Showing 60001 words to 63000 words out of 321579 words

Chapter 21 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

bubbuga tafin hannayensa akan bayansa, a hankali ya fara karanto addu'o'i yana tottofa masa asaman sumar kan shi..

"tun da yanzu kun riga da kunsan komai babu batun boye boye a tsakanina da ku, maganar gaskiya daliline yasa na shiga jikin ku don in samu kusanci daku saboda in tabbatar da abun da nake zargi akan family din ku..." da rudu suke kallon Imam, maganarsa ta daga hankulan su, owais daya fara dawowa hayyacin sa, cikin kunnansa ya tsinkayi maganar Sheikh Imam da mamaki ya dago da kansa yana dubansa..

yadan numfasa kafin ya daura cewa"ni Allah yayi min wata baiwa In har zan zauna tare da mutum mai bakin sihiri a jikin shi wlh sai naji a jikina, Mahaifinku da surukinku pravin na dade da sanin suna da sihiri a jikin su amma ban taba bayyana maku ba, saboda bani da isassun hujjojin da zan tunkare ku da maganar, lokacin dana fara kutsa kaina ga mahaifinku har na samu ya yarda dani rana ta farko daya gayyaceni don inzo in gana daku, sai da gabana ya fadi ganin yadda kukeyi masa biyayya sau da ?afa, kun yarda da mahaifinku kuna son shi, jikina yayi sanyi dama tun kafin na gane ma idona, sai da naji abakin mutane amma dana gani da ido abun ya karya zuciyata, nayi al'ajabi yadda kuka kasance masu kyawawan halaye da dabi'u kun fita daban, samun irinku zaiyi wuya, Allah bai rageku da komai ba, sai dai kash mahaifinku yayi muku cikas, 6atacce ne ku kuma tsarkakakku ne, wallahi a lokacin koda na fadamaku ba zaku yarda dani ba, zama ku iya tunanin turo ni akayi don inyi masu kazafi, watakil ma kusa a daure ni, shiyasa naja bakina nayi shiru, amma duk da haka ban hakura ba, saboda Allah ya jarabceni da kaunarku, naji inason in taimake ku shiyasa nabiyo ta bayan fage batare da sanin kowa ba, na fara kiran Owais ta boyayyiyar number, na fada masa ya bincika family dinsa akwai bara gurbi a cikin su...." dafe kai Chief Owais yayi da tafin hannunsa bakinsa abude da tsantsar mamaki yake kallon Imam wai ashe shine boyayyan mutumin dake kiransa awaya..
"Sheikh dama kaine boyayyan mutumin dake kirana awaya? Ya fada arude, murmushi Imam malik ya sakar masa"Nine Owais, nasan za ka yi mamaki, kamar yadda kake amfani da brain dinka nima haka nake amfani da kwakwalwata, ban taba bari ka gane nine ba, na toshe duk wata hanya da zaka iya bin diddigin layin da nake kiran ka da shi, bayan haka duk idan zamuyi waya ina canza murya saboda bana so ka gane nine..." dafe kansa yayi da tafukansa Shiekh Imam Ya basa mamaki, yayi zaton malamin addinin islama ne ashe bayan kasancewar shi alkali har ilmin computer gare shi saboda ba karamin wahala ya bashi ba, yasha ya zauna ya baje basirar sa gurin gano wanene boyayyan mutumin dake kiransa amma ya kasa kamar Aljani haka ya koma masa, kowa dake awurin yayi mamaki sosai..

Ru?e hannayensa Chief yayi"meyasa tuntuni baka fito fili ka fada min kaine ba? Why pls? Da ka fadamin ay da tuni na dauki mataki akai"

Shafa sumar kanshi imam yayi"Owais, koda na fada maka ba zaka yarda ba...."


"Dan Allah ku fada mana meke faruwane? Tun jiya kunbarmu a duhu, ku sanar damu mana! Kunce baba Ya kulle kansa adaki, meyasa yayi hakan? Wani laifine ya aikata da da yaja har kuka shiga mawuyacin halin nan.."? Cike da damuwa Ziyad ya tambaya yana binsu da kallo gaba daya fargaba ta hana su bude baki su furta..

