Showing 210001 words to 213000 words out of 321579 words

Chapter 71 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

masa ba akan ya tausayawa rayuwata, ya daina aikata fasi?anci da ni, shi fa musulmi ne kuma yasan babu kyau, namiji ya kusanci macen da ba muharramarsa ba! Haramun ne, ko don saboda mutuncinsa da na iyalinsa ya rufawa kansa asiri ya ?yale ni, in ba haka ba zan gudu in bar masa gidan, bayan na tona masa asiri...

Ba irin barazanar da ban yi masa ba, amma ya ?i saurare na. Bai da imani bai da tausayi, mugu ne..."

ta Wan dakata tana share ?wallarta, fuskarta akan Camera..

*"_watakil lokacin da zaku kalli video din nan, bana a raye na mutu, saboda ya ce ba zai kyale ni ba dama yake jira da zai kashe ni, kuma kun ga ni kaWai ce a gidan, yanzun nan na ga shigowar shi shiyasa na gudo Waki don in samu damar yi maku video. Don Allah don son ku da manzon Allah saw a duk lokacin da kuka kalli videon nan ku yi gaggawar kaishi ?ara gurin hukuma, sannan ku gudu daga gidan nan, kada ku 6ata lokaci, saboda shi Win mutum ne mai haWarin gaske, ya sha yi min barazana akan in har na kuskura na faWa ma wani abun da ya ke mini wlh sai ya kashe ni bayan haka zai kashe duk wanda na faWamawa shi yasa na kasa sanar da ku..."_*

Bata ?arashe maganar ba ta yi saurin katsewa, bugun zuciyarta ya tsananta jin takun tafiyarsa gab da Wakinta.

Cikin sauri ta janyo pillow ta zuge zip Winsa ta fasa soson ciki ta tura wayar a ciki ta maida ta rufe, juyowar da zata yi keda wuya kwatsam ya banko ?ofar dakin ya shigo.


Cikin rawar murya ta furta, "La'ila ha illa anta subhanaka Inni kuntu minazzalimin!"




*Daga Al?alamin Boss Bature=ؗ?=?%?*

?yal?yacewa ya yi da tantiriyar dariyarsa ta shaiWanu tare da Waura kwartayen idanunsa akan fuskarta ya shiga washe jajayen ha?oransa...

"Dama saida raina ya bani zaka dawo don ka cutar da ni! Wai kai wani irin shaiWanin mutunne? Mara imani da tausayi? Meyasa ba zaka rabu da ni ba?

"Saboda kinsan sirrina! Ba zan ?yale ki ba, ke barazana ce a gare ni..." Bai ?are maganar ba ta katse shi cikin fargaba ta ce, "In har baka fara bibiyar rayuwata ba, tayaya ni zan san sirrinka? Meyasa kake aikata fasi?anci da ni? Laifin me na yi maka? Kawai don ka azabtar da ni? Wallahi ?wara na mutu da in ci gaba da haWa jikina da naka! Kasa na tsani kaina, saboda ?azantar da kake goga min!..."


Cikin shesshekar kuka take yin maganar idanunta a cikin na shi, "Ba zan ?ara bari ka kusance ni ba, ko dai ka fita daga rayuwana ko kuma in tona maka asiri uban kowa yasan me kake aikatawa..."


Ko gizau bai yi ba, sai ma wani shu'umin murmushi da yake saki, "Tun da har kin san komai, kuma kina barazanar zaki fallasa sirrina, ba zan ?yale ki ba Ana, dama na faWa maki dama nake jira da zan salwantar da rayuwarki kuma na samu...!"


Gaba Waya ta ruWe da jin maganarsa, gumin tashin hankaline ya fara tsattsafowa ta ko'ina a jikinta, kafin ka ce me tuni tsigar jikinta ta fara tashi hai?am, la66anta na kerma ta shiga ambaton inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un!


Ja da baya ta soma yi tana neman hanyar da zata ku6uta daga gare shi, duk inda ta yi sai ya taro ta, gaba Waya suka hargitsa Wakin nata, ta dinga Waukar abubuwa tana jifar shi da su, ba yadda bata yi ba don ta ku6uta amma ta kasa saboda ya toshe duk wata hanya da zata iya guduwa, a ?arshe ya dam?i wuyanta ya maka da bango ya matse ta, idanunta suka firfito waje, numfashinta ya soma kokawar Waukewa, ta dinga fitar da nishi tana harba ?afafunta..

