Showing 111001 words to 114000 words out of 321579 words

Chapter 38 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

su"Baya agidan Ya 6ace akan idanuna"

gaba daya suka juya suna kallon ta, fuskarta tayi jawur saboda hucin ruwan zafin daya dake ta ga hawayen da suka cike idanunta, tunkan ta karaso Junaid ya sauko daga bayan zahra Ya nufe ta yana kuka, daukar shi tayi tare da rungume shi a kirjin ta, mami da ummi har suna hada baki gurin furta"anila! Wata irin 6acewa kike magana akai"?

Daga tsakiyar su ta tsaya tare da kallon su Mami, a halin yanzu tasan komai yazo karshe bata jin fargabar ta sanar da kowa tun da ita kanta rayuwarta na acikin hatsari.

Nan take ta labarta masu abun daya faru tsakanin ta da Uncle dan Iya, Tashin hankali tsantsa akan fuskokin su, adai dai Lokaci Abie da baba Mai gadi sun nufo falo shigowar shi kenan tunkan yayi parking mota, baba mai gadi ya sanar da shi zuwan jami'ai, Hankali atashe suka nufo ciki, Komai da Anila ta fada akan kunnan su.

"Duk da ya gudu ba zamu fasa abun da ya kawo mu ba, dg Ya bada Umarnin Mu bincike gidan gaba daya, don haka kubar hukuma tayi aikinta, naku kallo ne kawai..."

wanda yai maganar daga gani shine led team Win su

Kallon mahboob yayi wanda komai jinsa yake yi kamar a mafarki"muje ka nuna mana dakin mai aikin ku Ana, da dakin mahaifinku" dakyar ya iya amsawa da toh.

"Ina mai gadin gidan nan" jikin Baba mai gadi na bari Ya ce gani yalla6ai..

"Ka tabbata a ranar da abun ya faru baka ga gifcin kowa ba?

"?wara ka fada mana gaskiya idan ba haka ba, doka zatayi aiki akan ka" kamar zai fashe da kuka ya hau yi masu rantse rantse akan shi baiga kowa ba tun bayan da mutanan gidan suka tafi unguwa..

Ruko Hannun Mahboob Agent zahra yayi, suka bar sojoji agents biyar, a falon tare da su Anila, hudu suka nufi dakin Ana..

"Bayin Allah daga Ina? Tayaya zaku fadowa mutane gida? Wa kuke nema? Abie ne ya tambaya arude sai lokacin ya samu damar bude bakin sa.

Anila ce tay saurin Tarar numfashin shi da cewa"Abie zan fada maku komai,..." gaba daya suka kura mata idanu.

Nan ta soma zayyana masu komai daya faru tun daga ranar data shiga dakin Ana har ta gano wayarta.

"Ni da Benazir munyi maku karyar zamuje gidan Hajiya adama, toh ba can muka je ba, Gidan Dj mu ka je kai kara akan Uncle..."


?aura hannu biyu Ummi tayi akai tana zabga salati, zahra ta zazzare idanunta saboda tashin hankali, mami duk tabi ta rude Abie yace"Anila meyasa tun lokacin baki sanar dani ba?

"Saboda banaso In jefa rayuwarku cikin hadari, kuma koda na fada maku wallahi ba zaku yarda dani ba, shiyasa na yanke shawarar sanar da Benazir don mu nemi mafita"


"Amma Anila kinyi gaggawar sanar da jami'ai, meyasa zaki yarda da maganar Ana da tayi maki a video? Ki ka san ko ?azafi tayi ma shi saboda wata manufa tata? Sai kace bakisan halin Uncle din naki ba? Me zaiyi da yar aiki kafira! Kuma taya akai ita tasan yana da sihiri dudu yaushe kuka dawo gidan? Ummi ce ta faWa cikin rudu da bacin rai.

Abie Yace"baki kyauta ba Anila, Maganar nan acikin gida yakamata Mu yi ta atsakanin mu mu binne ta, amma sai kika fitar da ita waje gashi yanzu kinja mana, kuma wallahi in har abun da kika faWa ba gaskiya bane saina sa6amaki..." kowa da abunda yake faWa.

Agents suna atsaye suna sauraron tattaunawar su, Kamar zasu rufe Anila da bugu sai faWa sukeyi mata saboda basu yarda da abun da ta fada ba.


