Showing 198001 words to 201000 words out of 255288 words
Chapter 67 - Furen Juji Book 1 Hausa Novel Complete
zaman a cikin natsuwa sukayi shi tare da nuna kamilanci a tare da su,
Sai a lokacin da, Yusuf yaga sun zauna ya dan waigo da hankalishi gaba daya gurin su,
Yana masu sannu da zuwa a cikin harshe hausa,
Sai a lokacin ya waigo gefen gurin da Sonny din yake zaune tankar ruwa yaci shi,
Muryan Yusuf ne yaji yana cewa Mr Sonny meet , Maryam and Safiya our fiance,
Firgigit ya farko daga tunanen da yafara yi naganin yana holewa da wa yan nan kyawawan yan matan ,
Hannu ya mika wa maryam da niyar wai su gaisa,
Kai maryam ta gyada mai, alamar a,a cikin wani shu,umin murmushi amma acikin rata sai kiran Wa,iyazu billah, takeyi,
Subbahanallah lokacin da sautin muryan ta cikin wani irin murya ke cewa is forbidden in our religion,
Amma sai ta daga mai hannayen ta biyu ta hade su guri guda alamar gaisuwan musulmai,
Ba Sonny din ba har, Yusuf da Jibrin ma sun mato a sauraron shi,
Wow, yace I like your style girls,
Ai fa tuni maryam ta tafi da imanin Yusuf din wanda yake jin tankar a yau yafara ganin maryam din tashi,
Ga kuma wani abin bajinta da tayi a gaban shi yanzu wanda yakara sa shi jin ta a ran shi,
Duk yadda ta ga,suna girmama Sonny da mutunta shi bai sa tayi gigin bashi hannu ba,
Kamar irin yadda wasu wayayyu keyi wai saboda waye wa ko boko,
A gaskiya duk yadda zai yi insha Allah dole sai ya mallaki wanan yarinyar a rayunwar shi,
Nan ya shiga gabatar mashi da su da yaran da kuma bashi dan labari akan yaron shi a bokin shi Assalam,
Maryam ce tadan diba agogon wayan ta sai tadago kai ta dan kalli gurin da Yusuf yake zaune rungumay da Assalam
Alamar zasu tafi taimai da kai inda take nuna mai time cikin hikima,
Wani lalausar murmushi ya sakar mata saboda tun dazu yagane cewa a takure take zaune saboda ,
Irin mugun kallon da Sonny ke mata, daga inda yake zaune,,
Yusuf din ne ya mike tsaye daga inda yake yana cewa Jibrin ka mai da su gida saboda time din sallah ya kusa,
Ganin Yusuf din ya mike suma suka mike tare a lokaci guda suna mai yiwa Sonny din sallama,
Dakatar da su yayi ya shiga daga cikin gidan dan jim kadan yafito hannun shi dauke da wasu ledoji masu a lamar,tambarin shago a hannun shi,
Ledan dake dauke da tambarin, kamar na yan kwallo,
Ya,mikawa, maryam, sai kuma Safiya, da ya mikawa gudan,
Thanks, suka ce mai a lokaci guda yayin da kowace tadaga ledan suna mai gwadawa Yusuf din da Jibrin,
Yar dariyan yake yi maikama da yake, a fuskan shi,
Amma shi yusuf a ran shi jiyakeyi tankar ya shake Sonny din saboda irin manyatacen kallon da yaga yanawa maryam din,
Shiko Sonny wanda ya kashe su da ido sai mamakin wanan sarauniyar kyau da yagani a gaban shi,
Kamar yadda Jibrin yazo da su da farko hakama wanan karon shi da kan shi ya mayar da,su gida,
Shigar su gida yai daidai da shigowan kira a wayan ta,
Ko bata diba ba tasan cewa Yusuf ne,
Maryam, tayi yar murmushi, tadiba tana mai lumshe ido,
Don haka batare da ta tsaya gurin Anty Dije kamar yadda tai niyya ba,
Ledan tsaraban kawai ta aje mata a gaban ta, ta shige dakin su,
Itako safiya dama tana kofar gida bata karkare shigowa ba sun dan tsaya da Jibrin din ta a waje,
Maryam tana shiga daki tai receiving din kiran tana mai kara wayan a kunnen ta
Tana mai cewa Assalamu Alaikum, wani iri yaji a kunen shi yarrr a lokacin da sallamar ta yadaki kunnen shi din
Murmushi yayi yana tambayar ta da cewa sun isa gida lafiya ko,
Ta ansa mai da cewa lafiya kalau har ta shigo ciki ai,
Dariya yayi yana cewa
ai yasan ko minti nawa ne zai kai,su gidan dama,
Sai kuma taji a lokaci guda yai tsuki, ya wani ja wani, irin numfashi,
Cikin sanyi jiki murya maryam ke tambayan shi ?
