Showing 18001 words to 21000 words out of 255288 words
ta ba, gurin shi,,,
Mota ya bayar aka,dawo da ita har kwantagora, tare da kaya da ya saya mata, niki niki, ,,,
Wa,iyazu billah yar musulumai zamani ke nan babu ruwan da dataraiya da kowani irin mutum ita dai kawai ta samu kudi shine gurin ta,
Yadda ta canza kawai yasa Amina gane cewa gurin Joseph ta tafi,
Cike da mamakinta take kallon ta don ganin irin abinda take fitar wa,
Cikin dan rada take, cewa Aisha mutumiyar har kin fara bani tsoro wallahi don kin wuce sani na,
Tana kokarin jera, kayan makeup din ta a mirrow dakinta ne tai yar dariya, tace da nai may fa,?
Haba haba inji Amina Aisha ace har kuma Royce din mu ya wuce ga hausawa musulumai yan uwan mu ya koma ga Christian, haba dai haba gaskiya hakan baiyi ba,
Wani irin kallo ta watso ma Amina daidai lokacin da ta bude akwantin da tashigo dashi,
Kayan da Amina tagani ciki fam shi yasa ta kara zare ido waje,
Tace, shin Aisha kina nufin ,,,,,, nuna kayan tayi da dan yatsanta don tama kasa furta ko a,
Kwarai kuwa inji Aisha tana mai gyada ma Amina kai, tace
Uban wa zai bani wanan koda kuwa sau nawa ina bin mutum motar shi ko wani mafaka
Amma kinga wanan tana nuna kayan da hannun ta tace a free wallahi na,samay su Amina,,,,
Ido waje Aminat ke kallonta cikin mamaki tace a free fa ?
tace wallahi ko,
Amma dai gaskiya mutane ba zasu gane cewa babu wani alaka atsakanin ku mai zurfi,
Ina ruwana da mutane inji, Aisha, duk abinda zasu fada suyi ta fada mana,
Manja da doyan da Irish da, tazo dashi ta dibar ma Amina mai yawa,
Ita dai Amina sai mamakin kawar nata takeyi kawai,
Ace yanzu har da arna suke mu,amula, kai gaskiya Aisha tayi nisa wallahi,,,
Don haka, taja bakinta tai shiru kawai batare da tafadawa kowa,ba ita dai tasan cewa duniya ce zata fada ,,,,,
Tsaye yake yana waya da kanin shi, Samuel wanda ke zaune tare da baban su a kwantagora inda Samuel ke fada ma Joseph meeting din da elders sukayi a kan shi,
Yai mamaki matuka da jin zancen Samuel din don yasan cewa yana ikar kokarin shigurin ganin cewa ya kyautata wa Church din na su,
Badon komai ba saidon kawai ya kare martaban gidan su daga alumar su,
Cike da mamaki yasake tambayar Samuel labarin mahaifin su,
Dan shiru Samuel din yayi kadan kafin can,yace yana nan saidai gaskiya maganar tadan tayar mai da hankali,shi,
Kai kawai ya girgiza yana mai shafan fusakan shi in akwai abinda ya tsana yanzu shine yaga bacin ran mahaifin shi,,
Sallama yayi wa Samuel din yana mai jin haushi elders din na su, akan jefa mai mahaifi cikin damuwa,
Shin ina ma ruwan su dashi dazasu sa mai ido a harkokin shi,
Yasan cewa koda ya kira mahaifin shi ba wani maganar da zai ji a gamay da elders din,
A karshe ma yana iya ganin laifin Samuel da ya fada mai, zancen,
Tun yana tuna zancen har ya share maganar, gurin fridge ya nufa yadauko goran ruwa, ya tutula ma cikin shi,har saida ya zuke gora guda gaba daya ya wurgat da rubo, a dustbin,
Kiran wani Michael ne ya shigo mai a lokacin inda yake sheda mai cewa yason su hadu saboda maganar man Gas dayake son suyi a lokacin,
Michael mutum ne mai iyali shi duk da bawani babban mutum bane sosai,
Yasamu Michael da yaran shi suna wasan basketball, agidan shi
Yaran naganin shi sukayo wajen shida gudu suna mai oyoyo,
Rungumay su yai cikin jikin shi ya na dan shafa masu kumatun su,
Sun san zuwan shi gidan su alherine don haka ledar Sweet din da ya riko masu ya mika masu,
Murna da ihu suka hau yi suka shige cikin gidanan su binsu yayi da kallo
Nan take alkawarin da yaiwa Assalam ya fado mai arai,
