Showing 69001 words to 72000 words out of 255288 words

Chapter 24 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1369

yabasu amsar cewa shi yabar su ke nan har abada
Bazai kara dawowa cikin banyar bata ba saidai ya mutu a hakan,
Girman da yaran shi suka farayi ne yadan rage mai wahalar don suna zuwa yin dako a bakin kasuwa sukawo dan abin da suka samu ayini asarrafa,
Ko shi Ibrahim saida bukin KB da akayi ne yasan cewa suna da alaka da Joseph,,
Lokacin da yaga irin yadda Joseph ke yi agurin yazo yana fadawa mahaifinshi cewa baisan cewa IBO bane saida yaji yana yare acikin waya,
Abdulsamad yai dariya inda yakewa diyan shi bayanin ko ya suke da Joseph,
Nan ne ibrahim yace zai je gurin shi ya ziyar ce shi yagani ko za,a samu wani cigaba anan,
Maihaifin na Ibrahim baiki ba don yasan kowaye Joseph zai iya taimama wa ibrahim din,
Sai ko gsshi cikin ikon Allah ibrahim din yazo cikin kamata alheri don bai taba zaton cewa yaron zai can za cikin dan lokaci guda haka ba,
Ga sakon kudi har dubu hamsin anbashi yakawo wa mahaifin shi tare da tsaraba,
Kwanan shi biyu da zuwa inda yakoma shedawa Anty Dije zai koma,
Sako tabayar akai ma Joseph din wani robber da akai sild din shi
Sai kuma kilishi cikin envelop, mai yawa cikin wani babban leda tace Ibrahim yakai wa Joseph,

Bakaramin mamaki Joseph yayi ba lokacin da Ibrahim yagabatar mai da sokon da Anty Dije ta aiko mai dasu,
Dambun nama ne cike a roban sai kuma kilishi mai yawa,
Daga kilishin har Danbun Joseph yarasa wani yafi dadi daga ciki,
Sai mamaki yakeyi yana kada kai cikin jin nauyi, kamar a gaban anty din yake,
Shi yana gani kamar ta ksshe kudin da yakai dubu dari akan wanan abin,
Bai daga daga gurin ba sai da ya kira ta acikin waya yana mata godiya daga karshe ma yarasa may zai ce mata,
Mamaki kwarai anty tayi don jin yadda yake zabga mata godiya akan dan abinda baikai yakawo ba,
Shida ta lodo mata tsaraba har saida ta ba makwabta da kuma gidajen su ita da mijin ta,
Amma,shi gashi ko dubu ashirin bata kashe mai ba yata zabga godiya,
Shin shi Joseph din nan wani irin zuciya gare shi ne wai gashi da bawai, yasan kaidar zumunci ba ne a ddini,
Amma yarike ta tam kamar wata yar uwar sa ta ji,
Ita dai fatan ta dai,akullun Allah ya kebo Joseph, yadawo cikin Islam's,
A hankali Joseph ya maida tsarabar anty wani abincin shi na daban koda yaushe yana amfani da abinshi kadan kadan,

Wani irin gurnani take yi wanda har a fili zaka iya jin yadda takeyi wanan karar,
Joseph dake shirin hawa sama yagama kallon national news, a TVC,
Da sauri yai hanyar dakin na maman choima wace ke faman wani irin Gumza takar ana shirin yankar ta,
Da karfi Joseph da Ejoma ke kokarim daga ta daga kwanciyar da tayi tana fidda wanan sautin,
Cikin wani irin kara tabude idon ta tana mai cewa Joseph's da karfi,
Firgigit take kallon su da sauri ta rugumo Joseph din daga jikin ta,,
Sai kuma ta fashe dawani irin kuka tana magana maiban tausayi, cikin kuka,
Tana mai cewa,Joseph they want to carry u away from us,woooo,
Joseph da ya rungumo tsohuwar zuwa cikin jikin shi, yace mata sowaye,
Cikin kuka tace bata san su ba amma tana yawan gani su,,a tare dashi acikin su,, koyaushe,
Sai yaune babban su ya ce har da ita zai wuce in,har tana rike shi,
Shine wanan gumzar da take tayi cikin barcin ta da ihun da take ta kwasa yanzu,
Joseph yadan tallabo kan kakar tashi, zuwa jikin shi yana mai lalashin ta
Tunda yaga cewa tadan kwantar da hankalinta yasamu ya sata kwantawa don ko zata samu barci,
Yamike zuwa dakin shi jiki a sanyaye, zuciyar fam da tunane kala kala,
Ashe haka wanan yar tsohuwar ke wahala idan tace mai tayi wanan mafarkin,,
Hankali shi yatashi matuka yana tunanen may ke shirin samun shine haka,
Washegari, tunda safe Joseph yabar gida zuwa gidan wani babban pastor da ke zaune a cikin Lagos,
Saidai bayan bayanin da Joseph yai mai sai ya umarci da azo mai da wnan tsohuwae wurin shi
Joseph yakoma yazo da maman choima acikin shirinta na irin manyan matan IBO,
Pasto ya riko hannun mama zuwa yan wasu lokota,
Can sai ya sake yadan daga kai yana mai kallon Joseph wanda ke zaune gefen su saman wata far kujera, yana mai rike habar shi da hannu guda yana dan shafa, gemun shi,
Idon da pastor yadan tsura mai baisa Joseph ya canza daga yadda yake zaune ba tun farko,
Pastor yadan kada kan shi yai yar gyarar murya wanda yasa duk suka kura mai ido,
Don jin irin bayanin da zai masu gamay da mafarkin da takeyi,
Mama inji pastor kada ki damu wanwn bawani abin damuwa bane danki zai zama wani abu ne nan gaba shiyasa kike ganin wan nan abin,
Amma,zai bata holy water wanda zata dinga wanke fuskan ta dashi har zuwa sati,
Idan ta kara wanan mafarki sai su dawo, duk kan su,
Sukai godiya Joseph ya kawo kudi yabawa pastor pastor yaka da kan shi alamar aa ba,zai karba ba,
Yace we are just send to help, the, neediest,
Yai masu addu,a a baki dayan su inda sukai sallama dashi zuwa gida,
Tun,daga wanan ranan maman choima ta fara amfani da ruwan holy water, kamar yadda pastor ya umurce ta tayi,

