Showing 177001 words to 180000 words out of 255288 words

Chapter 60 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1394

guy din yai mai yau,
Allah ya kyauta ya furta a fili ya na mai ajiyar zuciya shi kadai a mota,
Saboda sanyin da jikin shi ya yi bai iya zuwa gidan su Jibrin da yai niyar zuwa ba a lokacin,
Don haka juyawa yayi zuwa gidan shi don ya dan samu natsuwa,

Maryam wace ke zaune ta zubawa plate din da ta zuba ferfesu a gaban ta ta kasa koda kai cibi biyu a bakin ta
Tun cibin farko da takai tasamu ta hadiye shi da kyat saboda sam bakin ta batajin dadin shi ko kadan, alokacin,
Sai dan daukan spoon din tayi tana dan juya,shi a ha kali, amma ta kasa kaiwa a bakin ta,
Wayan ta ne yai kara inda taga A,A ne ke kiran ta alokacin,
Sai da ta juya inda anty dije take zaune taga cewa hankalin ta baya gurin ta,
Sai ta mike a hankali zuwa dakin ta inda zata fi jin dadin sake jiki tai waya,
Bayan ta anty dije tabi da kallo mai kama da harara, ta sake dan guntun tsaki tace a fili mara hankalin yarinya kawai,
Zama tayi saman gadon ta a hakali tana mai ansa mai sallama,
Muryan shi taji yana cew may yasa may ki maryam naji muryan ki wani iri daban,
Ba komai ta furta ahankalin sai ta baka tausayi idan kaganta a lokacin,
Don har idon ta yakawo hawaye ko tankar zasu zubo mata,
A zuciyar ta tausayin kasu takeyi don ta san cewa raba su za,a yi, bada dadewa ba,
A,A ya sheda mata cewa zaiyi tafiya sai bayan kwana uku zai dawo, har ma ya fara hanya ko,
Duk da rayuwan maryam din ya baci don rashin sheda mata cewa zai yi tafiyan da bai yi ba da wuri sai bayan ya fara hanyar tafiyan shine zai kirata ya sheda mata,
Fatan adawo lafiya tai mai inda take ce mai Allah ya bada sa,an tafiya ya karba cikkn dadi rai da cewa Ameen nagode tawa,
Bayan sunyi sallama ta kashe wayan takai wani lokaci zaune inda take tana tunanen irin rayuwan A,A narashin sani darajan abokin zama,
Ku san ko yaushe haka yake mata wanan halin wani lokaci ma sai ya kai inda zai tafine zai kirarata ya sheda mata,
Safiya ta nuna mata rashin faidar irin wanan halin amma so ya hana taga lain malam din nata,
Kiran sallah dataji anayi na la,asar yasa ta aje wayan tamike don zuwa dauro alwala,
Anty dije ce a waje take ce mata, zancen zuwa dibo Naimat da sukayi ta shirya anjima idan Yusuf ya shigo sai ya kai su saboda safe yara zasu school,
Bata rai tayi don sam batajin dadin irin haka da anty ke mata tana wani cucusa ta ga Yusuf,
Gidan Naimat ne za,ace sai ya kaisu ita da yara, saunawa tana zuwa ita da su a saman mashin,
Matsala guda dai yanzu shine dan fitinar hawa mashin yana gari, zai sa mata ido,
Rai a bace ta ansa ma yar ta da cewa aida abari kawai weekend sai mutafi mu yini mata ko ?
Maryam kece fa kikace kun yi da ita jiya zaku zo ayau din ko?
Bata kara cewa komai ba don tasan ceqa ba yarda Anty zatayi da wani excuse din da za ta bayar ba,
Tuwon semo da miyar yauki sukayi don Yusuf dake agari kawai in badon yana gari ba suna da sauran abinci da zai kai su har dare,
Sai kuma gashi yau din Yusuf din baiwani yawan shigowa kamar yadda yake yi ba idan har yana gari,

