Showing 9001 words to 12000 words out of 255288 words
akai,
Amma a lokacin Dije tana secondary bata kare karatu ba balle tayi aure,
Bayan kare karatun tane ta hadu da wani dan makwabcin su Iliyasu ma,aikacin aikin custom ne,
Sukayi aure tun lokacin da dije ta tsaida miji tasha alwashin cewa za ta dauko maryam su tafi tare,
Amma sai uwar ta Inna, hussai tace mata sam bata yarda diyar ta ta dauko mata, wata wahala ba can daga kauye,,
Don haka Dije tabar wanan zance kamar ta fita batun sai bayan auren su da ILiyasu ne
Baba yaje dakan shi bobi ya dauko maryam da yan kayan ta yazo ya danka wa Dije ita amana,
Tun wanan lokacin Anty Dije ke kula da yar kaunar ta , ta cikin amana,
Har zuwa lokacin da Allah yabata nata haihuwa,
Assalam.shine nafarko sai Issalam, wace yanzu daga gareta ba,a kara samun wani ba, tukun har yanzu,
Mijin Anty yana zaune a can jibiya ne bakin border don da lagos yake har ya taba zuwa da su sai da anty ta kusa haihuwan Assalam suka dawo,
Inda mahaifiyar shi tace bata yarda ya koma da ita ba , don in yatafi da iyalinshi wai yana dadewa baizo gida ko kuma aike,
Tun wanan lokacin anty ta zauna kwantagora bata kara bin mijin ta abisa umurnin uwar mijin ta,
Saidai har yanzu abin bai canza ba don gwamma da da yanzu don yanzu baifi ya zo sau uku ba a cikin shekara,
Saidai yakan aiko masu da sako akai akai,
Maryan yanzu tana karatu ne a Girls day secondary school kwantagora,
Tana Ss² yanzu su kuma yaran antyn ta sun fara nursery a wani preravent school,,
Maryam ita ba fara bace kuma ba baka ba yar doguwa da ita bata da jiki tana da hanci madaidaici da ido masu dan girma,,,,,
Yau kusan satin shi biyar da barin gari yana can suna ta harkan man fetur,,
Saidai a kai akai suna yawan waya da abokan shi,
Musan man KB da jibrin wanda dama sun fi shakuwa da su tun suna yara,
Don duk irin wulakancin da ake mai lokacin suna yara na kasan cewar shi dan kirstan acikin su
KB da jibri a gaskiya ba suyi mai sukan ja shi zuwa gidan su ,
Idan kuma mahaifin shi yasani a lokacin yai mai dan karen duka,
Har akwai wani lokaci da ana bukin babban sallah yabar gidan su tun da safe zuwa gidan su KB , da kayan shi dunkule a leda a cewar shi zai bi su gurin yawon sallah ne,
A gidan su anyi bidan shi har angaji kasan cewa idan musulimi suna irin wanan buki su kiristan sukan killance diyan su a gida basu bari su fita ko ina,
Hakan yasa shi yin asubancin barin gida zuwa gidan su KB din,
Dashi akayi ai,kin komai na naman inda aka diban mashi zuwa gida dabara yayi da zai tafi yaba KB saura yace ya boye mai
Baban su KB shi yaraka shi da yaga yana labe ,labe
Suna zuwa tun daga nesa uban shi yafara yi mai sababi saida mahaifin KB ya bashi hakkuri,
Wucewan mahaifin su KB kadan akasamay shi akai ta bugu kusan duk wanda ya girmay shi a gidan ranan sai da ya doke shi,
Yana kallo naman da yaje kwadai yai wahalar aiki aka zuba a cikin ruwan kwata aka murje,
Duk da haka washe gari saida ya koma, wurin KB da zai tafi kasuwa yadan dade gidan sanan ya wuce, kasuwa,,
Iya gaskiya shi Joseph yana jin dadin zaman da su keyi da su KB da sauran friends,
Idan yana cikin su ana hira yakan ji kamar an yaye mai wani nauyi duk da ba magana yake yawan yi ba acikin su,
Yadda suke hira ana challenges din juna ko kuma kuma yayi ta kallon yadda mutane ke ta faman zirga zirga,
Abin yana burge shi so sai don idan a cikin yan uwan shi IBO yake sam babu wanan irin dabi,ar sai dai kawai kulun a na gurin bidan kudi,,,,
