Showing 24001 words to 27000 words out of 255288 words

Chapter 9 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1345

A hanyar shi ta komawa cikin garin Abuja yakara kiran wayar Joseph din saidai wanan karon muryan da dan sauki sosai a saman da zu,
Ejoma, yarinya ce matashiya yar kabilar IBO mazauna cikin garin kwantagora,
Tana zaune tare da yayanta da mijin yayanta wa yanda suka kawo ta garin kwantagora da zama,
Tun bayan gama karatun secondary din ta ta shaku da wani yaron hausawa,
Dan cikin gari shakuwar su ta samo asaline ta yawan zuwa sayen abu da Aminu Aliyu ke yawan zuwa yi a,shagon su Ejoma Ibire,
Har takai sun kulla, soyayya da Aminu din batare da kowa yasani ba,
Sai da abokan mijin yayan Ejoma suka gan su tare shine suka fada ma mijin yar nata,
Ranan tasha fada har d a duka agurin yayyen nata so sai hakan bai masu ba saida suka fada ma pastor don yai mata preach
Duk wanan abin bai raba Ejoma da Aminu ba illa ma kara shakuwar da sukayi so sai ,
Har ta kai Aminu yai mata alkawarin cewa zai aureta
Hakan yasa har ta yarda dashi har suka kai ga kara aikata masha,a a tsakanin su hakan yasa Ejoma ta fara bijirewa yayanta da mijin yar nata,
A karshe saiga ciki, shiko Aminu Aliyu yana jin ta ce ciki gare sai yace ai sam bashi yai mata ciki ba,
Duk yadda yayanta suka so a sulhuta maganar sam Aminu yaki yarda da zancen cewa ai cikin sane,
Hankali duk wani IBO dake zaune ya tashi da jin wanan labarin na zance Ejoma ,,
Ganin haka yasa mijin yarta ya koreta gidan nasu yace saidai ta koma can gurin Aminu,

Wayan shi yake kokarin ajewa bayan ya gama waya da wani Abokin shi da ke zaune a janhoriyar Benin republic,
Inda yake kwadaita mai yadda sana,ar motoci da shimkafar kasar wane ke da riba so sai a harkan,,,
Kiran Samuel ce ta hana shi aje wayan dai yai niya,
Inda Samuel ke sheda mai cewa mahaifin su yana fama da ciwon kafa sosai duk kwanakin nan,
Don har takai ko shago da gidan mai bai iya fita yanzun nan,
Hankalin Joseph din ya tashi sosai don yasan yadda yakanyi fama da ciwon kafar na shi
Sanadin ciwon kafar ya samo asaline tun wani hatsari da yasa mu a saman mashin,
Joseph yakira mahaifin nashi inda yake tambayar shi lafiyan jikin nashi
Amma sai Mr Ema din yace mai a meke ,you, no worry my child,
Na small problem ,
I go manager amm,,,
Yasan cewa zai shigo kaduna sati mai zuwa don akwai wani wanda yake son gani a kaduna din,
Hakan yasa bai cewa mahaifin komai, ba,

