Showing 237001 words to 240000 words out of 321579 words

Chapter 80 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

Jazz yakai shekaru Biyar, daddynsa ya rasa ranshi a wata tafiya da ya yi tare da abokan kasuwancin shi, daga London zuwa turkey, Jirgin su yayi Crashing, yana Waya daga cikin wadanda suka rasa ran su.

Turai tayi bakin cikin mutuwar shi har saida ta yi rashin lafiya kamar bazata rayu ba, bayan da ta samu lafiya, ta fara tunanin menene mafita? Saboda tasan a yanzu bata da gata daya wuce Allah, Wadanda suke kare ta daga sharrin Beatrice sun mutu, ta kuma san bazata kyale ta ba,
tunda yanzu ta samu damar da zata iya salwantar da ita, aikuwa awata rana kwatsam tajiyo firar da su ke yi tare da aminiyarta adaki akan yadda zasu kasheta su gaje dukiyar Abraham, har tana fadin ita babban bakin cikinta, gaba daya sunan Turai ne akan kadarorin sa, ga lauyansa dake kokarin tsaya ma turai da danta don su kar6i hakkinsu, sai kawar tace"abun daya kamata suyi kafin araba gadon dukiyar tashi, su bi ta bayan fage su kashe Turai, sai su bar danta su ruke shi a hannun su ta yadda ba za'a zarge su ba"

Koda jin wannan firar tasu hankalin turai ya tashi matu?a, tayi mamakin jin furucin matar Uncle din ta, ta rasa gane meyasa ta tsaneta har haka? Bata san cewa ita bata damu da dukiyar shi ba, burinta ta zauna lafiya da ita, amma da taga da gaske kasheta zasuyi sai tayi dabarar kiran lauyan mijinta ta fada mashi abun dake faruwa, ya nuna damuwarsa yace in ba damuwa su dawo gidansa da zama zai basu tsaro, sannan zai kai ?arar Beatrice akan furucin kisa da ta furta mata, turai ta nuna kin amincewarta akan shawarar shi, tace ita kawai bata jin zata iya cigaba da zama a kasar, ta rasa gatanta, ta tsani zaman london tafi son tayi nesa da su ta tafi can wata kasa inda zata raini danta, kawai ya taimaka mata su siyar da kadarorin mijinta da komai nashi batare da sanin Beatrice ba, Lauyan baiso shawarar data yanke ba, amma da dayaji irin barazanar da Beatrice keyi mata sai ya go yi bayan ta bar ?asar, kuma hada karin kalaman data furta na cewa ta tsani zaman kasar kuma shi mai biyayyane ga umarninta saboda amanar dake a tsakaninsa da Abraham.


ta bayan fage suka siyar da kadarorin Mijinta, dama Black card dinsa Yana a hannunta, tun bayan rasuwarshi ta ke boyen shi, Beatrice tasha tayi mata barazana akan ta bata komai nashi, a lokacin harta ?wace mata key din motar, nema take ta kore ta daga gidan, amma saboda gadon Abraham data ?wallafa rai akai Yasa ta dakata tana jiran ta kwace komai kafin ta koreta.

Batare da sanin Beatrice ba, Lauyan ya taimaka mata suka siyar da kadarorin Abraham gaba daya kudin ya zuba mata a account din sirri daya bude mata, shine ya bata shawarar ta dawo abuja ta zauna ta bar nahiyar su, saboda shi dan asalin nigeria ne mazaunin abuja anan family dinsa suke, karatune yakai shi england harya zama lauya acan.

A takaice da taimakonsa Turai ta gudu daga england tare da danta jazz suka zo Nigeria, agidan daya kama masu haya suka zauna, komai da ta ke bukata da kudin gadon su ta ke yi masu, Lauyan nan shike kula da su, duk da ba anan yake da zamaba amma baya gajiya da kiranta awaya don yaji ya lafiyar su..