Shidai dabiar hausawa tana mai a rayuwan shi don in ba haka ba da irin dukan da yasha yana da ya daina kula su,,,,
Don haka tun dawo war shi, kasar su yake tunane da nazarin irin sana,ar da ya kamata ya jona su KB aikai wanda zai jawo masi cigaban rayuwar su
Batare da,sun dogara da wani ba ko kuma da aiki gwaunati, kamar yadda akasarin hausawa ke yi yanzu,
Yau da ruwa aka tashi a garin na lagos don haka duk wanda yakai wani lokaci a waje go slow ta rutsa da shi,
Joseph wanda shigowar shi ke nan garin a lokacin, da ake tsula ruwan,
Tafe yake a hankali a cikin motar shi yana tafiya kamar wanda bai son yin,,,,
Idon shine yakai ga wani motar daukar kaya watau tirela,
Wace tayo dakon buhu,hunan shikafar yar gwaunati sai,dai,duk ruwan sama yasa duk ta fara jikewa ga masu motar nata wahala, da shi
Wani irin tunane yadar su cikin zuciyar shi wanda tasa shi dan yin murmushi a lokacin,
Gidan shi dake cikin, Apapa ya wuce direct inda yasamu maigadin gidan yabude mai get ya shige ,
Mai aiki naganin shi yatashi da murnan shi yafara kokarin hada mai dan abinda zai ci, tunda yasan cewa ogan nashi baya cin abincin waje,,
Yana ganin oga yasan cewa yau boza tazo don yasan cewa duk sanda ogan na shi ke gari duk kan su dake a karka shin sun yake wahalar kudi,
Wanka Joseph kafin ya fito har an hada mai girki mai lafiya,
Bayan ya gama ne yasamu daya daga cikin kujerun falon ya haye,,,
Don har zuwa wanan lokacin ruwa ake tsulawa, agarin
Don haka yana kwantawa sai shawar da zu dayayi tafado mai a rai, daga karshe ya jawo wayan shi yadan dinga dan,na wa yana kiran abokan shi daya bayan daya suna gaisawa,
Daga karshe ya kira KB inda suka dan dade suna hira akan ginar da ya bashi kula dashi na yan marayu
Yai mamaki kwarai da jin dan kudin da aka kashe wa ginan,
Inda ya yaba da irin saukin da aka samu a wurin kayan aikin unlike irin yadda anan inda suke harkoki basu tabuwa,
Don haka yai alwashi a cikin zuciyar shi zai gyara gidan mahaifin shi da suke a ciki very soon,
Kafin su kashe wayar KB ke tanbayar shi ko yaushe zai shigo KG, din,
Yace mai sai nan da sabon wata daidai lokacin da zasu fara yin shirin programs din su na wasan Daba da za suyi,
Sun dan jima a wayar suna hira sanan suka yi wa juna sallama, suka, kashe wayar ,,,
Su na sallama da KB yakira Daddy shi inda a lokacin daddy yana zaune tare da yaran shi suna hira,
Mr Emanuel yaji dafin kiran da Joseph yai mai a wanan lokacin,
Don dama shima yana da niyar kiran shi akan maganar ginan da yaji cewa wai yana wa wasu hausa wai da sunar tai mako,
Taupa Joseph yace a cikin ran shi watau abin duniya baya boyuwa kenan,
Can kuma yace ai ba mamaki don kusan shiya kuda suke da mutane dole wani zai iya fadawa baban nashi,
Muryan Mr Emanuel ce tadawo dashi daga tunanen da yakeyi inda yake cewa,
Joseph u, no dey hear word,
I always warn u about dis people,,
Jin uban ya ci gaba da fada ne sosai yasa Joseph yai sauri katse shi da ce,
Dad, am doing all dis b,cos of u
Saboda kai ke zama ko yaushe a cikin su indan har mun nuna cewa bamu tare da su a fili a baza mu samu biyan bukatar mu ba,,
Ajiyan zuciya Mr Emanuel yayi don jin kalaman dan nashi,
Shima ta fanin Joseph din sanyayar ajiyar zuciya yayi,
Don jin ya ciwo kan tsohon na shi cikin lokaci guda,
Bai tsaya wani dogon magana ba yai sallama da dad din, ya, kashe wayar
Don gudun wani sabon magana,
Rigingine ya ke kwance saman gadon sai tuna nen maganar Dad yakeyi,
