Showing 225001 words to 228000 words out of 255288 words
Chapter 76 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete
Dafa Jibrin din yayi yace mai ya kamata mu gagauta zuwa don baba ya samu wanan tsohon yai mai bayani yadai wani shirin kawo wa maryam kayan daki,
Mr Emanuel yana tsaye bakin kofar gidan shi rike yake da wani karfe da akatokara a tsakiyan gidan,
Motan Yusuf ce da ta shigo gidan yabi da kallo har zuwa inda ya parker ta,
Shima Yusuf yaji dadin ganin mahaifin nashi a tsaye alaman yaji sauki ke nan,
But ya bude masu aikin gidan ne sukazo da sauri suka fara fito da robobin da Yusuf ya,zo da shi,
Cikin gida suka shiga dashi shidai tsohon yana tsaye a kofa yana kallon su,
Bayan shigan su ciki sun zauna sai ga Samuel da Esther kaunar Yusuf sunfito,
Acikin yare suke magana tambayan shi sukayi da yare may ya kawo masu haka,
Esther ce ta bude robobin gani abin da ke cikki yasa ta fito da ido waje,
Mr Ema ke tambayan dan nashi kayan may wanan haka ,
Ba wani tsoro ko jin dari Yusuf yace wa mahaifin nashi wanda duk ya tsure shi da ido cewa
Kayan aure nane nakawo maku don kusa muna albarka akai,
Kafin ya karasa zancen shi yaji muryan mahaifin nashi cikin mashifa yace,
God forbids bad things,
Joseph are you out of ur mind,?
Sai da sauran yaran suka dan kadu saboda action din mahaifin nasu, irin yadda yayi,
Yusuf wanda dama yasan cewa za,a rina don haka ko gezau bai yi ba sai kallon mahaifin nashi yakeyi da addu,an shi abakin shi,
Maimakon fadan da Ema din yai niyar yiwa yaron nashi sai kawai daga mai hannu yana cewa park your things and go pls,
I don't want to see it here,
Esther wace ke tsaye daga kofa cikin wasu yan kananin kaya tace no, no papa ,
We want to test it ,
Is our brother weeding pop,,,
Kallon mamaki mahaifin nasu ke wa Esther din wace har takai ta fara daukan guguru guda tana kokarin kaiwa ga bakin ta,
Cikin wani irin daka tsawa uban yai wa Esther, magana har sai,da ta dan kadu,
Cikin dan turo baki tace me, i wan eater woo,
Tadauka takai ga bakin ta inda shima Yusuf, din yadan gutsura ya kai abakin shi ,
Samuel wanda ke gefe shima ya jawo nashi rabon a gaban uban suke ta cin abinsu suna hira hankali kwance,
Yusuf ya umurci kaunar shi da ta sam ma yan aikin su don suma su sheda,
Mr EMA wanda ke zaune murtun da fuska ya rike sandan shi ta sarautan su na IBO
Yace wa Yusuf yasan da cewa zai auri yar kabilad IBO nan bada dadewa ba,
Murmushi Yusuf yayi yace indai, musulmace may zai hana ya aure ta,
Amma idan ba musulma bace ba zai yi ba,
Duk mamaki maganar shi tabasu taya zai ce zai kara aure bayan yayi aure soon,
Amma rashin sani yasa su daukan cewa kila don dan uwan nasu yana musulmi ne,
Yadan dauki lokaci kadan ya bar gidan inda ya wuce ya kaiwa Abdulsamada nashi tare da Naimat,
Wace ke fama da laruran ciki a lokacin kamar za ta mutu,
Daga gidan ya wuce gidan Anty dije wace,kusan tun jiya baije ba,
Inko ba wanan dalilin ba ya za,a yi har ya kwana bai zo gidan na Anty shi ba,
A kofan shiga gidan yadan tsaya sai da yai gyara murya,tun daga nesa
Sanan ya kwada sallama kamar wani bako,
Jin muryan shi yana sallama a kofan gida yau,
Mamaki ya kama anty dije wace ke zaune tare da uwale suna ,zance akan auren,
Da sauri anty tamike cikin mamaki ta leka har kofan inda yake tsaye,
Bakin shi yana rawa yace, Anty ina wuni, ya gida da yara,?
Ikon Allah inji Anty Dije din,
Cikin mamaki tace Yusuf yau kuma a,waje zamu gaisa haka dakai,?
Murmushi yayi yadan sosa kai, nadauka ko akwai mutane ne acikin gidan,
Cikin girmamawa ya dan rusunna kasa ya ce,Ina wuni Anty ?
Ya gajiyan jama,a ?