Don yasan cewa yaro baya man,ta alkawari duk lokacin da yaga wanda yai mai alkawari bai cika ba sai ya tuna,,
Don haka ya kudurta a ranshi cewa da yabar gidan mic zai wuce yaiwa Assalam sayayan shi ne,,,,,,
ZEEE. MAKAWA
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
9⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
Yau gidan Anty Dije baka jin komai sai kamshin girke, girke ke tashi kala,kala,
Duk wanan kamshin anayin shi a kan maigidan da zaidawo yau daga gurin aikin shi can garin Lagos,
Tun jiya ya bugo masu waya yana mai sheda masu cewa yau zai iso, sanin da sukayi cewa ysna saman hanya,
Yasa su wanan girke girke da kara gyara gida duk da dai gidan nasu ko yau she fes yake,bazakace akwai yara agidan ba,
Bayan sun kammala aiyuman su ne sun gyara guri sai kuma,suka shiga gyaran jikin su,
Duk da zaman Iliyasu ma,aikacin custom ne hakan bai sa ya wadatar da matar shi da komai ba,
Don dai da ka ganta kasan cewa zaman hakkuri takeyi kawai, don babu wani kama na nuna wadata atare da ita,
Allah yasa mata hakkuri da dauri sosai don sam baka taba gane halin da take ciki,
Cikin wanan halin hakkurin da takeyi bai hana yan uwan mijin ta,sata gaba ba da fitina
Don su gani sukeyi ai duk wani bida na Iliyasu yana gurin Anty Dije da yan uwanta,
Idan suna wanan zancen bata bata ranta saidai tayi murmushi kawai,
Don takan ji dafin rashin gane sirinta da basuyi ba har suke ganin cewa komai na hannunta,
Basu san cewa dan uwan su ne mai laifi ba,
Harkokin shi kawai yake yi a can bariki abin shi,
Maryan zaune tana kwalliya a gaban madubi da ke kuryan dakin anty Dije
Wanda har in tana son yin kwalliya mai tsayi dole sai ta shiga har kuryan dakin na anty Dije,
Sauri take yi ta tafi karbo ma anty Dije dinkun nan ta a uguwar Rimaye,
Waje wata yar uwar maman su Anty Dije din don matar ta iya dinkin zamani sosai,
Atamfar code,viore ne mai ruwan makuba da milk, ajikin ta,
Dinkin riga da zani ce tai daurin baya ta kulle shi a tsakiyar baya,
Turaren Anty Dije tadan fesa kadan
, Saida tagama hada komai tadauko dan wani karamin hijabin ta, ta sa sai takalman Bella, da tasa, a kafar ta,
Cikin yar muryan nan nata take sallamar Anty Dije a hankali don gudun Issalam kada taji ta tace zata bita,
Don ance tayi sauri ta dawo, dawuri saboda kila dasu anty zatayi amfani
A gidan mama Asabe tasa mu bata karasa hada dinkin ba don haka tabukaci mama Asabe ta bugawa Anty Dije ways ta sanar mata cewa da dan saura kadan kafin a karasa,
Tana zaune tana jiran dinkin saiga wata budurwa yar gayu ta shigo gidan
Daganin yadda sukeyi da mama Asabe kasan sun saba sosai,
Inda maryam take zaune budurwar takalla tace ma mama Asabe
Asabe ina kika samo wanan yar budurwan mai kyauwo haka,
Saida mama Asabe tadan kalli gefen da maryan take zaune tana mai ci gaba da dinkinta tace,
Diya tace, tazo karban dinkin su ne
Kanyan anty da ake dinkawa tadan taba sanan ta kai zaune saman kujerar roba fara dake dakin da mama Asaben take dinki a ciki,
Turamay zani tafitar guda biyu masu ba,lain kyau daga cikin bakar ledar da tashigo da shi a hannu,
Kai inji mama Asabe amma dai wanan zanin akwai kyau wallahi kamar su sukayi kan su,
Budurwan tana wani ya mutse fuska tace niko kinga Asabe zanin bai suyi min kyau ba
Kodon bani kawai akayi shiyasa ban ga kyaun shi ba,
Mama tana dinki ta ce kedai yar rainin wayo ce taya za,a baki abu kice kin raina,
Amina halinki sai ke wallahi,
Ai ma, mutum abin arziki irin wanan zukakan zanuwar haka ki ce wai ke basuyi maki ba,
Gyalen da ta yafa ta kwabe, ta koma, daga ita sai wata yar rigar t,shirt ajikin ta,
Ta mike ta bude fridge din mama Asabe ta dauko roban ruwan Goje water tadan fara kwakwada,