Musalin biyar na na yamma ya shigo garin kwantagira bayan dan banzan gudun da ya dinga shararawa shi kadai acikin mota,
Tun kwanar shiga gidan su yafara ganin abin hawan su duk ya cika kifar gidan su,
Hankali shi ya tashi matuka daga ganin taron IBO haka,
Hon yayi mai karfi wanda dole suka bude mai get,
Da kyat yasamu inda yadan parker motar shi a can gefen cikin gida,
Tun bai fito daga cikin motan ba ya hango wata yarinya a tsugune gaban elders nasu,
Yana ganin haka ya san cewa wani case sukeyi mai karfi,
A hankali ya fito daga ccikin motar saidai ganin mutane a gidan ya hana shi bude bayan motar don ya fitar da tsaraban da yazo da shi,,,
Tun daga nesa yake jin yadda yarinyar ke gumza ta na ihu da kuka mai ban tausayi,
Tana, mai ba da hakkuri sai kawai yaji wani iri a zuciyar shi
Don komadai may tayi yakamata,su yi considering din ta a mace ce fa,
Ko kallon su baiti ba ya wuce ta gefen su batare da ya tsaya gaishe su yadda ya saba ba,
Wanan ya kalli wanan wancan ya kalli wan can,
Su na mamakin shi don basu san shi da halin rashin mutunci ba,
Samuel wanda ke labe tunda aka fara case din shine ya ke taron dan uwan shi cikin mutunci,
Nan yake washe baki babu ko ga ruwa ya fara labarta ma Joseph cewa
Na, Ejoma Ebere one hausa boy givern bele,,,
D hausa boy now say no b him do amm,
Na yin d elders wan punish har,,,
Y ,she, give her self to musulim boy,
Me ,I know ask u ooo,
Joseph ya ce ma Samuel wanda da har zai ci gaba da zubawa,
Roban ruwa yadauko ma kan shi daga cikin fridge din,
Ganin cewa Samuel baida niyar kawo mai komai
Eanka yafada don ya sauke gajiyar shi,
Daga cikin bayin yakre jin karar motocin su da mashunar su suna watsewa
Saida ya shirya tsab yafito cikin wasu kananan kaya,
Abin mamaki wanan yarinyar Ejoma yagani rakube bayan kujera a falon su, har yanzu tana dan sheshekan kuka,
Sai a lokacin yake gaisawa da mahaifin shi wanda ke zaune ya mike kafar dake mai ciwo saman wani tsohon tebur,
Joseph y u know greet my people,?
Baba me i don't have problem with dem woo,,
Waiting dis girl do here Dad ?
Yace mai zata zauna har asan yadda za,ayi da ita ne,
Don ta je tana bin yaran hausawa ga irin hawalan da wo mata, nan,
Wayan Joseph din ce tai kara a lokacin wanda hakan ne yasa shi samun sararin guda daga fadan baban,
Motar shi ya shiga ya bar gidan nasu don yasan cewa fadan sai ya kawo kan shi a karshe,,,,
Tafiya yake yi kawai don yasan cewa KB bai gari kuma ,
Don haka zuciyar shi ta raya mai cewa yaje wurin little friend kawai ya ganshi,,
Anty Dije ta gama abinci kenan tana ko gyara ko ina na gidan,
Daga waje yadan tsaya duk da cewa an bashi umarni akan ya shigo ko yaushe yake bukata,,,,
Amma sai yaji cewa bazai iya shiga ciki kai tsaye ba
Don haka daga daga,waje kadan yadan tsaya yace Salamu Alaikum don Allah ko Assalam na ciki,
Cikin mamaki mai ma Assalam sallama duk suke
Shiko Assalam har yagane murya da wani irin ihu yafita kofa inda Joseph ke tsaye yadaga shi sama cak yana dan juya shi,
Sai suka kama dariya a tsakanin su, daidai lokacin da duk sauran yan gidan suka leko ta kifar falo suna kallon su,
ร€nty Dije ke cewa a, Joseph shine baka shigo ba ka tsaya daga nan kana cewa kana ma Assalam sallama,
Dan sosai kai yayi da key din motar shi yace ai zan shigo nakira Assalam ne yai min jagora,
Falon anty ta bude mai yashigo daidai lokacin da maryam ta dauki buta don zuwa yin alwalar sallah magrib,,
Bayan sun gaisa da Anty dije sai kwai ta fara gabatar mai da abincin a lokacin don dama har ta gama komai,,,
Cikin nuna jin kunya yace mata ya gode bazai ci ba
To ke nan kai kana jin tsoron cin abincin mu Joseph shine shi Assalam, ka ke kawo mai sweet, time to time,
No haba Anty gaskiya ba hakana bane,
Kawai dai naga cewa nashigo late evening ne kin rida kin gama cooking din ki ko
Idanzaka ci kaci kawai don sama mu a aje extra ko yaushe,
Badon yaso ba yadan dauki spoon ya fara ci a hankali,
Yamai yar jin nauyi da kunya duk da cewa daga shi sai Assalam ne a falon zaune,


ZEEE MAKAWA
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
FUREN JUJI
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
1โƒฃ2โƒฃ
ZAINAB IDRIS MAKAWA