Wanan karon bata tsaya ba juyawa tayi zuwa cikin gida tace,
Alhamdullahi shigo don Allah ba kowa uwale ce sai yaran ka,
Wanan ranan abinda Yusuf yai mata yabata mamaki don koma mata yayi tankar wani bako, a gidan,
Sun kusa kai wani lokaci a zaune Anty Dije da uwale suna kara bashi magana,
Ya mike cikin jin nauyi yana masu sallama,da niyar wucewa,
Ita ma Anty mikewa tayi a lokacin tana cewa Yusuf may yasa ka hana baba ya kaiwa maryam din kayan daki,
Bakin shi yana rawan bada ansa yace, Anty aiko bani maryam ta aura ba, zan iya yi mata komai daya dace,
Don Allah baba yayi hakkuri pls, ba wai na raina bane,
Duk ka duka kwana nawa zamuyi a garin kinga ke nan kayan ya zama, barnan kudi,
Anty tai murmushi ta gyada kai alaman hakane,
Har zai fita sai kuma yadan ja ya tsaya yace Anty don Allah ki ba wa baba hakkuri,
Akan zancen lefen maryam din sai na,koma Abuja sanan zan sa a hada mata komai kamar yadda ya dace,,
Yusuf , inji anty maryam tace wanan zance ai yanzu ba namu bane
Mafanar kace kai da matar ka don ita keda abin ta,
Yadda duk kukayi a tsakanin ku ya wadatar da mu don haka mu nan babu ruwan mu,
Godiya yai mata yai mata sallama akan ,ai tafi ,
Hanyar shi takomawa gidane ya tsaya ya siyo masu fruit's kala kala
Gidan yai shiru kamar babu kowa aciki baka jin komai a lokacin sai karan na,urorin dake falon,
Sallama yayi tun daga bakin kofan yadan tsaya kamar wanda ke jiran iso
Daga kofan falon ya cire takalman shi inda ya dan tsaya daga shi sai sock's a kafan,
Sai faman baza ido ya ke yi ko zai ga maryam a falon,
Sai dai Maryam din bata falon a lokacin,
Son ganin maryam din ya keyi a lokacin faren manyan idon ta yake son yin arba da su,,
Safiya ce tafi daga cikin kitchen din dauke da wani dan roba, a hannun ta,
Sannun da zuwa tai mai gami da karban ledan da ya shigo dashi gidan ga hannun shi,
Saida ta aje ledan sanan ta danyi wa maryam din flashing ga,waya,
Maryam din tafito saye cikin wani dogon riga na shadda, dark pink,
Tasa wani mayafi mai fari, shara shara a saman rigar na ta,
Fuskan ta yasha gyara kamar wace zata gurin buki a lokacin,
Takalmin kafan ta hill shoes fari ne mai fari sol so sai din nan
Tasa wani abin hannu fari mai farin sarka a wuyan ta,
Maryam tayi kyau sosai da wanan kwalliyan , a hankali take takowa daga corido din zuwa inda yake,
Har ta iso gaban Yusuf bai iya magana ba sai ajiyan zuciya da yake ta faman saki,a hankali,
Gefen kujerar da yake zaune maryam din tadan zauna gami da yi masa sannu da zuwa,
Shakan kamshin maryam din yayi nan take yaji wani irin natsuwa da bai taba ji ba ya zo mai,
Safiya wace ke gidan a lokacin itace ta tajawa Yusuf burki a kan irin yadda yake jin maryam din, a lokacin,
Safiya ce tafito daga cikkn uwar dakin sagale da jakar ta tasa hijab din ta,
Maryam cikin muryan nan nata mai kama da ta rowa tace wa safiya din,
Ke kuma ina zaki kuma, ?
Safiya wace ke ta kokarin gyara hijabin ta tace au so kike dama in kwana nan,
Ina na gyara maki ko ina yadda ya kamata to may kuma,zan tsaya jira, again,
Haba Yusuf wanda wani irin farin ciki ya ziyarci zuciyar shi a lokacin
Kamar wanda akabawa sabon rai a ranan, sai cewa yayi
Safiya har zaki koma ke nan tun yanzu ?
Barin sa driver yazo ya kai ki ko ?
Safiya tace ai da ka barshi kawai zan hau mashin,
Maryam wace tasan kwana. Zancen hawa mashin din,
Yace no, no no bari kawai yazo ya kai ki dama wanan zuwan nazo da security da yawa,
Bai fi minti biyu ba sai ga wani yana sallama a waje haka maryam naji tana gani safiya ta wuce ta bar ta da sunan zata dawo gobe,
Yusuf wanda yana ganin tafiyan Safiya din sai yayi tsaye yana kallon maryam
Wace ke zaune tana wasa da yatsun hannun ta ta harde hannayen ta wani cikin wani, a lokacin,
Kunyan Yusuf ya hanata motsawa daga inda take zaune,
Batai aune ba sai ganin Yusuf din tayi kusa da ita zaune,
Wani irin shu,umin murmushi yake sake mata
Cikin wata irin murya yace maryam tawa zo mu shiga daga ciki ko ?