My ya samay ka uncle, kuma,?
Ya saki wani ajiyan zuciya yace,
Kyale ni kawai maryam nayi da na sanin zuwan ku gaida wanan dan iskan wallahi,
Mutum kamar maye kadinga kallin matan mutane haka,agaban ma,ajen su ,,
Baki ji yadda kirjina yake min zafi ba wallahi inda badon bako na bane da ba,abin da zai hana in dake shi yau,
Sakin ajiya zuciya maryam din tayi ta lumshe idon ta,
Tace kasan wanda baida tauhidi bai dauki irin wanan abin a matsayin sabon Allah ba,
Tace amma sai naga kamar mun fi shi laifi ai muda muka tafi hakana gurin shi batare da mun sa zumbudeden hijabi ba
Yusuf daga inda yake ya lumshe idon shi saboda jin abinda maryam din tace don tabbas gaskiyar maganar ke nan,
Wani irin kishin abinda Sonny din yayi dazu ya baibaye mai zuciyar shi,
Sai da kyat yai kokarin kwantar da zuciyar shi, saboda kasancewa Sonny bakon shi, ne,
A haka sukayi sallama da maryam din yana mata godiya akan irin yadda suka yi da bakon nashi,,,
Bayan sallamar su yai zaune yana mai kallon wayan nashi tankar maryam din ce a gaban shi a lokacin
Sai kuma ya juya tunanen irin hali rayuwa na maryam,
Abinda yafi burgeshi da ita shine, hakkuri, ladabi girmamawa uwa,uba addini, gashi ba ruwan ta da duniya,
Don dai ya fahinci cewa Maryam irin matan nan ne dake kona mutum farat daya,
Don duk abinda zakai masu da wahala su tanka ma akai,
Maryam ce zaune tare da Safiya agaban anty dije wace mamaki ya cika,ta,
Ledan safiya ce akafara zazagewa inda sukaga wani dogon riga da turare guda biyu, sai kudi zube sabbi kar dasu, zasu kai kimani dubu dari koda hayi akai,
Sai kuma aka jawo ledan Maryam, wanda ke dauke da wani dogon riga baki mai kyau da kuma rigar barci irin ta matan turawa,
Wanda da kasa zai iya baiyanawa mace tsiraicin ta,
Turare kusa kala biyar sai kuma wani dan kit mai dauke da dankune da sarka,
Sai kuma kudi dollar's na America, sabbi ful da su suka zubu a cikin wani dan takarda,
Duk kan su mamakine ya cika su don ganin wanan irin kyautar na bajinta da Sonny yai masu,
Duk kan su sun rasa bakin magana saboda yawan kayan da tsadan su,
Anty Dije ce ta numfasa tace a karo na farko tunda suka bude kayan kwasa ki samin a leda safiya har Yusuf ya shigo,
Daga haka suka,watse kowa da abinda yake sakawa a zuciyar shi,
Gurin mahaifin Yusuf din suka fara zuwa wanda yai mamaki kwarai daganin Sonny din a gatin su,
Saboda sanin da yayi ko waye mahaifin Sonny din dakuma sani shi kan shi Sonny din,
Sosai yaji dadi yai kuma alfahari da ganin su atare da dan nashi,
Abin sha yasa aka kawo masu amma sam Yusuf ko ruwan su bai taba ba,
Sai mai faman danne dannen wayan da yake yi abin shi,
Shi dai Sonny din ne ya tatuli giyan shi sosai ba tare da wani buguwa ba,
Bayan sun dan dauki lokaci a tare da tsohon ne inda yake bukatan Sonny da yadan ziyar ci church din su don special prayer,
Ba wani mussu Sonny din yace zai yi kokari yazo kafin ya koma,
Da haka sukayi mai sallama inda yake tajin dadin a cikin rayuwar shi,
Zaune suke su biyu a falon shi Yusuf din sai TV dake ta kara shi kadai,
Kowan su da abinda yake faman yi a cikin systems din shi,
Sonny wanda ya kasa shakat da,samun sukuni a cikkin zuciyar shi tun ganin da yaiwa maryam ya dan yi gyaran murya,
Wanda hakan yasa Yusuf dan dagowa daga abinda yakeyi ,
Ya dan wani marai,raice muryan shi yace pls, Joseph ,
Ina son ka taimaka min duk da nasan cewa abune mai wuya agare ka yanzu,
Don nasan muna da bambancin addini, but idan har ka iya la,akari da cewa wanan ba komai bane Just life ne,
Nasan cewa zaka iya taimaka min, for a few times,
Yusuf wanda ya tattaro hankalinshi yana sauraron Sonny din don jin ko may yake da bukaya agurin shi har yake mai haka,