Cikin shakakkar murya ta furta, "A.. Al... Allah bab ba zai ta6a barin ka ba, Allah sa...ssai ya saka min cutarwar da kayi min, idan kana tunanin kashe ni shine mafita ka jira ka gani, ni zanyi silar tonuwar asirinka, kaima zaka mutu ne... "


Akan idanunta ya girgiza jikinshi ya ri?iWa ya sauya suffar shi ya zama dodo, tsantsar tsoro da tashin hankali mara misaltuwa suka ziyarci zuciyarta, duk da tashin hankalin da take a ciki bakomai take tunanowa ba face ?an uwanta da Aunty Anila sune damuwarta, babban ba?in cikinta zata mutu batare da ta fallasa asirin shi ba. Bata da mafita da ya wuce Allah, yana kallonta da idanunsa da babu Wigon imani a cikin su, A haka da ya sha?eta jikin bangon kokarin keta mata haddi yake yi.

Tana a cikin mawuyacin halin nan kwatsam idanunta suka hango mata Baby Junaid dake kokarin buWe ?ofar dakin ta, ya zuro hannunsa ta ciki.

Wani irin faWuwar gaba ta ji, kamar ta fasa ihu, saboda tsoron kar ?an Iya ya gansa don tasan muddin ya gansa sai ya kashe shi.


Da ?arfi ta dinga yin kuka tana fasa ?ara, duk don ta hana shi jiyo sautin muryar Junaid dake kiran sunanta.


Junaid da ya ji kukanta, ya fago da idanunsa kaitsaye suka sauka akan bayan Wan iya, a firgice ya razana tare da kware bakinsa ya fasa gigitacciyar ?ara ya bi ya ruWe tsigar jikinsa ta shiga tashi ganin dodo.


Wani iko na Allah kwata kwata dan iya bai jiyo shi ba, kuma ya bashi baya, kuma harda ihun da Ana ke saki ya hana ya jiyo kukan Junaid.


Girgiza kanta ta dinga yi, da hannu ta dinga yi masa alamar ya gudu ya gudu.

Nan take Wan iya ya ji aransa akwai mai kallonsa, yana kokarin juyawa,

Junaid da ya gama razana cikin ikon Allah tsoro yasa ya juya a guje ya nufi Wakin mommynsa, yana gudu towel dinsa na ?wancewa, har tuntu6e ya yi ya faWi ya mi?e da ?yar yana kuka ya shige Wakin su.

Yana shiga ya fara neman gurin da zai 6oye kansa.


Jikinsa na kerma ya buWe wardrobe, ya taka gidan farko ya ru?e na biyu da hannayensa ya haye sama ya kutsa cikin kaya ya 6oye, adai dai lokaci Wan iya ya saki Ana ta yanke jiki ta fadi ?asa bata mutu ba sai dai ta fita hayyacin ta.


Ya juya cikin sauri ya fito daga dakin ya soma neman wanda ya shigo gidan ya dudduba ko'ina bai ga kowa ba, har Wakin Anila ya shiga a lokacin Baby Junaid ya daWe da sumewa, bai ji wani sauti ko alama da zai bayyana masa akwai mutun ba.


Hankalinsa ne ya kwanta da ya tabbatar babu kowa kuma ya tuna basu dawo ba, ya baro su acan gidan Abdallah babu wanda yasan ma ya dawo gida.

Lokacin da ya koma Wakin ya taras da Ana, sungumarta ya yi a saman kafaWarshi ya 6ace daga inda yake ya dira a Wakin sirrinsa, ya ajiyeta anan bayan da ya kafeta da sihiri ta yadda bazata iya ta6uka komai ba in ba da izininsa ba, ko magana ba zata iya yi ba, balle ta motsa jikin ta, kwata kwata bata a hayyacin ta. Ashe tsawon lokacin da suke ta neman Ana tana a Wakin sirrinsa, shi kaWai ya san inda ya 6oyeta, ba ci ba sha, bata iya komai, ta zama mutun mutumi, babu rabon Ana ta rayu, ya riga da ya gama da ita.