Captain yaseer daya gama Fusata zuciyarsa tazo wuya rai a6ace yace"nagaji da jiran ku fada mana, gaba daya kun tada mana hankalinmu, kuma kunki ku sanar damu meke faruwa, wlh da nasani da banzo ba.." ya fada yana girgiza kansa..

Marairaice fuska justice yayi tare da kallon sheikh Imam tamkar zaisa kuka yace"Dan Allah baba Imam ka fada mana tunda su sun?i su sanar damu, pls ku taimaka ku fada mana meke faruwane mun kasa gane inda zancenku ya dosa...."

bai ?arasa maganar ba, Chief Owais Cikin raunaniyar muryarsa da ta disashe ya fara zayyana musu abunda ya faru jiya kafin a fara family meeting, tiryan tiryan ya fayyace musu tun daga biri har wutsiyarsa..

Tashin hankalin da ba'a saka mashi date, tun kan ya karasa suka fara jefawa junansu kallon kallon mai nuni da tsantsar al'ajabi da rudani hadi da tsantsar tashin hankali, ga wani irin faduwar gaba da suka fara ji, Lokaci daya suka zazzare idanunsu jin abun da basu taba zata ba, murya na rawa Justice ya furta"ba zai ta6a yiwuwa ba Owais, wannan wani irin labarine mai kama da almara? Bazai ta6a zama gaskiya ba wlh, Owais ka sake bincike watakil kunyi kuskure, Baba bazai ta6a zama daya daga cikin azzaluman mutanan ba, ka bani mamaki Owais ka rasa wa zakai wa kazafi sai baba? sai kace bakasan halin shi ba"? Cikin fusatacciyar murya ya fada tsabar bacin rai shatun jiyoyon wuyansa sun fito rudu rudu kan fatarsa..

"Tayaya zaku yarda da abunda wata tsohuwa bare ta fada? Wallahi karya takeyi maku, ba momma bace, wanda ya mutu baya dawowa ba, ni batai min kama da mai hankalin ba, makiya ne suka turota don tayi ma grandpa kazafi, Ai wlh da nasan abunda makirar matar nan ta aikata, da tun lokacin dana ganta kwance kan sofa, zan danne hancinta da fillow har sai ta bakunci lahira...."

Captain yaseer daya gama rikicewa jikinshi na 6ari ya dubi Imam malik daya sadda kanshi ?asa "shekh pls kayi masa rukiya, Owais Ya haukace, He needs a psychiatrist to examine his brain, he's not well, Owais would never say this in his right mind, saboda wlh bayin kansa bane, Owais ba zai taba fadin maganar nan da hankalinsa ba, zai iya yiwuwa aljanunne suka shige shi, dad...Uncles pls kuce mana karyane abunda Owais ya fada akan grandpa, ni nasan ba acikin hayyacinsa ya fada ba, Baba ko kiyashi bazai iya kashewa ba, balle rai..."

tashin hankali Ya hana Ziyad furta kalma, kunnuwansa sunjiye mashi abunda ya fi karfin jin shi, baima san sa'adda ya fara unbottoning din rigarsa ba, saboda wani zafi daya taso mashi, still basu gasgata maganar owais ba, amma fa sun kaWu ba kadan ba saboda sunsan mawuyacin abune Owais yayi masu karya saboda ba halinsa bane, kawai suna jin tsoron su gaskata abunda ya fada musu ne.. Gaba daya ubannin nasu sun kasa magana saboda sun razana da ganin yadda suka Waga hankulansu, ta wani bangaren zuciyarsu ta karaya da jin kalaman dake futowa daga bakunansu, bayin Allah saboda yardar da sukayiwa kakansu sun kasa yarda da maganar da aka fada musu akansa..

runtse idanu shi yayi gam a hankali wasu zafafen hawaye suka fara shararowa kan kuncin sa, cikin shesshekar muryarsa mai rauni ya furta"sheikh ni dama nasan za'a rina, baba ya karya mana zuciya, wlh ba kazafi nayi masa ba, shine Elder na gidan kurkukun kaddara kamar yadda kukaji, zaku Iya tuna yaran da nake ruko agurina? Wanda nace maku sojojin america ne suka tsince su a dajin Evil forest kuma suka dam?a case din mu a hannun hukumarmu? To wadannan yaran suna daga cikin fursinonin kurkukun kaddara, A Lokacin sun ku6uta daga gidan kurkukun ne, ai kowa daga cikinku ya gansu a ranar farewell dinner din Uncle Hateem.." nan fa kwakwalensu suka fara tariyo masu fuskoki yaran masu bala'en kama da wasu daga cikin su, still basu gasgata maganar shi ba, amma fa sun fara shan jinin jikinsu, maganarsa ta haifar musu da kowanto..

