Showing 222001 words to 225000 words out of 321579 words

Chapter 75 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

kasa tantance wanda ya aikata masu hakan, yana rufe baki a tsiwace ta ce,


"Ina a cikin hayyacina! Na yi rayuwa a cikin kurkukun ?addara na tsawon lokaci, tun ina da shekara 11 na tsinci kaina a kurkukun, ba irin tashin hankalin da ban gani ba, an yanka mutum an feWe gaba na, an yi mani wankan jini! Na ga abubuwan tashin hankalin da sun isa su saka ni in haukace amman hakan bai faru da ni ba, sai wannan ne zai sa in fita hayyacina har in kasa gane wanda ya aikata mini? Wannan azzalumin shine ya sadaukar da ni a kurkukun, kuma shine ya yi ma mahaifiyata asiri a ranar da ta haife ni ta tafi ta bar ni tsawon shekaru ba a san in da take ba saboda tasan wani sirrin shi da ya danganci kurkukun ?addara, shine kuma ya yi ma Uncle Wina Shureim tare da makwabciyar su asiri saboda ta ce bata son shi Uncle Wina take so sannan kuma yana jin haushin mahaifinta Sheikh Imam. Shi Elder ne! Duk abun da aka zayyana yana aikatawa wallahi..." Kuka ne ya ?wace mata ta du?ar da kanta, duk da yadda ta yi maganar da tsawa har tana nuna Alhaji Musan da hannu ya sa6a ma dokar kotun amma al?alin ya kasa dakatar da ita, gaba Waya kotun ta karaWe da hayaniyar mutane, ?arfin halinta ya matu?ar burge mutane, kuma ta ba mutane tausayi, hatta al?alin ma ta bashi tausayi, umarnin a mayar da ita wurin zamanta al?alin ya bada, kusan a tare Benazir da Owais da Shureim harda kakanninta da ?an uwanta prisoners duk suka mi?e don su tarbe ta, kotu fa ta harmutse da hayaniya, har saida al?alin ya bubbuga gavel Winsa tare da ambaton, "Order, order!" Sannan kotun ta daidaita, daga haka al?alin ya sanar da kotu zata tafi hutu na Wan wani lokacin kafin a dawo a ci gaba da sauraran shari'ar.


Bayan wa'adin da al?alin ya Wauka ya ?are aka dawo zaman ci gaba da sauraran shari'ar. A lokacin lauyan masu ?ara ya bu?aci Benazir, Batool, Shuraim, Ummi da kuma Sheikh Imam duk suka fito ya yi masu tambayoyi, duk suka amsa mashi saidai ba komai da ya faru da su suka faWi ba sun bar wasu abubuwan matsayin sirri, haka shima lauyan dake kare Alhaji Musa ya yi masu tambayoyin ba kamar Batool ya fi yi mata tambayoyi game da komawar su kurkuku, a lokacin har saida al?ali ya bu?aci a gabatar masa Dr Mark, Chief Owais ne ya yi ma kotu bayanin cewa ya gudu amman suna akan binciko shi za su samo shi su kawo shi kotu shima da sauran likitocin dake da sa hannu a case Win.


?arshe dai sai da aka ?ure lauyan alhaji Musa saboda tarin hujjojin da aka gabatar a gaban kotu waWanda ke nuna yana aikata duk laifukan kuma yana cikin elders, tun kan a dawo kan Pravin ya tabbatar ma kotu yana cikin elders don yasan shima za a samu hujjojin da zasu tabbatar da shi ba kamar da ya ga harda vedio recording Win alhaji Musa na cikin Cell Win hukumar Isod aka kunna ma al?alin in da wasu maganganun da ya yi suka tabbatar da laifukan da ake tuhumar shi, ya san shima sun yi maganganun da Owais shiyasa ya saduda, amma ya ce ma al?alin wllh Baba Obie ne ya yaudare shi ya saka shi cikin su ba da son ran shi ba.


Bayan sauraran tarin hujjojin lauya mai ?ara, al?ali ya tambayi lauyoyi masu kare waWanda ake tuhuma kan ko suna da sauran abun da za su ce,


Gaba Waya wutar su ta Wauke, saboda basu da wani ?warin gwiwa ko hujjar da zasu iya kare su, gashi akwai masu son su nemawa dattijon arzi?i sassauci saboda da yawansu mutanan da suke mutunci da shi ne, da ?yar wani bayerabe daga cikin su ya yi ?arfin halin mi?ewa ya ce,


"Your Honor, while we acknowledge the severity of the crimes committed, we urge the court to consider the defendants ages, health, and social status. We request leniency in sentencing."