Daga baya ne da ya tabbatar ta mutu sai ya ha?a rami ya binneta a ciki, sati Waya kafin zuwan Isod Agents, shiyasa lokacin da suka ha?a ramin suka taras da gawarta bata yi komai ba saboda bata daWe da mutuwa ba da kuma ikon Ubangiji.. >?y?



RIJF (ANAH)


(Kunji komai da ya faru a tsakanin ?an iya da Ana)


~__________________________________=?%?

"Cau cau, gafara dai, namiji Uban maza, The mastermind behind the conspiracy da girman kujerarka Uban munafukan duniya, sarkin mugaye, an buga da kai an barka Jan wuya Alhaji Musa. ?aramin su babbansu, ko ku ce big boss, duk nine. Mai izza, mai arzi?i, mai jiji da kai, shugaban azzaluman duniya, wanda mutuwa ke tsoronsa, dodon dodonni, wanda ya fi ?arfin kowa saboda sihirin sa..."



Kirari ya ke yi ma Alhaji Musa yayin da ya ke shiga cikin Cell Win da ya ke. (=??)



Abun al'ajabi ba ya ?arewa duniya, ni kaina da nake rubutawa saida na razana da ganin Wan tahalikin nan, gar?ame a cikin Cell, wato ruwa ne ya daki babban Zakara.



Ba ka jin komai sai sautin nishinsa da gurnaninsa kamar wani namun dawa, yana a zaune dirshan a ?asa kamar mabaraci, ko suturar kirki babu a jikin shi, sai gajeran wando ba?i, ?afafunsa a Waure suke da leg irons.


Dana kallesa sai da gabana ya faWi ganin yadda halittarsa ta sauya, rabin fuskarsa ya lalace sakamakon Acid din da Unaisah ta watsa masa, fatar gurin ta zagwanye gwanin ban ?yama, da ido Waya yake gani Sakamakon ruwan acid din da ya shiga idonsa Waya ya lahanta shi, gaba daya fatarshi ta lalace da raunukan bulalan da Evils suka yi ma shi har yau bai daina jin raWaWin azabar su ba, idan suka fara masa zogi ba halin ya sosa saboda da zarar ya sosa sai fatar ta Wuri ruwa ta fashe ta dinga fitar da gur6ataccen ruwa mai Woyi, kafaWarsa ta hagu da Unaisah ta yanka da zarto ta kumbura suntum har surgery aka yi masa a gurin amma still bai warke ba, ciwon har ya shafi hannunsa na dama ya kumbura suntum ya zamar masa jalli joga.

Gaskiya Unaisah ta lahanta bawan Allahn nan ba kaWan ba, da zai samu damar da zai ku6uta wallahi ita ce mutun ta farko da zai fara kashewa har lahira, a yanzu haka da yake zaune wutar ba?in ciki ce ke ruruwa a cikin zuciyar shi.



idonsa ya kaWa jawur kamar an watsa barkono a cikin sa, ga wani jan ruwa da ya kwanta a ciki.



Yana jin kirarin da DG ke yi ma shi, ya murtu?e fuska kamar gwaggon biri saboda muni, ?yan?yami da ?yamarsa ne suka cika Owais ya kasa zama sai dai ya tsaya a tsaye, ya toshe hancinsa da hanky.



"Allah ya yafe maka Musa, tun a duniya kenan ka fara ganin sakamakon zunuban daka aikata, ina ga idan aka binne ka inda dukiyarka ko wani abu da kake ta?ama da shi ba zai cece ka ba sai mugun halin ka? Ko da yake ba zuwa na yi don in yi fira mai tsayi da kai ba, nasan yanzu ka gane Allah Waya ne! Da juyi Waya Allah ya rikito da kai, ya kar6e komai da kake ta?ama da shi, ya Webe albarkar rayuwarka, ya raba ka da kyawun suffarka! Ya kar6e dukiyarka da ?arfin sihirinka! Ya raba ka da kowa naka, ya kuma zubar maka da mutuncinka, ya bar maka ranka da ba?ar zuciyarka don ka ga ishara da idanunka, kai hatta ?an jami'iyarka sun soke ka daga member Win su, sun ma ce a ?addara cewa basu taba saninka ba, saboda kowa gudu yake ya ra6eka ta shafe shi. Matarka tana a kwance gadon asibiti rai hannun Allah, tun lokacin da ta ji abun da ka yiwa jinjirarta daka raba ta da ita, nan take ta yanke jiki ta faWi, yayanka Alhaji Ubaid ya yafe ka daga zuri'arsu, ya ce a daina ma kiran ka da Musa Wadata, saboda Alhaji Mu'azzam Wadata ba ubanka bane, ya fayyace ma kowa dangantarku, mahaifiyarku ?ar aiki ce a gidan su, halinta sak irin naka, bayan da mai gadin gidansu ya yi mata ciki, ta ?ulla makirci ta ce cikin Alhaji Mu'azzam ne, sai da tasa ya aureta bayan ta yi silar mutuwar mahaifiyar su Alhaji Ubaid, ta asirce Alhaji Mu'azzam, da ta haifo ka, ta ci gaba da mu'amala da mai gadin gidan, harta samu wani cikin ta haifi ?anwarka, saboda Mu'azzam ya samu matsalar haihuwa, ?a'?anta duk ba nashi bane, ta yi ne don ta ci gadon shi. Abun da na fahimta, shaiWaniya ce ta haifi shaiWan, mugun halinka a nono ka tsotse shi..."


