Showing 15001 words to 18000 words out of 321579 words

Chapter 6 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

daddy kada ka biyewa son zuciyarka! Nasan siyasa ce ke nema ta rufe maku ido shiyasa kuke gudun in auri Aisha kuma maganar nan har yanzu ma ba Wanda yasan da ita daga gidansu sai nan, dan Allah kubarni in aureta in rufa mata asiri, Nine fa nayi silar jefasu a halin da suke aciki ita da mahaifinta, meyasa ni ba za ku ga laifina ba sai laifinta ta? Ita da nayiwa fyade"?

hajiya layla Ta balbale shi da masifa tace"ko yaki ko yaso aisha ba mutuniyar kirki bace, abunda mahaifinsa ya fada akanta gaskiya ne, dama ita can bata yarda da ita ba, munafukar kullum tana yawo cikin hijabi kamar ta Allah, ashe maza take bi, gashinan zata bata mata tarbiyar Wa, don haka ta yanke duk wata alakarsu da sheikh Imam malik, zumuncinsu Ya kare.

Gaba daya suka juya ma Dr shureim baya, duk wannan abun dake faruwa Benazir bata sani ba, Saboda bata agidan ta tafi Abuja gidan Uncle Musa.


Shiekh Imam malik ya yi ta Jiran zuwan Alhaji Ubaid Ko shureim don Yaji daga garesu amma Yaji shiru wai malam yaci shirwa.

Har dai ya yanke shawarar zuwa gidan da kanshi don yaji ya ake ciki.

Bayan ya isa Security Officer din dake tsaron Gidan Ya shiga yayi mashi sallama da Alhaji Ubaid.

Sai ga Jam'in ya dawo yace mashi Ya shiga daga ciki.

A falon gidan Shiekh Imam Ya zauna kan Sofa Yana Jiran fitowarsu, Tsawon mintuna Sai ga Alhaji ubaid da Hajiya layla sun fito daga part dinsu, akan sofa suka zauna suna fuskarshi, tun daga yanayin fuskarsu Ya fahimci babu lafiya, kamar basu taba yin dariya ba, Koma arzikin gaisuwa bai samu ba.

ya yi tsammanin zasu bashi hakuri kan abun kunyar da dansu yayi ma yarsa, amma sai yaga akasin hakan, bayan da ya kora masu jawabin abunda ya kawo shi Alhaji Ubaid Yace Yayi hakuri ya rungumi kaddara, Amma shureim bazai auri Aisha ba, saboda sun yi bincike akanta sun gano ba mutuniyar kirki bace ta saba bin maza.."

bai dire maganar ba Sheikh Imam Ya doka masa tsawa Rai amatukar bace Yace"amma baka da Mutunci Alhaji Ubaid, ka bani mamaki, mutumin banza mutumin wofi, yau da kanka kake yiwa aishana kazafi? Yarinyar data taso agabanka tuntana karama kasanta farin sani, har alfahari kakeyi da ita saboda kyawawan halayanta, ba kamar yarka Benazir ba da kowa yasan bakin halinta data gada awurin jatumarta, Ni ban ta6a aibata yayanka ba saini zaka aibata nawa Ubaid? Akwai dan iskan dayawuce danka daya keta mata haddi? Nayi zaton in masifa ta same ni kaine mutun na farko da zaka fara rufa min asiri ka sharemin hawayena ashe na yaudari kaina!!...."

Dakyar ya ?are maganar hawaye wasu nabin wasu akan kuncinsa Yaji zafin maganar Alhaji Ubaid.

Hajiya layla ranta Ya 6aci matuka da jin yadda sheikh Imam Ke gaya magana akan ya'yanta, dama ba mutunci gareta ba, tana da sonkai, nata kadai ta sani, ko da take zumunci da su Albarkacin Alhaji ubaid suke Ci.

Nan ta shiga surfa mashi ruwan masifa zagi ta uwa ta uba kamar zata dokesa, saboda rashin kunya, kwata kwata sheikh Imam bai damu da maganganunta ba saboda yasan halinta, Bata da kunya fitsararriya ce, kuma dama ita tabarmar kunya da bori ake naWeta.

Alhaji Ubaid kasa magana yayi, saboda Zuciyarshi da tayi rauni saboda maganar Sheikh Imam malik ta karya Zuciyar shi, Ya danji tausayin shi amma da ya tonu hudubar da shaidan yayi mashi saiya canza ra'ayin shi.