"Bayan mun kai farmaki, Munyi nasarar ceto wasu daga cikin yaran, A yanzu haka suna akwance gadon asibiti karkashin kulawar likitoci, Aminina omar shima an kwantar da shi tare da dan uwan yaran Salsabeel, har yau basu farfado daga Coma ba, Idan har yanzu baku yarda ba zan iya nuna maku videos din yaran da muka kubutar..."

Wayarsa ya zaro daga cikin front pocket din aljihunsa ya kunna masu video din fursinonin ya nuna masu gaba daya suka le?a suna kallon su, gasu nan a kwankwance saman gadajen asibiti jikinsu sanye da patient uniform, har sheikh imam saida ya kalla, ya kuma kunna masu videos din su Unaisah daya dauka yayin tattaunawarsu a questioning room, wlh sun girgiza gaba dayansu ashe basu ji komai ba agurin khala, sai yanzu da suka ji ainihin labarin azabtarwar da akeyi masu agidan kurkukun ?addara, abun ya taba zuciyarsu sosai, kamar zasuyi hauka saboda tausayin su daya kama su, su Captain duk sun yarda dagaske ne abunda owais ya fada musu sai dai basu yarda kakansu Obie yana daga cikin azzaluman da suka azabtar da su ba, saima cewa sukayi koda zasu yarda labarin na zahirine amma bazai taba yiwuwa baba ya aikata ba, saboda su sun yarda da shi sun kuma san halin shi, sheikh Imam Ya kasa furta kalma, saboda raunin da zuciyarshi tayi, baiyi zaton abun ya munana har haka ba, sai ambaton Inna lillahi wa'inna ilaihurraji'un yakeyi Bai ma san sa'adda ya zabura ya mike tsaye jikinsa na 6ari Ya kama zarya a tsakar falon ba, Cazbahar hannunsa tuni ta jima da barin yatsunsa ta faWa kan floor, har kwalla saida ta zubar masa bai bari sun gani ba yayi saurin sanya tafin hannunsa ya goge ta, hakika Baba Obie ya karya Zuciyar Imam malik, bai taba zaton zai iya aikata makamancin rashin imanin nan ba, abu biyu dayafi kona masa rai ya karairaya zuciyarsa irin yadda suka shafe shekaru suna aikata fasadi a doron ?asa batare da an kama su ba, Yaji takaicin irin azabtarwar da sukayiwa yaran da basu ji ba basu gani ba, abun takaici yaran jininsu ne, babu imani ba tausayi suke azabtar da su, labarin da owais ya basu ya fama masa tsohon raunin da ke a cikin zuciyarsa, Bazai ta6a mantawa ba, yaso ya fada musu ainihin dalilin dayasa ya fara zargin ahlinsu sai dai ya kasa ganin halin da suke a ciki, abun dayafi damunsa makomar Ahlin Obie, ya'yansa masu daraja da kima a idon duniya, babu na banza acikinsu, kowa yabonsu yakeyi saboda kyawawan halayensu da dabi'unsu, amma fasikin mutumin nan saida ya zubar masu da mutuncinsu! Bai kyauta ma kanshi ba, da alama abun ya taba zuciyar imam so yake yayi kuka don ya fitar da abunda ke ransa sai dai ya kasa saboda bai son suga rauninsa hakan zai iya ?ara jefasu a mawuyacin hali..

a karo na biyu ya share kwallarsa yayin daya basu baya, saida ya daidaitsa nutsuwarsa ya daure ya cije cike da karfin hali ya juyo ya fuskance su a lokacin sun kasa yin kukan na zuci sukeyi mai radadin gaske...


