Showing 27001 words to 30000 words out of 321579 words

Chapter 10 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

ya ji shi, a firgice na kalli saitin inda nake jin maganar sa a hankali cikin sanda na karsa bakin kopar da zata 6ula da kai bayan gidan, a zaune na hango shi kan Waya daga cikin kujerun sha?atawar dake a wurin, a lokacin na dan ji tsoro saboda ban tsammaci zanga mutun a irin wannan lokacin ba, amma sai na dake saboda ina son in san wanene kuma ina son jin wayar mecece ya ke yi a tsakar dare! Ni abunda yafi daure mun kai duk rooms din dake acikin gidan da falo ya rasa inda zaiyi waya sai a backyard, hakan yasa na dasa masa alamar tambaya, aikuwa cikin sanWa na matsa gaban tukwanan furannin da ke a bayanshi na zukunna tare da kasa kunnena ina sauraron shi.

"Kada ku bari ta yi 30 Mins a cikin ramin, zamu iya rasata ne, ku kasance a ankare, da zarar kun ga jami'an sun tafi da shi, kuyi hanzarin ha?a ramin ku Wauko Jinjirar, Sannan bayan kun cire ta daga ciki, Ku kashe daya daga cikin karnukan ku, Ku je ku zuba ?asusuwan shi a cikin ramin"

Lokacin da naji wannan maganar wani irin faduwar gaba na ji duk da ban fahimci inda zancen nashi ya dosa ba, gaba daya nabi na rude amma a haka na toshe bakina na cigaba da sauraron shi saboda ina son inji karashen zancen na shi.

"Bana so a samu matsala, dole sai kun yi taka tsantsan! ka da ku yi gangancin da wani zai gan ku, idan ba haka ba kun sauran sauran,"

Ya faWa tare da yin rejecting call din ganin ya mi?e yasa na yi saurin zu?unnawa ?asa da rarrafe na dinga tafiya cikin sanWa sai da na ga nayi nisa da backyard din, tukunna na mike da sauri na koma dakina na ja kofa na datse.

Aranar na kwana da tunanin wacece naji Uncle Musa yana bada umarnin a ha?a ramin da take a ciki a curo ta? Kuma yace a kashe kare a zuba ?asusuwan shi a cikin ramin? Menene manufarsa ta yin hakan?"

A lokacin gaba daya na ruWe, na kasa gane komai, dakyar bacci 6arawo ya yi awon gaba da ni, tun daga ranar ban kara samun kwanciyar hankali ba, saboda tunanin wayar dana kama Uncle musa yanayi atsakar dare, zuciyata ta dinga azalzalata akan in tunkare shi in tambaye shi game da wayar da na ji yanayi, sai dai tsoro da fargaba sun hanani yin hakan, bayan haka bansawa raina wani mugun abun ya ke yi ba saboda na yarda da Uncle Musa, daga baya ma sai na watsar da zancen na cigaba da yin harkokin gabana.

Taj da ya kasa kunne yana sauraronta, tuni ya mike zaune saboda mamakin daya daure zuciyar shi.

Benazir ta Waura da cewa, "Lokacin da na kudiri Aniyar saina gano koma wanene ya shiga tsakanin Ya shurem da Aisha, da kuma munafukin da ya ?ulla mata makirci a ?asar Germany, Lokacin da na saci hanya na shiga dakin Aunty Zainab na tambaye ta meya faru a tsakanin Dr Shureim da iyayen mu saboda ina zargin bakomai suka faWa mana ba, bayan zainab ta fayyace mini komai, Hankalina atashe na koma Waki na, inata wasi wasi akan wayar nan dana ta6a kama Uncle Musa yana yi a bayan gidan sa, sai da na zurfafa tunanina nayi dogon nazari kafin na gano wayar nan fa da Uncle musa yake yi akan babyn Ya Shureim ce.

