuf yayi suka dawo gida Nigeria,
A cikin nasarorin da yasa mu harda zama shugaban youth na median na Africa,
Sun samu kowa lafiya agidan inda suka,samu taro mai kyau,
Maman Choima kallo guda taiwa maryam ta kauda kai agare ta saboda irin yadda taga canji cikin lokaci guda,
Pipkin yafi kowa murnan ganin little mum ta dawo a lokacin,
Tunda Yusuf suka sauko ya shiga gida bai fita ko ina ba don yana son hutawa,
Maryam taiwa duk wani wanda ke gidan atare da,su kyauta ta musan man,
Hakan ya sa masu son matar ogan nasu azuciyar don dai sun fahinci bata da keta,,,,,,
Lokacin sanyi ne, don haka kusan goma na safe amma Yusuf ya na kwance makale da matar shi wace bata da wani hutu idan yana gida,
Barci sukeyi amma ajikin shi take kwance saboda jikin su akwai gajiya,
Wayan Yusuf wace ke yashe a gefe guda tai kara har wayan ya kusa karewa suna kwasan barcin su a lokacin,
Maryam ce tai kokarin dagowa daga saman kirjin Yusuf, din,
Itace tadan dauko wayan daga inda yake a yashe,
Idon shi da dan sauran barci a kai sai kuma haushin wanda ya tada shi daga barcin shi da yake yi na safe mai dadi
Samuel ne ya gani a rubuce saman screen din wayan shi,
Samuel how are you ?
Brother we are coming to Abuja this morning with papa,
Yusuf din wanda yaji maganar kamar daga sama zubur ya mike daga inda yake kwance,
Maryam wace a lokacin tana cikin bathroom shi kadai yai zaune a bakin gado yana tunane da nazari,
Shawara guda shine ya kai su gidan shi guda kawai ya kai masu masu aiki can,
Ganin shi a bakin gado cikin yanayin damuwa ya sa maryam saurin karasowa gurin shi da,sauri tana cewa uncle lafiya,
Kan shi yadaga a hankali ya kalle ta kamar kada ya fada mata sai yaga ai sani zatayi,
A hankali kamar wanda zai fadi wani mugun zance rai a dan bace
Hakan yasa maryam wurgat da dan towel din dake a hannun ta kasa,
Da sauri takaraso gu4in shikin tambaya take cewa
May yafaru ne wai batare da ya kalle ta ba yace wai baba da yan uwana zasu yau din na,
Maimakon maryan ta nuna razanan ta afili sai Yusuf yaga tana murmushi,
Tace ashe barin fita in fara abin taron baki yau muna da bakine haka agidan,
Kallo yabita dashi na mamaki don yazaci ta nuna mai kyamar ta karar akan su
Ta mike da niyar ta wuce taji ya riko hannun ta, ta baya cak ta tsaya guri guda
Muryan Yusuf ne da yajawo ta zuwa jikin shi yana cewa maryam baki tsoron zuwan su gidan nan,
Tsoro ta tambaya cikin mamakin jin maganar shi tana mai wani irin kallo
A kwai matsalane halan, gazuwan su tatambaya cikin nuna rashin damuwa,
Bai ce komai ba shima mikewa yayi batare cewa komai ba,
Sai sai maryam tai masu girki inda takuma sa a,gyara masu dakunan kwana, amma Yusuf bai da labarin haka,,
Sun iso garin bayan sallan la,asar alokacin maryam tana dakin ta na sallah,
Azaton Yusuf sukadai ne zasu zo yan gidan su sai gashi ya ga mutane masu yawa,
Yan manyan church din su ne tare da mahaifin shi wai sun zo wani taro ne a wani church irin nasu,
Duk yawan abincin nan sun cinye abinsu sai kari suke bida,
Nan ihu yatashi da kiran sunan Jesus, maryam tun daga dakin ta na sama take jin wanan ihun nasu,
Sai kalman Innalillahi take iya maimaitawa kawai, a bakin ta,
Yusuf wanda yaso yakai su masauki amma fafir sukace su a an zasu sauka,
Sau guda maryam din ta sauko kasa gaida su suna zaune ga kwala be a gaban su sai dai bazata iya tantance kona maye ba,
Cikin zulunbun Hijab din ta har kasa baka ganin komai nata sai dan round face din ta kawai,
A natse take tafe Yusuf na gaba tana bin shi baya cikin natsuwa,
Duk kunya takama shi ganin irin yadda suka baje tumbi da kuma sake jiki suna ta faman dura giya a cikkin,
Duk kunya da nauyi ya kama Yusuf wanda rayuwan shi duk yabaci amma bai,da yadda zai yi ne kawai,
Kowa sai kallon maryam din yakeyi kamar zasu cinye ta danya,
Tundaga wanan ranan maryam batakara saukowa ba,
Saidai Yusuf yasayo mata abinda za ta ci ko take bukata,
Kwanan su goma sanan sukabar masu gida inda kafin su wuce baban Yusuf yake cewa shi yafi son Yusuf ya auro yar yaren su,
Tafiyan su ba karamin dadi yaiwa Yusuf ba wanda ya dinga ji tankar yai kuka saboda ansha mai giya a gida,
Masu gyaran gida yaturo sukai wa gidan nashi, kwal komai saida aka wanke,
Yafara zuwa office bayan dawowan su a can KB yasamu Yusuf yana bashi labarin yadda Jibrin ya auri Sadiya,
A cewan KB wai harda mahaifin shi yace kada ya yi wanan auren amma Jibrin din ya dage akan sai yayi,,
Kuma yanzu ga shi sai sukan Yusuf da maryam yake yi duk inda ya zauna,
Yusuf yaso ya bata rayuwan shi akan yadda Jibrin din yai mai sai dai yaga cewa babu abinda a gwada mai a rayuwa yanzu,
Baiwa maryam zancen ba sai bayan kwana biyu a lokacin yana aiki a cikin computer shi
Maryam tana zaune a kasa ta sa fruit a plate sai sha takeyi
Idan ta sha tabare ta sawa Yusuf a baki yana yi yana aikin shi,,
Maryam Yusuf ya kirata batare da yadago kan shi daga aikin da yakeyi ba,
May kika sani akan rabuwan Jibrin da safiya ?