Jukin maryam din ne yai sanyi, ji tayi duk wani irin kasala ya lullube ta,
Tunanen abinda ya faru a tsakanin su daren jiya ya fado mata a rai, a hankali ta dan lumshe idon ta zuciyar ta ya shiga rawa,
Tunanen ya zo mata wai yau ita maryam ce tare da Yusuf a matsayin mijin ta
Muryan Yusuf taji yana cewa wai har yanzu maryam bazaki daina wanan damuwar ba,
Ki sake ranki da ni maryam ki daina wahal min da zuciyar ki, hakanan,
Hannu ya mika mata alamar tazo gare shi maryam wace a yanzu bata da zabi sai hakan ta dan mike a hankali zuwa gare shi,
A hankali ta tako zuwa gare shi inda ya riko hannun ta ya ka mata zuwa jikin shi
Rugumay ta yayi tsam yana mai sauke numfashi gudada ,
Sai kuma yadan dago ta yana kallon ta duk yadda yaso su hada ido dashi maryam ta kasa,
Wani irin kallo yake mata shi dai a duniya kallon maryam bai isan shi ,
Komai nata sha,awa yake ba shu tun tana karaman ta,
Daban yake kallon maryam din da sauran mata,,,,,,,,
ZEEE MAKAWA YELWA
[5/4, 7:09 AM] βͺ+234 703 055 6607β¬: πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
FUREN JUJI
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
9β£0β£
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI
KUNA MATUKAR SANI NISHADI DA JIN CIKAKKEN KARFIN GWUIWA YAN UWA , HAKIKA DOLE IN JINJINA MAKU GAMIDA GODIYA A GAREKU DIMBIM MASOYA NA NA ASALI,
NAGODE NAGODE NAGODE KWARAI ALLAH YA BAR ZUMUNCI YAN UWA,,,,,,ππππππππππ
Kwanan su biyu a kwantagora yan uwa da abokan arziki suna zuwa taya su murnan aure
Inda wasu ke cin su taran rashin fada masu da ba,ayi ba sai dai kawai suji labari,
Kafin wani lokaci har labari ya karade gari mutane na cewa wai don kwadayi mahaifin maryam ya daura wa diyar shi aure da dan IBO tubabbe
Wasu ma cewa suke yi da dan arne yai wa yar shi aure don kwadayin duniya,
Wanan irin maganar yakai har zuwa kauyen da mahaifiyar maryam din ke aure,
A,gidan buki wasu mata ke hiracewa yanzu ai duniya ta lalace ace mutun dan musulmai jikin musulmai don kwadai ya dauki yar shi yabawa dan kafirai, saboda kwadayin duniya,
Aje a haifa wa mutun jikokin arna suzo daga karshe su addabi mutane da kafirci,
Mahaiyar maryam wace,ke zaune tana sauraren su,
Rayuwan ta ya baci a lokacin amma sai ta daure tankar bata san da su mutanen suke ba,
Kishiyar tace ma taba da ansa da cewa ai musulmi duk musulmi ne,
Shima bahaushe ai yare ne, don ba balarabe bane ai ko?
