Showing 69001 words to 72000 words out of 321579 words

Chapter 24 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

dan mayafin da ta yafa ma kanta tuni ya bar jikin ta, kwakwalwarsa ce ke kokarin tariyo masa abun daya faru!



Nannauyar Ajiyar zuciya ya sauke, tunawa da komai daya faru tun farkon shigowarta, yayi mamakin baccin daya sha, wani iko na Allah kwata kwata babu inda keyi masa ciwo, saima wata lafiya dayaji a jikin shi, kamar ana dawo masa da kuzarinsa, yana ji aransa silar kira'ar qur'nin da Unaisah tayi mashi ne, kuma dama shi qur'ani waraka ne.


Slowly ya zame hannayensa daga kan gefen fuskarshi, Ya daura tafinsa saman lallausar sumar kanta da aka kitsa, A hankali Yake shafa gashin nata har na tsawon mintuna, kafin ya dan dago da face din tata, hakan ne ya bashi damar kallon fuskarta dakyau, wata irin nutsuwa ce ke shigar shi, yayi fatan ace bai farka daga baccin daya dauke shi ba, saboda kwanciyar hankalin daya samu..


Tunawa da sallar asubahi da bai yi bane yasa shi saurin mikewa ya sauka daga kan gadon, shaf shaf ya fada toilet yayi wanka kafin Ya dauro alwala, Ya fito waist dinsa daure da towel, Ya nufi walk in closet dinsa Ya shirya kansa cikin jallabiya, kafin ya nufi prayer corner dinsa after Ya gama sallar, yayi addu'o'i har da hawayensa, kafin daga bisani Ya mike Ya nufi gadon, a hankali ya kwanta yana fuskantarta, yaso ya tashe ta tayi sallah sai dai ya kasa yin hakan saboda bai son ya katse mata baccin ta, ya lura kamar ba ta samu isasshen bacci, ya fahimci hakanne saboda alamar daya gani saman kwarin idanunta da sukayi ja, kuma yasan shine silar shigarta halin da take a ciki, tsantsar tausayinta da kaunartane suka mamaye zuciyarsa ko gajiya da kallon ta ba ya yi, mutumin da saboda kamun kansa da gujewa abun da zai sabawa mahaliccinsa bai ta6a bari ya ke6anta kan shi da macen da ba muharramarsa ba, balle har su hada shimfida, amma yau saboda halin da yake a ciki ya kasa ankarar da kanshi kuskuren yin hakan saboda a buqace yake da son samun wanda zai kwantar masa da hankali..


Akan idonsa ta fara yamutsa pinkish lips dinta da suka bushe ?amas.



ziraran eye lashes dinta sai kerma suke yi, Tunawa yayi da ranar farko daya fara ganin fuskarta lokacin data kira sa video call da kuruciyarta, a ranar kasa runtsawa yayi saboda tunanin yar tahalikar nan..


Da alama baccin nata ya ?are, ?o?ari take ta bude idanun ta da suka kumbura saboda kukan da ta sha, daura tafin hannunsa ya yi a saman gefen fuskarta, a Wan firgice ta zare idanun ta.



kaitsaye suka shiga cikin nashi wani irin shock taji ganin Chief agabanta, ganin yadda ta ruWe ne yasa shi sakin tsadaddan murmushin nan na shi, baisan ya ?ara jefa ta a rudu ba, duk tabi ta dabarbace sam takasa ci gaba da kallonshi, saboda yanayin data tsinci kan ta..



"Na samu bacci silar karatun alkurnin da ki ka yi min, I can't thank you enough baby..."

ya faWa tare da dan shafa sajen gefen fuskarta da ya kwanta luff, shiru tayi tana jin yadda zuciyoyinsu ke bugawa saboda kusancin da suke da juna..



 I m so sorry, I made you cry, nima bada son raina ba, banso kika ga raunina ba, na kasa jure abunda ke damuna ne.." ya fada yana kare mata kallo.