Ejoma ce zaune a saman wani dutse dake ta, bayan dakunar kwanan su zaune,
Duk abin duniya yakai mata ko ina sai tunane take yi lokacin da Amina ke mata kalamai masu ratsa jiki
Har yake mata tayin shiga cikin addinin su yana cewa zai aure ta zai zamay mata tamkar uwa ko uba,
Dan siririn hawaye ne ya silalo mata daga cikin idon ta ya biyo ta kumatun ta,
Muryan Aminu ke mata yawo a kwakwalwal ta inda yake cewa bai taba ganin wata mace mai irin surar jikin ta da yaji yana so ba aduniyar nan in har zata amince mai shi yayi alkawarin aurenta,
Wa yan nan kalaman ne sukayisukayi tasiri a zuciyar Ejoma har ta yarda da maganganun Amina yai galaba akanta,
Don Alokacin tana ganin kamar cewa tafi ko wata mace dace, da masoyi,
Kamshin turaren shi na THE wanda ya hade dana JOJOBA,
Shiya dawo da ita daga tunanen nadamar da takeyi a lokacin,
Kamar ya wuce inda zai tafi amma kuma sai yanan yarinyar da irin yadda yaganta zaune a takure yasa shi jin wani irin tausayin ta alokaci,guda ya tsargu mai a zuciya,
Cikin yaren su na IBO yake mata magana, a cin taushin harshe,
Yake mai ce mata may ke faruwa da itane har hakan yafaru da ita,
Wani sabon hawaye tafara shirin sakowa saida ya dakar ta da ita,
Cikin daga mata hannu yace
Hy ,I don't want dis your cry, cry pls,,,
Just tell me what happen with u,
Nan takoro mai da duk abinda yafaru tunda ga farko, tana fadi cikin sheshekar kuka,
Yana tsaye hannu cikin Aljihu yana saye da farar suit, sai bakin wando,
Wata yar jar ,T-shirt ke ta cikin rigar suit din nashi,
Ya kafa farin glass a idon shi wando ,zaka iya ganin fararen idon shi kar daga cikin glass din,
Yakai wani dan lokaci a tsaye yana nazarin yarin wace duk taba shi tausayi,
Don yasan cewa wanan abin yana daga cikin destiny' din ta ne dama,
Bayan dan tunanen daya yi na yan dakikoki, sai ya dan nisa kadan wanda ko ita ba lalai ne in har taji ba,
Nobar wayan Aminu yabukata daga gurin ta, ba, bata lokaci ta bashi dama nobar na a kanta ta haddace shi tsab,
Tana mika mai bai tsaya ba ya juya kawai ya wuce abin shi, batare da yace ma mata komai ba,
Tuki yakeyi amma zuciyar shi jin ta yakeyi kamar zata fito daga cikin jikin shi,
Why some people are not trusted,
Why men's are cheating girls nowadays,
Some say girls are to blem too,
Amma shi a gurin shi ai mace abin tausayi ne sosai,,
Amma wasu maza sun dauki mace abin wulakantawar su duk lokacin da suka gama da ita,
Sosai maganar Ejoma ya tsaya mai a rai gashi ta bijirewa iyayen ta,
Shikuma saurayin yayi rejecting din ta at last, su kuma yan uwan ta mai makon suyi hakkuri da ita,sun ki sun dauko ta sun kawo ta nan ,,
Unguwar su jibrin ya nufa don KB baya,gari yana Abuja,
A wayar shi yakira,jibrin din yana maisheda mai cewa yana son su hadu,,
Inda yake yai mai kwatance gurin wani aikin hannu da yake koyo,
Joseph saida suka,sha kwana sundan yi tafiya kadan batare da ya waigo inda,jibrin yake ba ya ce,
Ko kasan Aminu Aliyu masuga,
Jibrin wanda tun shigar shi motar baiyi magana ba ya sai yanzu,
Yace dangida namasuga, ke nan ko don naji kace namasuga wanda ke uguwar jankidi,, ko ?
Joseph wanda yakai iyakar kaduwa yace ban san ko a ina yake ba,
Yana mai karya kwanar filin kwallo yake ce ma jibrin ina son ganin shi ne,
Ok kawai jibrin ya ce mai da yace hakana,
Nokia shi ya ciro cikin aljihun shi ya kira wani kanin shi Abdullahi,
Yake tambayar shi ko yasan inda Abdullahi yake zama,
Gurin da Abdullahi yai masu kwatance suka tafi,
Aminu yana zaune saman mashin din shi lipan wani abokin shi yana tsaye suna magana ya ji ana mai horn da mota abayan shi,,,
Abokin ne ke ce mai ga wata hadadiyar mota fa kamar suna magana nake ga,,
Aminu wanda ya juya bayan shi sai gefen shi kawai mutum zai iya hangowa,,
Jibrin ne ya isa inda su Aminu suke yai masu, sallama, nan yake sheda ma Aminu cewa,, suna son ganin shi pls,
Bayan Aminu ya saurari duk abinda jibrin ya tambaye shi ne,
Ba musu ya ce masu lalai yana tare da Ejoma sai dai ai ba wai lalai dole bane ace shi kadai ke taraiyya da ita,
Maganar shi taba Joseph mamaki, duk bayanin da suke yi bai yi magana ba sai kallon su kawai yake yi,
Daga karshe Aminu ya dan bugi kafadar jibrin yana cewa,,
Haba jibrin may zanyi da kafira ina zan kaita, kai min adalci mana kaima,.
Kasan cewa ba abinda zanyi da arniya kamar Ejoma a gidan mu,
Jibrin Joseph yace cikin wata irin murya mai nuna gajiya da sauraron magana,
Muje kawai dan Allah, is ok hakana,
Ido yabi su dashi har suka bace mai dagani,
Inda abokin shi yake ya koma yana tsuki yace ji mun wa yan nan fa wai akan zancen Ejoma Ebere ne suka zo suna bata min lokaci,
Ina ni ina KAFIRA ,,, ARNIYAR banza, wace ko kama ruwa batayi,
Dariya mai karfi abokin shi ya shiga yi don jin kalaman Aminu,
May kake ma dariya haka ne wai
Nuna shi da yatsa yayi cikin dariyar yace bata kama ruwa kai sai yanzu ka san da haka bata kama ruwa,
Lokacin da kake holewa da ita duk wanan baizo ma arai ba sai yanzu,
Malam kawai kayi JAHADI mukan mu je Onitsha musha bukin gaban dodon tsafi,
Kai dan Allah shere kawai da banzaye kaji ni duk in rasa wace zan aura sai ARNIYA
Kaifa mutumi dafa cewa kayi zaka musuluntar da ita ka aure ta to yanzu ina zancen musuluntar ya tafi,
Kai jafar ka ga alamar musulunta a,wanan yarin balle har kai zancen yinta,
Jafar yace gaskiya tunda tana,son ka musuluntar ta ba wani abubane mai wuya,
Kai malam kaga idar har kana ra,ayi zaka iya,don wanan ai taimako ne,,,
Ka jin tsoron Allah Aminu,
Kamar yadda baka so a diyar ka ko wata yar uwanka wallahi su ma haka ne wanan abin yake da zafi a gurin su,
Kamar ace kaunar ka ko diyar ka ta hada connection da Dan ,Ahalkitabi, ya zakaji a zuciyar ka,
Har kuma ace ya bata ma yar uwar ka, ko diyan ka,, shin zaka ji zafin abin da yai ma ko kuwa,???
Duk wanda yan dake, gurin su kace gaskiya da ciyo wanan abin hakan bai kamata ba,
Zafin maganar su ya ji don haka ya hau mashin din shi, ya,buga ya bar gurin cikin fushi,,,,