Jibrin ne yakira shi a waya yana mai complain akan KB wanda yanzu sam ya canza sosai,
Har zuwa lokacin da Jibrin din yakai karshen maganar shi Yusuf bai ce mai ufan ba,
Sai ma murmushin da yai mai alokacin da yaji cewa ya kai karshen korafin,
Yace Jibrin kafi kowa sanin halina a halin yanzu ,
Nai maku hanyar wanan business din ne don ku samu madogara har ku taimaka ma wasu daga cikin mutanen ku,
Tun a wanan lokacin ni ban kara damuwa ko wani irin hali kuke ciki ba ,
Idan har nace zan dinga bin didigin may kuke ciki da aiyukan ku ke nan badon Allah natai maka maku ba.
So kamai don Allah kafita batun shi kasa mai ido kawai , nadade da sanin irin halin da yake acikin tun lokacin da yai aure,
Addua kawai nake mai akan Allah ya sa ya gane gaskiya batare da yafada acikin halakaba
Kaiwai mu bishi da addua kaji pls ka dai na yiwa dan uwanka mugun fata,
Tsigar da yake magana ne yasa Jibrin jin wani irin nauyi don shi ya,kamata ace yai wanan maganar amatsayin shi na dan uwa kb da sukafito cikin kabila daya,
Nan yake shedawa Jibrin cewa ai yana kwantagora saboda yana son yai spending din sometimes with his Dad,
Wanka ya fada don ya dan ji dadin jikin shi ko zai rage jin kasalan da yada may shi, tun dazun,
Wasu kananan kaya yasa wando da riga duk bakake sai kwalar rigar ce kawai ke da ja,
Kamshi turaren shi na THE da JOJOBA yana nan kamar kulun,
Saida yafitane yasamu yadan ba masu gadin shi wmai dan ihi sani kamar yadda ya saba yi masu idan yazo,
Su ko sai addu,a suke zabga mai tankar yau yafara masu irin haka,
Indai har yana gari to sun yake talauci ke nan su sai dai kuma in bayan ya wuce,
Maryam wace a lokacin tana daki zaune tafito daga wanka tana saka riga don shiryawa saboda tasan cewa yau fita dole akan ta,,,,
Muryan shi taji yana sallama tuni zuciyar ta ya tsinke, saboda addu,an ta na fatan kada ya shigo bai ciba,
Muryan yaran Anty Dije taji suna mai sannu da zuwa tare da fada mai cewa zai fita da su da little Mum,
A tsorace maryam ta sake tsaki saboda yawan suruntun yaran da yai yawa,
Tau fa zuwa ina da daren nan yake tambayar yaran,
Suna hada baki gurin cewa gidan Anty Naimat, zamu tafi tare da little mum
Wani murmushi yayi mai sauti yana cewa cikin daren nan zaku bazaku bari da safe ba,
No, Uncle inji Assalam gobe akwai school bamu zuwa ko ina,
Idan mun fita sai na gama zan je nadauko ku ke nan,
Tsigar da yake maganar shi yasa yanayin maryan jin tsoro don tasan ceq zai zube su nan ne yatafi nashi tsabgar,
Idanu ta zare don tagona manufar zancen shi da sauri ta kalli agogo inda taga takwasa saura na dare,
Muryan anty ce ya katse ta tana cewa wai ina maryam ta zuba ma abinci,
Da sauri ta karasa daurin dankwalin dake hannun ta tun kafin anty ta balbale ta tafito,
Karan daurin zanin ta ne dake bada sauti idan ta taka yasa shi daga lumssasun idanun shi yadan dubi gefen datake tafiya,
Wasu shaddane jikin ta masu ruwan makuba dinkin fitted ne anyi aikin wuta akai an darza wasu duwatsu kanani suna walkiya,
Sai wasu takalma plat masu dan tudu kadan adudugen su,
Ganin shi zaune a cikin falin nasu alokacin yasa tai mai
Sannu da dawowa tace mai a takaice ta wuce abinta zuwa kitchen,
Mamakin iya kwalliyan wanan yar karamar yarinyar yake yi,
Yarinyar duk yadda tai kwalliya sai ya burge mutum,
Already abincin yana a cikin kula don haka daukowa kawai tayi takawo mai inda yake zaune,
Kai maryam har kin ban tsoro da,wanan kulan naki ,
Masan da naci dazu baiko gama aikiba fa yadda yai maganar saida kowa falon yai dariya har maryam din dake ta faman daure fuska,
Harara maikama da murmushi ta sakar mai ta gefen ido tace aiko tunda munyi dole kaci shi uncle,
Assalam ya jowa yana cewa zo ka tayani my son kada in kasa ccinyewa ni kadai,
Bayan tagama zuba mai dan kadan tamike tsaye ahankali tana mai kokarin wuce,
Sunan ta yakira a hankali yana mai langabar da kan shi cikin marairaicewa kamar dan karamin yaro ya na mai cewa haba little Mum ai wanan yai muna yawa,
Mikewa tayi gami da dan mai hararan wasa wanda yakarawa fuskan ta kyaun kallo,
Tace cikin yar murya irin nata,
You have to eat, it ,all so pls excuse me,
Da sauri Yusuf wanda sam ya manta cewa anty Dije tana gurin yai niyar kamo ta cikin wasa,
Maryam wace a zaton ta dagaske kamota zai yi sai ta dan zille mai tayi waje tana dariya ,
Wanan abin yasa anty dije cikin farin ciki amma sai tai kokarin boye farin cikin nata agaban su,
Don haka sai ta nuna cewa bata fahince shi ba takawo wani zance na daban,
Kwalaben turaren wuta anty bawa su maryam sukaiwa Naimat din,
Inda Yusuf koda bai gani ba afili yai murna sosai irin yadda yaga tana kokari da yar uwan nashi,