Cikin sanyin murya ya tambaye su tun da suke arayuwarsu sun taba fuskantar mummunar kaddara ko wata jarabawar rayuwa irin wannan"? har suna hada baki gurin furta aa sukace su tun da suka taso rayuwarsu basu ta6a fuskantar kaddara mara kyau ko wata jarabawar rayuwa ba, nasara da jin dadin rayuwa kadai suka sani, idan ma akwai abun daya taba sanyasu kuka da idanunsu to bai wuci ranar da suka rasa mahaifiyarsu ba, acewar su His excellency, gyada kai sheikh imam yayi idanubsa cike tab da kwalla yace"wannan ne karo na farko da zasu fara fuskantar mummunar jarabawar rayuwa, yace shi tunda ya taso rayuwarshi yana jin labarai iri iri na irin jarabawowin da mutane suke fuskanta wasu su daga hankalinsa wasu su sashi zubar da kwalla saboda tausayi, amma bai taba jin kaddarar data girgiza shi irin tasu ba, yajiye masu bakin ciki da takaicin abunda mahaifinsu ya aikata musu, ya tausayawa rayuwarsu, amma kada su karaya, nan ya fara yi musu nasiha mai tsuma zuciya...

_Abun da akeso a yayin da Allah ya jarabce bawa da wata mummunar kaddara, Ana kwadaitar da su da su amsa jarabawan da hakuri da godiya suyi biyayya ga Allah, domin hakan yana tabbatar da gafara da lada daga Allah, kuma Allah yana tare da masu hakuri, sannan dukkan tsanani yana a tare da sauki_

_Wani lokaci Allah yakan jarrabi bayinsa da musibu domin ya daukaka su, kuma ya kankare zunubansu, kamar yadda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yake cewa_


_(For every misfortune, illness, anxiety, grief, or hurt that afflicts a Muslim, even the hurt caused by the pricking of a thorn, Allah removes some of his sins.")_

_ Duk wata musiba, ko rashin lafiya, ko damuwa, ko bakin ciki, ko cutarwa da ke damun musulmi, ko da wata ?aya ce da ta same shi, Allah yana kankare masa wasu daga cikin zunubbansa"_



A cikin suratul Ankabut ayata 2

_Allah buwayi yace"Ashe Mutane Suna Tsammanin Cewa Za'a Barsu, (Don Kawai) Sunce Munyi Imani, Alhalin Kuma Su Baza'a Jarabcesu / Baza'a Fitinesu Ba?_



_Acikin suratul Surah Al-Baqarah Allah yana cewa_



_Wa lanablu wannakum bishai im minal khawfi waljoo i wa naqsim minal amwaali wal anfusi was samaraat, wa bashshiris saabiroon._



_"Kuma lalle ne, zamu jarrabe ku da wani abu na tsoro da yunwa da nakasa daga dukiya da rayuka da 'ya'yan itace, kuma ku yi bushara ga masu hakuri."_



_"Ku tuna cewa hikimar Allah da iliminsa sun wuce fahimtar mutum, Maimakon tambayar dalilin da ya sa Allah ya jarrabe mu, ya kamata mu mai da hankali ga amsa jarabawowin da imani, da hakuri, da godiya_


_Annabi Muhammad (SAW) ya ce, "Babban lada yana tare da fitintinu masu girma, idan Allah ya so mutane sai ya jarrabe su, kuma wanda ya yarda da shi ya samu yardarsa"_

_Kaffarar Zunubai Allah yana iya jarraba mutane domin ya tsarkake su daga zunubansu, kuma idan suka yi haquri za a gafarta musu zunubansu._

_And sometimes Allah tests us with calamities and sometimes with blessings, to show who will be thankful and who will be ungrateful, and who will obey and who will disobey, then He will reward or punish them on the Day of Resurrection _


_Kullum ka Wauka cewa kana cikin jarabawa ne, domin dukkanin rayuwarka jarabawa ce, Allah zai jarabceka da abubuwa daban daban, waWanda ka sani da waWanda baka sani ba, tsammaninka kayi juriya kayi ha?uri_

_Ba kullum ne zaka samu rayuwarka ta kasance maka yadda kake so ba, akwai ranar farin ciki, sannan kuma akwai ranar ba?in ciki, akwai ranar samun riba, sannan kuma akwai ranar (faWuwa) yin asara"_

_Haka jarabawar rayuwa take, amma babu makawa duk abinda ya faru gareka, idan kayi biyayya ga Allah, sannan kuma kabi manzonsa, ha?i?a zaka kasance daga cikin masu cin nasara a duniyarsu da kuma lahira"_