Turai bata yi aikatau saboda rashin kudi ba, ra'ayin kanta ne, aranar da data tsinci Domestic Staff ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Application daga Obie estate a social media yana yawo
hakanan taji tana son ta jaraba neman aiki, ko ta samu family din da zata jingina da su, musamman da taji labarin Family din Obie, nan take ta cike form din da bayanan ta, cikin Ikon Allah bayan kwana uku sai ga sakon Interview invitation ya shigo ta email din ta.

taji dadin da ba zai misaltuba, ko da ta tashi zuwa yin interview din sai ta sanya sutura mara tsada, ta tafi tare da Jazz, a lokacin ba hajjaty bace head maid ba, bata ma kaiga zuwa Nigeria ba a lokacin, bayan da taje head maid din lokacin ta yi masu interview ta tantance waWanda suka kware gurin aikatau, Turai tana daya daga cikin su, taji dadi sosai musamman da suka ware mata dakin ta, gaba daya ta dawo da zama tare da Jazz dinta ta baro gidan da ta ke haya.

a lokacin tana jin dadin zaman gidan saboda baba Obie yana mutunta ta, yana kuma son danta jazz, Kowa ya tambayeta ina daddynsa sai tace masu bazata iya tunawa da rayuwarta ta baya ba, ta dinga nuna kamar tayi loosing memory saboda kawai batason kwata kwata labarin inda take ya komama Beatrice, tasan ba kyaleta zatayi ba, ta dade tana boye ma kowa identity dinta, ga dukiya tana da ita amma bata nunawa, ko jazz baisan tana da arzi?i ba, sai bayan Shari'ar Elders Ta damka mashi gadon shi, bayan ta labarta mashi komai game da danginta da irin rayuwar da tayi agidan Uncle dinta, ta kuma bashi hakuri na kin fada mashi da batayi ba da kuma dalilinta nayin hakan.
Turai ta musulunta ne saboda kyautatawar da musulmai yan uwanta masu aiki sukeyi mata, tana jin daWin yadda suke yin mu'amalarsu wannan ne yaja hankalinta har ta musulunta, ta sauya sunan ta daga Harriet zuwa Khadija, shi kuma Jazz daga Eric zuwa Abubakar, sunan Jazz nickname ne da baba Obie ya ke kiran shi da shi saboda yadda ya ke son Music.

Tsanar da hajiya saratu tayi mata ta samo asaline saboda auran ta da sir mubarak yayi bayan rasuwar matar shi ta farko, a lokacin Saratu ta tsani talaka bare mara asali, kuma tana zargin danta shege ne shiyasa batason asan labarin ta, wannan yasa ta Waura mata karan tsana a lokacin, taso ta shiga tsakaninta da sir mubarak lokacin da taji suna soyayya amma Allah bai nufa zataci galaba ba har saida Ya aureta Ya dauke ta daga gidan baban tare da danta ya mayar da su gidan shi karkashin kulawar shi =ؔ?

*(Wannan shine ta?aitaccen labarin Turai da Jazz)*



*BAYAN WASU SHEKARU DA RASUWAR ELDERS=?%?*





Katafariyar Jami'a ce da ke a cikin birnin Abuja, tana Waya daga cikin makarantun da suka shahara a faWin ?asar, kuma tana daya daga cikin makarantun da suka wadatu da ababen more rayuwa.



Shin meke faruwa ne a cikin wannan Hamshakiyar makarantar, naga interior designers daga kamfanin Zahra World Of beauty sun dage damtse sunata ?awata katafaren event hall din makarantar, da wajen Pool da kayan ado masu matu?ar Waukar ido da jan Hankali..


Ashe Yau babbar rana ce mai muhimmanci ga malaman makarantar, kasantuwar yau ce rana ta farko da za su fara yaye Waliban jami'ar da suka kammala karatu.


Gaba Waya Glass windows din Makarantar, da saman gate din makarantar wani hadadden rubutune ke displaying Wauke da sunan Jami'ar.



Da abaka labari ?wara ka gani da idonka, don haka ni ma bazan bari abarni abaya ba, dani za'ayi shagalin yaye daliban nan, saboda in bawa idanuna abinci...



Around ?arfe 12 na safe daidai agogon Nigeria ta buga, a wannan lokacinne School buses suka fara shigowa ta main gate din makarantar, Wauke da Students a cikin su, daga jikin buses din hada Tambarin makarantar da suke mai Wauke da sunan Imam Educational Institute (IEI)


Kaitsaye buses din suka nufi Parking space na jami'ar.

