Showing 18001 words to 21000 words out of 321579 words

Chapter 7 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

baby cikin gidan, batare da sanin kowa ba, Ya nufi daki da ita Ya kwanta kan gadonshi yayin daya rungume Yarshi a kirjin shi, Zuciyarshi cike fal da bakin cikin abunda yayi ma Aisha shine silar komai, yaji takaicin tafiyarta, yaji kunci da radadin rasata da yayi.

Dakyar ya samu nutsuwa, ya buWe fuskar babyn ya zuba mata idanunshi da suka kada jawur yadinga kallonta kamar zai hadiyeta, A hankali ya sumbace ta a saman forehead dinta da cheeks dinta, wani irin tsantsar sonta ne ya lullu6eshi kamar ya mayar da ita cikin shi, a kalla ya shafe rabin awa yana kallonta, aranshi ya ayyana inama ace ta hanyar aure suka same ta da sai yafi kowa farin cikin zuwanta duniya, amma ahakanma Ya gode ma Allah daya bashi ita, addu'o'i sosai yayi mata har yai mata huduba da sunan*FATIMA BATOOL*

Bai tashi sanin yana a cikin musibaba, Saida Ta farka tsakar dare ta fara tsala kukan Yunwa, A firgice ya farka ya rasa ina zai tsoma ranshi yaji dadi duk yabi ya RuWe, ya sungumeta akan kafadarshi ya sauko daga kan gadon ya dinga zarya da ita a tsakar dakin yana lallashinta haWi da jijjigata.

Sakamakon kukan data dinga tsalawane Yaja har mutanan gidan suka farka daga bacci, Cike da mamakin jin kukan jinjira a cikin gidansu.

Da gudu Suka nufo Dakin Dr shureim Alhaji ubaid da hajiya layla sai Mai aikinsu zainab, suna shigowa suka iske shureim ya rungume baby a kirjin shi.


Cike da mamaki suka tambaye shi yar wacece? Donsu kwata kwata basu san Aisha ta haihu ba, sun dai san abunda ya faru tsakaninta da shureim.

Jin yayi shiru bai basu amsa ba yasa hajiya Layla ta doka mashi tsawa tace shureim ba kaji ina magana ba? Yar uban wacece wannan"?

Cikin sanyin murya yace"?ata ce, babyn da Aisha ta haifa mince, Baba Imam ya koreta daga gidansa, shine ta kawo min ita jiya da daddare"

Bai ?are maganar ba Hajiya layla tayi tsalle ta dire tace"Wlh bazata sa6u ba! Shegiyar zaka kawo mana acikin gida? So kake kaja mana surutu agurin mutane? Wato shi uban nata ya koreta saboda gudun abun kunya sai mu zaka jajubo mana annoba ka kawo mana agida? Saboda baka da hankali"?


Ta inda take shiga bata nan take fita ba, Kamar zata rufesa da bugu, Kalamanta sun Kona ransa, musamman data kira yarsa da sunan shegiya, bai kula ta ba hankalinsa na akan fatima dake ta kuka surutunsu Ya kara hargitsa kwakwalwarta duk tabi ta rude ga yunwa tana ji.

Alhaji Ubaid Yace"shureim, kayi hakuri da abunda zance, badan bana son jininka ba, sai don gudun abun kunya, kuma kaga an kusa fara zabe in har maganar nan ta fita wlh za ka ja min asara ne, don Allah ka dauki yarinyar nan ka kaita gidan marayu su kula maka da ita, Inyaso sai ka dinga zuwa kana dubata..."

sai a lokaci Ya fuskance su da wata irin fusatacciyar murya yace"Wan ku ne shegen da yayi wa uwarta ciki ta haifeta, wallahi ba inda zan kaita! Ban taba sanin baku da imani ba sai yau da kuka nuna min, Yarinyar nan koba dan kasancewarta jinina ba Yakamata ku tausayamata, Jaririya ce fa? Ta rasa mahaifiyarta, ni kadai na rage mata, ya kuke so tayi da rayuwarta ne"? Idanunsa cike tab da kwalla yai maganar.

Aunty Zainab tayi kokarin tayashi fadan amma Hajiya layla ta koreta daga dakin ta fuce tana kuka saboda sun bata tausayi.