Yasan cewa za su kara kwasar rikici da tsohon nashi,
Idan har tsohon yaji cewa zasuyi wasan nin matasan kasar kwantagora a cikin su har da shi Joseph din wanda yaba da gagarumin gudun mawar shi a taron da za,ayi,,,,
Cikin, gwanin ta yake tukin motar shi daidai lokacin da ya ke kokarin shiga get din gidan su,
Mahaifin shi da aboksn shi, suna zaune saman wasu benci guda biyu, da ke harabar gidan,,
Cike da sanyi jiki yake tunda yai arba da su zaune suna ta dirkan giya sai shewa sukeyi a tsakanin su,,,
Nan da nan maganar Jibrin yazo mai arai inda yace komai darajan mutum idan ance yana shan giya,
Kimar shi da girman shi ya zube ke nan a idon duk wanda ya ganshi a hakan,
Don haka sai yaji a, lokaci guda duk wanda ke gurin kimar su ta zube mashu a idon shi,,
Yan samarin da ke gefe suna karta suka zo suka tare shi cikin murna da jin dadin ganin shi,,,
Buth din motar shi ya bude masu suka fara jidan tsarabar da yazo dashi zuwa cikin gida,
Inda dattawan ke zaune suna dirkan giya yanu fa don kwasan blessing,
Kirari wani daga cikin su ke mai irin kirarin yan gidan su da ake masu a can kasar su,
Jin kirarin yadan sashi yin yar murmushi daga nesa saboda yana son wanan kirarin na kakan su da ake masu,
Karasowa yayi inda suke yadan yi kamar ya duka yace masu barkan ku da gida,
Gabada yan su sukace mai blessing my child,
Ya hanya ya ya kabaro lagos yai dan murmushi yace daga Abuja yake shine yace bari ya kara so nan,,
Wani dan gajere mutum daga cikin su yadan kalle Joseph din daidai lokacin da yake zuba bommi a cikin wani cup,
Yace waiting dis boy want, in dis town, no b last month i saw him,,,
Baban Joseph da ya sha yai tatil yace cikin murya tsatsaye,
Na, me send for him wooo, i wan tell him about d white men,
Joseph da yaga kamar shirmay suke zubawa ga warin giyar bommin da su ke sha duk ya cika mai hanci,
Sai cewa yayi sai anjimar ku yana kokarin shigewa,
Wani daga cikin su ya dan yafito shi da hannu yana mai alamar yazo ya zauna
Wani daga cikin sune ya iya bude baki yana cewa come nd join us my son,
No tnxs kawai yace yana mai kokarin mikewa tsaye yabar gurin
Tunda ya shiga gida baiyi marmarin fitowa ba saboda yan dattawan dake waje suna holewar su,,,,
Sai sha daya na safe ya ke shedawa su KB yana cikin gari,
Duk sunyi mamakin jin cewa yana gari don basu sa rai cewa zai shigo very soon haka ba,,
KB ne ke ce mai ya na tafe yanzun nan,
Sai Joseph din ke ce mai ya bari har zuwa yamma don dama wani program yazo yi a church din su,,,,
Church kan ya ciki makil yau saboda kiran gagawa da akai ma duk wani mabiyin wanan church din
Kamar irin su Joseph da iyayyen su ke ciki yazama dole su zo wannan taron da ance mai ma,anace taron,
Wasu turawane ke perching kamar kuma shawa da umurni suke ba sauran mutanen,
Inda suke neman hafin kan duk wanda ke cikin addinin da ya kawo gudun mawa mai tsoka
Indan an hada kudin daga baya sai su shiga daji inda kauya wa suke su fara masu wa,azi da kuma jan ra,ayi da abin duniya, har su samu galaban jan ra,ayin su
Ihu da murnan jin wanan shawaran church din ya rude dashi, saboda suna ganin cewa zasu iya cin galabar yan kauye da,dama a, hakan,
Kafin wani lokaci an fara yawo da ture ana karban gudun mawan gurin jama,a,
Wani dan kyamushashen bature ya kara tashi yace
Wani hanya kuma guda da zasu bullowa al,umma dashi ita ce
Suna da wani baiwa da zasu iya kara jan ra,ayin mutane da shi cewa,
Duk wanda baida lafiya za su warkar dashi indan har yaji sauki to ya zama dole ya bi akidar su,,,