Shiri yakeyi sosai saboda tunda safe yake son takama hanya zuwa kano don dibo wasu kaya da wani tsoho yai mashi tallan kayan company,
Duk shirin da,Joseph keyi hankalin shi na gurin kakar shi wacce ta nuna batason zuwan shi garin kano sam,
Saida ya gama,shirin tsab ya sauko cikin shigar kananin kaya,
Kayan ya karbe shi sosai don ya fitar mai da surar shi tsab,
Karfafan namiji mai duk wani siffa mai nuna karfi daga jikin da namiji
Saidai Joseph ba mutum bane mai son magana don haka ko murmushi da wuya kaga yayi ta, kasafai,
Guda guda yake tako hannu shi guda na acikin ajihun wandon shi guda kuma yana dauke da yar briefcase din shi,
Direct saman kujerar da maman choima take zaune ya nufa inda shima yazauna gefen hannun kujerar,
Yadan langabo kanshi zuwa saman kan maman Choima din,
Mama ,I, gona miss u, wooo,
Kamar yadda yasaba fada mata duk lokacin da zaiyi tafiya mai yar nisa, dasu,
Cikin muryan da tanu cewa ta manyanta tafara magana,kamar haka,
My child , god dey with u,for D whole time , u go spend there,,,
Ejoma dake gefe ta amsa da fadin Ameen,,
Joseph yamike tsaye yana dan gyara, wandon shi, tare da yi masu sallama,
Motar da zaitafi da ita Ibrahim ke ta faman gogewa da kakabewa,
Nan sukayi sallama da ibrahim din yabashi dan kudin da zai yi amfani dasu kafin yadawo,
Adduan dayaron ke mai kullun tasashi jin dadin rayuwar shi aduk lokacin da uai mai ita,
Ahankali ya furtawa ibrahim din da Ameen, tnxs brother,
Yaja motar shi yai gaba yanama Ibrahim horn alamar bye,bye,