Amma abun da ya Waure min kai shine Meyasa Uncle Musa zai yi haka? A raina na ayyana ko dai yana son ya yi mashi hankaline saboda rashin hankalin da ya yi na binne ?arsa, amma kuma dana kara yin tunani sai na gano wannan fa yafi karfin abunda nake hasashe, ganin an dauki kwanaki Uncle Musa baida niyar fallasa shi ya dauki yarinyar, bayan da kunnanshi ya ji irin bakar wahalar da Ya Shureim yasha bayan ya binneta kuma ya yi danasani, to amma meyasa da farko Uncle Musa ya nuna baisan komai ba?

Bayan mun yi waya da Ya Shureim har ya fada mini yasha jaraba kiran layin wayar Uncle don ya nemi taimakon sa, amma baya samun shi, tun daga nan ne na fara zargin da akwai wata mummunar manufa atare da shi.

Ban tunkare shi da maganar ba, saboda a lokacin ka zo mini da maganar zaka turo magabatan ka ayi maganar auren mu, shiyasa na watsar da maganar na bar komai araina. Bayan mun yi aure da kai, A lokacin Daddyna har ya samu nasarar lashe zabe ya zama gwamnan jihar wanda tun da ya hau mulkin bai ?ara lafiya ba, saboda ciwon ?afa da ya matsa mashi, ba irin maganin da ba'ayi mashi ba amma ciwon yaki ci ya?i cinye wa. Wani iko na Allah da zarar an fita da shi kasar waje don a nema masa lafiya sai ciwon nashi ya warke, amma da zarar an dawo da shi Nigeria ciwon na shi yake komawa sabo, a karshe da yan jam"iyarsu suka fahimci ciwon nashi bame ?arewa bane, sai suka shawarce shi da ya aje mulkin yaje ya nemi lafiyarsa, Shekara daya yayi kafin ya sauka, zaman Jahar ya gagare shi silar hakan iyayenmu suka koma Dubai da zama, Ni kuma saboda auren da na yi ne yasa suka barni a Jos.

A lokacin Uncle Musa ya zama Shahararran dan siyasa, ganin sa yayi mini wuya saboda bai cika zuwa Jos ba tun da iyayen mu suka koma Dubai, ya Waga ?afa da zuwa Jos daga Abuja sai ?asashen waje, Kuma duk in na kira phone numbers dinsa bana samu.

A ?arshe na yanke shawarar tura mashi text message, na rubuta mashi komai dana ji ya fadi a cikin wayarsa, sannan na yi mashi barazanar ko dai ya dawo da babyn Shureim, Ko kuma in tona masa asiri a gurin Daddy da Mommy har da ma Ya Shureim din.

Da tura mashi sa?on ko minti biyar ba'ayi ba, sai ga kiran Uncle Musa ya shigo wayata, na yi mamaki sosai saboda tunda nake kira ba'a picking.

Bayan na Waga ko sallamata bai amsa ba ya ce, "Benazir! Ni za ki yi ma kazafi? Yaushe kika ji ina yin wannan maganar? Bayan haka ni miye haWina da yarinyar Shureim da har zansa a binno ta daga rami? Me zanyi da gawa..."?

Bai ?are maganar ba na ce, "Haba Uncle, wlh baka isa ka raina mini hankali ba! Da kunnena na ji ba gaya min a ka yi ba, Wlh babyn Shureim tana araye kuma ta na a gurin ka, Kai kasan inda ka kaita, kuma na rantse idan har baka dawo masa da ?ar sa ba, saina tona maka asiri.."

Ina ?arashe maganar na kashe wayar, cike da saran zai neme ni.

Aikuwa ba zato ba tsammani a yammacin ranar da na yi waya da shi sai ga kiran shi ya shigo waya ta, a lokacin baka a gida, bayan na Waga kiran na ji yace in fito wajen gidana ya turo da escort dinsa yana jirana a cikin Mota.

Na Wan ji fargaba amma da ya ke lokacin ina jin tashen rashin ji, bana jin fargaba kuma bana jin tsoron tunkarar koma uban wanene.

Batare da saninka ba, na bi Escort dinsa acikin mota ya kawo ni guest house din Uncle Musa dake anan Joss.

