Showing 270001 words to 273000 words out of 321579 words

Chapter 91 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

kaya, na jikinki sun yamutse, banaso suga abunda zai sa su zargi wani abu"

cike da rashin yarda ta furta"basaina shiga ba, idan munje gidan zanyi musu bayani"

?aure mata fuska yayi"zakiyi abun da nace maki ko kuwa"?

Cikin sauri ta nufi closet room ta shige.

Jim KaWan ta fito Jikinta sanye da abaya fara, tayi rolling mayafi akanta, Yana a zaune bakin gadon yabi ta da kallo from head to toe, ta yi mashi kyau a cikin abayar, ta fito a balarabiyarta.

Mi?ewa yayi tare da nufar kofar dining room "ki biyoni" cike da jin shakkar shi tabi bayansa.

Saman dining chairs suka zauna suna fuskantar Juna, ga kayan dinner sha?e da table din gabansu, ya lura har yanzu a tsorace take da shi, duba da yadda Jikin ta ke kerma..

"Zaki iya ci da hannunki! Ko in baki abaki"!

Da jin Hakan Yasa cikin sauri ta Wauki glass of juice me sanyi ta kwafa abaki tana sha tana satar kallon shi yayin daya sadda kan shi ?asa sai taga kamar murmushi ya ke yi amma bata gaskata hakan ba.


Bai yi zaton yarinyar ta samu tarbiya har haka ba, da wuya ya jaraba mace da tayin kanshi ta?i amincewa sai akan Batool, tsoron Allahnta, da kamun kanta, da kuma yardar da tayi masa sunfi komai Jan hankalin shi a gare ta.


Satar kallonta yayi, tana tsaka da cin meatloaf mai dan karan daWi, Yatsun hannunta nata kerma kaf kaf kamar wacce sanyi ya kama, Allah Allah take ta gama ta tafi gida.


KaWan taci ta dakata, tare da duban shi "yaya Owais, na koshi, dama dazu naci abinci gidan biki, zan tafi basai ka kaini a mota ba, Unaisah tana can tana jiran ka, kaga dare ya yi sosai"

Yanayin yadda ta ke yin magana cikin sanyin murya ba ?aramin jan hankalinsa ta ke yi ba.

Bata ?are maganar ba, Ya katse ta da cewa"ban yarda kin koshi ba, You're still hungry, Either eat more, or we'll stay here forever"

arude ta soma cuccusawa abaki, taci samosa, taci spring rolls, ta hada da straw berry shortcake, Tana gamawa ta kai hannu ta dauki milk shake ta sha sosai duk yana kallonta, bakin ta yayi dama dama da cake.

Tana haki ta furta"yaya Owais na ci da yawa yanzu, zan tafi"

bata jira amsar shi ba ta mike tana zazzare idanun ta.

"Muje nakai ki a mota ta, idan kikayi min gaddama zamu kwana anan ne" a firgice ta amsa da toh.

"Ki jira ni a falo, zan shiga ciki in sanya suturana" amsawa tayi da toh.

Akan idonta ya fuce daga falon ya nufi Cikin bedroom.

Cike da zullumi take ta jiran shi, babban tashin hankalinta, ummin ta da daddynta tasan zasu nemeta, gashi ta manta ma inda ta jefa wayarta.



Tasan idan ta koma gida zasu iya yi mata faWan daren da tayi a waje, kuma zasu tuhumeta akan Kayan da ta canza a jikin ta, Ya ilahi ta furta tana dafe goshinta daya jike da gumi.


Fitowa yayi jikin shi sanye da jallabiya ash, ya ru?e car key dinsa a hannu.


"Na manta kayan dana cire a closet room"


ta faWa batare da ta bari sun haWa idanunsu ba.


"Zaki iya zuwa ki dauka"

cikin sauri taje ta Wauko kayan ta ?uWundunesu a hannunta.


Bata iske shi a falon ba, hakan yasa ta fito harabar part din, a parking space ta hango shi a tsaye Ya jingina bayan shi jikin motar shi, ba wadda sukazo gidan da ita ba.


Kafin ta ?araso Ya buWe mazaunin driver Ya shiga, tana ?o?arin buWe back seat muryarsa ta katse ta"Am I your driver"? Cike da izza ya furta.

Da sauri ta dawo mazaunin gaba Ta bude ta shiga ta zauna tana ta faman sauke a jiyar zuciya, ta Wanyi mamakin ganin shi ne zai yi driving da kan shi bayan bata saba ganinsa yana driving ba.