Tambayar ya bata mamaki sosai a lokacin don bata zaci zai kara maganar ba,
Uncle gaskiya ni abinda safiya tafada min bawai nayarda bane,
Fada min may ta fada maki maryam bata boyewa mijin nata komai ba azancen da safiya ta fada mata,
Hmmmm kawai yace bayan da ya fahinci maryam tagama zancen ta,
Maganar tasa Yusuf ya kasa aikin dake a gaban shi yadan dago daga duken dayake,
Hannayen shi ya hada guri guda yadan fura iska ta tsakiyan su,,,,
Dasafe idan Yusuf yafita gurin aiki sai shida yake dawowa gida wata rana yakan dawo daguri kuma,
Yau ma sun rabu lafiya tsakanin su Yusuf yatafi yabar maryam tana daga mai hannu
Ta koma ciki ba a dauki wani lokaci ba barci ya kwashe ta,
Kaman ance ta bude idon ta sai wata budurwa tagani a dakin,
Ta na saye da dan guntun buje daidai cinyar ta, sai rigar jikin ta baki mai kama da shimi,
Tashi maryam tayi taga kwancen da take cikin mamaki don budurwan ta gaban mirrow tana shafa jan baki a bakin ta,
Cikin hausa mai surki da yare tace kin tashi matan yayan mu,
Murmushi maryam tasake mata, nashigo kina barci shine nace barin kyale ki,
Har nai wanka baki farka ba sai yanzu dama zan fitane akwai saurayi da zai zo,
Zaune maryam takai inda ta sako kafafun ta kasa cikin mamaki,
Amma ga yadda taga budurwan na murmushi sai tadan sake ranta itama,
Yanzu dai mu gaisa sunana Ruth ni kaunan mijim kine da fatan ya baki labarina,
Takarashe zan cen da son jin ansan da maryam zata bayar
Cikin murmushi maryam tace kece Ruth ashe ko yau she yana zance a kanki kuwa
Ruth taji dadin hakan don sai da ta dan yi murmushi mai baiyyana hakora,
Maryam tace barin kawo maki abinci ko kafin ki fita,
Cikin daga hannun ta tace da sauri No, no no ki barshi kawai
Sai nadawo idan brother ya dawo saiki fada mashi pls,
Daga haka tafita kusan a tsirara take maryam ta sauke ajiyan zuciya bayan fitan ta,
Hamdallah ta yi ga ubangiji da yayo ta musulma,
Abinda maryam ta lura dashi shine Yusuf naji da sister shi Ruth sosai don haka tadauki alwashin kyautawa Ruth din itama,
Duk yadda yake son kasan cewa da Maryam din kamar da yanzu bai samun haka,
Tun yana daurewa har yakai yau bayan yadan shawo kanta ne komai ya kammala,
Sai kawai yaga har barci ya kwashe ta ko yanzu sam bata son bashi hadin kai kamar farko,
Saman dining table suke kowa na kokarin karyawa amma banda maryam wace tasa ruwan tea din ta gaba tana kallo
Yusuf ne da kanshi ya matsa mata har tadan sha rabi,
Abuguda ke damun maryam yanzu kamar yadda su Ruth da Grandma ke damun su da waka tun da asuba ko tana son yin addu,oi basu bari saboda ihu da kuma suraitan su,
Yau ma kamar kullun bata samu barcin dare da dadi ba takai wani lokaci a kwance, saboda masu wakan church dake tashi cikin dare suyi tayi,
Wanka maryam din tafito tana zaune gaban mirrow Yusuf yashigo dakin yana kokarin daura cliffs a hannun rigan shi,
Tun daga nesa tace mai ina kwana uncle ya ki ki beauty, nashigo na samay ki kina ta barci ai,
Murmushi maryam tayi tace yanzu sai da safe nake dan samun barcin don hayaniyan nan na dare bai bari inyi barci,
Baiyi magana ba sai ido da yadan tsura mata tausayi tabashi acikin rashi don yasan cewa dama hakkuri takeyi kawai,
Don irin yadda suke yi da wata ce yasan da yanzu an kwashi yan kallon dan abin nasu harda gaiyya aciki,
Sallama yai mata yace zai dan shiga gari don ba aiki a ranan,
Bayan fitan shi tadan sha fruit don shi abincin ta ita saboda ko da bata damu da abinci ba ita,
Saida taga tadan kara kwantawa don