Wakan secret lover's ke tashi a motar inda Yusuf ke marming a hankali,
Yana tukin motar tankar wanda bai son tukin alokacin, a hankali,,
Wayar shi ce tai kara inda yaga kb ne bai fi minti biyar ba yakashe wayan,
Sai kuma ga kiran Jibrin ya shigo again, kamar hadin baki,
Yadai mutumina yace da ya dauki wayan, alokacin wankan dake tashi bai bari suji may yake cewa,
Amma dai taji lokacin da yake cewa gani nan da su maryam za mutafi unguwa,
Batasan ko may yace mai ba sai murmushin da taga ya dan yi,
Fuskanta na gefen widow tana sauraron abin da mawakan ke fadi gamay da secret loves, d two hearts dat beat together,
Kaman kada ya gama wayan sai wani irin annashuwa yazo mai a lokaci guda,
Muryan shi ya kashe ta yadda yaran dake bayan motar baza su iya jin ko may yake cewa ba
Maryam ya ambato cikin muryam maikama da wanda ke rada, yace,
Kiyi hakkuri da ni pls duk da nasan cewa bai kai matsayin da zaki soni a zuciyar ki ba
Badon komai ba sai don kasan cewa na tankar FUREN KAN JUJI,
Don banda wasu yan uwan da zan gwada wa alumma inyi alfahari da su, acikin su,
Kinga kuwa hakan zai sa duk wani mutum mai raunin imanani ya ji kyamar hada wani alaka dani kamar yadda iyayyen Sadiya sukai min ikirari da hakan,
Abin mamaki sai maryam taga kawai hawaye wasu na bin wasu a fuskan shi
Abinda bata taba gani ba a rayuwan ta taga namiji na kuka haka,
Itama maryam haka kawai batasan lokacin da hawaye wasu na bin wasu afuskanta cikin kukan tace may injiwa
Ni uncle bana kyamar yan uwan ka tunda mahaifana basu kyamace ka ba tun farko,
Cikin murya maikama da rada tace kawai dai malam A, A da mukayi nisa da shi nake jiwa,
Murmushi yayi daidai lokacin da zasu karya kwanar da zai sada su da unguwar su Naimat,
Hasken motane ya hasko mata motar A, A din tare da wata yarinya a tsaye hannu rike da na juna,
Yana saye da wani dinkin shadda light green
Ganin hasken yaimai kau a lokaci guda yasashi kokarin kate fuskan shi da hannayen shi,
Gaban maryam ne yabada damm kardai A,A karya yai mata dama,
A zaton maryam Yusuf baigane cewa A A din ta bane can suka wuce, a baya,
Wayan ta ta jowo takira layin wayar shi, tambayar shi tayi da ya isa lafiya ko?
Ya amsa mata da cewa a,a lafiya kalau har ma na kwanta,




ZEEE MAKAWA YELWA
[4/10, 6:23 AM] 0mmer Farouk: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
7⃣2⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI


IY,YA,NA,A ABBUDDU WA,IYYAKKA NAS,TA,INN,



Duk da ga hasken street light's da ya haske ko ina a titin da kuma hasken abin wuta da ke gittawa jefi jefi a lokacin,
Baisa idon maryan ganin haske ba alokacin, magana Yusuf ke mata amma sam bata ji may yake cewa ba ,
Sai ji tayi yana cewa idan kun shiga kada ku dade zan dan je in dawo pls,
Hakan ne yasa ta gane cewa sun iso gidan su Naimat din ke nan,
A hankali ta sauka motar batare da ta dauki ledar sakon da Anty ta bata takawo ma Naimat ba,
Yusuf din ne bayan ta sauka ya miko mata ledae yabata takar ba a darare, tawuce zuwa cikin gidan,
A lokacin yaran da suke a tare har sun isa ciki ko sun ririke Naimat din,
Sun sami Ibrahim a gida don haka bawai wani sake jikin ta tayi ba,
Saboda dama hankalin ta baya tare da ita a lokacin,
Ganin yanayi da maryam ke cikine yasa Na,imat dan maida hankalinta gare ta,
Saidai maryam din tayi kokarin yin dariya irin ta yake din nan,
Fira sukeyi amma zuciyar ta ya,gurin abinda idon ta ya hasko mata, dazun nan,
Sakon da,aka basu ne sukawo wa Naimat maryam ta bata tai mata bayanin akan ko wanin su sai wani mugun kamshi ke ta shi,,,
Nan Naimat din ta dinga jin dadi saboda wanan sakon da akai aiko mata,
Sun kai kamar minti talatin Yusuf yadawo inda yakira ta layin wayar maryam din,
Tare suka fito da Naimat don ta gaisa da Yusuf din wanda har zuwa yau bai taba shiga gidan Naimat din ba,
Itakan maryam karfin hali kawai takeyi a lokacin saboda abinda tagani yau karara cin amanar da kusan ko da yaushe safiya ke fada mata cewa A, A cin amanarta kawai din ya keyi,
Amma ita sam so ya hana taga gaskiyan hakan da ake fada mata
Magana sukeyi amma acikin yaren su na IBO ne don haka maryam takoma jikin mota ta dan jingina jikinta a kai,
Saboda irin yadda take jin kafafunta baza su iya daukanta ba,
Kallo guda zakai mata zaka ne cewa babu kwanciyar hankali a tare da ita alokacin,
Shigar su mota ba,wanda ya kara yiwa wani zancen komai kowa da abinda yake sakawa a zuciyar shi,
Sun shiga gida tana tsaye tanawa anty bayani sakon Naimat amna sam Anty ta kula da cewa bata a cikin hankalin ta ,
Ledojin da Yusuf ya sayo masu kaji gassasu da kuma drinks masu sanyi da tsada,
Sai wasu kayan tarkace su sweet da sauran su biscuits, kala, kala har leda biyu,
Gudan ledan dagani tarka cen maryam ce a ciki amna lokacin da anty Dije ke ce mata tazo ta dauki nata sai cewa tayi anty tabarshi a gurin ta,
Tasa kai kawai daniyar shigewa dakin su, batare da ko ta juyo ba,
Anty Dije cikin haushi take cewa maryam wai ke wata irin yarinya ce mai taurin kai,
Dan Allah ki duba wanan yaron bai fasan ko mu suwaye ba Allah ya hada mu dashi har yake muna irin wanan biyayyan tankar wasu yan uwanshi na Jini,
Ke ko duk kin bi kin takurawa wa rayuwar ki,
Kin hana rayuwar ki farin ciki, kullun a cikin tsangwamar kan ki da tashin hankali,
Maryam kan tana daki zaune saman gadon ta sai hawaye takeyi na takaici,
A haka ranan ta kwanta ko kayan jikin ta ta kasa cirewa kafin ta kwanta,,

Zaune yake inda ya idar da sallah walha kamar yadda ya saba yi,
Jikin shi saye da wata bakar jallabiya mara hannuwa,
Zaune yake a takure yana jan casbi da hannu guda a hankali,
Wayan shine Jibrin din ya kira shi yana,cewa ga,shi ya taso zuwa KG din shima,
Nan dai sukayi sauran bayanin irin abinda zai zo mai da su na bukata wanda bai samu sayowa ba,
Suna sallama da juna sai abinda yafaru jiya da dare ya fado mai arai,
Ashe bayan ya aje su maryam gurin da A,A yake tare da wanan yariyar yar makarantar su ya koma ya samay shi,
A hankali yafito daga cikin motar shi daya dan Parker nesa kadan daga inda suke,
Tafiyan shi irin na gogagun matasa yan bariki da yake ko yaushe har yazama mai jiki, shi yakeyi ya tun,karo inda suke,
Da farko bai gane ko waye ba sai da Yusuf din ya zo gab da su yagane cewa shine,
Hannu ya mika mai don su gaisa amna sai Yusuf din yaki sai dai ce mai da yayi sallamu Alaikum,
May yasa baku zantar da gaskiya a cijin rayuwa mai karya zai haifar ma arayuwa,
Yaudarar diyan mutane tankar wani taki ne da mutun ke zuwa bawa acikin gonar shi,
Don duk abinda ka shuka sai ka girbi abinka ga hannun ka,
Yauda gobe dama masu karin magana sunce sai Allah,
Yariya ta dauki amana da gaskiya tabaka amma kai ashe yaudar ta kakeyi,
Ko da yake itace dai dama bata san da haka ba amma ai duk wani wanda ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login