Maryam dake zaune gefe tana mamaki da kallon ikon Allah,
A, ranta tace wanan duk cikin wayewa ne haka kuma,
Ka cire hijab a gidan mutane, idan maigidan yafado fa ya zatayi,
Muryan Amina yadawo da ita daga tunanen da takeyi
Amina ke cewa mama Asabe bayan ta gama shan ruwan da tadauko a fridge,
Tsaraban Aisha ne fa Aisha mama Asabe, ta tambaya da mamaki,
Ita fa inji Amina kinsan ta da,kwashe kwashe, wani dan Arne ta samu yake kashe mata kudi haka,
Arne fa inji mama Asabe mai dinki, Amina tace wallahi ke dai,
Niko bayerabe ne musullumi ai ban iya zama da shi balle iyamuri kirsta,
Mama Asabe tace ke ko indai musullumi ne ai ba matsala, tunda Allah bai hana aure a tsakani ba
Amma ace kirsta gaskiya abin baiyi ba,
Amina tai wani irin turo baki tana mai daga kafada da watsar da hannayen ta alamar nuna oho ba ruwan ta,
Mama Asabe tace amma dai Amina nagane zancen ki har da kushi a ciki
Nan gardama ya kaule masu tsakanin ita da mama Asabe
Daidai lokacin da mama tagama hada dinki tana kokarin nikewa tasa a cikin leda ta miko ma maryan, din,
Tamike tana mai ce madu sai anjimar ku, mama tace ku rage min tsarabar Lagos in ankawo maku
Dariya maryam tayi kawai ta ce to mama zan fada mata in naje,
Ganin motar Ya Iliyasu a kofar gida ya tabbatar mata da isowan shi, gari,
Cikin nuna farin ciki da jin dadi ya iso duk daxtasan cewa ba wai wani abu zaizo masu da shi na marmari ba,
Amma dai tana murna Allah yakawo masu shi lafiya
Yana zaune saman kujera rungumay da yaran shi ta shigo dan matsakaicin falon nasu,
Har kasata kai tana mai sannu da zuwa yai yar dariya yace little mummy ance min an aike ki ,
Tai mai anzo lafiya da murnan ta shima a cikin fara,a yake ansa mata,
Iyalin iliyasu sun cewa ko ba komai indai har yana gari suna cikin farin ciki a ko yaushe
Don gidan su yacika da baki masu zuwa da yan bukatun su akai akai,
Kasan cewar zukatan mutane ya mutu yanzu don ba,a maida roko bakin komai ba,
Sai kaga mutum magidanci bai aikin komai sai bin gida,jen masu dan abin hannu ana rokon su, na cefane,
Yau kwansn iliyasu biyu da dawo wagarin don kusan sati guda yake yi idan ya zo garin,
Zaune suke suna hira shida Anty Dije bayan fitan wasu mata yan uwan shi da suka shigo
Wani almajiri ne yai, sallama a kofar gida ya ce ana kiran Assalam wai a waje ,
Daga Anty Dije har mai gidan ta, saida suka kara tambaya cikin mamaki,
Maryan wace ke kitchen tana kokarin gyara kitchen din
Zuwa tayi tadan leka don taga kowaye ya aiko kiran Assalam haka,
Tsaye suke jingine da wata mota mai kamar ruwan kakin soja,
Dan lekawa,tayi kadan daidai yadda basu ganinta tadawo cikin sauri ,
A,kofar shiga falo ta hadu da ya iliyasu, da ke kokarin fita waje don yadiba,
Duk kan su maryam suke kallo don jin ko waye a wajen,
Inda Anty Dije take tsaye ta nufa tace cikin murya kasakasa wanan mutumin ne fa wanda Assalam yake lakewa,
Iliyasu da ke tsaye ke tambayar maryam waye ne a wajen wai,
Murya cikin taushi anty Dije tace wanan abokin jibrin din gidan baba bala dana fadama,
Kasancewa duk wani abu mai muhinmanci sai anty ta fadawa mijn ta don gudun zargi,
Dan shiru yayi can kuma sai yakama hanyar wajen
Basufi minti koda uku ba sai gasu sun shigo cikin gidan duk kan su,
Shi maigidan shi ne gaba, sai su biyu a bayan shi,,
Ya iliyasu nacewa jibrin nadauka ma ko wani bako ne da naga ka tsaya a waje kana cewa wai akira ma Assalam,
Bayan sun zauna a falo ne suka dan taba hira a tsakanin su inda aka gabatar masu da abinci,
Duk da Joseph baiso cin abincin ba am a saida ya illiyasu yasa shi ci
Sannu sanu daga hiran su yafara sake jiki har zuwa lojacin da Assalam suka dawo daga gidan kakan nin su,