Bayan na fito daga motar, escort din ya rakani har cikin falon gidan, Ina shiga na taras da shi a zaune saman Sofa ya Waura ?afa daya kan Waya, fuskarsa kwata kwata babu annuri kamar bai taba dariya ba, Nima na haWe rai fiye da yadda ya haWe ta shi fuskar, tunkafin ya bani iznin in zauna na samu guri kan sofa din dake fuskantar shi, na zauna tare da Waura ?afata Waya kan Waya hakan ba karamin daure mashi kai ya yi ba.

Tambayar farko da ya yi min shine in fada masa gurin wa na ji maganar dana fada masa?"

Na ce in har yana so in fada masa to ya fara kawo min Babyn Shureim.

Lallashina ya fara yi duk dan in faWa masa, na sanya kaifi nace wallahi ya daina wahalar da kanshi saboda bazan faWa ba, dole sai ya fara kawo mini yarinyar.

Shu'umin murmushi ya saki tare da cewa bai damu ba in je in fada ma duk wanda zan fadamawa, saboda bani da hujjar da zan iya tuhumar shi, balle har in tona masa asiri, kuma in bi a hankali in ban iya kama barawo ba sai barawon ya kama ni.." na yi dariya hada shewata na ce, "Ka bani mamaki Uncle, ina yi maka kallon mutumin kirki ashe kai din mutumin banza ne! Ka yi zaton bansan komai ba?"

Na faWa ina zare mashi idanuna, a lokacin yanayin fuskarsa ya sauya zuwa tsantsar al'ajabi da rudani.

"Benazir Ni kike kira mutumin banza? Ido cikin ido batare da jin shakkata ba? Kin manta matsayina agurin ki?"

Harara na galla masa, "Na je na fada Uncle, Wallahi Hakkin Aisha bazai ta6a bari ka gama da duniya lafiya ba, Ka cuce ta Ka cuci Yaya shureim ka kuma cuci Babyn da suka haifa"!

Ina magana hawaye na shararowa kan kuncina.

"Ashe dama duk kyautatawar da ka yi mana ba don Allah bane, sai don saboda wata mummunar manufa taka, baiwar Allah Aisha saida ta nuna batason zama agidan da ka kama mana haya a kasar germany saboda hankalinta bai kwanta da shi ba, sannan ta nuna rashin jin dadin ta akan zaryar da kake yi cikin gidan duk weekend sai ka zo ka kwana ga kudi da kake kashe mana, ni da kaina na kare ka agurinta na nuna mata cewa kada ta damu Uncle dina mutunne mai son yin alheri kuma dukiyar ka ta halal ce kasuwanci kake yi, sai daga baya na gano komai, arzikin da kake ta?ama da shi ba ta hanyar halal ka tara shi ba, mu ka raina ma wayau da sunan kasuwanci kake yi, bayan haka ina zargin kana a ?ungiyar asiri ta yan shan jini, kuma kaine ka haWa Aisha da mahaifinta, wato ka yi amfani da damar da kake da ita, a lokacin da kake zuwa ka kwana a gidanmu, sai ka bari dare ya yi sai ka saci hanya batare da sanin mu ba ka ke shiga Wakin Aisha, ka dauketa video da hotuna, wama ya sani ko asiri kake yi mata shiyasa har batasan kana yi mata hakan ba, wallahi ka ci amanar yardar da na yi maka! kuma na rantse da wanda raina yake a hannunshi in har baka dawo mana da babynmu ba saina fallasa asirin ka...."

Tun kafin in ?arasa maganar, Uncle Musa ya doka min tsawa yana huci kamar mayunwacin zaki, saboda tsabar fusata da bacin rai jikin shi ya dinga fitar da gumi, abun da ya daure mashi kai ya kuma Waga hankalinsa shine ta yaya akai duk nasan abunda yake ?ullawa?" Sam ya kasa magana sai huci yake fitarwa, Idanunsa sun kaWa jawur.