In a cool voice tace"ba laifin ka bane, daga zuciyarka ne, I understand that something bad happened that put you in this difficult situation of worry, but I want you to know that I will never leave you in such a situation, It is my duty to calm you down, and I will help you find a solution after that, I will remind you, no matter what, kada ka bari hankalinka ya gushe, jarumtakar nan taka da nutsuwarka su nakeso na gani atare da kai, komai ya same mu arayuwa muyi hakuri mu mika lamuran mu ga Allah shine zai nema mana mafita".



har cikin ranshi yaji dadin kalamanta masu sanyaya zuciya, harya fara tunanin irin rayuwar farin cikin da zasuyi idan sukayi aure, zai more rayuwarsa saboda samun mace tagari kamar ta.



"Ka fada min meke damunka pls, amma idan sirrinka ne da bai kamata in sani ba, to kada ka sanar dani, kuma koda baka fadamin ba, nayi maka alkawarin zan tayaka da addu'a Allah yaye maka damuwarka ya kuma kawo maka mafita acikin lamuranka"



bai san sa'adda ya saki murmushi ba wanda har sai da fararen hakoransa suka bayyana, saboda dadin kalamin ta, ita kanta batasan ya akai ta samu kwarin gwiwar furta masa su ba, kamar ancire mata jin nauyin sa hada karin tausayinshi daya mamayeta.



 My secret is yours, Unaisah, Even if no one understands me, I m sure you will understand me, sai dai bana jin zan iya fada maki abunda ke damuna a halin yanzu saboda banaso na daga hankalin ki, amma nasan zaki ji agurin daddynki idan na fada masa" cike da kasala ta dago da kanta, ta fuskance shi idanunsu suka shiga cikin na juna, hakan yasa numfashinsu ya dinga gaurayewa dana juna saboda qarin kusancin da suka samu da junansu..


Tsananin tausayinsa ne ya kara kamata, ganin yadda cheeks dinsa su kayi suntum, reddish eyes dinsa sun kara ciza launinsu hasken ya rune zuwa ja, bakomai take hangowa cikin idanun nasa ba face tsantsar damuwa da tashin hankali.


Cikin muryar raWa ya furta

 Thank you for taking care of me, I can't wait to have you as my wife& 

kunyar shi ce ta kama ta, dama dakyar take jure kallansa saboda nauyinsa da take ji..



"Ku yi hakuri, jiya na bar ku kuna ta jirana, ban kuma kira na fada maku bazan dawowa ba, banji dadi ba"



"Kada ka damu, komai ya wuce.."


"Kin lura da time..." ya fada tare da nuna mata katafariyar agogon dake manna jikin bangon dakinsa .. ' kallo daya tayi mata tare da jinjina kanta..

"Ki shiga toilet dina ki yi alwala...


Saukowa tayi daga kan gadon ta nufi toilet dinsa, tana tafiya kamar wadda ?wai ya fashe mawa akai, gabanta nata faduwa, kwata kwata bata son shiga toilet dinsa saboda glass wall din dake gare sa wanda ke a waje na iya ganin komai na cikinsa, batasan ya zatayi amfani da shi ba, abun da take ma zullumi kada Chief ya gane mata budurcin ta anata wautar =??

Agaban kofar toilet din ta tsaya tana dan zazzare idanunta kamar wadda tayi ma sarki karya fadawa suka turketa.


ita a wurin ta kauyacine ta tambaye shi ya ake amfani da toilet din, kanta ya kwance, ranta ne ya bata ta juya baya taga idan yana kallon ta, juyowar da za ta yi keda wuya, idanunta suka sauka akan nashi yayin da yake gyara kwanciyar shi.

Idanunta ne suka dinga nuna mata kamar murmushi ya ke sakar mata, zuciya da sake sake saita dinga ayyana mata da gangan yace ta shiga toilet dinsa don ya ganta..

lumshe idanun shi ya danyi, lokaci daya ?wa?walwarsa ta fara tariyo masa maganganun da suka tattauna tare da grandpa dinsa.



"Wife to be...." can kasan makoshi ya furta..


Kamar jira take ya kira sunanta, jikinta na bari ta baro bakin toilet din, don batajin zata iya shiga.


Daga gaban gadon ta tsaya tare da amsa mashi "Naam ..."



"Idan ba zaki manta ba, last time mun yi magana akan hotunan dake a cikin diary din yarinyar nan, har yanzu baki tuna komai dangane da su ba..."?