Sannan su kara tabbatarda cewa har wa yan dake a ciki idan su na da wata cuta zasu iya zuwa a warkar amma da sun ji sauki ya zama wajibi a kara masu mukami acikin church,,,
Joseph najin haka ya mike kamar mai waya a zuciyar shi yana cewa yan yaudara ne kawai da cuta,,,,,,,
ZEEEE MAKAWA,,,,,,,,,
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
6⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
Zaune take gaban mirrow tana dressing kusan duk abinda mace zata bukata na fente fuskan zamani ta na dashi a gurin,
Dogon rigar atamfa ce ajiye saman gadon ta gefe hade da dan kwalin shi da gyalen shi,,,
A hankali tadauko rigar ta zura a jikin ta, ta gyara tsayuwar rigar cifcif a jikin ta ,
Ta mika hannu ta dauko dankwalin ta fara daurawa a kan ta,
Batafi minti shidda ba taga komai takara feshe jikinta da turare,har zuwa gyalenta,
Kinsan da gyale da hijab sun fi daukar kamshi a kayan mace,
Saboda hatsari mace ta dinga shafa turare a jikin ta yana kawo wa mata breast cancer so sai, wlh,,,,
Amma idan kin dan sa wa top din ki is ok ko ina ki kabi zaki na kamshi so sai, har na wani lokaci (pls be aware)
Wasu takalma ta jawo wanda sukayi matching colour da gyalen ta, da yan kunen ta ,,,,
Tsaye take gaban mirrow tana kare wa kanta kallo,
A, lokacin wayar ta yai kara cikin sauri ta dauko murmushi tayi don ta san ta bata lokaci,
Haba Aisha kin san fa cewa ance ba makara don Allah kada kisa a rufe get ba mu shiga ba,
Daidai lokacin ta rufe kofar dakin ta, don gudun kada yan kan,nen ta su shiga mata cikin dakin suyi mata barna,
A kofan gidan nasu ta iske Amina kawar ta cikin motar saurayin ta suna jiran ta,
Baka jin komai a motar sai sautin kida dake tashi kamar kune mutum zai fashe,
Duk inda suka bi dule a waige su don jin,karar kidan motar da ya hayhake ko ina,
Tunda ta shiga motar gaisuwa kawai ya hadasu da saurayin Amina
Ba su tsaya ba sai wani mating wuri da aka killance a rubuta da manyar haruffa, kamar haka,
SAFARA MOTEL,,,,,,
Sai wasu yan kananin gloves da ke haska wanan rubutun yana bada launi kalakala,
Duk saurin da sukeyi sun makara don sun samu an rufe get, ko,,,
Komawa Aisha tayi baya tadan jin gina bayan ta da mota, da sukazo da ita,
Tunda har an rufe get yanzu dole sai ta samu partner da zasu shi ga,
Sauriyi Amina ne keta faman zirga zirga bidan wanda yadace ya hada Aisha Sanda da shi,
Sanin halinta na zama first class ya sa bai yi gigin hada ta da kowa ba,
Wata mota ce ta dan no inda suke tsaye tunda ganisa kaji engine din motar kasan yar lafiya ce,
Rangerover sport, ce ta dan no tun daga nesa aka kashe mai ido da hasken motar,
Duk da bai san kowaye ba aciki yasan wanda yasan shine,
Don haka yai tsaye guri guda har na cikin motar ya fito
KB ne yafara fitowa ta gefen mai zaman, banza,sai kuma Jibrin wanda ya balle, marifin motar baya ,ya fito,
Tunda ga nesa ya gane su KB don haka yasan cewa,
Yanzu za ai solving din problem din su, ma,ana Aisha ta samu irin da zai hada su,
Joseph ne yafito karshe sanye yake da dinkin shadda mai ruwan makuba ,
Sai sarkar gold da zoben gold din guda biyu a hannun shi,
A hankali yake takowa har zuwa in,da su KB suke tsaye da Lawal abokin su,
Hannu sukayi da lawal din inda ba bata lokaci lawal ke fada ma su bukatar shi,
Ya na mai nuna Aisha inda take tsaye, cikin second duk suga wai amma banda Joseph, wanda kamar ma bai gane may ake nufi ba,
Inda lawal yaci gaba da fadin sun bar pass din su, a