Showing 84001 words to 87000 words out of 321579 words

Chapter 29 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

Owais ya zabga tagumi yana sauraron shi jikinshi duk yayi sanyi la?was..

"Cikin ?an?anin lokaci zumunci mai karfi ya shiga tsakaninmu da shi har na koma babban malaminsa dake yi masa hidima da ta shafi addini, idan zai fidda zakka ko sadaka ni yake tuntuba, wani lokaci idan yana neman shawara baya tuntubar kowa in bani ba, toh a kullum in muka zauna muna yin fira da shi bashi da maganar data wuce ta jikanshi Owais, abakinsa na ji cewa kai jami'in bincike ne na sirri, kuma hukumarku tana da ?arfi gurin yin ya?i da ta'addanci.

Koda na ji hakan saina nemi da ya bani number Winka don mu dinga gaisawa saboda nima na ji ka kwanta mun a rai, bai kawo komai aransa ba ya bani number Winka, idan ba zaka manta ba har waya ya ta6a ba ni muka gaisa da kai.." jinjina kai Owais ya yi.


Bayan na dawo gidana, na shiga social media na fara bincike akan shafukanka, ta hanyar comment din da mutane su ke yi maka yasa na fahimci irin ?wazon dake gare ka, abun da ya fi burgeni yadda mutane suke yabonka da jinjina maka akan gaskiyarka da son adalci, duk wanda zai yi magana akan ka sai ya kurantaka, bayan haka mutane marasa gaskiya suna jin tsoron case dinsu ya shiga hukumarku saboda baku yi masu da sau?i.

Bayan na gama bincike na akan ka, abu Waya da nake tunanin zai yi min wahala shine ta yadda zan tunkare ka, nasan kaitsaye idan na faWa maka komai ba zaka taba yarda ba tun da kakanka ne mafi soyuwa agare ka, har kulle ni zaka iya yi, shiyasa na yanke shawarar kiran ka asirrance, kafin na yi hakan saida na nemi ilimi akan ta yadda zan yi hakan batare daka bi diddigin layina ba saboda na gano you're a cyber expert..

Lokacin da ya ?arasa masa labarin, kwata kwata hankalinsa bai tashi ba, saboda a halin yanzu babu abun da zai ?ara bashi mamaki a duniyar nan tun daga kan kakansa..

"Owais, yanzu tun da na faWa maka komai, pls ka yi ?o?arin yin magana da kakan naka, tun da yana kula ka, ina so ka tambayesa game da malam Jazuli nasan ba zai rasa sanin sa ba, duk da ina ji araina kamar basa a raye, amma duk da haka ka tambayesa, ?wara mu san meya faru da su, wlh har yau danginshi nemansu suke yi musamman matar shi.

Jiki asanyaye Chief Owais ya mi?e tsaye, cikin sanyin murya ya ce,

"Baba Imam thank you for sharing everything, na ji dadi, kuma in sha Allah zanyi magana da grandpa, duk yadda muka yi da shi zan sanar maka."

Hugging Win juna suka yi, kafin ya ru?o hannunsa har bakin motar Taj ya rako shi.

Har ya buWe motar zai shiga sheikh Imam ya ce ya Wan jira akwai sa?o da zai bashi, ya amsa mashi da toh.

Cikin sauri Imam ya koma Cikin apartment nasa, jim kaWan ya dawo hannun shi ru?e da date boxes (kwalayen dabino) Ya mi?a ma Owais ya sa hannu ya kar6a,

"Idan ka koma gida, ka ba su Unaisah da Ummi, ka gaishe min da su.."

Tsananin tausayin shi ne ya kama Chief Owais, saboda ya fahimci sa?on na Ummi ne yake son ya bata, amma sai ya fake da sunan su Unaisah kafin nata saboda baya son ya gane komai baisan ya riga da ya sani ba.

"In sha Allah zan kai masu, ina ?ara godiya baba Imam, you have done so much for us, we can't repay you, Allah yasaka maka da alkhairinsa..."

Murmushi sheikh Imam yayi masa tare da amsawa da Amin, bayan sun yi sallama ya shige cikin motar tare da kai hannu ya Wan dafa kafaWar Taj dake sharar bacci, firgigit ya farka yana tambayar waye ne..

"Daga yin waya na ji ka shiru baka dawo ba." Murmushi ya yi."Na kira ummu Unaisah ne mun daWe muna waya bayan mun gama kuma bacci yai awon gaba dani, "

Ya ?arashe maganar tare da tambayar ina sheikh Imam ya ce ai har sun yi sallama da shi ya koma ciki su tafi kawai.

Amsa mashi yayi da toh kafin suka tafi...

Kafin su karaso Taj ya lura da yanayin fuskar chief kwata kwata babu walwala kamar an ?ara ninka masa damuwarsa..