(Ya mai girma mai shari'a, yayin da muka amince da girman laifuffukan da suka aikata, muna ro?on kotu da ta yi la'akari da shekarun waWanda ake tuhuma, da lafiyar su, da kuma matsayin su na zamantakewa. Muna neman a sassauta hukunci) Ya faWa tare da komawa ya zauna.


Bayan nazarin da Al?ali ya yi, ya Wan numfasa na wani lokaci, kafin ya Wago ya dubi ilahirin mutanen dake a kotun.

Cikin kakkausar murya ya furta.

"I have reviewed the evidences presented in this case, and I find the defendants guilty on all counts, The crimes committed are among the most heinous and reprehensible imaginable..." Karanto hukuncin da kundin tsarin dokokin ?asa ya tanada ga dukkan laifukan ya yi kafin ya dun?ule hukuncin da kotu ta yanke masu ya ce,"The court hereby, sentences each of the defendants to, Life Imprisonment without the possibility of parole (Waurin rai da rai batare da sakin layi ba) a cikin kurkukun ?ar?ashin ?asa."



Sallallamin da jikokin Obie ke yi ne ya cika kotun, ba ka jin sautin komai sai na, Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un.!


Gaban Elders ya shiga faWuwa cikin firgici da kiWima suke ?ara zazzare jajayen idanunsu, ganin yadda reshe ya juye da mujiya, abun da suke yi ma wasu yau sune za a yi mawa, kurkukun ?ar?ashin ?asa da al?ali ya faWa wani kurman kurkuku ne saboda tsaronsa da u?ubarsa ya sa mutane suke yi masa la?abi da kurkukun azaba, saboda mawuyacin abu ne mutun ya zarce watanni batare da zafin jail Win ya lahanta fatar sa ba, ?untatarsa kamar ?abari, baka ganin kowa babu haske cikin duhu, Wan hasken da za'a iya samu na wasu hudoji ne guda uku da ke a saman jail Win, dai dai da wanda zai kawo maka abinci ba zaka gansa ba, ta wata ?aramar ?ofa da ke a jikin ?ofar jail Win su ke zuro maka kwanan abinci, kai kanka ba zaka san an kawo maka abinci ba, in har ba ka jiyo motsin buWe ?aramar ?ofar ba, daga kai sai halin ka a cikin jail Win nan, ba shige ba fuce, da yawa waWanda ake kaiwa cikin kurkukun miyagun ?an ta'adda ne masu haWarin gaske, kamar Elders Win dai.



Al?ali bai dakata ba ya Waura da cewa, "Dukiyar su da suka mallaka ta haramtacciyar hanya, Kotu ta mallakawa waWanda abin ya shafa.." Ya faWa yana kallon bangaren da fursinonin Kurkukun ?addara suke a zazzaune kan kujeru sun yi shiru sun nabba'a, fuskokinsu Wauke da murmushin farin ciki, kamar su zuba ruwa ?asa su sha, sun ji daWin hukuncin da aka yankewa Elders, ransu fari tass, ba don Dg ya gargaWe su akan su nutsu ba in an shiga zaman shari'ar, da ba abun da zai hana su fasa ihun murna.



"?adarorinsu da suka mallaka ba bisa ?a'ida ba, za a yi gwanjon su, abun da aka samu gwamnati zata yiwa ?asa amfani da su..."



Al?ali Salahudeen bai dakata ba, ya ci gaba da cewa, "Bayan haka kotu ta soke duk wata daraja da mu?ami na su, bugu da ?ari, kotu ta bayar da umarnin a saka sunayen su a cikin rajistar masu aikata laifuka ta ?asa!"



Al?ali Salahudeen yana kai ?arshen maganar shi, ya dam?i gavel Win gefensa mai kama da metal hammer ya buga da ?arfi saman table Win gabansa,

(shari'a ta ?are) Zauren kotu ya harmutse da hayaniyar al'umma, masu kuka suna yi, masu murna suna yi, masu 6acin rai suna yi, kowa da abun da ya dame sa.