Tunda Imam Ya fara yi musu nasiha jikin su yayi sanyi lakwas, Imani ya kara shigarsu, nasihar shi ta ratsa zuciyarsu sosai, musamman daya tunasar da su irin yadda annabawa suka fuskanci jarabawowin rayuwa masu tsanani kuma sukayi hakuri sukai biyayya ga Allah, sai suka ga tasu jarabawar bakomai bace somun ta6i ne, sannan yace yasan basu fara ganin komai ba, sai lokacin da abun ya fallasa duniya ta sani a wannan lokacinne zasu fara fuskantar kalubalen rayuwa amma baya son su karaya, kuma su daina jin fargaban mutane su sani, laifin nan basu suka aikata ba, Allah ya sani, kuma yana atare da su, don haka su mika lamuransu gare sa, sannan su dage da yiwa kansu addu'a akan halin da suke a ciki, shima zai tayasu, In sha Allah wata rana sai labari, zai zama kamar ba'ayi ba, sai dai tashin zance, kuma kada su kuskura duk runtsi duk wuya su jefa kansu a mawuyacin hali saboda maganganun da mutane zasu fada akansu, koda zasu rasa mukamansu ne kada su karaya, mutane basu da wuta basu da Aljanna ba zasuyi masu hisabi ba, kada su ji kunyar laifin da basu suka aikata ba, koda za'a cuzguna masu ne, ayi musu kazafi, ko azage su aci zarafin su, kada su kuskura su canza daga yadda suke, saboda sau dayawa mutane suke jaza ma mutun bakin cikin da zai zaiyi silar da zai tsani kansa ya kuntata har yayi tunanin kashe kanshi bayan yin hakan kuskure ne babba ba...=ؔ?

Yayin da yake yi masu nasihar ya haWa gumi akan fuskarsa kamar babu A.c a falon, har lokaci bai zauna ba, yana daga tsaye yana fuskantar su batare da gajiyawa ba, wlh ji sukayi kamar ana wanke damuwar dake a cikin zuciyarsu, ga wani sanyi dake ratsa jikinsu, imam ya karfafa masu gwiwarsu, Ya farfado da jarumtakarsu, aransu har sunji zasu iya fuskantar kowani irin kalubale da zasu fuskantar...

"Kuma ku sani, Nima ina atare daku, zan tayaku ya?i atare zamu cinye jarabawar nan da take tunkaro mu, in sha Allah, zan tsaya maku tsayin daka don ganin baku tozarta a idon duniya ba" ya faWa yana kara jaddada musu da murmushi akan fuskarshi, wannan maganar da yayi ta faranta ransu, har basu san sa'adda suka saki murmushi akan fuskokinsu ba, kusan atare suka mike tare da nufar shi, atare suka hada baki gurin yi mashi godiya kamar zasu durkusa kasa, sun ma rasa bakin magana, sukace su basu san dame zasu iya biyanshi ba, saboda basu da abun da zasu biyashi da shi Allahne kadai zai iya biyan shi, Bazan iya misalta dadin da imam malik yaji ba, daya bayan daya yabisu ya rungume su a kirjinshi..

Daga bisani Ya umarce su da suje suyi wanka kuma in akwai sallar da basuyi ba toh suyi gaggawar ramata dama so yake ya samu su samu natsuwa sannan yayi masu magnar sallar, babu musu suka amsa mashi da toh..=ؔ?



Gaba dayansu a part din iyayen su mata da ke a cikin gidan Suka shiga, wanda tun bayan rasuwar su, basu daina amfani da shi ba, masu aikin gidan suna shiga su gyara shi akai akai, kullum zaka taras da part din a atsaftace kamar akwai me rayuwa acikin sa, aduk time da suka ji kewar iyayen su mata, idan suka zo gidan a part din suke huce gajiyar su.


Bayan sun yi wanka sukayi sallah, daga bisani suka fito falo, kamar yadda suka bar sheikh Imam haka suka taras da shi, a kewaye da shi suka zazzauna, ya tambayi ina yan aikin gidan suka ce tun jiya suka hana wani daga cikin su shigowa main falo..



Sheikh Imam yace a kira su, don su girka musu abinci, bai kare maganar ba, Prime minister ya tari da numfashin shi da cewa"basai an kirasu ba, daga rana irin ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login