Ya mike Ya fara gaya ma sheikh Imam magana Yace"ya jira ya ga abunda aka tura masa, zaisan ba kazafi yayi ma Aisha ba" Ya juya ya nufi dakinsa sheikh Imam Yana atsaye jikinshi na kerma zuciyarshi cike fal da tunanin menene Alhaji Ubaid zai nuna masa"?

Bai karashe zancen zucin ba, sai Ga Alhaji Ubaid Ya fito hannun shi ruke da wayarsa Ya mi?a ma Sheikh Imam"gayanan ka gani da idonka"

Yatsun hannunsa na kerma Ya kar6i wayar lokacin daya daura idanunsa akan Screen din wayar saida Zuciyar shi takusa dakatawa da bugawa saboda tsabar firgitar da yayi, a lokacin Jikin shi yadinga tsuma idanunshi suka kada jawur, baisan sa'adda Ya saki wayar Ta fadi kasa Ya juya cikin fitar hayyaci ya fuce daga gidan Yana tafiya kafafuwanshi na hardewa kamar zai kife kasa.

Bayan fitarshi Zainab mai aikinsu Taje ta fada na Dr shureum abunda Iyayensa sukayi na sheikh Imam Malik, Ransa ya 6aci a zuciye yaje ya same su ya dinga yi masu fada kamar zai doke su, Yace basu kyauta ba, meyasa zasuyi ma sheikh Imam haka? Shifa makwabcinsu bayan haka sunyi zama na amana, amma saboda rashin adalci da son zuciya sun rufe ido akan rashin gaskiya suka ci mutuncin shi, babban abunda yafi kona mashi rai abunda suka nuna ma Sheikh Imam ya gani, yaji zafi sosai, amma su ko a jikinsu.


Aisha tana zaune cikin dakinta a kan gado, tana tsaka da shayar da babynta, Baba Imam ya fado dakin Afujajan ko sallama baiyi mata ba, Jikin shi na zubda Gumi Yakai hannu Ya dam?i ?eyar Aisha da ita da yar duka Ya wurgo su tsakar falo Ta kife kasa Yarinyar ta fashe da kuka kamar ranta zai fita, Da gudu masu aikin gidan suka fito sakamakon Kukan Aisha da suka jiyo, Aunty Laura dake a cikin dakinta tana tsaka dayin waya tajiyo kukan Aisha dana jinjirarta, batasan sa'adda ta jefar da wayar kasa ta watsa da gudu Ta shigo falon tana haki, Gabantane ya yanke ya fadi ganin Sheikh Imam tsaye yana huci kamar mayunwacin zaki ga Aisha da jinjirarta yashe a kasa suna kuka.

Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un Ta faWa tare da nufar Aisha donta taimaka mata ta mike sai dai kafin Ta karasa Sheikh Imam Ya doka mata tsawa Yace"karki kuskura ki taba ta! Idan ba haka ba, abakin aurenki" cak ta tsaya jikinta na kerma.

"Allah Ya isa tsakanina dake Aisha, Allah Tsine maki Albarka, In sha Allah sai kinga sakayyar abunda kikai min" waro idanu waje Aunty laura tayi, Hankalinta amatukar tashe, gashi ba halin tayi magana balle ta dakatar da shi, maids din suka daura hannayensu asaman kansu cike da tashin hankalin jin furucin sheikh Imam ga yarsa, ba su taba zaton zai yi mata haka ba, su din amintattunsu ne, koda asiri Ya tonu agidan suka gane Aisha tana da ciki basu ta6a nuna sun sani ba saboda basa son abunda zai zubar da martabar sheikh Imam da ita Aisha.

"Kin cutar da rayuwata kin yaudareni Aisha, Idan aure Kikeso Meyasa ba zaki fada min ba inyi maki!? Sai kika zabi ki zubarmin da mutunci na, inayi maki kallon mutuniyar kirki ashe ke din fasika ce, mara tsoron Allah, Dama tun farko banso Kika je Germany karatu ba saboda hankalina bai kwanta ba, ashe bayan da kika je karuwanci ki ke yi acan, naga komai Aisha an nuna min videos dinki da hotunanki tare da kato, Yau silarki An zageni anci mutuncina Aisha wlh nayi danasanin haihuwarki da akayi"W'



*DAGA AL?ALAMIN BOSS BATURE=?%?
'?*



*Game bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*=?%?=؋?=؞? &?=ؔ?=؞?>???