"Ba a shaidar dan Adam, tun da har kuka ga na kai karar Uncle dina da kaina, Yakamata Ku yarda dani, Ni ban aikata laifi ba, Ummi Itama Ana yar adam ce, ko da kasancewarta me aiki, na rayu da ita tsawon shekaru, nasan halinta Ciki da bai, fiye da yadda nasan halin Uncle, Ana ba zata ta6a yi masa kazafi ba tun da har ta fada toh Ya aikata ne.."

ba ?are maganar ba Abie Ya daka mata tsawa"kar in kuskura In kara jin bakin ki mara kunya, wallahi in har suka gama binciken nan basu gano komai ba ki kuka da kanki.."

cikin shesshekar Kuka tace"nima zanyi fatan hakan Abie, amma mawuyacin abune.."


"Aunty Aneelerh dan Allah kiyi shiru, Ki rufa mana asiri ki daina magana, ni nasan daddy bazai aikata abunda kike zarginsa ba, In sha Allah bazai ta6a zama gaskiya ba" Zahra ce ta fada tana kuka.

Wani kallon tausayi Anila tayi mata, Junaid Sai kara kankameta yakeyi kamar zai koma cikin ta.

A bangaren Agent zahra, bayan Mahboob Ya buWe masu dakin Ana, suka shuga daga Ciki suka fara gudanar da bincikensu Har suka kare basu gano komai ba.


Suka tasa ?eyar shi Yakaisu dakin Uncle dan iya bayan sun shiga nan ma suka fara binciken ko'ina na cikin dakin, Mahboob duk yana kallonsu gabansa nata faWuwa.

A karkashin gadon shi sojoji suka zaro wasu akwatina Guda hudu, Balle murfin sukayi, bakomai bane a ciki ba face kudi bendir bendir sabbi fitigill mahboob har saida Ya dafe kirjinsa saboda razanar da yayi,

Kallon saman ceilling din dakinsa sukayi Agent zahra Ya ba sauran agents din Umarnin su babbake ceiling din, Mahboob ne ya dauko masu katuwar guduma suka taka drawer, har suka cimma ceilling din, da guduma suka yi nasarar 6alle wani sashe na ceilling din dakyar da sidin goshi tunkan su karasa Kudi suka fara faWowa ?asa yan dubu dubu, wlh tsabar kidima yasa mahboob ya firgita cikin rudu, saboda yasan daddynsu baida wannan kudin, mutumin da shegen makonshi bai bari ya biya masu bukatunsu kanshi kadai ya sani, hakkinsu daya yake basu shine abincin da zasu shi, amma suturarsu da abun hawa da sauransu su suke siyawa kan su bai damu da lafiyar su ba sai ummi ke fafutuka.


Kudin sai fadowa kasa sukeyi kamar ana zuba yashi sun ta????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
ru akan pillow tili gudu.

Bayan sun gama da Ceilling din, Suka bude fankaceciyar wardrobe dinsa suka fara zazzago kayan Jikin ta, daga kasa cikin drawer chest dinta suka ga wasu makudan kudaWen sai faman jinjina kai su ke yi.

Kurama bangon da wardrobe din take yayi da ido tare da nazarin yadda take

"ku dauke min wardrobe dinnan daga jikin bango" agent zahra ne ya bada Umarni, Hada karfi agents din sukayi gurin ture wardrobe din tun daga tushenta suka 6a66ako ta tare da jingine ta gefe Waya.

?urawa bangon idanu sukayi basu ga komai ba, can Agent Yace su fasa bangon, aikuwa suka fara ?wan?washe shi da gudu ma, har saida Marbles Ya zube kasa, nan take wata boyayyiyar kofa ta bayyana a jikin bangon, ashe zahra yaga abun daya gani.


"Ku bude ta," ya basu Umarni, bayan sun cire kofar, duhu suka gani, tunkan suyi ma mahboob magana yayi saurin Wauko masu fitilar saman drawer Ya mika ma agent, ya kar6a tare da masa godiya kafin suka shige ciki.

Da farko yaji tsoron Yabi bayan su amma kuma yana so Yaga karashen al'amarin na ubansu hakan Yasa yabi bayan su.