Bayan ya tashi motar, ya yi reverse ya fusgeta da matsakaicin gudu motar ta fuce daga gida.



~____=ؘ?_____=؋?______


*=?%?UNAISAH=ؗ?*



tana tsaka da sharar baccin ta, Kwatsam hasken Wakin Ya Wauke Wuff, sai na Candles da ke ci, ?arar qira'ar alqur'anin daya karaWe Wakin ne Ya farkar da ita a firgice ta farka tana zare sleepy eyes Win ta, wata irin faWuwar gaba taji sa'ad da ta lura babu hasken fitilun Wakin sai na candle lights!


Zuciyarta ta shiga harbawa da sauri da sauri kamar ana mata lugudan ta6are a ?irjin ta.

Bata ta6a tsintar kanta a cikin tsoro irin na wannan lokacin ba tun bayan rabuwarta da kurkukun ?addara!

Abu biyu ne yazo aranta, watakil Yaya Owais ne Ya kashe hasken Wakin sa'ilin da take bacci don ya bata mamaki, ko kuma Electricity din gidan ne Ya samu matsala, gaba daya ta manta menene yayi silar farkawarta daga bacci.

A tsorace ta furta"Yaya Owais? Kai ne ka shigo? Kana ina? Nasan kaine ka kashe min hasken Waki, dan Allah kayi min magana, gaba daya na tsorata.."


Ta faWa tare da mi?ewa daga kan kujerar, jikinta nata kerma kamar mazari.

La66anta na kerma ta kuma cewa"hubby, pls kada ka wahalar dani, bazan iya jurewa ba, idan kaine ka yi min magana ko hankalina ya kwanta, tun Wazu nake jiran zuwanka... "

bata ?arashe maganar ba, Unexpected ta tsinkayi sautin takun tafiya a cikin kunnanta daga bayanta, tuni tasha jinin jikin ta, jin ya?i amsa mata yasa tayi tunanin ba ya ya Owais ba ne, wani ne ya shigo gidan, nan fa ta ?ara shiga tashin hankali, tsoro ya hana ta juya ta fuskance shi, sai faman zazzare idanunta ta ke yi, dakyar ta iya ?yalla idanun ta ta cikin mirror Win gaban ta ta soma hango shi da taimakon Candle lights...


Walking magestically ya ke nufo cikin bedroom Win kamar baison taka ?asa, daga ?asa ta soma ?are ma shi kallon ?urullah da tsantsar ruWani da fargaba saboda bata tantance wanene ba, tsayin sa ya zarce na Chief Owais.

Sanye ya ke cikin shiga ta larabawa, wata hadaddiyar dishdasha long tunic, launin ivory white ta bayyana tsantsar zazzafar surar sa mai matu?ar jan hankali, daga fadadan kafadunsa wata madaidaiciyar bisht cloak ce (alkyabba ) launin Golden-brown, daga gefenta da bakin ta gaba daya adon duwatsu masu daraja ne lullu6e da rigar, sai kyalli su ke yi suna she?i, wuyan hannunsa na dama yana asanye da Expensive rolex Watch irin wadda sai dan wane da wane su ke sanyata, both mid fingers dinsa suna a sanye da gemstone-encrusted rings, yayin da kafafunsa ke asanye da hand made Leather arabian shoes, mayar da idanunta tayi akan fuskarsa cike da fargaba take kokarin gano wanene sai dai kash rabin fuskar tasa yayi covering dinta da Gold leaf Mask, gaba Waya kansa a naWe ya ke da turban, irin naWin larabawa, daga kasan rawanin doguwar sumar kansa ce ta zubo, wutsiyoyin kitsonsa biyu suka hauro ta saman kafaWarsa har izuwa kan broad chest dinsa, daga bayan sa wata sumarce har mid back dinsa mai kyan gaske tana ta she?i brown shar da ita..

Duk ?amshim da bedroom din ta ke yi saida ?amshin turarensa ya disashe shi, wani irin sweet fragrance mai rikita shau?in bawa, daga yanayin tafiyarsa ta fahimci yana da izza da qasaita daga gani mutum ne mai tsantsar ilmi da aji kuma wayayye mai cikar kamala da nutsuwa.