~___________________________________~




fashewa tayi da matsanancin kuka sam ta kasa buWe baki ta yi magana saboda bakin cikin tsinuwar da mahaifinta yayi mata, bata taba zaton zaiyi mata haka ba ko da kuwa ta aikata abunda ya ke zargin ta da shi, ta rasa gane wanene yayi mata kazafi? Laifin me tayi masa"?

A lokacin Aunty Laura kasa jurewa tayi, tana jin koda zai sake ta ne sai tayi magana, Cikin fushi da nuna bacin rai tace"wallahi ka bani mamaki baban Aisha! Idan rai ya baci ai hankali bai kamata ya gushe ba, shin Ina ilminka ya ke da har zaka bari shaidan da zuciya su rinjaye ka! Kai fa ba mahaukaci bane, Da hankalin ka amma tayaya za'ay wa yarka kazafi ka yarda harka dauki mummunan mataki akanta...." bata kare maganar ba, sakamakon Marin daya kifa mata akan kuncinta, tuni hawaye sun cuccuko tab da idanunta, taji zafin marin da yai mata.

Ganin hakan Yasa Maids din gidan suka sha jinin jikinsu, daya bayan daya suka bar falon zuciyarsu cike fal da tausayin Aisha da babynta.

Murmushi Aunty laura tayi tana kallon cikin idanunshi da suka kada jawur sai tsuma yakeyi yana huci..

"Bazan fasa magana ba wlh, ko da zaka kashe ni ne! Wlh ka bani kunya kuma ka bani mamaki, sannan kaji kunya wlh, Tun wuri kayi gaggawar janye hukuncin da kayi ma Aisha tunkafin kayi danasani! Abune da ka sani na sani, kai da Aisha kuna da makiya masu jin haushin daukakar da Allah yayi maku kai baka tunanin sune suke kokarin 6ata maku suna? Bayan haka videos din da kake ikirarin an nuna maka ka ganta da ?ato Ka duba dakyau ba fuskarta aka dauka akayi editing ba"? Ta jefa mashi tambayar tana akai masa harara sam baya fahimtarta, ya riga daya hau kan dokin zuciya..

Sassauta muryarta tayi"yakamata ka dinga amfani da kwakwalwarka da kuma saninka, idan Aisha batayi abun kunya ba, to kai ne zakayi babban abun kunya, haba Imam ko da ace Aisha ta aikata laifin da kake zargin ta, kai ba maiyi mata uziri bane kaja ta ajiki don ta shiryu, korarta da za ki yi shi ne mafita? Hmm duk dai inda Aisha zataje Yarka ce, Kuma kowa yaganta zai ce diyar imam malik ce, Kaga kuwa babu ribar korarta! bana so kayi danasani mara amfani ...."

Kalaman Aunty Laura sunso suyi tasiri acikin Zuciyarshi, Amma duk idan Ya tuna abun da idanunsa suka gane masa sai yaji wani irin kunci a cikin zuciyar shi, saboda shi yasan wacece Aisha, yana da tabbacin videos din da aka nuna mashi ba editing bane itace da kanta"


Sheikh Imam bai dauki hudubar Aunty laura ba, ya ce ma Aisha ta tashi Tabar mashi gidan shi! baya bukatar ganinta, yana karashe maganar ya fuce yabar gidan.

Maids din da Aunty Laura suka kewata sunata aikin lallashinta da bata hakuri, bata taba ganin bakar rana irin ta yau ba, har addu'a tayi Allah ya dauki ranta ta huta amma dayake Lokacin mutuwar nata baiyi ba sai bata mutun ba.

Kasa tafiya tayi saboda bata son ta tafi, mahaifinta Yana fushi da ita, ga tsinuwar da yayi mata, tafi son Ta roki yafiyarsa inyaso saita tafi.

Tsawon kwana uku tana zuwa dakinsa donta bashi hakuri bai ta6a sauraronta ba, Ko gaisuwarta baya amsawa, gaba daya ya Wauke ?afa da yi mata magana, ko kallon ta bai son yi.