Tunkan Owais ya ?arashe maganarshi Musa ya fasa wata irin kururuwar ba?in ciki, har saida gefen bakinsa ya fashe jini ya dinga WiWWigowa, dama a raunace bakin yake, abun da ya fi tsana a rayuwar sa shine tushen shi, wani ?ululun ba?in ciki ne ya tokare zuciyarsa, ya ji zafi da Alhaji Ubaid ya fallasa sirrinsa wlh da zai gansa a gabansa ba abun da zai hana ya binnesa da ran shi.


Yana gurnani cikin fushi ya furta, "Idan ma kana faWamin ne don in saduda, to ka daina, ba a halicci zuciyata da rauni ba, ba zan ta6a karaya ba, ba abun da zaisa na yi nadamar abun da na aikata!"


?yal?yacewa da dariya Owais ya yi hakan ya 6ata masa rai..


"Ina mamaki ne mutumin da rabin fuskarsa ya lalace, ba hannu Waya, ba ido Waya, wai shine ya ke da audacity din da zai iya furta wannan maganar? Me ya rage maka da bazaisa ka yi nadama ba? Bayan ga tsoro nan da tashin hankali kwance cikin idonka...."



wata shu'umar dariya ya saki kamar jaki na haniniya.


"Na ci dubu sai ceto, ba yadda kuka iya da ni, na riga dana ci riba, babu hukuncin da za ku yi min wanda zai kai wanda na yiwa rayukan dana azabtar, raina Waya ne tak, da shi na kashe Waruruwan rayuka, da shi na azabtar da rayuka, da shi na 6ata zukatan rayuka, wanda har abada ba za a ta6a mantawa da ni ba.."


ya faWa yana damula mummunan bakinsa.


Owais ya ji zafin maganarshi, ganin kamar babu alamun karaya a tare da shi, a ransa ya furta wannan wani irin shaiWanin mutunne? Anya mutun ne Musa? Gaba daya Elders sun saduda banda shi, in wani ne yake a halin da yake a ciki wlh ko kalmar alifun bazai iya furtawa ba, amma da ya tuna wanene Musa gurin girman kai da izza sai ya fahimci koda ya karaya ba zai bari ya gane ba ko dan ya ba?anta masa rai.


Hakan yasa shi sakin murmushin gefen fuska.


Kafin ya soma yin magana cikin nutsuwa yana kallon cikin idanunsa.


"WaWannan rayukan daka azabtar yanzu suna a cikin rahamar Ubangiji, sun barka da tarin hakkinsu akan ka, idan kana farin ciki saboda ka zalunce su to ka daina, kanka ka zalunta Musa! Ai kai musulmi ne, kuma ka san Allah baya yafe hakkin dake atsakanin bayinSa. Me ya ja ma shiga halin da kake a ciki?" Ya faWa yana nuna sa cike da ?yan?yami.


"Hakkin waWannan rayukan, sune zasu baibaiyeka da fitintinu iri iri har abada, bayan haka bari na yi maka fashin ba?i tun da na fahimci kai dabba ne, jahili, kuma da?i?i.."

cikin fushi ya ke jifar Owais da harara da idonsa Waya kamar ?wayarsa zata faWo ?asa.