Ganin baida niyar yin magana yasa naci gaba da cewa, "Kuma kaine ka shiga tsakanin Yaya Shureim da Aisha, ka yi masa asiri kasa yayi mata fyaWe ba'a cikin hayyacin sa ba, komai dake faruwa kana bin diddiginsu kana samun information a gurin yan le?en asirin ka, Hatta Mahaifinmu baka ?yalesa ba, kana amfani da sihiri gurin juya shi don yabi ra'ayin ka, bayan haka kaine ka turama Daddy videos din Aisha daka dauka tare da kai sai ka 6oye fuskarka don karsu gane kaine kabar fuskar Aisha saboda tsabar mugunta da zalunci irin naka! kuma kai ne shaidanin da ya tunzura mahaifinmu akan karya kuskura ya yarda Shureim ya auri Aisha in ba haka ba zai rasa kujerar da yake nema kuma mutane zasu juya mashi baya saboda abun kunyar da Shureim ya akaita, munafukin Allah kaita faWa masa kauli da ba'adi har saida ka shiga tsakanin daddy da Ya Shureim...".


Ban kai ga ?arasa maganar ba ya katse ni ta hanyar bugun table din gabansa da hannunsa, Jikinshi har wani jijjiga yake yi saboda bacin rai.


"Benazir! Bana so ki jefa rayuwarki a cikin hadari! Ina mai gargadin ki, Tun wuri ki yi gaggawar janye zargin da kike yi mini, tun kafin ki yi danasani" Na yi tsalle na dire na ce, "Wlh Uncle bazan janye ba, saboda ni akan gaskiyata nake, ba zargin ka ni ke yi ba, tabbaci gare ni, kai baka yi mamakin tayaya akai nasan sirrinka ba uhum? Na faWa ina kallon cikin idanunshi, wlh a lokacin ya razana dani ba kadan ba, amma da yake shu'umin mutunne sai ya dake ya tirje akan cewa ba gaskiya nake fada ba, ?azafi nake yi masa.

raina a 6ace na juya zan bar falon ban ma jira ya karasa maganar shi ba, har na kusa fucewa Ya dakatar dani ta hanyar kiran sunana na tsaya ina jiran jin me zai ce.

"Ki fada mini komai kike so a duniyar nan zan yi maki shi, amma maganar zaki tona min asiri bata taso ba, Ki yi watsi da maganar nan, nifa Uncle dinki ne, In kika tona mini asiri kamar kin tona ma family din mu ne, ki dawo mu sasanta tsakanin mu" A hankali na juyo na fuskance shi.

"Baka so zaman lafiya ba Uncle, ai wlh in har kana son sasanci to ka dawo mana da babynmu, ni kuma nayi maka alkawarin babu wanda zaiji maganar nan! Ni ita kadai nake so bandamu da abunda kake aikatawa ba, wannan tsakanin ka da Allah ne, duk wanda ya yi da kyau ya sani, kuma dai akwai mutuwa akwai hisabi kowa zai girbi abunda ya shuka ne..." Dafe kanshi ya yi da tafin hannunsa kamar mai fama da ciwon kai,

"Meyasa kin fiye taurin kai da kafiya ne? Yakamata ki iya bakinki Benazir! Har yanzu bakisan wanene ni ba! Sabo da kaza bai hana in yankata! Wlh zan iya salwantar da rayuwarki, kuma idan na kashe ki na kas??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????he banza."

A lokacin gabana ya faWi na kuma sha jinin jikina amma ban bari ya gane hakan ba, saima na yi dariya na ce, "Idan ma kana tunanin kashe ni shine mafita agare ka, to ka daina, saboda hujjojin dana fada maka ina da su, bani kadai ke da su ba, Nima ina da mutanene da nake yin aiki tare da su, idan yau ka kashe ni, wlh zasu fallasa asirin ka ne duniya tasan me ka ke aikata, ka ga kuwa baka da wata mafita da ya wuce ka bini ta lalama"

Maganar da na yi ta Waga hankalinsa matu?a, Zuciyarshi ta hasala kamar ya rufe ni da bugu haka yake ji.