Kusan dare suka raba ana abu daya, kowa yana akan bakanshi.

Hakika dr shureim Yaci wahalar Iyayenshi, kullum sai sunyi barazanar kashe mashi ?a in har bai fitar masu da ita daga gidan ba amma Yakiya.



wulakancin yau daban na gobe daban Sun daura mata karan tsana ba gyaira ba dalili, Aunty zainab ce ke shayar mashi da ita a boye batare da sanin su ba.

Hajiya layla har Waukar babyn tayi batare da sanin shi ba, ta fuce da ita daga cikin gidan, a lokacin yaje masallaci yin sallah sai da ya dawo ya duba dakin shi bai ganta akan gado ba, ya fito arude yana nemanta, Aunty zainab ce ta fada mashi taga hajiya layla ta shiga dakin shi, tana da tabbacin itace ta Wauke ta, hankalinsa ya tashi, ya dinga kiran layinta bata picking, time data dawo cikin motarta ta shigo gidan ya nufeta yana huci yace ina yarshi tace tabada ita sadaka.

Ji yayi kamar ya dauketa da mari, ya dinga rokonta akan ta dawo mashi da yarshi tayi banza ta kyale shi, yai hakuri Ya jira time da Alhaji ubaid ya shigo gidan, ya tuntube shi da maganar ya dinga rokonsa akan ya yi ma mommynsu magana ta dawo masa da yarsa, Alhaji ubaid bai kulasa ba saima yace tayi abunda ya dace.

rai a6ace Ya nufi Kitchen Zainab tana a ciki tana yin girki taga yashigo ya dauki wuka Ya fita da ita aguje tabi bayanshi.

A lokacin Hajiya layla tana a zaune kan kujera tana danna waya batai aune ba, taji ya Waura mata wuka a akan wuyanta, ta zare ido gabanta na faduwa, shureim yana huci yace"kodai ta fada mashi inda takai mashi baby, ko kuma ya kasheta"

adabarbarce tace"nashiga uku shureim ni zaka kashe? Mahaifiyarka? Saboda kawai na kawar da ?azantar zina daga cikin gidan mu"?

Ihunta da Alhaji Ubaid ya ji yo ne yasa shi watso wa da gudu Yafito daga dakin shi ganin abun da Shureim ke kokarin yi ne Ya tada hankalinsa kafin Ya karaso Shureim Yace"kana karasowa zan hada dakai in kashe!" ba arziki Alhaji ubaid Yaci burki yana lallashin shi akan ya aje wukar zasu dawo mashi da yar shi, Zainab tana kallon komai dake faruwa, ko kadan bata sa baki ba, saboda taji dadin barazanar da Shureim yayi masu, tun da su ba Allah aran su.

Hajiya layla data gama tsorata cikin shakakkar murya ta fada mashi sunan gidan marayun data kai Batool.

Sakin wukar yayi da gudu Ya fuce daga gidan Cikin motar shi Ya tafi.

Kafin marecen ranar sai gashi ya dawo da babynsa, ya rungume abunsa a kirjin shi, baiwar Allah tayi kuka har ta gaji idanunta sun kada jawur dakyarma ya samu Caregivers din dake rainon yaran suka bashi ita, saida ya basu cin hanci harna Dubu dari shidda kafin suka damka mashi ita.

Abun da ya Waurewa shureim kai, Mugayen halayan da iyayensa suka sauya wanda ada ba haka suke ba, har kwara hajiya layla yasan tunfil azal bata da mutunci, batason talaka, ta tsani talauci, ga girman kai, amma mahaifinsu Alhaji ubaid ba halinsa bane, Shi shaidane babansu mutumin kirkine amma tunda ya faWa harkar siyasa ya canza shima, Ya rasa gane meke faruwa ne? Duk wannan badakalar da aka sha Benazir bata sani ba, ko awaya inta kira su don su gaisa ko suka kira donsu gaisa da ita babu wanda ya taba gigin faWa mata.

don wlh da ace ta sani zasu sha ruwan mamaki saboda masifarta, har hajiya layla data gado shakkarta take ji, zata tsayama shureim ne kuma babu wanda ya isa ya Waga ma yarsa yatsa agidan.