Unaisah ta gama ruWewa, Tsoro da fargaba suka cika Zuciyarta da ke tayi mata dakan sakwara, aranta tana ta tunanin wanene wannan Hamsha?in saurayin? shin tayaya akai ya shigo gidan Auranta? Kwata kwata bata yarda Mutun ne ba, tafi alakanta shi da jinsin jinn saboda zubin sa!


Anya kuwa Yaya Owais ya sanya malamai suyi safkar alkur'ani a gidan kafin ta tare?


Tana kokwanto saboda gayanan tunkan aje ko'ina ta fara ganin ifritun Aljani..



Yawu ta haWiya mai zafi makoshin ta ya bada sauti ?utt, cikin rawar jiki ta fara tunanin mafita! Gashi tamanta waya agida balle ta kira wani ta fada masa Aljani Ya kawo mata farmaki, ita kadai baiwar Allah, tunanin guduwa tayi duk da tasan ba lallai takalman kafarta su bata hadin kai ba saboda tsinin su.

Ganin Ya kusa karasowa cikin Wakinne Yasa Ta fara neman gurin da zata 6uya cikin rawar jiki ta soma ja da baya cikin sanWa don karya ji takun ta.


zukunnawa tayi ?asa da rarrafe ta dinga yin tafiya ta nufi karkashin gado ta shige ciki ta 6uya gabanta nata faWuwa, aranta tana mai cigaba da ambaton La'Ila ha'illa anta subhanaka Inni kuntu minazzalimin"


~________________________________


A hankali ya ?arasa shigowa tsakiyar dakin, cikin takun ?asaita ya nufi gaban gadon, Unaisah dake a karkashinsa tana le?en ?afafunsa da ke tunkaro gadon, tashin hankali tuni gumi ya wanke fuskarta, runtse idanunta ta yi gam ta dinga karanto Ayatul kursiyo a cikin zuciyarta da sauran addu'o'in neman kariya daga sharrin jin.


A hankali ya zauna daga gefen gadon ya Waura ?afarsa Waya kan Waya..


Zuciyarta ce ta tunzurata akan ta duba ?afarsa taga idan irin na mutanene ko kofaton jaki irin na aljanu kamar yadda Aunty Danejo ta ta6a bata labarin cewa Idan aljanu suka yi suffar mutane zaka iya gane su ta kafarsu saboda ba irin na mutane bane, Kofaton Jaki gare su.


Cikin sanWa ta zu?unno da kanta ta ?urawa fatar ?afarsa ido, Har saida gabanta ya faWi ganin kafar tasa fara sol kamar ta jariri yadda kasan bai ta6a taka ?asa ba, hasken fatar sa irin pure shining white Win da ba acika samun shi ba ne naturally.


RuWewa tayi, duk da tana kokwanton kamar mutunne tun da bata hango kofaton jaki ba, zuciyarta ce ta raya mata idanunta ne suke nuna mata ba daidai ba, watakil owais ne girgiza kai tayi in har Owais ne bazai ta6a zama fari ba.

Ganin Ya motsa kamar ya mi?e yasa ta katse zancen zucin nata, kanta harya fara ciwo, ga yunwa da bacci tana ji, ga zullumi da fargaba sun cika zuciyarta..

Shigewa toilet ya yi, tana lekensa taga glashin bangon toilet din ya disashe, aranta ta ayyana ya koma mazauninsa kenan, tunda ance toilet gurin zaman aljanu ne, cikin sauri da rawar jiki ta fito da niyar ta fece, kwatsam ta hango tamfatsetsiyar waya ajiye saman bedside drawer, fasa fita tayi

Yatsun hannunta na kerma ta dauki wayar ta danna number din daddynta ta kira ta kara a kunne cike da fargaba..


Unexpected wayar Taj dake aje kan bedside drawer ta fara ringing, at same time suka farka.


"Wanene Ke kira" ta tambaya tana duban Taj daya dauko wayar yana kallon screen dinta yace"ban sani ba amma bari na Waga maybe wani emergency call ne"

Amsawa tayi da ''to'' Picking yayi ya kara a kunne

ko sallama batayi ba ta fashe da kuka kamar ranta zai fita.

Har Benazir saida taji yo kukanta, hankali atashe suka dubi Juna..

Har suna haWa baki gurin furta"Unaisah! Meke damunki? Meyasa ki kuka um miya faru wayar waye kuma wannan"?