Har na Waga kafa zan fuce na sake tsinkayar muryarsa a cikin kunne na, "Ko don saboda abun da ke a cikin ki, Yakamata ki yi takatsantsan idan ba haka ba, zaki jefa rayuwarsa a cikin haWari ne..."

Wani irin faduwar gaba na ji, saboda a lokacin bansan ina Wauke da juna biyu ba, cikin sauri na dafe cikina tare da zare idanuna akan fuskar shi, gaba daya na bi na ruWe, Murmushin mugunta ya sakar mun saboda ya gano lago na..

"Benazir, nafi karfin ki nesa ba kusa ba, wlh baki isa ki ja dani ba, ?aramar yar iska mai kwana da wando, saboda baki da hankali ki rasa wa zaki tuhuma sai ni? Kinsan wanene ni kuwa?? Ki fara sanin wanene ni kafin ki yi ja in ja dani, Sannan zan ?ara tuna maki, kina da miji, kina da juna biyu, kina da iyaye, kuma kina da ya ya mafi soyuwa a gare ki, Ina fata Kin fahimci abunda nake nufi???"

Yana karasa maganar ya juya ya nufi up batare da ya sake waiwaye na ba, har saida ya 6ace ma ganina kafin na kawar da idanuna daga barin kallon sa.

Har na dawo gida ban daina tariyo maganarsa a cikin kunnena ba, Saboda hankalina ya tashi sosai, Lamarin Uncle Musa ya fara bani tsoro, na riga da na gane mugun mutunne shi, mara imani, kuma tantirin shaidani nasan zai iya aiwatar da komai don ya rufawa kansa asiri..

Bayan sati biyu na je ganin likita batare da saninka ba, bayan doc yayi mini gwaje-gwaje sakamakon ya nuna ina dauke da ciki na sati biyu, nan fa hankalina ya ?ara tashi kwata kwata ban yi farin ciki da cikin ba a lokacin saboda zai zama rauni na, kuma ina jin tsoron in haife shi saboda fargaban kada Uncle Musa ya salwantar da rayuwarsa, Ko ya Wauke sa kamar yadda ya dauke Wiyar Ya Shureim, wannan dalilinne yasa nayita yunkurin in zubar da cikin Angel, wlh Allah shine shaidata badan bana son shi ba, Kawai a lokacin muna yawan samun sabani da kai saboda bani da kwanciyar hankali, Damuwa tayi mini katutu, kullum cikin zullumi da fargaba nake yi saboda nasan Uncle Musa bazai ?yale ni ba, kamar yadda ya fada dole ya dauki mataki akaina, kuskuren da na yi shine ?in sanar da kai, Na ?i faWama kowa nabar abun a matsayin sirri, saboda gudun kada na faWa ya koma mashi karshe inja ma kaina da kuma dangina don har lokacin ban saduda na kyaleshi kan fito da yarinyar Yaya Shureim ba, ka ji dalilin da yasa a duk lokacin daka kamani ina yunkurin zubar da cikinta ka tuhume ni dalili, sai ince maka bana son ya'ya, kuma bana son cikin saboda zai bata mini shape Win jikina, Amma a zahirin gaskiya bada son raina ni ke yin hakan ba, gaba daya rayuwar aurena da kai wani abun sai daga baya na gane bayin kaina bane, nasan bana jin magana, amma wlh Taj na so mu yi zaman lafiya sai dai na kasa faranta maka, saima cuzguna makan da nake yi hakanan bakai mini komai ba, kawai sai inji haushin ka, da tsanarka acikin Zuciyata, hatta mai aikin gidanmu Janet na ji na tsane ta, laifin da bai kai ya kawo ba idan ta yi mini bana ?yale ta, saina azabtar da ita...."

Kasa ?arasa maganar ta yi saboda kukan da ya ?wace mata, Ha?i?a Zuciyar Taj ta karaya, tsantsar mamaki da al'jabi sun ruke zuciyar shi tamau, duk da sanyin A.c din dake a dakin hakan bai hana shi fitar da zufa ba, jikin shi har tsuma yake yi, wani irin tausayin Benazir ne


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login