Shureim harya fara tunanin sun hakura, ganin kwana biyu basu bi takanshi ba, hakan ba karamin dadi yayi mashi ba, ashe wata wutar bala'en ce zasu kunna mashi.


Alhaji Ubaid yasa aka kulle mashi bank account dinsa, Ya hana shi abincin gidan shi, duk wani abu da yayi mashi a matsayin uba saida ya kwace shi, hada key din motarsa ya kwace ya kasance baida ko sisi, ita kuma zainab da hajiya layla ta gano tana shayar da yarsa kuma tana satar abinci aboye takai ma shureim aikuwa tayi mata shegen duka da girmanta da komai ta kuma koreta daga gidan gashi bata da kowa a nigeria danginta da komai suna a egypt haka tayi ta gagari cikin gari.

Dr shureim ya shiga matsananciyar damuwa, da shi da yarshi suna a tsaka mai wuya, Ya rame yayi duhu, Itama jinjirar ba lafiya, ga yunwa da rashin bacci, kwana su ke yi idon su biyu har rokon su yayi kan su taimake shi kada ya rasa yarshi suka kiya saima su ka ce In har yana so su mayar masa da komai nashi da suka kar6a to ya mayar da Batool gidan marayu, kusan kullum sai ya jaraba kiran layin Uncle musa don ya fada masa halin da ya ke a ciki saboda yasan shi kadai ne zai goyi bayansa sannan ya taimaka masa amma ko ya kira layin a kashe ya ke samun shi, baisan ya zaiyi ba, ga Hajiya layla tace in har ya kuskura ya kira wani nata don ya taimaka mashi Allah ya isa bata yafe ba shiyasa ya kasa kiran Ammin su.


Baida wata mafita daya wuce ya gaya ma Allah, A karshe ya dauki yarsa yabar masu gidan.

Ko a jikinsu damuwarsu daya kada su rasa dan su amma donta yarinyar basu damu ta mutu ko tayi rai ba.

Baisan Ina zai nufa da ita ba, a wannan zamanin bakowane zai kula maka da dan ka tsakani da Allah ba, gashi bakowa ya sani a joss ba, saboda rabi da kwata na rayuwarsa a gurin amminsu yayita can Kasar egypt.

Tafiya ya ke yi Jikin shi ba kuzari, ya rungume babynsa a kirjin shi, Zuciyarshi cike fal da tunanin makomar rayuwar yarsa.

Tuntana kuka har ta gaji tayi shiru bacci ya Wauketa, kwatsam aka fara ruwan sama tamkar da bakin kwarya, ya rasa ina zai sama masu mafakar da zasu zauna, Baiwar Allah tana tsaka da baccinta ruwa ya farkar da ita, Ta dinga tsala kuka ya rasa ina zai kaita don kada ruwan yai mata illa.

a karshe dai ruwan gaba daya akansu ya ?are, Har dare ba adaina ruwan ba, saida daren Ya tsala ruwan Ya dauke a lokacin Ya ma fidda rai da ita saboda Zuciyarta ta daina bugawa Jikinta ya saki.

Anan ne ya yanke shawarar binneta, Saboda yaga baida wata mafita, in har ya barta wahala zata cigaba da sha, mutane ma ba zasu kyale ta ba za'acigaba da tsangwamarta ne tunda har iyayensa sun shegantata sun kirata da kazanta inaga mutanan waje?

Kowa ma zai samu kwarin gwiwar cuzguna mata ne idan ta girma, kwara ya saukaka mata ta huta itama, yasan in ta mutu Allah zaiji kanta.

A lokacin kwata kwata baya acikin hayyacin shi kamar ya fara zaucewa, Da hannayenshi Ya ha?a rami, Ya sakata a ciki ya kwantar da ita yayi mata addu'a, Yana kallon yatsun kafafunta dake motsi alamar bata mutuba, amma Ya rufe ido saboda bayason taci gaba da shan wahala Ya rufe mata kasa a jikinta ya daddale gurin da kafafuwan shi, anan ya zauna kamar mahaukaci yaci gaba da sambatu shi ka Wai daga bisani ya suma akan kabarin ta.


Bayan sati Biyu da afkuwar lamarin, Dr shureim Ya farka a gadon asibiti, ya fara lalubar Yarsa Yaji shiru babu ita a jikin shi, Yabi ya rude hankalin shi Ya tashi, ya sauko daga kan gadon Yana fadin Ina yarsa! Ina fatimarsa! Ina batool dinsa! Tana Ina"?