Dakyar ta shanye kukan, Cikin shesshekar murya tace"yaya Owais baizo ba, Inata jiran shi ni kadai agidan tsoro nake ji, kuma yanzu wani ifritun aljani ?aton maridi ya shigo dakina, baka ganshi ba daddy, dogo fari fat kamar fatalwa ya saka kayan larabawa, tun dazu nake boye a karkashin gado har saida Ya shiga toilet sannan na samu na fito har na dauki waya, wallahi daddy Mutuwa zanyi in baka zo ka Wauke ni ba, kashe ni zai yi, dan Allah daddy ka zo tare da Baba Imam ya kora mana aljanun gidan da ayar Allah, in har ba so ku ke ku rasa ni ba.... "


da?yar ta ?are maganar..

Han???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?kalin Benazir idan yai dubu to Ya tashi, Taj ne kadai bai Waga hankalinsa ba, kallon juna su ka yi.

Kafin wani ya furta kalma kiran ya katse.

"Bazan iya jira ba, zanje kawai na tafo da ita, tayaya zai barmin ?a a irin wannan lokacin tana ta jiran shi, wunin yau ko abinci bata ci ba saboda sunce zasu ci agidan su, gashi harta fara gane ganen aljanu"

Cikin 6acin rai ta ?arashe maganar tana ?okarin saukowa daga kan gadon Taj yayi saurin ru?o hannunta, cikin fushi kamar zatayi kuka tace"kana fa jin abun da tace! So ka ke mu rasa ta ne? Tun kan aje ko'ina har ya fara nuna rashin kulawa akanta! Ba fa dan na gaji da ita na bashi ita ba"

Murmushin gefen fuska Taj yayi"Ummu Unaisah, Ki kwantar da hankalinki, ruWewa tayi ne amma ba aljani bane tagani, Mijin ta ne"

AruWe Benazir tace"ita fa da kanta tace aljani ne! Unaisah batasan fuskar Owais bane da zata rasa gane shi!? ina Owais yaga hasken fata? idan kai baka dauki maganarta serious ba nina Wauka.."

tana ?arashe maganar ta fusge hannunta daga nashi ta nufi closet ta dauko veil ta yafa.

"Karki Fita Benazir, ban baki izni ba, ki dawo zanyi maki bayani.."


"Ai fa sai ka yi Tajo, kaima kasan ba sauraron ka zan yi ba... "


~____________________________________>?z?=ؘ?~


_A 6angaren Unaisah, batasan ya akai kiran ya katse ba, ta dinga trying baya zuwa, kamar ta yi hauka, batai aune ba, kwatsam ba zato ba tsammani taji motsinsa abayanta, Kamar numfashinta zai Wauke tsabar razana, bugun Zuciyarta ya tsananta, gumi Ya cigaba da tsastsafo mata ta saman goshinta da hancin ta, wani irin tsoro ne ya ziyar ce ta, duk tabi tasha jinin jikin ta..._

Kafin tayi wani ?wa??waran motsi sanyayyar Muryarsa ta ratsa kunnanta"My Phone.... "


Ya Ilahi Wani irin ruWanine Ya cika zuciyarta jin muryar ifritun Aljanin tayi mata shige da ta wani wanda ta daWe da rasa shi arayuwar ta, muryarsa da ko a mafarki taji ta saita shaideta, ko da tana a cikin maye ne..

Kwata kwata batasan wayar wacece ta Wauka ba, sai da taji maganarsa, tana zazzare idanu ta Wan saci kallon wayar da ta ruke a hannun ta, ?ara zare idanunta tayi tamkar ?wayar idon zata faWo ?asa a kiWime take kallon hoton ta da ke akan Wallpaper Win wayar ganin abin ta ke kamar a mafarki kamar idanunta sun samu matsala....!


Mutun Waya ta ta6a turama hoton ta whatsapp dinsa, kuma a time din data tura masa hoton view once ne ba a iya Waukarsa ko ayi sharing even screenshot amma tayaya ya samu hoton? Nan ta ke ta ?ara tabbatarwa kanta ba mutun bane, sakin wayar tayi ta faWi kan floor


?arfin halin juyawa tayi slowly ta fuskance shi cike da fargaba ta Wan saci kallon fuskarshi, bata iya ganin ta dakyau sai dai Kyawawan sleepy eyes din sa waWanda ke a lumshe

Ko a mafarki taga me irin tsayuwarsa sai ta gane shi, Amma tagaza yarda da abun da zuciyarta ke raya mata, a ganin ta bame yiwuwa ba ne, cike da fargaba ta Wan matsa dab da shi ta Wan tsaya jikin ta na kerma ta ke ?are mashi kallon ?urulla...