Saboda ai larabawa sune tushen musulunci amma basu kyaman auren musulmi dan uwan su ko wani irin yare ne shi,
Bayan sun dawo gidane abin yadamay ta don haka tafadawa maigidan ta duk yadda sukayi da mutanen,
Wayan shi ta ara ya kira mata maryam din wace a lokacin tana zaune tana gyaran fruit,
Ganin nomban mijin mahaifiyar tane yasa ta saurin daukan wayan,
Cikin ladabi ta gaishe shi ya tambayi lafiyan ta tare da dan mata nasiha akan zaman aure,
Ya mikawa mahaifiyar nata, inda tadauki wayan tana cewa yar baba ya kuke ya jama,an ku da sauran mutanen
Ya maigidan naki yake, maryam din tana ansa mata da fadin lafiya kalau yake,
Yar baba kiwa Allah ki bi mijin ki sauda kafa , yi nayi bari na bari,
Kada ki bari komai yafito daga gare ki, duk halin da kika gani kiyi hakuri ki kokarta ki magance matsalar,
Maryam wace tun tana cewa tau har takasa magana,sai hawaye dake fitowa daga idon ta,
Nasiha sosai mahaifiyar nata tai mata tare da ja mata kunne akan maganganun mutane,
Da bayan hannun ta take share hawayen dake gangaro mata a fuska,
Daga,bayan ta taji an rungumota duk da tasan kowaye hakan bai hanata dan firgita ba,
Wayan ya karba daga hannun ta ya gaisa da Inna din yai mata godiya inda yake sheda mata cewa zasu shigo gurin ta kafin su wuce,
Maman ta daure tace mai kada su shigo yanzu yabari sai wani karon saboda yanzu ba,a dade da auren ba,
Yai mata sallama inda take ta mai godiya da fatan alheri da gamawa lafiya da duniya,
A hankali ya juyo da fuskanta zuwa gare shi suna fuskantar junan su
Kamar wanda ke rada yake magana, bana son kina bata wanan kyakyawan fuskan naki da hawaye ki daina fitar dasu haka pls,
Yadan kara dago da kanta ya kaleta yace maryam ina fatan muyi rayuwa da Insha Allah ba rabuwa a cikin ta,
So kada zancen mutane ko wasu yan uwanki yatayar maki da hankali,
Hannuwan nashi yasa yana mai goge mata fuska a hankali ,
Wani irin sha,awanta ke fisgan shi a lokacin, don haka a take idon shi ya canza kala, saboda wani irin mugun sha,awan mai sa kasala ke fisgan shi,
Kamar may rada yace mata baki ce min komai ba maryam,
Maryam din cikin wani irin murya wanda ke nuna karayan zuciya saboda tsoron ganin yadda idon Yusuf din ya sauya, alokaci guda,
Tace insha Allah fatana ke nan ,
Fatan ki may maryam ? Yana mai kara matsota a jikun shi,
Tace a hankali Insha Allah nace ba rabuwa ni da kai ,
Matseta yayi sosai a jikin shi kamar za,a kwace mai ita,
Idon shi ya lumshe ya na sakin ajiyar zuciya saboda ko ba komai maganar ta yai mai dadi a rai,
Sai yadan kallo ta yana mai daga kan shi sama yace,
Godiya ya tabbata ga Allah ubangijin talikai, maryam har kullun zanci gaba da godewa Allah subbahanahu wata,ala
A kan baiwar da yai min na mallakar mace kamar ki kamila,wace tasan may nene Allah da manzon sa suka ce,
Kiran sallah magrib da aka fara yi shi yadakatar da shi inda yadan jaye ta kadan daga jikun shi yana mai lumshe ido,
Bayan shi maryam tabi da kallo bayan gitan shi daga kitchen din,
Tana mai ajiyar zuciya a filli,
Wanan ne karo na farko tun bayan daura auren su da taji wani abu gamay da Yusuf din,
Zaman kwana biyun da sukayi a gida guda yasa har ta dan fahinci kowaye Yusuf din,
Shi mutum ne mai saukin kai ga kokarin ba natare da shi hakkin shi,
Duk da dai sabon aure sukayi amma tadan fahinci yan abubuwa adangance da shi din,
Itama gudun kada ta makara ta mike ta fada daki ,
Har ta idar da sallah ta zauna tana lazimi a gurin tare da yin tasbihi,
Batabar gurin ba har Yusuf din yashigo yana dauke da basket din abinci da aka kawo daga gidan anty dije,
Maryam din ce tamike tare da bin shawaran safiyan ta,
Saman dining taka kulolin inda tai mai bissimillah cikin jin kunya da nauyi,
Bawani abinci suka ci ba,sosai sun dai dan taba kadan,
Wayan shi tai kara inda ta fahinci cewa da ma,aikatar su ne yaje waya,
Mikewa maryam din tayi tsam tafara kwashe kayan da sukaci abincin zuwa kitchen,
wanka ta fa da Inda tadan bata lokaci gurin gyaran jikin ta cikin bathroom din,
Tana,zaune tana shafa mai da turare, dan gyara jikin irin ta mata taji motsin, shigowan Yusuf din,
Bai wani bata lokaci ba,shima wankan ya shiga don kamar har yafi maryam din tsabta, ma,
Daure yake da bathrobe a jikin shi yana kokarin goge ruwan jikin shi da dan karamin towel,,
Yar jakar kayan da yazo da ita garin ya bude inda ya fito da kayan kamshin shi yakara gyara jikin shi tsab,
Ta mirrow suka hada ido dashi ya wani dan kashe mata ido guda,
Hakan yasa tai saurin dukar da fuskan ta a kasa
Murmushi yayi kawai yaci gaba da,yin abinda yake yi,
Batai aune ba taji muryan shi gab da ita yana cewa yau ina,son in cire wanan mugun kunyar da ake min wayo da,shi,
Murmushi maryam tayi kasa,kasa saboda maganar da ya yi yana kallon yadda take wani takuran kan ta guri guda,