Likitan dake dubashi Ya rurruke shi Yana kokarin kwantar masa da hankali, aikuwa ya bangaje shi da karfi har saida doc din Ya kife kasa.


Hajiya layla Da Alhaji Ubaid da ke a waje suna jiran tsammani, muryarsa da suka jiyo daga cikin dakin yana kwala ma batool kira yasa suka yi saurin shigo cikin dakin, yana ganin su ya nufe su yana tambayar su Ina yarsa take? Ta na ina? Hajiya Layla tace suma basu san Inda ya kai ta ba, abun da ya faru bayan ya bar gida suka baza jami'ae don su nemo shi, cikin sa'a jami'an suka tsintoshi a sume a gaban wata bishiya, amma basu ga yar shi ba, shine suka garzaya da shi asibiti, Yau sati biyu kenan baya a cikin hayyacin shi.."

sai da tayi wannan maganar ya tuna da abunda ya aikata ma Batool, wani irin jiri jirin tashin hankali Ya gani acikin idanun shi, ya dinga ambaton inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un kamar maganarsa zata kare! wai mike faruwa da rayuwarshi kamar wanda akayima jifa? bala'i daga wannan sai wannan.

Bai karasa jin zancen ba, Ya watsa da gudu Ya fito daga asibitin, suka biyoshi a cikin motar su, Ya dinga gudu kamar zai fadi kasa, har titi Ya hau mota ta kusa bankade shi Allah ne dai Ya tsare shi dakyar Ya gano gurin da ya binne ta, Ya zube kan gwiwowinsa, Jikinshi na kerma Ya ha?a ramin wani irin faduwar gaba Yaji ganin kasusuwanta, Harta mutu ta rube kashinta kadai ya rage, daddafe kanshi yai da tafukan hannayen shi saboda matsanancin ciwon kan da yaji, nan Take Ya yanke jiki ya fadi a sume.

A lokacin motorsu Alhaji Ubaid ta karaso gurin da yake, bayan sun fito suka taras da shureim rai hannun Allah, ga ramin daya ha?a abude sai kasusuwa birjik a cikin sa.

Basu tsaya bata lokaci ba, Alhaji ubaid Ya dauke shi ya shigarshi da shi cikin motar, suka koma asibiti da shi.

Tun daga wannan Lokacin shureim bai kara hankali ba, ya zama mahaukacin karfi da yaji, bayagajiya da sambatu yana fadin wayyo Allahana, na kashe Batool, da hannuna na binne ta acikin rami, Batool ta mutu ta zama kashi, Naci amanar da aisha ta bani, Allah bazai barni ba"

sai da takai ga ko sallah shureim bai iyayinta cikin nutsuwa, A lokacin Hajiya layla da Alhaji Ubaid sun ji tausayin shi sun kumayi danasanin tilasta mashin da sukayi akan yarinyar gayanan sun ja ya binneta ta mutu, shi kuma Ya haukace.

saida ya shafe wata daya bai dawo daidaiba, A lokacin Hajiya layla ta dawo da zainab mai aikinsu gidan tana daya daga cikin masu bashi kulawa duk da baya acikin hayyacin shi tayi kokarin tambayarshi meya faru? A haukan nashi Ya fayyace mata komai, tayi bakinci sosai sai dai bata ga laifin shi ba, saboda tasan me yaja mashi ya aikata hakan, haka ta dinga kokarin kwantar mashi da Hankali.

Ganin za6e ya kusa ga mutane sun fara yi masu surutu akan Halin da shureim ya shiga duk da kullan da sukeyi mashi amma an asamu wasu daga cikin ma'aikatan gidan sun fitar da sirrin su a boye, Hakan Yasa suka yanke shawarar tura shi Egypt, to a lokacin ya Wan fara dawowa hayyacin shi tunkafin ma suje mashi da maganar ya tattara yanashi yanashi batare da saninsu ba ya tafi egypt saboda bayason zama tare da su sun fita aranshi, bayan ya isa ne ammin su ta kira hajiya layla ta sanar da su shureim yazo sai dai bata gane meke damun shi ba, ko magana ba ya iya yi mata.