Aunty laura ta yi kokarin ta tunbi Hajjonsu don ta sanar da ita abunda ke faruwa don tasan ita kadaice zata iya take mashi burki A lokacin da take kokarin kiran layin Hajjo batasan sheikh Imam Ya shigo dakin nata ba, aiko batai aune ba, taji ya fusge wayar ya Maka ta da kasa ya take ta da kafarsa, yana huci ya gargadeta akan in ta kuskura ta fada ma wani wlh abakin auren ta, ba arziki taja bakinta tayi shiru ta zubawa sarautar Allah ido.

Aisha ta shiga tsaka mai wuya, damuwa takusa tayi mata illa ko ma ince tayi mata illa, da abun ya ishe ta, ta kunna wayarta sakonni sukai ta tururuwar shigowa, ko Waya batayi sha'awar budewa ba ta lulubo layin Anila ta danna mata kira, don bata jin zata iya fadama Benazir saboda sun fita aranta batason komai daya shafe su.

Lokacin da Anila taga kiran malama Aisha tayi mamaki bayan tsawon watannin data dauka bata neme su ba.

Bayan ta daga kiran tayi ta tambayarta meyasa ta yada su? In sun kira basu samun layinta, kuma tayi tafiya ko sallama ba ta yi masu ba.

Cikin shesshekar Kuka Aisha ta kwashe komai daya faru ta sanar da Aneelerh, Aneelerh Tayi kuka taji bakin ciki da takaicin abunda dr shureim yayi mata, Duk da tasan ba halinsa bane, kuma taji zafin Hukuncin da baba Imam yayi ma Aisha, sannan taji tausayinta sosai, Aisha tace mata tayi danasanin zuwanta germany karatu saboda anyi mata kazafi an daura mata laifin da bata aikata ba, Hankalin Aneelerh ya tashi sosai har tace mata zatazo gidan tare da Abie da Mami donsu tayata bashi hakuri ya yafe mata.

Cikin sauri Aisha tace karta kuskura ta fada masu halin da take a ciki, Baba Imam yana da bad temper idan ransa ya 6aci baya ji baya gani sai daga baya ya ke yin danasani, Idan har yasan ta fada mata abunda ke faruwa da ita, to kuwa zai kara hukuntata ne, amma ta roke ta akan ta tayata da addu'a in sha Allah komai zai tafi daidai.

badan Aneelerh taso ba tace mata toh amma dan Allah kar ta tafi ta zauna agidan, idan ma ya matsa mata akan ta bar masa gidan toh toh tazo gidan su ta zauna, Aisha tace mata toh.

Bayan sun kammala waya Aneelerh bata ?ara samun kwanciya hankali ba, saboda zullumi da fargaban kada Aisha ta tafi, gashi ta hana ta faWa ma Benazir halin da take a ciki ta kuma hana itama tazo gidan saboda gudun kada laifinta ya shafe su.

Tayi azan Baba Imam zai sassauta hukuncin daya yanke mata, Ganin har anyi kwana biyu bai kara yi mata maganar ba, haka Aunty Laura ma tayi tunanin yaji nasihar ta ne shiyasa ya ?yale Aisha, Hankalin su har ya dan kwanta.

a daren wata ranar Alhamis, tana tsaka da yin bacci, ta rungume babynta da ke bacci akan kirjinta, Sai ga sheikh Imam Ya fado dakin Yana huci Ya tashe ta daga bacci Yace ta tashi tabar gidan bai son ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ganinta, Ta yi nesa da shi idan ba haka ba zai kashe yarta, Ya tsaneta baya son ganinta kuma wlh in har ta bari wani yasan tayi cikin shege ta haihu Sai Ya lahantata, tace mashi baba kada kayi min haka! Idan ka kore ni a cikin daren nan ina kake tunanin zan tafi? Bayan ka hana in nemi taimakon dangin mu, nifa yarka ce baba, amana ce agare ka, nasan da mahaifiya ta, tana araye wlh koda ace ni karuwace ba zata kore ni ba, saima taja ni a jikin ta don in shiryu, balle kai da ka taso tare dani ka sanni ciki da bai, ka tarbiyantar dani, kuma ka yarda dani amma a yau kaine kake korata? Saboda kaddara ta afka min? Bai Saurareta ba, Tana kuka ta sauko daga kan gadon, ko Aunty laura bata sani ba adaren ranar shekh imam Ya kori aisha daga gidan Har bakin gate Ya rakata Bata dauki komai nata ba sai yar wayar data tsira da ita.

a bakin gate din gidan Alhaji Ubaid ta tsaya hannayenta rungume da jinjirarta dake ta sharar baccinta.