Lokacin da suka shigo munafukin dakin, mai ruke da fitilar ne Ya haska masu Cikin sa, bakomai bane a cikinsa face Kayan tsafi, hada kwarangwal din mutune da layoyi, zare idanu Mahboob yayi Jikin shi Ya hau yin kerma, Yana kokarin Ja da baya atsorace cikin rashin sani Ya taka wani guri mai kamar danshin ruwa nan take kafarsa ta zurma ya fasa kara, cikin zafin nama wani agent ya dam?i hannunsa, dakyar Ya fito da kafar shi, bawan Allah duk yabi ya rikice, lallashin shi sojojin sukayi har suka samu Ya dan dawo hayyacin sa..

Agent zahra dake bin dakin da kallo karaf idanunsa suka hango mashi digger da shabir, a wata kusurwa hada busasshen jini a jikin su.

Da hannu ya nuna ma sojoji su Yace"Ku dauko mun su" Cikin sauri suka kwaso su tare da kawo mashi a kasa suke zube su, Zukunna wa yayi tare da daukar digar yakaita gaban hancin shi, Yamitsa fuskarsa yayi tare da kallon Inda kafar Mahboob ta zurma nan take ranshi ya bashi wani abu aka binne a gurin.

Umarni yaba agents din su ha?a inda kafar Mahboob Ta zurma.
Da sauri biyu daga cikinsu suka dauki digger da shebir, suka nufi gurin suka hada karfi gurin tone kasar gurin.

Mahboob dake ta zare idanunsa Sai ja da baya yake yi.
?ananun ?wari ne suka soma gangarowa ta cikin ramin.


Ganin yadda suke ta sara kasan da karfi ne yasa Zahra ce masu Su bi a hankali saboda su samu damar ganin me aka binne a gurin.

Kwatsam! Suka fara hango Hannayen mutun barbade da kasa.

Aje kayan aikin sukayi sai sukayi amfani da hannayensu gurin Janyo da gawar suka fito da ita waje gaba daya ?asa ta barbade jikin ta, wani iko na Allah batay komai ba, babu alamun ru6ewa a jikin ta, daga gani bata jima da mutuwa ba, Allah dai ya nufa sai anganta, wata kara Mahboob Ya fasa tare da fashewa da kuka Ya zube kan gwiwonsa Yana ambaton"ana ! Ana! Ana! Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..wallahi itace! Ana ce, ta mutu, Wayyo Allahana na bani na lalace.."

da rarrafe ya nufi gawar, Ya ruko yatsanta dake asanye da zoben daya bata da shi Ya gane ta.

Gaba daya Jikin agents Win yayi sanyi lakwas zuciyarsu ta karaya, ransu kuma ya 6aci sosai.

"Yaro, wacece wannan din? Wani agent ne ya tambaya.


Cikin kuka Yace"mai aikin gidanmu Ana da muke ta nema itace" kallon kallo suka jefawa juna, hasashen su Ya zama gaskiya..

Duk wannan abun dake faru su mami dake a falon basu son komai ba, saboda sun yi nesa da su basu iya jiyo sautin komai..


Kwatsam suna zazzaune a saman sofas na falo, suka soma jiyo kukan Mahboob kamar ana zare ransa, Hankali atashe suka zabura tare da mikewa kafin su motsa sai ga shi ya watso da gudu hawaye jaga jaga da fuskar shi yana karasowa bai iya furta kalma ba Ya yanke jiki ya faWi asume, har suna hada baki gurin ambaton sunan shi basu kaiga karasawa gare shi ba, kwatsam saiga agents sun biyo bayan shi, biyu daga cikinsu sun dauko gawar Ana asaman wani buhu, wa'iyazubillah tsabar tashin hankali kasa motsi sukayi, saboda al'ajabin daya rikirkita su, har agents din suka ajiye gawar a tsakiyar su basu motsa ba.


Anila bata san sa'adda ta saki Junaid ya fadi kasa yana kuka, zubewa tayi kan gwiwowinta akan gawar ana da hannu ta dinga kakka6e kasar dake akan fuskarta har saida ta goge ta sosai ainihin kamannin fuskarta ya fito.


Cikin shesshekar kuka ta dubi agents din"A.. a ina kuk.. Ka samu gawarta"?

Agent zahra yace"a wani dakin sirri dake a jikin dakinsa wanda kofarsa bayan wardrobe dinsa take.."

fashewa tayi da kuka, Zahra tuni ta jima da sumewa, ummi ma nan take ta yanke jiki ta faWi.