Hajiya layla tace ta taimaka ta lallashe shi sannan ta bashi kulawa, ya samu tabin hankali ne sakamakon buguwar da kanshi yayi garin tukin mota ya yi accident har jinya yayi a asibiti.

Karya da gaskiya ta dinga fada mata har ammi ta yarda da maganarta tace in sha Allah zatayi kokarin bashi kulawa, hakan ba karamin dadi yayiwa hajiya layla ba.

Bayan komawarsa egypt ya gaza jure radadin da zuciyarshi keyi mashi kullumne sai yayi mafarkin Batool a cikin rami tana kuka, Hakan ya ?ara dagula mashi lissafi har takaishi ga fadawa harkar shaye shaye ya zama cikakken dan kwaya.


_(Kunji alakar dake atsakanin Ummi da su Benazir da kuma shiekh Imam malik, da kuma kaddarar datayi silar rabuwar su da ita, Bayan haka duk wata sa'insa da dr shureim yakeyi da iyayenshi bayan dawowarshi daga egypt a lokacin dayaji sau?i ya dawo hayyacin shi ya kuma daina shaye shaye, wannan rashin jituwar ta samo asaline daga abunda sukayi mashi, yana yawan furtawa hajiya layla sune silar masifar daya shiga, ita kuma tace basu bane saboda lokacin da zai aikata bai yi shawara da su ba, bayan haka Hotunan da yake yawan kallo acikin wayarshi hoton mutun biyune! Hoton Aisha da kuma hoton Yarsa Batool daya ta6a dauka a wayarsa, ko bayan dawowarsa Nigeria bai yarda yarsa batool ta mutu ba, saboda a lokacin duk in zaiyi mafarki da ita araye yake ganinta ba amace ba, sannan kasusuwan daya gani a cikin kabarinta yana kokwanton bana mutun bane kamar na kare ne, bayan haka yana mamakin yarda tayi saurin zama kashi in two week da binne taW' shiyasa yake zargin akwai wata makarkashiya, amma daga baya ya hakura da tuhumar iyayensa Ya dauki dangana, Benazir bata tashi sanin abunda Ya faruwa ba saida ta baro gidan Uncle musa aranar ma tare da shi suka zo joss din da iyalinsa Sara da kanwarsa Hajiya laura dake zaune agidansa, anan sukaji komai daya faru abakin Alhaji ubaid sai dai bai bayyana masu ukubar da su ka yiwa shureim da yarsa ba, sun dai fadi laifin shureim na binne Batool da yayi, Uncle musa ya nuna rashin jin dadin shi har fada saida yayi masu akan sakacin da sukayi har suka bari shureim ya binne yarsa, Benazir kuwa saboda bakin cikin abunda shureim yayi ma Aisha da kuma yar daya binne saida tayi jinya gadon asibiti saboda tana da fusatacciyar Zuciya, bayan da aka sallame ta daga asibitin ne, ta taka taje har gidansu anila ta rufe ta da fada akan boye matan da tayi, anila tay ta kokarin fahimtar da ita cewa ba laifinta bane, Aisha ce ta hana ta sanar da ita saboda gudun abun da zai biyo baya in mahaifinta yaji ta fitar da sirrin, aranar saboda fadan daya kaure tsakanin Benazir da anila saida mami da abie suka rabasu dakyar bayan sunci uban juna, abie ya tambayi meya hadasu faWa, anan Anila ta fayyace masu komai, hankalinsu ya tashi matuka basuji dadin abunda ya faruwa ba, Ita kuma Benazir acikin labarin da Anila tabada nan taji wani abu daya Waure mata kai tamau har ta kudiri aniyar saita gano koma wanene ya shiryama Aisha da yaya shurem makirci, saboda ta gane ba laifinsu bane, tuggune aka shirya masu, musamman ita Aisha da aka yi mata kullalliya tun a kasar germany, bayan Benazir ta dawo gida, batare da sanin kowa ba, ta shiga dakin zainab mai aikin su ta tsare ta da tambayoyi akan ta fada mata meye faru tsakanin shureim da iyayen su saboda taji aranta bakomai suka sanar da su ba, anan zainab ta fayyace mata komai, bayan ta baro dakin zainab din ta koma nata dajin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login