Abamu na Allah da Annabi,
A taimaki almajara sadaka saboda Allah,
A,wani gidan mai daidai shiga garin kano, wasu almajirai ne suka baibaiye wata mota, da wani matashi acikin wani yaddi mai ruwa toka,
Da sauri saurin ya ja glass din motar,shi sama saboda gudun kada su damay shi,
A daidai lokacin Joseph ya parker tashi motar kusa da ta saurayin,
Daga cikin motar shi yakewa saurayin kallon mamaki,
Wata yar jagora wani tsohon makaho da, ta kurawa Joseph ido tun lokacin da ya tsayar da motar shi,
Da kai yai mata alamar tazo ba bata lokaci tasake sandan dan tsohon makahon da take ja zuwa inda Joseph din yake,
Dan Allah ki karbi wanan duk almajirin dake gurin nan ki bashi sadaka,
Kafin yakara sa mika mata sai gawani dan dukaken mutum mai yar wani doro abaya ya iso gurin cikin sauri,
Ataimaka ma almajiri da sadaka Alhaji,
Malam haru, gashi yabamu yace duk wanda ke gurin abashi saboda Allah,
Kafin minti biyu duk sun baibaye motar Joseph Alhaji yadda kai muna Allah yai maka
Allah yasa agama da duniya lafiya,
Wata yar tsohuwa da aka jawo duke a nanade cikin wani keken, turawa,
Tace, Allah ya tsare Allah yabada sa,a Allah Allah yasa afi,haka arayuwa,
Daidai lokacin mai zuba mai a motar ya gama zuba mai man da ake zubawa,
Yaciro kudin shi ya mika mai, ji yayi ana gardama bada yaran almanirai masu bara ba,
Yakara yafutu yaron dake tsaye cikin yagagun kaya gaban rigar a bude, robar baran shi duk tayi dauda
Ya,mika mai kudi, sukai dubu biyar yace su raba aikuwa nan guri kaure da suratai,
Shika har ya harba motar shi zuwa cikin gari don yasamu ya isa inda akai mai masaukin kwana,
Kafin gobe, su tafi tsohuwar maikatar su diba abinda suke so aciki, su saya,
Alhaji sabo, wani tsohon mai kudine wanda yasamu kariyar arziki
Yanzu baida komai sai sayar da yan kaddarorin dake gare shi, yake akai kai don ya samu dan abinda, suka ci shi da iyalin shi,
Yakira abokan sanar ashi sukai mutun biyar don su sai waban injin din amma sai suyi mai tayin tsiya ta yadda zai fadi warwas,
Shine wani yaron shi na da dake lagos yai ma su Joseph talla ko za,su saye, suyi amfani da shi,
Tun,cikin dare, da ya shigo Alhaji sabo ya zo har masaukin shi don su gana saboda in har yakai gobe
Mahassadan shi na ita bata zancen su soke al,amari don ganin cewa bai farfado ba ko kadan,
Bayan sun gaisa Alhaji Sabo yafadawa Joseph irin halin da yake ciki da kuma yadda makiyan shi suka sashi agaba don kada ya farfado,
Joseph yai nazarin wanan bawan Allah sosai har yaji yana son ya tallafa mai,
Dama da Sonny ne zasu sai wanan kayan suyi masana,an ta dashi can,Lagos din,
Don haka sai yaba Alhaji sabo shawaran cewa, may zai hana ya canza sana,a yagani,
Amma yabashi shawara ya tafi yai nazari akai, duk abin da ya gani yafada mai
Kamar masu jira aiko tunda suka ga su Joseph tare da jibrin da KB dasuka iso kano aranan suka samay shi
Sai aka fara zuwa gaisawa da su tamkar an san inda suka fito,
Daganan aka fara tambayar ko daga wani gari suke,
Wata irin masanan ta zasu yi ai ko yakamata sukira wa, yanda suka san kan injin su diba masu don gaskiya injin din ya dade, da, lalace,
Tun nan Joseph yagane cewa agent, din mahassadan Alhaji Sabone,
Ganin irin body guard din dake biye da Joseph da mutanen shi gashi kuma suna ta son yin suka amma ba fuska,
Bayan sun gama dibawa Joseph yasa adibo mai enginers masu aikin kwarai daga lagos zasu biyu jirgi, su zo
Su di mai kyau engine din idan baiyi mugun baci ba,
Bayan Joseph yakoma masaukin shine yake ba su jibrin labarin hiran shi da Alhaji sabo,
Gashi kuma sunga zahiri duk da bawai sun bada fuska ba a gun mutanen,
Bayan ma,aikatar sunzo sun diba engine din sai suka tabbatar da cewa dan gyaran da za,ai mai kadan ne don komai nashi lafiya lau yae
Kuma na,da ne mai kyau yanzu ba,a samun irin, shi so sai,
Tausayin wanan bawan Allah Joseph yaji sosai sai yaga yakamata yai mai hanya,
Shikuma Alhaji Sabo kamar yasan cewa Joseph na wani planing akan shi,
Sai gashi ya gaiyaci Joseph har gidan shi gurin iyalin shi,
Gidan ba, laifi baba ne amma, dai da alamar porvaty, aciki,
Amma akwai addini, ga ladabi da sanin ya kamata atare da su,
Wani dan karamin yaro a gidan yazo da sauri yadinga fito da butoci yana direwa agaban mutane,
A, gaban Joseph yadire wani butan silver mai ruwan gold,
Har zai wuce sai Joseph yajawo shi zuwa jikin shi yana tambayar shi sunan shi,
Amma sai ya ce wa Joseph, barin muyi sallah kada mu makara sai in fada ma,
Joseph yasake yaron yana mamaki yadda yara kanana suke iya akidar addini tun suna yara,
Shin wai duk haka musullumai sukewa yaran sune tun suna kanana ko kuwa,,
Murayan dan yaron ya katse Joseph din yana cewa uncle kayi alawala, kada mu makara mu tsaya baya kaji, ba kyau,,
Joseph yai murmushi yace kayi kawai zan biyo ka a baya ina jiran wani ne,
Sai yaji wani irin nauyi da kunyar hakan
Tunda yake baitaba jin nauyi ba sai yau, dan karamin yaro na sa shi ahanya,
Kafin su fito daga sallah Joseph yabar gidan, cikin yar damuwa,
A can masaukin shi yana isa ya jefar da top din shi a saman kujerar dake dakin
Gurin fridge yanufa yadauko goran ruwa ya ballemarfi ya kafa a abakin, shi sai roban duk ya kwakwade ruwan, cikin roba,
Ya wurgat da roban can gefe guda saman gado yafada jagab,
Sai kuma yakai kwance tabayan shi yana mai lunshe idon shi kamar mai barci,
Ringing din wayar shi tasa shi bude idon shi, dake lunshe kusan yan mintina,
A, cikin sauri yajawo wayar don kada kiran ya katse
Nobar anty Dije ce ke kiranshi,bayan sun gaisa,dashine take sheda,mai cewa Asalam ne ke magana dashi,
Yana karban wayan sai ce mai yaron yayi, uncle wai bazakazo gurin walimar saular su little mummy ba,
Da farko baigane may yaron ke nufi ba, saidaga baya,
Ya,fahinta da abin dayaron ke nufi, Anty Dije ce takarbi wayan take mai baya yadda akayi,
Wai cewa yai Joseph din zaizo sai kace i, bazai zo ba,
Tana fadin hakan kawai sai yagane cewa akwai abin da akace wa yaron agamay dashi,,,,,