Ya tambaya akagare da son jin amsar ta, shiru tayi jim tana kokarin tunanowa, bakomai ya fado mata arai ba face hotunan nan na dakin su da suka tsin ta, dama tana ta kokwanton kamar a cikin diary din suke.


Cikin sauri ta furta"Na tuna, bari naje na dauko maka"


Calmly ya furta okay, cikin sauri ta fuce daga dakin har wani ajiyar zuciya take saukewa.



Mikewa zaune yayi tare da jingina bayansa jikin head board dinsa, dawowarta kaWai ya ke jira..



Bayan ta koma ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?dakin bata iske kowa ba, sai da tafara shiga toilet ta watsa ruwa tayi alwala sannan ta fito ta dauko hijabi tayi sallah a tsanake, bayan ta gama ta dauko hotunan data ajiye a cikin drawer chest, cikin sanda ta wuce part dinsa batare da wani yaganta ba.


After some minutes Yaji motsin shigowarta, da sauri ya kalle ta, karasowa tayi tare da samun wuri gefen gadon ta zauna, hannun ta ruke da hotunan ta mi?a masa"tun da jimawa na tsince su a karkashin gadon mu, a lokacin ina tsaka da neman wayata, bansan su wanene akan hoton ba, kuma ban san waya kai hotunan dakin mu ba.."

kar6ar hutunan yayi daga hannunta, ya shimfida su akan tafinsa tare da daura idanunsa akansu, lokaci daya yanayin fuskarsa Ya nuna tsantsar radani da mamaki..



"A daren ranar da muka baro part din daddyna, mun dawo nan saboda wayata da nake nema, ni da Batool muna tsaka da neman wayar acikin dakinmu, kawai sai naji Batool tace min a ina kika samu wadannan hotunan? Nan nake fada mata inda nagansu, sai tace To ay mutumin aunty Ummi ne wannan, Ita kuma wannan kin tuna ?awarta baturiya wadda sukazo airport atare wata fara sol launin idanunta blue, da tayi wannan maganar nan take sai na tuna ta, itace kawar aunty Ummi mai suna NATASHA, sai nace mata Amma taya akai tasan Mutumin aunty ummi ne wannan, shine tace Zata faWa mini, amma dan Allah kada in fada ma aunty Ummi, saboda ta ta6a gargadin ta, akan bata son ta ta6a mata waya, sai nace mata naji ba zan fada ma Aunty ummin ba..." tun da tafara Kora masa jawabi, Chief owais ya kafe ta da idanunsa da suka cika da al'ajabi



"Shine tace min wai ranar aunty ummi ta shiga toilet aka kira wayarta, garin ta dauka kawai tayi picking call din, nan tagan shi kwance acikin kwamin wanka, kumfa ta lullu6e jikinsa sai fuskarsa kadai ta iya gani, a fahimtana shi baiga fuskar Batool ba, ita kadai ce ta gan shi watakil ta kare front camera din wayar da yatsan ta tun da ba sanin takan waya tayi ba, koda ta fada mini hakan, mamaki ne ya kamani, har na fara kokwanton maganarta, saboda nayi mamakin ta yadda har ta iya ruke kamannin fuskar mutumin da tagani farat Waya a video call bayan haka waye ya kawo hotunan adakin mu"? Ta fada tamkar tana tambayarsa..



"A tunanina Aunty Ummi ba zata taba yin gangancin da zata kawo hotunan dakinmu ba, tun da har ta ta6a gargadin Batool akan daukar mata waya thats mean bata so tasan sirrin ta"



tunkan ta karasa maganar ta lura da yanayinsa da Ya sauya, shiru tayi tana jiran jin me zaice..



Mi?a mata hoton Alhajin yayi"me zan yi da shi" ta faWa tare da ruke hoton a hannun ta.



"Kin san wanene wannan mutumin"? Girgiza mashi kai tayi..



Murmushin takaici ya dan saki tare da cewa He is your mom's uncle, Alhaji Musa Wadata, former president of our country After that, his sister Hajiya Laura is my daddy's second wife"


Bai karasa maganar ba, ganin yadda ta zabura ta mike tsaye tana zazzare idanun ta cike da rudu akan fuskarta..