Prison Officers tare da Soldiers ne suka tasa ?eyar Elders suka fito da su harabar kotun, mutane daddabe da su, ?an Jarida sai neman tattaunawa suke yi da iyalansu sun ?i basu haWin kai saboda tashin hankalin da suke a ciki.


A wata ?atuwar Prison Van za a shiga da su, wasu har sun fara shiga, Musa yana ta gurnani yana tirjewa kamar 6auna, bai aune ba, ya tsinkayi muryar hajiya Sarah a kunnansa. "Ba na ta6a faWa maka ba? In har akwai mai cutar wani tsakanin ni da kai Allah zai yi masa sakayya..." A firgice ya waigo yana fitar da hucin 6acin rai.

Tana a tsaye ta sanya ba?ar abaya da ni?ab.

A hankali ta zame ni?ab Winta, ta watsa mashi kallon ?as?anci. "Hakkin Unaizah ne ke bibiyarka, la'ananne... "


Ta faWa tare da tofa mashi kakin majina saman fuskar shi, ya yi wata zabura kamar zai cafkota sojoji suka rurru?e shi, tare da ingiza shi cikin motar kamar dabba sai waiwayonta yake yi cikin ?unci da ba?in ciki.

Yana tsaka da waiwayon ta, ya hango hajiya Layla a bayanta bakinta washe kamar wadda ta tsinci ha?ori, Waga mashi hannu ta yi, "Allah ya raka taki gona Musa, Allah ya ?ara nauyin ?asa, sai mun haWu a filin hisabi na lahira.."


Ta ?yal?yace da dariya, wani irin ba?in ciki ne ya ziyarce shi kamar ya haWiyi zuciya.


"Ina maka fatan sauka ?abari lafiya, kar ka wani damu zan ci gaba da kula da mommyna.."


A Wimauce ya kai idonsa ga Omar, yana tsaye bayan Chief Owais, wlh kwata kwata bai lura da su ba a kotun saboda bai Waga idonsa ya dubi kowa ba ashe duk sun hallara.


Unexpected ya tsinkayi muryar Sheikh Imam Malik a cikin kunnansa. "Musa ina tayaka murnar kar6ar sakamakon zunubin ka na duniya.. "

Cikin 6acin rai ya wurga idanunsa gurin da Imam Malik ya ke, gabansa ne ya faWi ganin Ummi da Shureim sun saka Imam Malik tsakiya, daga gefen su Batool da Unaisah ne tare da Benazir, sai faman washe baki suke yi.



Ya Ilahi! Kamar ya fasa ihu yake ji saboda ba?in cikin da ya turnu?e zuciyarsa, yana ?o?arin buWe baki ya yi magana Isod soldiers suka turmu?a kan shege bayan motar, suna juyo kururuwar ba?in cikin da ya ke saki.


Daidai Lokacin da Isod soldiers suka fito da baba Obie suna ?o?arin shigar da shi bayan motar, ?a'?ansa da jikokinsa suka kewaye shi, suna ta kuka kamar ran su zai fita.


Ya dinga bin su da kallo Waya bayan Waya, cikin karyewar zuciya, kallon bankwana yake musu, saboda ya san ba zai sake ganinsu ba, wannan tafiyar bata dawowa bace ta mutuwa ce.



Babu Saratu a cikinsu, a gida suka kulle ta a Waki, Momma ma bata halarci kotun ba, da wasu daga cikin jokokinsa.


Da raunannun idanunsa ya dubi ?a'?ansa cikin sanyin murya ya ce, "Ku yafe min, yawancin yaran da nake sadaukarwa na ku ne, wata?il idan kuka yafe mini in samu salama a cikin Zuciyata"


A tare suka haWa baki gurin furta, "Zamu yafe maka, amma ka fara amsa bu?atar mu, ka musulunta baba, muma shi kaWai ne fatan mu, ko mun samu mu dinga saka ka a addu'ar mu."

Girgiza kanshi ya yi zafafan hawaye na sintiri kan fuskarshi ya ce, "Kuma kun sani, tuba na ba zai kar6u ba a wurin Allah, ban tuba ba saida asirina ya tonu? Bayan na sani na take sani?"