Da hannu guda yake tukin motar hannu shi guda yana yi yana shafan fuskan shi a hankali,
Wata bangararen zuciyar shi kuma maganar Aminu ce ke mai yawo a kai,,,
Tsawon lokaci suka dauka yana tafiya a hankali da motar,
Ba, wanda yai ma wani magana tunda suka fara tafiya,daga shi har Jibrin din,,,
Gidan Anty Dije kawai zuciyar shi taraya mai yatafi alokacin,,
Kofar gidan Anty Dije yai parking jibrin baiyi mamakin hakan ba don yasan cewa yakanzo gidan,
Sai a lokacin ya dan kalli jibrin din yace mai, ina son in,gaida sune,,,,
Bayan shigar su cikin gidan sun samu Anty da yara a falo suna karatun hadda,
Nan suka zauna suna kallon yadda anty ke wa yaran karatu cikin fasaha,,,,,
Joseph yana zaune gefe duk sai yaji yaran sun kara birge shi,,,
Saida suka gama ne Anty Dije ta waigo inda suke suka fara gaisawa,
Nan sukan dan fara hiran karatun yarw sai kuma na yanayi dake zuwa,,,,,, saidai hiran duk akan zafin da aka fara ne a lokacin,
Maryam maryam Anty Dije ce ke kwalawa maryam kira a wanan lokacin
Maryam wace ke daki tana gyarawa ta ansa daga can,,,,,,
Daidai kuma lokacin da wayar da ke a cikin aljihun rigarJoseph tai kara,
Aisha ya kike, ?maryam wace ke shigowa don amsa kiran Anty Dije
Idon shi, a lumshe yake magana yadafe goshin shi,
Batare da ta kalle su ba tace Anty gani
Baki gaida mutane ne maryam , ?
Wai may yasa baki iya gaida mutane, maryam, sai a lokacin ya bude idon shi da suke a lumshe,
Ya sauke su ga wace ta shigo falon
Cikin kwantar da murya kamar ta shagwaba, ta dan rusun na tace ina wunin ku, a kunya ce,
Jibrin ne ya amsa mata da lafiya lau,
Jin gudan bai amsa mata ba yasa tadan saci kallon shi inda yake zaune,
Dammmm gaban ta yafadi don gani wanan dan Christian

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login