Dagudu Assalam ya fada jikin Joseph yana murna,
Batare da yai magana da kowa ba ya mike tsam rike da hannun Assalam zuwa gurin motar shi waje,
Sai a lokacin Ya Illiyasu yake tambayan jibrin ko waye Joseph din,
Nai yai mai kwatance da mahaifin shi da kuma mahaifiyar, shi,
Saidai bai fada mai ko waye Joseph din ba ayanzu
Yadai bashi labarin haduwar su da Assalam har yadda jinin su ya hadu,
Lokaci guda don yace ma ya illiyasu kusan ko yaushe su kayi waya sai yatambaye shi labarin sturbonboy,
Abinda da da mahaifi, duk mai son mutun akace yaso dan shi,
Hakan yasa ya illisu jin dadi har a cikin zuciyar shi,
Ganin su mukayi Assalam da kaya nike nike sun shigo harda keken yara,
Gaba daya muma fito waje muna kallon wanan irin shakuwar
Bayan sun aje kayan ne yaya yagaiyace su cin abin cin dare a gidan shi,
Joseph din yaso ya doje yaki zuwa saboda yana son ya shiga evening services yau,
Amma ba yadda ya iya kawai sai ya amsa gaiyatar yaya din,
Saidai su uku suka zo tare da KB akazo wanan karon,
Abincin hausawa mukayi yau tuwon shinkafa fara da miyar Alaihu da yakuwa, sai yar kabewa da mukasa da busashen kifi,
Mundauka cewa baza suci abincin ba sai gadhi duk an cinye sai kwano kawai,
Duk kan su sunyi mamakin ganin anyi girkin mutanen da a gidan matashi kamar ya iliyasu,
Saboda sanin da sukayi yanzu kiuyya bai bari mata suyi girki mai kama ciki, da dare,
Saidai kawai aima namiji taliya ko indomie da dare ko dafa duka,
Saboda kiuyyuya kawai, don kada a motsa jiki,
Hira sosai sukeyi yan sungama cin abincin kamar sun dade da sabawa da junar su,
Shiko Assalam yana manne a jikin Joseph har yai barci,zuwan wanan lokacin,
Ganin haka ya iliyasu yaba Joseph bakin cewa duk lokacin da yazo kuma yana son ganin Assalam yashigo kawai gurin anty Dije,
Kuma miyar da yace yana so na hausawa yadinga fada mata ai mai, irin da yake so,
Wanan shine silar kara shakuwar yan gidan su Anty Dije da Joseph,
ZEEE MAKAWA
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
1⃣0⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA,
Zaune suke a majalisar su,inda suke hira duk marance ( yamma ) akantitin B C G titin da ya mike zuwa kaduna , minna Abuja tare da,wasu yan kauyu kar dake hanyar,
Duk marance a nan su KB ke yada zangon su, suyi ta hira ko aita shan matar juna a tsakanin su,
Wanan abin ko yaushe yana kara burge Joseph don saman yan yaren su basu da lokacin hakan ,
Ko yaushe ana cikin kasu ko bakin titi gurin bidan kudi,
Yan zun kuma sai dai in har yaso shiga taro saidai ya yaje koda clubs ko kuma wani park ire iren wuraren sheke aya amma ba irin haka ba da hausawa ke yi,
Shiyasa shi har gobe yana sha,awar tarbiyan bahaushe,
Joseph jin shi yakeyi kamar bai da wani harkan komai a gaban shi,
Zuciyar shi na mashi fes a duk lokacin da yake cikin irin wanan yanayin,
Wani matashi mai suna sulaiman ne yazo sama wata mashin rober,rober yanata,washe baki,
Ya sayo sabuwar abin hawa, sai sam barka kowa ke mai a lokacin saboda ya huta da yawo a kasa ko saman kabukabu,
Kowa sai zuwa yakeyi yana duban man shin din cikin kulawa, da yiwa Suleiman fatan alheri,
Joseph dake waya a lokacin kuma yana kallon su sai abin ya daure mai kai so sai
Don saboda mashin kawai da ko gabadayan su zai iya sai masu wanda ma yafi wanan tsada suke ta ma suleiman murna haka,
Sai kawai yaji tausayin su yakara kamashi duk da sunan wai suna aiki gwaunati ke nan amma gashi yar mashin kawai na basu sha,awa,
Jesus crisis yace a zuciyar shi don ba karamin sa,a ya taka ba shi da Allah ya maishe shi haka cikin su,
Don ai a da duk tare suka