A ranta tana ta ambaton La'ila ha'illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin..

Cikin rawar Murya tace"Bab.. Bawan Allah kaji tsoron Allah kada ka cutar dani! Ka faWamin Wanene Kai? Mutun ko aljan? Kasan ni ne? A ina ka sami hoto na? Me kuma ya kawo ka gidan aure na har cikin Waki na"?


shiru babu alamun zai furta kalma, ko motsi bai yi ba bai kuma Waga idanunsa ya dube ta ba..

Almost minutes..

Batasan ya akai take jin wani abu a zuciyarta wanda bazata iya misalta shi ba, kuma duk duniya mutun Waya ne idan tana atare da shi a kusa da ita take jin wannan abun...

Kafin ta ?ara furta kalma, taga Ya motsa ta Wan zare ido tana duban shi, gently ya sanya hannu Waya akan fuskarsa ya soma ?o?arin cire mask Win sa..

Lokacin daya zame Mask din gaba Waya Ya sake shi Ya faWi ?asa wata irin zabura Unaisah tayi kamar zata watsa aguje saboda ruWewar da ta yi, Ilahirin jikinta Ya kama kerma kamar mazari, gaba daya ta rikice tabi ta ruWe ta razana da ganin fuskar mutumin data rasa tsawon shekaru akan fuskar Ifritun Aljanin nan, tsigar jikinta duk ta tashi, wani irin faduwar gaba take ji a kirjinta kamar ana buga ganguna.

Kyakkyawar fuskarsa da bazata taba manta kamanninta ba saboda haddar da tayi mata.

cikin Wimuwa ta soma murza idanunta da yatsunta sosai don taji aranta gizau ya ke mata bashi bane, saida ta gama murje idanun ta buWe su still babu abun daya sauya yana nan yadda ya ke.

Kamar mahaukaciya Ta bushe da dariya lokacin Waya kuma takama kuka tana fadin"ba zaka ta6a bari in zauna lafiya ba, ka mutu ban huta ba, fatalwarka bazata bari in zauna gidan aurena lafiya ba, ka hana zuciyata sukuni a gidan iyayena nan ma ka biyoni don ka tarwatsa aurena! Meyasa zakayi min haka? ya ka ke so nayi da raina? ko so ka ke nima na mutu nabiyoka mu rayu a kabari Wayane um"? tuni idanunta sun kaWa jajir.


"Idan so kake mu rayu a tare, ka kashe ni sai mu koma kabarin ka a tare, nima zanso hakan saboda bana jin dadin rayuwana batare da kai ba.."


ta ?arashe maganar tana matsawa kusa da shi, kamar ancire mata tsoronsa da fargabansa daga zuciyarta, tun da ta sama ranta cewa fatalwarsa ce.

A hankali ta kwantar da kanta saman broad chest dinsa, ta zagayo da hannayenta ta saman bayansa, batasan ya akai ta tsinci kanta da jin wani bakon al'amari atare da ita, bugun zuciyarta a cikin nashi, nutsuwa da kwanciyar hankalin da taji a jikin ta sa'ilin data haWa jikinta da nashine yasa ta kara ruWewa, ta dinga jin kamar shine ba fatalwarsa bace tunda in fatalwace bazata iya riqeta ba duk da haka ta kasa gaskata cewa Danish ne.

Cikin kuka tace "Ka Wauke ni, mu tafi ?abarinka, mu rayu a tare, bazan ta6a gudun fatalwarka ba my Man, nasan nice na hanaka kwanciyar kabarinka" ta riga ta sallama masa kanta yayi duk abin da zai yi.

Duk wani motsinta yana jinshi a jikin sa, bugun zuciyarta, shesshekar kukanta, fitar numfashinta, dumin jikin ta da ?amshin ta.


Tayaya zai iya fahimtar da ita cewa ba fatalwarsa bace! bai mutu ba yana araye? Tayaya zai iya kare kansa daga gare ta, yana jin fiye da abun da take ji aranta, banbancin Wayane shi yasan tana araye kuma ya nisanta kanshi da ita saboda manufar sa..


Yana jin yadda take ?ara nar?e mashi a jiki kamar zasu koma mutun Waya...


Numfasawa yayi a hankali cikin nutsatstsiyar muryarsa ya furta.


*_"UNAISAH, I'M NOT A GHOST! I'M NOT A


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login