Ro?onsa suka dinga yi suna masa magiya kamar zasu haWiyi zuciya, Sheikh imam Malik ya sanya baki ya ce ya taimaka ya amsa bu?atar ?a'yansa shine abu na ?arshe da zai yi musu a duniya, da ya san halin da ya jefa su da bai musa akan bu?atarsu ba, har yanzu suna son shi, kuma musuluncin da zai kar6a kan shi zai yi mawa, shi ba zai ce kar ya musulunta ba, babu wanda ke shiga tsakanin bawa da mahaliccinsa, in Allah ya so shi da rahama sai ya ga ya samu sassauci.."

Kalamai masu tausasa zuciya Imam Malik ya furta masa, amma baba Obie ya kafe akan bakansa.


Sojoji suna ?o?arin su shigar da shi, kwatsam! Muryar Hajiya Saratu ta karaWe kunnuwan kowa.


"Baba! Baba...!" A ruWe ya shiga wurga idanunsa yana ?o?arin ya hango ta, kamar mahaukaciya, babu kallabi ko takalma a ?afafunta, twins suna a biye da ita, hannayen kowan nan su ru?e da mayafinta da takalmanta, ganin halin da take a ciki ne yasa mutane suka dinga darewa suna bata hanya don ta wuce, kowa ya razana da ganin Minister of Health cikin wannan halin.


Hankulan Yayyenta ya tashi, basu san tayaya ta buWe ?ofar Wakin da suka kulle ta ba, wallahi da gudu ta nufi baba Obie tana ?arasowa ta rungume ubanta tana kuka, shima kukan ya 6alle masa, hankulan kowa dake a gurin ya dawo kan su, gwanin ban tausayi, baiwar Allah mace mai rauni, a lokacin ta fidda rai da shi, cikin shesshekar kuka ta ce, "Baba ka yi ha?uri, kulle ni suka yi a cikin Waki shiyasa ban zo ba, meyasa zasu hanani ganinka bayan wannan ne gani na ?arshe tsakanina da ubana. Baba ka yi ha?uri ni dai na yafe maka duniya da lahira, Ubangiji Allah Ya yafe maka, kuma zan dawwama ina yi maka addu'a akan Allah ya yafe maka zunubbanka..."



Kalaman Saratu sun karya zuciyarshi, rungumar da ta yi mashi tasa ya ji sanyi a cikin zuciyarshi.


"Saratu, mahaifin ku ya ?i kar6ar musulunci..."


Sheikh Imam ne ya faWa yana daga bayanta.


Baiwar Allah ita sam ta manta baban nasu ba musulmi bane, hada guzurin cazbaha ta kawo mashi wadda zai dinga yin tasbihi da ita a cikin jail.



Maganar Sheikh Imam Malik ce ta tunasar da ita, nan fa ta fara ro?on shi tare da dam?a mashi casbahar a cikin tafin hannunsa ta dun?ule masa yatsunsa don kar ya yada ta.


"Baba na ro?e ka ka musulunta saboda tsoron Allah baba, ba don saboda mu ba, don Allah ka taimaka ma rayuwana..." Tana kuka hada majina, har lokacin bata raba jikin ta daga na shi ba.


Tunkan ta ji amincewar shi ta shiga karanto mashi kalmatusshahada, cikin karyayyar murya ya dinga amsa mata har ?arshe.


Gaba Waya suka haWa baki gurin furta, "Alhamdulillah, Allahu Akhbar..."

kwata kwata ba su yi zaton zai iya furta Kalmatusshahada ba.

Suna kuka suka ce, "Mun yafe maka baba, duniya da lahira, Ubangiji Allah ya yafe maka."


At lease ya samu sassaucin radadin da yake ji a cikin zuciyar shi ganin ya faranta masu.


Sheikh Imam Malik ya tausaya masu bai san sa'ar da hawaye suka fara zarya kan kuncin shi ba.


"Baba na canza maka suna, daga yanzu Imam zamu dinga kiran ka ba Obinna ba..."

Cikin kuka ta faWa, murmushi ya yi, idanunsa akan fuskarta a lokacin ta Wago da kanta.



Ya sumbaci goshin ta, ya mi?a ma Hateem hannu ya matso kusa da shi yana share ?wallarsa, shima ya sumbaci goshin shi tare da hugging nasa, Sharafudeen ya matsa ya rungume shi, tare da sumbatar goshinshi, da sauri Deen da Lateef suka rungume shi, suma ya sumbaci goshin su, Abdul Razak ya matsa ya sumbace shi, Sir Mubarak ma ya je ya rungume shi sosai.