Anila ta dubi abie daya kame atsaye shida mami tana kuka tace"yanzu kun gasgata abunda na fada maku ko? Gayanan kun gani da idonku, Ana ba sharri tayi masa ba, bayan ya gama lalata rayuwarta shine Ya kasheta Ya binne don kada asirinshi Ya tonu.."

baba Mai gadi daya gama rudewa yama raWa ina zai sa kansa.

Agent zahra ya fayyace masu komai da suka gani adakin Dan Iya.

Yace sun dauki bayanan da suke so Saura su kama shi, kuma suna neman goyan bayansu In har ya taka kafarsa a cikin gidan su yi hanzarin sanar da su sannan zasu tafi da gawar ana don su karasa binciken su akanta, idan suka gama zasu yi mata jana'iza, bayan haka sun kulle dakin dan iya dana Ana, kada wanda yayi kuskuren bude shi.

Kafin su tafi da ita Anila da abie da Mami suka zuzzukunna agaban gawar suka dinga yi mata addu'o'i.

Abie yace Idan zasu yi jana'izar su sanar da shi yanaso ya halarta suka amsa mashi da toh.

Bayan tafiyar su, Abie Ya dauko ruwa Ya yayyafa ma wadanda suka suma, koda suka farfado cike da damuwa suke tambayar mafarki sukayi ko gaske ne abun da su ka gani?

Abie ya faWa masu abunda sojoji su ka ce, ya kuma ce suyi hakuri su rungumi kaddara, dan iya bai kyauta ma kanshi ba Ya ha'ince su Ya karya masu zuciya, bai ta6a zaton zai iya aikata rashin imanin na ba, ummi tana kuka tace Allah ya isa tsakaninta da shi, in sha Allah sai yaga sakayyar cin amanarsu da yayi da kuma abunda yayi ma Ana, anan har Ta labarta masu lokacin da take zuwa gyara masa badroom dinsa duk in taci karo da makudan kudi Sai yace mata bana shi bane, kudin Campaign ne da yan siyasa ke bashi, a karshe dayaga tacika sanya mashi ido saiya hana ta shiga dakin Kwata kwata, yace ta daina zuwar masa daki, a duk lokacin daya bukace ta zai shigo nata dakin, akan wannan maganar har fada sukayi batare da sanin kowa ba, kuma tun daya buga mata warning bata kara shiga dakinsa ba in bashi ya kirata ba, har yanzu abun yana ?ona mata rai amma bata taba faWa ma kowa ba sai yau da Asirin shi ya tonu.

Akalamina bazai iya misalta tashin hankalin da suka shiga ba, sunyi kuka tamkar ba gobe, Zahra da mahboob Har saida zazza6i ya lullu6e su bayin Allah, basu ji ba basu gani ba Ubansu Yaja masu.


Sai da takaiga Mami da Abie ne suke lallashin su su kansu karfin haline kawai sukeyi saboda matsanancin halin da suke a ciki.

Ahaka basu Ji komai ba, dan wannan introduction ne na abunda ya ke aikatawa.

Kamar masu zaman makoki, haka sukai ta alhini, baci ba sha kamar masu azumi..

Batare da sanin su ba, baba mai gadi ya tattara yanashi yanashi ya gudu daga gidan, saboda tsoron kada laifin ubangidan sa Ya shafe shi.

Wuraren Karfe Waya da rabi na rana, saiga Isod soldiers din sunzo gidan, gaba daya suka kewaye gidan bisa Umarnin Dg, sune zasu cigaba da gadin gidan har zuwa lokacin da zasu kama Wan Iya=?%?


~_______________________________
Dr Jidenna

Yana a zaune kan Kujerar Officers dinsa ya Waura ?afa daya kan Waya, as usual asanye yake da Ankara riga da wando, ya daura lapcoat fara akai, ga karkatacciyar hular nan tasa ta inyamurai daya kifawa kansa kamar kujera yar tsugunno, wuyansa yana a rataye da statescope, a tsanake Ya ke yin Operating Laptop dinsa dake akan desk din gaban shi, sanyin A.c na ratsa shi, Hankalin shi kwance bai da wata damuwa, yana aiki yana shan coffee din sa dake a cikin cup din gabansa.


Wayarsa ce tayi ringing, saida ya mula ya sha iska tukunna yayi picking tare da karawa a kunnansa..