ZEEE MAKAWA
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
3⃣0⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA,,,

Duk, abinda ya kamata Joseph yayi ya aiwatar a kano, Don haka sai yai shirin komawa gida,
A cikin dare, Sonny ya bugo mai waya cewa ya fi bukatar su aje wanan engine din a garin Abuja,
Aboda haka yanzu dole Abuja Joseph zai ratse don neman gurin da zasu yi wanan aikin,
Dashi da Jibrin ne ke ta faman yawon neman guri, inda ya kamata,
Wani sabon side ne suka samu a NYanya, acan zasu yi wanan masana,antar,
Tun da aja fara wanan aikin sau guda Joseph ya dan zo Lagos yaga su mama,
Sam yafita duk wani zancen zuwa kwantagora yanzu saboda baida lokacin hakan bukatar shi kawai ya ga wanan masa,nantar yasamu kafuwa kamar yadda suke so,

Ma,aikatar dake aikin gurin yau ma kamar kullun su halarra sun fara aiyukan su,
Kwasam sai suka dinga jin wani irin ihu na tashi tankar mace na ihu tana neman taimako,
Wasa wasa sai jin ihun sukeyi yana karuwa kafin kamar a inda suke, aiki karan ke, fitowa, sai gani sukayi wani irin iska mai karffi yana kada ganye da ciyawon dake gurin,
Mutun daya daga cikin su yafara yar da abin digar da ke a hannun shi,
Ya,arta ana,kare, ganin haka sauran ma,aikatar gurin suka fara, arcewa, kowa sai kwasan gudu yakeyi ba mai tsayawa jiran wani,
Suna ji suna gani gurin ya gagare su aiki dole suka bido nobar jibrin wanda alokacin shima yana shirin zuwa diba su,
Dariya ya fara yi lokacin da suke fada mzi yana ta faman kyalkyalar dariya
Yana isowa ya shima yaji wanan sautin tun daga ne sa aiba girama,ba, arziki ya fada motar shi sai maida nunfashi guda guda yake yi,
Sai da yatabbatar yabar unguwar ya dauko wayar shi ya buga ma Joseph,
Kwance yake daga shi sai rigar barcin shi dark blue yana saye da wani dan gajeren wando,
Kwance yake tare da Aisha ya rungumay ta, a cikin jikin shi sai kwasan barcin su sukeyi,Aishan, wacce ta shigo jiya da,dare,
Dukkan su suna tare da gani kowan su nada gajiya atare da shi,
Karar wayan da Jibrin shi da KB suke ta bugo mai a jere da juna yasa Joseph a hankali bude idon shi
Hannun shi yamika saman side drower din shi inda wayar shi ke ta faman tsuwa,
Saida yai yar tsuki alamar jin haushi kiran a wanan lokacin,
A,llo, yace cikin lumsherwar ido, idon shi wanda ke cike tab da barci, alokacin,
Cikin tashin hankali Jibrin ke magana man an samu matsala fa,
Kai Jibrin wanan kira haka tun da safe, haba,haba kasan fa ina son hutu,
Kai Baba anfa samu matsala sosai nake fada ma,
New side

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login