Na ?ura idanuna ina jira inga su wanene Waliban dake a cikin Buses din.

Lokacin da Bus divers din suka yi parking, kofofin motocin suka soma buWewa

Tabarakallahu


Gaba Waya na ruWe ganin Ex-prisoners na kurkukun ?addara suna fitowa daga cikin buses, sanye cikin uniform din su kyawawan gaske sun sauya daga ka gansu kaga ya'yan hutu wadanda suka gaji arzi?i.



Yan Secondry School Win suna a sanye da kyawawan Uniform Win su, ?an matan sun yi rolling head scarf, ya yin da mazan kowan nan su ka kalli kanshi haWaWWen haircut ne na wayayyu.


Admins din makarantar ne su ka yi inviting Waliban Makarantar Imam da iyayensu donsu taya yan uwan su murnar kammala karatu, dress code din da suka basu shine uniform din su shiyasa kowannan su ya sanya uniform din shi banda Yan jami'a su nasu kayan gidane as usual suna asanye da Casual dress na kece raini.


Rayuwa kenan, waya taba tunanin bayin Allahn nan zasu samu yan'ci da canjin rayuwa? Shiyasa kada ka taba fidda rai da rahamar ubangiji, babu wani yanayi na dundundun a duniyar nan, in ma bakaji dadi anan ba in kayi kyawawan ayyuka zakaji daWi aranar gobe ?iyama, fada ce ta Allah buwayi, dukkan tsanani yana tare da sau?i, kuma Allah yana tare da masu hakuri, ga misali nan mun gani arayuwar fursinonin kurkukun ?addara, rayuwarsu su ke yi cikin jin dadi da walwala babu takura, babu tashin hankali, babu fargaba, ba wahala sai zallar gatanci da jin dadin rayuwa.


ko wanda ya taso cikin gatantawar iyayensa bai kai su jin dadi ba ayanzu saboda kulawar da suke samu, babu abunda suka nema suka rasa sabanin da, da kullum cikin uniform daya suke, kulle adaki daya, cikin kurkukun karkashin ?asa, abinci sau daya arana, ba shige ba fuce, rayuwar ?unci da takaici, rayuwa mai cike da fargaba, rayuwa mara yan'ci amma yanzu komai ya zama labari >?)?


Fuskokin su Wauke da murmushi cikin raha suke fira a tsakanin su Yayin da su ke tafiya atsanake suka nufi event hall din da za'a gudanar da taron.

Katafaren event hall din Ya Cika makil da mutane babu masaka tsinke, ya kawatu da colorful balloons and streamers, ga wata katuwar banner mai Wauke da rubutun

*Congratulations Graduates!*


Daga gaban Hall din dogon table ne mai Wauke da Katon Cake tare da refreshments, and a microphone for the speeches, gaba Waya admins din makarantar suna a zaune kan kujerun gaban table Win.



da sauran manyan masu ruwa da tsaki a harkar ilmin kasar duk sun hallara, kowan nan su ya kure kur'adakansa shiga ta mutunci ta alfarma.


gaba Waya manyan bakin da aka gayyata tare da iyayen yaran suna a zaune kan kujeru na alfarma da aka kawata musamman saboda su.


Daga tsakiyar Hall din ?awatattun kujeru ne aka jera wanda asaman su Students suka zauna.


Daga gefe Waya na Hall din wasu hadaddun Chairs din ne musamman saboda Graduates din aka tanade su.


Graduates din suna asanye da graduation gown da suka Waura asaman outfit dinsu, launin navy blue with golden trim, sun sanya
Mortarboards On their head.


Yan Jarida da photographers sun hallara domin gudanar da aikin su.

Iskar Hall din ta gauraya da fragrance din mutanan dake a cikin shi.

Hayani ce ta cika ko'ina sai fira ake cikin raha da annushuwa...


Wasu gungun students na hango sun ke6e gefe daya suna tattaunawa atsakanin su ?asa ?asa kamar basu son aji me suke cewa.