"Dr.adam ya akai? Ina aiki ka katse ni, ba nace nayi cancelling meeting din da zamuyi ba.."

bai ?are maganar ba, muryar dr. Adam ta katse shi"sir ba wannan ba, akwai matsala, Idan kana a office kayi gaggawar guduwa idan ba haka ba, ka mutu..." cikin rudu yace"bansan zancan banza Adam! In gudu sai kace wani 6arawo? Ka manta da wa kake magana? Md ne fa, ka duba layin da ka kira ko kayi mistake ne..." katse shi dr Adam yayi cikin rawar murya yace"kutmar Uban md din! don ubanka ka gudu nace! Asirin mu ya tonu, sun san komai, sun san cewa da sa hannunmu ake sadaukar da jariran su In har ka bari suka ritsa dakai ka mutu, Ni ma ganin nan zan gudu in bar ?asar"


Tuntsirewa yayi da dariya"bana son shirme da shiririta, yanzu ba lokacin yin tsokana bane"

Dr adam yace"ba tsokanarka ka na keyi ba, dagaske nake maka, ka gudu yanzun nan ko ka kwana a ?abarin ka"


"Ka fahimce ni, rayuwar mu tana a cikin haWari, yanzu haka da nakeyi maka magana, gidan dan iya, a kewaye ya ke da Sojoji ni ma kaina ya Waure na rasa gane tayaya akai hakan ta faru? Taya suka san komai..."

"Bari na kira obinnan muji, Ni nasan labarin nan ba gaskiya bane, waya isa ma ya tona asirin dattijon arzi?i balle har a kama shi, bayan suke rike da kasar da iznin su ake komai..." katse kiran yayi ya dannawa Layin baba Obie kira, tana shiga ba'ayi picking ba, kira ya dinyi baya picking..

"Kai ko ka daga mana! Nasan a bakin ka ne zanji gaskiyar zance"

Knocking Kofa Yaji daga waje, rai a6ace yace"pls bana bukatar ganin kowa, na ce na fasa meeting din.." bai kaiga ?arasa maganar ba, suka bankaWo kofar, da karfi, a zuciye ya dubi mai shigowa da niyar ya tsawatar ma su, A fadace yai pointing din su, da indext finger dinsa, cak ya tsaya kamar andasa mashi aya, ya shiga zare jajayen idanun shi kamar na mujiya, cikin shi ya duri ruwa duk yabi yasha jinin jikin shi..

Isod Agents ne suka shigo su huWu sanye da black suits

?aya daga Cikin su ne Ya nuna masa Id Card dinsa"sunana Agent Jabeer Osman daga hukumar Isod, muna gayyatarka zuwa headquarter din mu, ka biyo mu mu tafi salin alin, batare da kayi kuskuren da zaisa wani ya gane meke faruwa ba, Idan kuma kace za ka yi mana gaddama..." bai ?are maganar ba, ya Wage masa gira tare da kai hannu ya shafa bindigar dake soke a qugunsa, tsantsar tsoro ne da tashin hankali akan fuskar dr jidenna, jikinsa ya kama kerma kamar mazari, zufa ta wanke goshinshi, sai faman sharceta yakeyi da yatsunsa,

Agent Jabeer ya kara da cewa"bayan haka, Iyalinka suna a karkashin kulawar sojojin mu, kasan me zai biyu baya idan ka bijire ma na"

Agent din dake a gefen Jabeer da hannu ya nuna masa kofa"this way please" cikin rawar jiki ya bi su suka sanya shi a tsakiyar su, gaba daya hospital staffs din babu wanda yasan meke faruwa, sun ga dai Md jidenna a tsakiyar bakinsa masu bakaken suit sai washe bakiyi yake yi suna fira, wasu daga cikin visitors har gaishe da shi su ke yi yana amsa masu dakyar dakyar.

Shi ka Wai yasan musibar da ya ke a ciki, marassa Ta cika da fitsari..

_______________________________=?%?


Horn din Mota ne Ya karade kunnuwan mai gadin wani katafaren gida, mikewa yayi daga kan bencin da yake a zaune, cikin sauri ya karasa tare da zuge gate din gidan, ta shigo da motarta a parking space ta ajiye, da sauri mai gadin gidan Ya nufi motar, Ya buWe mata Car door, fitowa tayi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login