Owais dake kallon komai shima ya zo ya yi hugging nasa tare da sumbatar goshinsa, ?an jarida da ke kallon komai sun ma kasa mayar da hankalinsu kan aikinsu, sai aikin share hawaye suke yi, basu ta6a ganin soyayya tsakanin Uba da ?a'ya irin wannan ba, kowa al'ajabi ya ke yi, duk irin cutarwar da ya yi masu amma basu daina son shi ba, wannan bakomai bane face Ikon Allah.


Cikin raunanniyar murya ya furta, "Allah Ya yi maku Albarka..." Ya mayar da dubansa kan Imam Malik ya ce, "A matsayina na mahaifinsu, na baka amanar su, na mallaka maka ?a'?ana, ka maye musu gurbina, ga autana duka na baku amanarta, ita kaWai ce mace a cikin ku tana da rauni, don Allah Imam ka amshi tayi na ba don mugun halina ba... "


Cikin sanyin murya sheikh Imam yace,

"Na kar6a hannu bibbiyu Imam, zan ru?e maka amanar su, In sha Allah bazan bari su yi maraicin Uba ba..." Murmushin ?arshe Baba Obie ya sakar musu, daga haka sojoji suka shigar da shi cikin motar.



Wani irin kuka hajiya Saratu ta fashe da shi, ta zube kan gwiwowinta tana ambaton, "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..!"


Cikin sauri yayyenta suka rurru?eta tare da mi?ar da ita tsaye, Hateem ya rungumeta a ?irjin shi, suka haWu suna lallashin ta cike da ?arfin hali.


Suna a wannan halin, suka jiyo kukan Praveen kamar ?aramin yaro, yana ta sambatu yana ambaton sunan Hajjaty da ?a'?anshi, kusan a tare suka kai duban su kan shi, yayin da Prison Officers suka nufi Wayar motar kurkukun, sai tirjewa yake yi, idanunsa jawur ya ke duban twins Winsa da Saratu da ta Wago da kanta daga ?irjin Hateem tana duban shi.


Haushin shi da tsanar shi ne ya cika zuciyar su, babu alamun sun ji tausayin shi.


Zaid ne kaWai ya Wan tausaya mashi har ya je gaban shi ya Wan rungume shi, Sir Mubarak ya nufe shi yana zura hannu cikin trouser pocket Winsa ya zaro wasi?ar da Hajjaty ta bayar a bashi, ya zura mashi a cikin aljihun gaban rigar shi sannan ya ce, "Hajjaty ce ta bayar a baka, bata samu damar zuwa ba, tana a kwance gadon asibiti tana jinyar zuciyarta, idan ka samu halin karantawa ko a cikin jail ne ka daure ka karanta..."


Wata irin karayar zuciya mai haWe da nadama ce ta riske shi, bai ?ara samun damar furta kalma ba, Prison Officers suka tura ?eyarsa cikin Motar.


Iyalan ?an Iya ne kaWai ba a samu wanda ya halarta ba, sun fi kowa fusata, dama can ba son uban nasu suke yi ba.


A kan idon kowan nan su motocin suka fuce daga arean kotun.


Kafin mutane su watse, Al?ali Salahudeen sai da ya nemi ganawa da ahalin Obinna, musamman ya zauna da su a office Winsa bayan ya bayyana musu irin halin da ya shiga na jin abun da Obie ya aikata, ya kuma jajanta musu sannan ya jinjinawa Owais da ?an team Winsa bisa ?o?arin su na kamanta adalci da gaskiya.



Kafin barin su kotun, chef na gidan Owais wanda ke kula da Wakin Natasha ya kira Owais a waya cikin tashin hankali ya faWa masa cewa ya je kai mata abinci, ya iske ta kwance ?asa rai hannun Allah, tana yin bleeding ta hanci da baki, yanzu haka sun garzaya da ita Obie Hospital.


Hankalin Owais ba ?aramin tashi ya yi ba, a hanzarce ya faWa ma su Ummi abun da ke faruwa da Natasha, ya ce ma Sajeed da Sajeeda su shiga motarshi, a gaggauce suka shige cikin motocin su, a lokacin Sarah ta ji komai itama


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login