"Unaisah bata picking call, bansan meyasa ba, tun kafin inzo hall din nan nake ta kiranta..." Sajeed ne ya faWa yana duba agogon hannunsa, shima yana daya daga cikin graduates

Haris Yace"nima inata kiranta bata Wagawa, Na kira Batool itama batayi picking ba, ban san me ya tsayar da su ba"! ya fada fuskarsa a yamutse.

"May be basu kammala shiryawa bane..." sajeeda ce ta faWa matashiya mai jini ajika, itama Graduate ce.


Zeenatu da ke a tare da su bata tanka ba, Saboda hankalin ta baya atare da su, yana akan wayar ta da take dannawa ga dukkan alamu da saurayin ta take chatting duba da yadda take sakin Murmushi, tayi kyau a cikin graduation gown din ta.


"Hmm Ko kuma suna can suna bacci ba" acewar Javed..

Sajeed yace "Bana so afara basu gama hallara ba, musamman Unaisah nasan dole a neme ta idan za'a bada award"



Kafin wani daga cikin su ya kuma yin magana, Sautin taken makarantar da aka kunna Ya katse hanzarin su, Kowa ya nutsu yana sauraron University Anthem din su..


Bayan da taken Ya ?are, Kowa Ya koma gurin zamansa, School Dean ya soma yin magana babban mutunne yana magana gently hankalin kowa ya koma kansa.



"Distinguished guests, esteemed faculty, proud parents, and most importantly, our graduating students, welcome to the graduation ceremony of the Freedom's Gate University"!



"Today marks a significant milestone in the lives of our graduates, It is a day to celebrate their hard work, dedication, and perseverance I am honored to lead this institution, and I am proud of each and every one of our graduates.."


Gaba Waya jama'ar dake a hall din suka soma yin clapping!


Fuskarsa Wauke da murmushi ya karasa Speech dinsa mai ma'ana..


Vice Dean of Academic Affairs ta Waura da cewa


"Today is a big day for us, a day we will never forget, a day of remembrance. It marks the first day our first student graduated from this university. Coincidentally, today is also the anniversary of the day we opened this school."



"Over the years, our school has gained fame and received awards from around the world, thanks to our talented students who have become symbols of our glory."



Wan dakatawa ta yi da yin bayanin idanunta akan mutanen dake sauraranta suna ta tafa hannayen su.



Numfasawa tayi cikin nutsuwa ta Waura da cewa"Before I finish my speech, Ina farin cikin gabatar da wadannan lambobin yabon ga hazi?an daliban da suka kammala karatun su, ha?i?a sun cancanci ayaba masu saboda ?wazon su da jajircewar su dan ganin sun cimma wannan matakin"!




da jin wannan maganar ta vice Dean nan fa hankalinsu su Sajeed Ya tashi jin shiru sauran ba su ?araso ba.



"ko bamu faWa ba, kun san su wanene waWannan fitattun da zamu kira sunayen su.."


Tunkan Ta karashe maganar students suka din ga ambaton sunan Unaisah da twins da Zeenatu saboda kowa yasan su da kaifin basira.


"ina fata suna a kusa kuma suna sauraron mu.."


Ta faWa tana bin graduates din da kallo kafin ta soma kiran sunan ukun farko kamar haka Sajeed Ubaid wadata, da Sajeeda Ubaid wadata, da kuma Zeenatu Ubaid wadata.

mi?ewa su ka yi daga kan kujerarsu, gaba daya idanu suka dawo kan su, suka ruke hannayensu cikin na juna, walking gently suka nufi kan stage fuskokinsu dauke da murmushin farin ciki..


Department Chair of cybersecurity ce ta dam?a ma Sajeed kyautarsa wani hadadden wrapped box ne mai faWi tare da certificates na shaidar kammala degree dinsa na farko.

hannayensa na kerma cike da zumuWi ya kar6a cikin girmamawa yayi godiya.


Director Of the Human Rights Program Ya bawa Sajeeda da Zeeenatu awards da gifts din su, cike da tsantsar farin ciki kowan nansu ya sanya hannu cikin girmamawa suka kar6a.

cikin harshen turanci su ka yi godiya tare da nuna irin farin cikin da su kayi, su ka kuma ba sauran yan uwansu dalibai shawarwari akan su dage da karatu su maida hankali ta yadda zasu zama wasu agobe.