Labbanta na kerma tace"tayaya hakan zai yiwu? Me ya kawo hotonsa a dakin mu"!

"Ina zargin mutumin nan yana Waya daga cikin Elders na gidan kurkukun kaddara, in har ya zamana dagaske hotunan nan sune acikin diary din yarinyar, a labarin da kika bani, ta ta6a fada maki nickname din mahaifinta ne Jan wuya, sannan a shafin farko na diary din ta akwai nickname din sa a rubuce, jan wuya kuma yana Waya daga cikin Elders kamar yadda Danish ya faWa mun nicknames dinsu da suke amfani da su a gidan kurkukun, bayan haka kawar ummin nan, zai iya yiwuwa mahaifiyarta ce ko marikiyar ta ..."



tashin hankalin da ba'a saka mashi date, da tsantsar rudani suke kallon kallo atsakanin su, cikin rawar murya tace" In kuwa hasashenmu ya zama gaskiya, to kenan bai rabu da Aunty Ummi ba? Yana atare da ita, Sannan shine ya sadaukar damu! Ni da babyn Uncle shureim..."?


Dakatawa tayi da yin maganar kamar an tsikare ta, lokaci daya takuma zare idanunta alamar ta tuna wani abu



"Are you okay," ya faWa yana dubanta, Jinjina mashi kai tayi adabarbarce tace"shine.. ! wallahi shine.. mutumin nan shine Jan wuya mahaifin Unaizah, saboda Ina zargin Yarinyar Wurinsa yar uwar Unaizah ce saboda kamannin su ya 6aci, kamar twin sister din ta ce, a ranar dana fara ganin ta sai da na razana..."

Nan ta labarta masa farkon haduwar su da Zeenatu, wlh sai yanzu ya gane dalilin dayasa farko daya daura idanunsa akan hoton unaizah yai tajin kamar yasanta aran shi, ashe saboda kamanninta da zeenatu ne, Ya San ta, tun da kuruciyarta, lokacin da Hajiya sarah take zumunci da hajiya saratu tana yawan zuwa da ita estate Winsu kafin daga baya ta Wauke kafa da zuwa..



gaba daya sun rude da lamarin, Cikin sauri ta kuma cewa"bayan haka, rannan ina tsaka da neman Sim card din da daddyna ya saka min acikin backpack din Unaizah, aranar ne ma Na curo texbooks din ina dudduba su, ina da tabbacin silar neman sim dinne yaja har hotunan suka faWo daga cikin diary din batare dana ankara ba, wani abu daya daure min kai, ina a zaune tsakiyar gadonmu Ina tsaka da neman sim din saiga sajeed Ya shigo dakin mu kamar baya a cikin hayyacin shi..."



nutsuwa Chief yayi yana sauraranta yayin da take basa labarin, idan tana bada labari tiryan tiryan babu kuskure kamar yar jarida sai ya dinga tuna mommynta, ya faminci halayenta da dabi'unta sunfi karfi ta bangaren mommyn ta.



"Da ya sake jaraba Kiran layin wayarsa, kwatsam sai muka ga kiran ya shiga sai dai ba'a daga ba, daga baya munyi waya da me lambar har na bata hakuri nace wrong number ne na kira, amma sai na nemi alfarmar inaso mu dinga zumunci da ita saboda ta kwanta min arai na, toh daga nan ne muka shaku da junan mu, kusan kullum sai ta kirani, ko bata kira ba, to ni zan kirata ne, wlh bantaba sanin mommyna bace, sai a ranar dana kira layin ta, bayan ka fayyace min komai daya faru da ita, nayi al'ajabin taya akai sajeed yayi guessing number din zeenatu"?



Dafe kansa yayi da tafin hannunsa, gaba daya suka zurfafa tunanin su.



"A labarin da kika bani, kince Sajeed Ya fada maki zai iya gane fuskar mahaifinsa Idan ya gansa ko"? Jinjina mashi kai tayi"Eh, haka ya faWa mini, kuma wani abun daure kan nidai dana kalli hoton akaro na farko sai naga sunyi kama da Sajeed kamar yayi kakinsa.."

baisan ya akai ya kara jin ?arfin gwiwa atare da shi ba.