Don shi azaton shi Sonny yafi karfin ya bukaci abu agurin shi bai samu ba
Tambayan shi yayi cikin karaji da cewa just go a head tell me whay you want,
Saida yadan lashe bakin shi sannan yakai kallon shiga kwaya Idon yusuf da idon shi da suka kada sukayi jawur,
Yace I just want you to barrow me that your fiancée,,,,,,,,,
ZEEE MAKAWA YELWA
[4/28, 5:39 PM] ‪+234 902 951 1701‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
8⃣0⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI
Cikin wani irin zafin nama, Yusuf ya dago kan shi yakai wa Sonny kallo,
Idon shi sunkada sunyi jawur kamar garwashin wuta,
Sai kalman Innalillahi ya ke iya mamaitawa,a cikin zuciyar shi a lokacin,
Ji ya,keyi tankar, yai tako guda ya,shake Sonny din har lahira,
Kirjin Yusuf har wani irin bugawa yakeyi ya rasa ma awani duniya yake duk idon shi ya rufe a lokaci guda bai ganin komai,
Kalman nan ta Innalillahi da ta zauna mai a baki, itace yake ta nanatawa a cikin zuciyar shi,
Sonny wanda sam bai kula da irin halin da Yusuf din ya shiga ba alokaci guda,
Yusuf yadago kai da niyar yiwa Sonny din wani irin mugun zagi,
Amma sai Sonny din yace "Yes, cikin irin nuna ko in kula din nan,
Yusuf yakara jin wani irin tukukin zafin rai ya taso mai tankar ya make bakon nashi mai halin Dan Akuya,
A hankali Sonny ya,furta I really want to meet her again,
I want to ask her some question a bout her religion,,
Yaci gaba da ce tace gaisuwa da shi addinin ta ya hana don haka yake son jin karin bayani,
Saboda yasha gani others Muslims girls suna sharking din hannu da su,
Sai a wanan lokacin Yusuf da ke jin kan shi tankar wani namijin zaki yadan ji sassauci a zuciyar shi,
Kan shi ya dukar kasa tankar badashi Sonny din ke magana ba a lokacin da irin yadda yake ji,
Sai zuwa yan mintuna,masu yawa Yusuf yace cikin dasasshiyar murya,
Aiko da baka gan ta ba ni zan iya yi maka bayanin abinda kake nufi,,
Sonny wanda bai so jin hakan ba don shi maryam din ce yaso taimai wanan bayanin da bakin ta,
Sai da ya dauki cup din ruwan sanyin dake gaban shi yadan kurba a hankali,
Sai ya dan ja numfashin shi kadan yace wa Sonny kamar yadda kasa ni cewa duk wani addini bai yarda mata da maza su dinga cudan ya guri guda ba,
Sonny din yadan ce Ok,
Yusuf yaci gaba da bayani ya ce mai Allah ubangiji ya umurci, Annabin rahama, da ya hani mata akan cudanya acikin maza,
Su zauna a dakunan su su yi ibadan su,
Sannan su boye tsiraicin jikin su ga kowani irin namiji,
Hat ta muharramin su ba ayarda yaga wasu sassan jikin su ba idan bada wani dalili ba,
Sonny yana kada kai yace, Ok,
Yusuf yaci gaba da maganar shi yana cewa don haka kaga ashe duk macen da kaga tana hurda a cikin mazaje, ta kaucewa addinin ta, ne, tana bin ra,ayin son zuciyar ta,
Yakara da cewa duk diyan musulmuz jai mata ana haihuwan su tare da wanan sunnan a cikin zuciyar ta,
Sonny wanda ke ta sauraren shi tunda yafara bayani,
Yai wani irin numfasawa, saboda sharhin da Yusuf ke mai akan kamun kai na "ya mace,,
Yace to duk mata daga mata har har tsofaffi da yan mata,
Yusuf wanda yakara kai cup din ruwa a bakin shi ya kada mai kai yace eh, hakane,
Wow inji Sonny din wanda ke wani lumshe idon shi don jin abin mamaki daga gurin abokin shi,
Gani yakeyi Yusuf din ya jefa kanshi cikin addinin da babu freedom ko kadan,
Don may za,a ce har yara kanana irin su maryam basu da freedom din rayuwar su,
Baiko karasa,saurare ba wayan shi tai kara hakan yasa suka watse daga hiran da suke yi,
Wanka yafito yana daure da dan karamin towel,, a jikin shi sai dan karami da yake goge ruwan da ya kwanta mai a suman kan shi yake dan tajewa a hankali,