Tana kuka Ta kalli sararin samaniya taga hadari ya hadu bakikkirin Babban tashin hankalinta kada a barke da ruwa sama batasan Ina zata sanya yarta ba.

Anan ta yanke shawarar kiran dr shureim duk da bata da tabbacin yana nan ko bai nan don tunda abun nan ya faru bata kara jin duriyarshi ba tun da ba fita ta ke yi ba, wayarta kuma akashe take, ko ya kira ba sani zatayi ba.

sau uku tana Kira baya Picking, sai ana hudune taci sa'a yai picking tace"shureim ina a kofar gidanku, Baba Imam ya kore ni daga gida, Ka zo ka kar6i yarka, idan ba haka ba zaka rasata ne"! Tana karasa maganar, ta kashe kiran.

Ko mintuna biyar ba ayi ba sai ga dr shureim Ya fito jikin shi sanye da jallabiya, kallo daya da yayi ma Aisha saida gaban shi ya fadi ganin yadda ta rame idanunta sun kaWa jawur sun kumbura, A lokacin yaji kunyar hada ido da ita kamar ya ha?a ?asa ya binne kanshi, tsantsar tausayintane ya kama shi sam bai ma lura da babyn hannunta ba.

Karasawa yayi kusa da ita, harya bude baki zaiyi mata magana ta dakatar da shi"ban kiraka don muyi magana ba, Yaya shureim nagode da abunda ka saka min da shi," ta fada tare da manna mashi yarinyar da ke a nannaWe cikin towel dinta a kirjin shi yai sauri rungumeta wani irin sanyi yaji ya ratsa zuciyar shi.

"Gatanan Itace abunda muka samu, nabar maka ita amana, badan bana sonta ba na baka ita, sai don bana so tasha wahala tunda ni yanzu bani da kowa banma san inda zan tafi ba, wata rana zan dawo in kar6i abuna, Inaso kayi mata huWuba da sunan mahaifiyata FATIMA BATOOL, Idan har kabari rayuwarta ta cutu ka sani Allah yana sama yana Kallonka, Nima kuma bazan yafe maka ba, akwai ranar hisabi"

maganganun Aisha sun karya mashi zuciya, baisan sa'adda ya fashe mata da kuka ya dinga yi mata magiya akan kada ta tafi tabarshi wlh yana sonta ashirye yake da ya aureta yayi mata alkawarin zai wanke laifinsa zai share mata hawayenta, zai kula da rayuwarta, tace mashi ya makaro, Lokacin daya kamata ya furta mata hakan ya riga daya wuce, sai bayan daya 6ata komai, sannan ita bazata taba auren namijin daya santa ba.

Ba yadda baiyi da ita ba amma ta kafe, har cewa yayi ta shigo ta kwana agidansu amma takiya, ta juya zata tafi yabi bayanta yace sai dai su tafi atare saboda bazai iya rayuwa batare da ita ba, sannan Yar da tabar masa, shi baida abunda zai shayar da ita ta taimaka ta dawo suyi aure su rufawa kansu asiri da kuma yarsu.

Aisha bata saurare shi ba, da taga dagaske Dr shureim binta zaiyi sai ta watsa da gudu Shima yabita aguje a karshe ta bace ma ganin shi... =?-?

Tun daga wannan Lokacin dr shureim bai kara ganin Aisha ba, babu wanda yasan Ina ta dosa, Anila saidai taga sakon data tura mata.

_Aneelerh bazan Iya jurewa ba, ko gaisuwata bai amsawa, bansan shi wani irin uba bane, ni dai banyi dacen iyaye ba, Yanzu haka da nake rubuta maki text Win nan, Ina akan hanyar zuwa airport wlh idan nabar ?asar nan bazan sake dawowa Cikinta ba, tun da yace baison gani na, aneelerh agaban kowa Yaci mutunci na, agaban maids Win gidanmu, yayi mun korar kare hada tsine mun yayi kamar wani jahili shi baisan ?addara ba ne? Idan har na biyewa zuciya zansha poison ne in mutu."_

A daren ranar bayan Dr shureim Ya koma da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login