"Babe abun da nakeso dake, komai da muka tattauna a tsakaninmu mubar shi a matsayin sirri, kija baki ki yi shiru, har yanzu bamu kai ga tabbatar da abun da muke zargi ba tukunna, masu iya magana sunce idan baka iya kama 6arawo ba, shi barawon sai ya kama ka, ina fata baki fada ma auntynku Ummi kinsan labarin su ba"!



Jinjina mashi kai tayi"ban fada mata ba"



"Good Girl, kibarni da ita, ni zan tuntubeta dakaina, agurin ta zan samu karin bayani dangane da shi, in har ta bamu hadin kai, zamu yi amfani da ita gurin kama sa, don ba ?aramin shaidani bane, mutunne mai hadarin gaske, tunkararsa abune mai wuya, kamasa bazaiyi mana sauki ba, dole saida dabara sai kuma mun hada da addu'a..."



Har ya ?are maganar bata farfado daga duniyar tunanin data lula ba, maganganun Unaizah ne suka fara dawo mana acikin kwakwalwarta, tabbas za ta yi farin ciki kuma zatayi bakin ciki idan hasashen su ya zamana gaskiya akan Uncle din mommynta, hakan na nufin Unaizah yar uwarta ce ta jini! ya ilah, wlh Alwashine ta daukarwa kanta, sai ta kashe shi da hannun ta..



Cikin sanyin murya tace idan har muka tabbatar da zarginmu akansa, nima zan bada gudummuwata gurin hukunta shi, saboda nayi ma Unaizah al?awarin abu biyu, kafin mutuwarta, ta rubuta min wasika don in ba Mommynta da daddynta su karanta, abun da yasa ban baka wasikar ba, saboda amana ce ta bani, sannan ta roke ni akan in daukar mata fansar cin zalun da mahaifinta yayi mata, tana so in kashe shi da hannu na..."

kasa karasa maganar tayi saboda kukan daya sarke makoshin ta, sakamakon tunawa da Unaizah, ta fama raunin da ke kwance a cikin zuciyarta.



Sauko wa yayi daga kan gadon, ya tsaya daga gabanta suka fuskanci juna, tuni ta jima da sakin hoton hannun ta Ya fadi kasa.



cikin shesshekar kuka tace"Ka taimaka min dan Allah, nasan bani da karfin da zan iya kama shi, amma in har kuka kama min shi zan iya kashe shi, wlh na tsani mutumin nan fiye da yadda na tsani mutuwa ta, ban taba ganin mutun mara imani, tantirin fasiki kuma azzalumi irinsa ba, inaso yaji radadin da Unaizah taji a lokacin da take akan gabar mutuwa, zan hada masa jini da majina akan fuskarsa, fiye da yadda Unaizah tayi kukan bakin cikin daya kunsa mata, Ka taimaka min hubby, ku barni in kashe shi na roke ka..."



hawayen dake sauka kan kuncin ta ya soma sharewa da tafin hannunsa.



"Kukan ya isa haka Unaisah, in har ya zamana shi ne mutumin da muke zargi, ni Chief nayi maki alkawarin zan taimaka maki gurin cimma burin ki akansa, koda hakan zai saba ma doka ne, Ni zan yi maki hanyar aiwatar da hakan ta cikin sau?i, a hannun ki zai mutu Unaisah, sai kin azabtar da shi kafin ki kashe dan iskan..."



batasan sa'adda ta soma sakin murmushin farin ciki ba, gani take kamar har ma sun riga da sun kama shi saboda zumudin ta aika shege lahira, ada fansar mutun daya tayi niyar dauka akansa amma ayanzu da take zargin Uncle din mommyntane, Sai ta kara fansar mutun biyar akansa, Fansar auntyn Ummi da fansar abun da yayi ma mommynta, da kuma fansar prisoners, Cikon fansar mutun na biyar da zata dauka shine Uncle Uzair in har akayi bincike aka gano sune suka kashe shi =?%?



Batai aune ba taji ya manna mata peck on her Cheeks, cike da jin kunyar shi ta sunnar da kanta kasa..

Bata bar bedroom dinsa ba, har saida suka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login