Kamar wanda aka sawa tunane a cikin rayuwar ta,
A yadda yake ji yanzu, ko da zai rasa rayuwan shi akan taimakon a addinin shi zai yiwa musulunci hidima so sai,
Dan haka ya karkare shirin shi yana mai aiyana abubuwa da dama,
Wasu dinki ne irin zalekar nan wando da riga masu laushi, da santsi,
Falon gidan ya fito inda yasamu har ankawo masu abinci daga gidan Anty shi,
Shima Sonny din a cikin shigar kanan kaya yafito daga dakin da yake yana saye, da, wani dan farin glass a idon shi,
Gaba daya saman dining table suka nufa don su ci abinci sun fara bada wani dadewa ba sai sukaji,
Sallama a bayan su, koda Yusuf bai juya ba yagane cewa Aisha ce da kawar ta,
Cikin wani dinkin buje da riga na shadda kowacen su take,
Dinkin ya wani matse masu jiki duk ya fitar masu da suran jikin su,
Nonon su duk ya wani turo kamar a fili a gaban rigar, da suke saye dashi,
Sonny wanda don burgewa baiko iya kauda idon shi a kan su,
Har zuwa lokacin da suka karaso gurin da su ke zaune,
Aisha ta taso gadan gadan da niyar zuwa ta rungumi Yusuf,
Cikjn wani murya mai kama da ta tsohon soja ya daka mata tsawa,
Cak ta tsaya guri guda tana mai wani shu,umin kallon,
Cikin muryan shagwaba tace mai haba Joe, may ye haka dan Allah,
Yaushe rabon da in gan ka ne wai pls ?
Da har zaka hanani hugging naka,
Takara she maganar kamar wata yar karamar yarinya,
Hey, girls' inji Sonny inda yake kokarin nuna masu seat, don su zauna,
Wani irin mugun zama suka yi sun wani turo boom din su baya yai wani tare kaman kayan wanki,
Nonuwan su ya wani turo gaban riga kamar yan matan clubs,
Yusuf wanda sam bai kaunar ya kara daga kai ya kalle su saboda sun bala,in zube mai a fuska har zuciyar shi,
Suna wanan betsere, betseren suna wani jan ra,ayin maza,
A gaban su Sonny yake tambayar Yusuf cewa su wayan nan yan matan addinin su daban ne da na su maryam ko ?
Yace cikin rashin fahinta yana nuna hakan da hannun shi,
Duk da sundan fahinci may yake nufi hakan bai hana su ci gaba da shakiyancin duniyan da suka sa gaba ba,,,
Nan suka kare, watsewan su inda Yusuf yagaji yai masu kora da hali sosai amma sai Sonny wanda yaji dadin kasan cewa dasu yai masu alheri irin ta bajin ta, din nan,
Fita sukayi inda suka fara nunawa Sonny cikin gari,
Jibrin kusan shine mai yiwa Sonny bayani akan irin al,adun kowani culture da yake tambayan su akai idan ya gani,
A gajiye suka dawo gida don haka sallah kawai Yusuf yayi ya haye gadon shi daniyar ya kwanta ya huta amma sai yaji sam ba zai iya ba,
Batare da yaji muryan maryam din ba,
Hello little mummy, yawani shake muryan shi tankar dan yaro,
Maryam wace a lokacin tana zaune gaban mirrow dake dakin nata tana dan shafa mai a jikin ta,
Ta sauke wani lalausar murmushi wanda har Yusuf din yaji shi daga inda yake,
Sai da hakan shima yasa shi yadan lumshe nashi idanuwan a hankali,
Ya gajiya uncle maryam din ce take tambayar shi a hankali cikin nuna kulawa,
Bari kawai maryam wanan bakon nawa duk yasa ni gajiya wallahi,
Komai sai ya kwankwance shi kamar tsohon bature, ko likita,
Tausayin shi maryam taji a irin yadda yai magana,
A hankali tace mai kasan ance bakon ka Annabinka so kayi hakkuri dashi har lokacin da zai koma,
Jikin shine yai sanyi a irin yadda maryam din tai bayani kuma gaskiyane zancen ta,
Sai a lokacin yake tambayan ta Anty Dije, wace, ke ta faman tambayar shi tun safe,
Tadan lumshe ido kamar yana ganin ta a fili tace,
Tunjiya da muka dawo take ta tambayar ko yaushe zaka shigo ,
Yanzu haka tana falo a zaune nasan kuwa kila kai take dan jira agurin,
Ya Sallam yace wallahi maryam har na kwanta saboda gajiya,
Gashi kuma naji ido na kekas don rashin barci, saboda gajiya,
Gabobin jikina sai ciwo suke