"Yanzu na ?ara yarda cewa zalunci ?ai?ayi ne da ke komawa kan me shi?a, abun da baka sani ba, silar tonuwar asirin ka, ?ar ka Zeenatu ta kashe kanta saboda jin wanene Ubanta da kuma zaluncin da ya yi ma ?ar uwarta Unaizah..."

bai ?are maganar ba Musa ya yi wata irin zabura kamar zai mi?e, ya zaro idonsa waje cikin tashin hankali da ba?in cikin jin abun da kunnuwansa suka jiye ma shi.

"Meyasa na ga tun yanzu ka fara karaya, ai ban kai ka in da na ke son ka je ba, bayan haka rayukan daka ?ullawa makirci cikin kankanin lokaci sun warke daga raWaWin da ka ?unsa musu, Shureim da Ummi suna atare da ?ar su Batool, da zarar mun gama shari'arku, zamu shafa fatihar auren su..."


cikin ?unci da damuwa ya ?ara murtuke fuskarsa, ji yake kamar ya binne kansa don bakin ciki, zuciyarsa sai tafarfasa take yi..


"Sheikh Imam malik, da ka ?ullata a ranka, ka daWe kana zaluntarsa don ka ?unsa masa bakin cikin da zai yi silar mutuwar sa, a yanzu haka yana nan da ransa da lafiyarsa, harma ya je gano matarka Sarah da ke a kwance gadon asibiti, ka duba ka ga fa duk irin cutarwar da ka daWe kana yi masa bai ji komai ba.."


Wata wutar ba?in ciki ce ta taso mashi ya dinga buga kansa jikin bangon bayansa, jikinsa ya Wau zafi rau, ya Ilahi, Ya rasa ina zaisa ranshi ya ji dadi? Duk tsawon lokacin da ya Wauka yana wahalar ?ulla masu makirci don ya ba?anta masu rai kenan yanzu komai ya tashi a banza? Hakan na nufin ha?arsa bata cimma ruwa ba? Kwata kwata Imam bai ji zafin komai ba a ransa? Shifa duk a zaton shi imam malik yana a kwance gadon asibiti rai hannun Allah, ciwon zuciya ya kama shi ashe wai har yana da kuzarin da zai iya taka ?afar sa!


Chief Owais da ya lura ya haWa masa sha tara na ba?in ciki wani sanyi ya ji yana ratsa zuciyarsa..


"Ka kwantar da hankalinka mana ai ban ?arasa maka labarin ba, ?anwarka Laura..." Zare idanunsa ya yi cikin damuwa.



"Sakamakon razanar da ta yi lokacin da ta ji komai game da kai, ta haWiyi zuciya ta mutu."



gigicewa ya yi gaba Waya ya rikice har baisan sa'adda ya fara cizge akaifunsa ba, duk ya faffasa su, jini ya dinga tsattsafowa.


"Sannan, na ji abun da ya faru da kai, na taya ka ba?in ciki, ashe shatun bulalin jikinka, Evils ne suka zane ka, bayan sun tu6e maka suturarka ka dinga ihu kana kuka, suka shafe maka jikin ka da gishiri suka jefa ka cikin ruwa, na ce dama tsakanin shaiWan da Wan uwansa shaiWanu ana samun sa6ani? Sai kuma na ji wai na hannun damanka Mark ne ya ci amanarka, ya musanya maka zuciyar Batool da ta giant, abin takaici! A ?arshe burinka bai cika ba, kuma zaka mutu baka cika shi ba...."

Wani nishin ba?in ciki da Alhaji Musa ya saki nan take ya burkuta zawo a cikin wandonsa, wari ya cika cell Win.

Chief Owais ya toshe hancinsa da bakinsa da hanky, har sai da ya yi kakarin mai.

Da ?yar ya iya furta, "?ato da kai kana sakin kashin zaune, ko ka yi zaton ni kaWai nake tare da kai..."


Ya faWa tare da nuna masa surveillance cameras Win dake a kowace kusurwa, "Ba wai iya jami'an isod ke kallon ka ba, duniya ce take kallonka..."


Wata zabura Alhaji Musa ya yi jikinsa ya hau kerma kamar mazari, tashin hankali tsantsa ne akan fuskarsa, kunyar duniya ta kama shi.


6a66akewa da dariya Owais ya yi, "Haba ranka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login