Jama'ar da ke a hall din sai tafa masu su ke yi, musamman yan uwansu Walibai tsabar zumuWin su tayasu murna, suna ta daga masu hannu tare da ?wala masu kira..


Komai da ke faruwa akan idanun Hajiya sarah da su Alhaji ubaid da sauran Yan uwan su da su ka hallara, sam sun kasa rufe bakunan su saboda farin ciki kamar waWanda akayiwa albishir da gidan Aljanna.


suna saukowa daga kan Stage cike da zumuWi su Haris suka nufe su da fara su ka soma rungume su suna taya su murna, daga bisani suka nufi gurin iyayen su da ke tunkaro su, rungume su su ka yi sunata taya su murna.


Taken makarantar da aka kunna ne yasa Kowa yayi shiru tare da komawa mazaunin su..

Bayan da taken Ya dauke, Dean of the School ya soma magana


"And now, it is my pleasure to present the 'Excellence in Computer Practice' award to an outstanding graduate from the Computer Science (CS) Department."


gaba Waya hankalin masu sauraro ya koma kan shi cike da zakuwa suke jira suji karashen zancen shi.


"The recipient of this award is *UNAISAH ZAHEER TAJUDDEEN"!*


gaba Waya students suka soma tafi suna shewa saboda farin cikin jin Unaisah ce kamar yadda suka zata.


"I WILL REPEAT, UNAISAH ZAHEER TAJUDEEN, PLEASE COME FORWARD AND RECEIVE YOUR GIFT"


shiru Babu alamun mai sunan zata amsa.


Yan uwanta Walibai sai neman ta su ke yi a cikin hall din, kowa ya baza idanu yana jira yaga ta ina zata 6ullo sun san mawuyacin abune ta yi fashin zuwa school.


Rashin baiyanarta ya haifar masu da rashin jin daWi, daga malaman nasu har daliban da bakin da suka hallara gaba daya sun ?agu da su ganta kamar kamar me.

"UNAISAH ZAHEER TAJUDEEN! TANA INA NE? KO BATA ZO BA NE"?

Duk wani mai numbar wayarta saida ya jaraba kiranta amma kwata kwata bata picking daga ita har iyayenta ba wanda ba'a tuntuba ba.


Gunagunin da mutane suke yi ne ya cika hall din.

"Meya hanata zuwa"!

"Bata da lafiya ne"?

"In bata da lafiya meyasa ba'a faWa mana ba"?


Kowa da abun da ya ke faWa.


"Sir, Unaisah bata zo ba, bamu san dalili ba, saboda bata kira ta fada mana ba, kuma mun jaraba kiran layinta bata Wagawa",

Sajeed ne ya daga murya yana magana, Hankulan Kowa ya dawo kan shi.


"amma idan ka bani izni zanje gida na dubo ta..."


Vice Dean tace "mun baka izni sajeed ka yi sauri..." (sunyi mashi alfarma ne saboda muhimmanci Unaisah a gare su)


amsa wa yayi da toh bayan daya mikawa Haris gifts dinsa ya ruke masa, ya juya cikin sauri Ya nufi kofar fita daga Hall din.

Bai kaiga ?arasawa ba, Unexpected ta shigo ta kofar hall din da gudunta gaba Wa ya hankali ya dawo kanta..


Wow Tabarakallahu Ahsanul khalikin! Kamar ranar suka fara ganin ta, kowa ya ?ura idanun sa akanta.



Tana gudu graduation gown dinta na tashi sama saboda iskar da ta yayo, hakan ya bayyana Outfit din ciki data sanya, fitted gown ce ba?a, tayi tighting din jikinta ba Dan laifi, kamar a jikinta aka dinkata, daga wuyan rigan ta matse ma sha Allah in ka ganta bazaka taba cewa ?wailar nan bace ta kurkuku komai ya fito raWau, gudun da ta ke yi ne yasa jikinta ya dinga girgiza, musamman wide curvy hips dinta sun cika 6ul6ul da su.


Fatarta tayi haske sosai sai she?i ta ke yi tana walwali daga gani taji gyara da tsadaddun mayukan gyaran fata, ga wani shu'umin ?amshin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login