"My in-law, meya faru ne? Na ga kamar babu walwala atare da kai." Yamutsa fuskarsa ya yi ya furta, "Kada ka damu pls.." gyaWa kai Taj ya yi tare da kallon date boxes din dake akan laps dinsa bai dai tanka ba....

Can ya tsinkayi muryarsa a kunnansa, "Zaka iya tuna sunan malamin nan da matsafa suka handame shi da ?a'yan shi a lokacin da ku ka yi ma su leken asiri?" Ya tambaya yana duban shi..

shiru ya Wan yi jim yana kokarin tunanowa.

"Am.. kamar Jazuli ne amma ban ji da kyau ba saboda a lokacin sun yi nesa damu, bamu iya jin me su ke cewa sosai..."

Murmushin takaici Chief yayi jin abun da yake tunani ya tabbata, amsa mashi ya yi da okay, daga haka bai ?ara tambayar shi ba, shima kuma bai nemi sanin meyasa ya tambaye shi ba har suka koma gida.






*Welcome, Littafin kurkukun ?addara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*

3196407426

First bank

Bature Hafsat Muhammad,

*bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan number din 08103884440*~_____=؞?______=ؗ?_____=ؘ?_____???___~





*daga Alkamin Boss Bature=؋?
'?*


Bari mu koma baya mu ji meya faru bayan kwana Waya da afkuwar lamarinS'




Bayan sun koma cikin main falo kowan nan su ya samu wuri saman Sofa ya zauna, yanzu da suka Wan samu nutsuwa damuwar su da tunaninsu ya karkata akan halin da Hajiya saratu da momma suke a ciki, sun so da suka fita raka imam daga can su wuce Villa, amma sai basu yi hakan ba saboda akwai bu?atuwar su fara yin nazari akan wani muhimmin abu..


Kafin su fara tattaunawar, Sharafudeen ya zaro waya ya kira layin sarauta, bayan ta Waga kiran muryarta cike da damuwa ta soma tambayar shi. "Why babe ka barni cikin damuwa, ko bacci ban yi ba jiya saboda rashin kwanciyar hankali, pls ka fada min menene ya faru da hajiya Saratu? how did she get the shards that hurt her face, na tambayi su twins sun ce suma basu sani ba, amma suna zargin faWa ne ya haWata da hajjaty, shin da gaske ne? kuma meyasa ina ta kiran ka baya shiga, baka dawo ba kuma baka faWamin zaka kwana a gida ba, kodai wani abu ya faru ne?"

"Ki yi hakuri da ban samu Waga kiran ki ba, ban kuma kira na ji a wani hali kuke ciki ba, am really sorry, in sha Allah nan da 30 mins, zamu shigo villa din, and we can discuss then" Ta amsa mashi da toh,

"Ya jikin marasa lafiyan namu?"

"Babe the doctors gave me some information about Sarah's condition since yesterday, they've cleaned and treated her facial lacerations, and she's receiving antibiotics to prevent infection, they assured me she'll feel better in a few days, in sha Allah"

Da yake handsfree ya sanya wayar gaba Waya suna sauraron maganar Sarauta.

"What about Momma? Ita ya jikinnata? Is she getting better?"

"Who's Momma?" Ta tambaya saboda bata gane wa yake nufi ba.

"I mean the old lady" Ya amsa mata.

"Oh, she's getting better, according to the doctor's explanation, Her brain injury has caused short-term memory loss, and they can't restore her memory, If she doesn't remember herself."

Da damuwa a fuskarsa ya dubi ?an'uwan nasa dake sauraron bayanin sarauta..

"Babe, zan iya sanin wacece? tayi min kama da momma, amma tafi momma tsufa, ba dan momma ta mutu ba da sai in ce ita ce, and One thing puzzled me when I sat next to her she was mentioning Honeyboy and Superstar, who are they?

Bai san sa'adda murmushi ya kubce mashi ba ya Wago suka haWa ido da prime minister, wanda idanunsa suka cicciko tab da kwalla.


"Nagode da kulawarki agare su, idan na shigo zamu yi magana, Saratu tana magana?"

"Bata farka ba, allurar da su ka yi mata ne bata sake ta ba, amma muna sa ran zata farfado nan bada jimawa ba."


Sallama su ka yi da juna, Ya aje wayar tare da maida hankalinsa akan yan uwansa dake kallonsa.


"Menene mafita? Bai kamata mu ja baki mu yi shiru ba, batare da mun Wauki mataki akan abunda aka yi wa Auta ba"

His excellency Deen ya ce, "Ni so nake insan wani mugunne yayi mata haka? Meyasa? Me kuma ya kai ta Wakin Hajjaty?"

Abdul Razak ya ce, "Wallahi raina ya 6aci abun ya ?ona mini rai, muna a cikin mawuyacin halin nan aka samu wani mara imanin ya zagaya ta baya yaje ya cutar da ita, so yayi ma ya kashe ta badan Allah ya kaddara maids sun je Wakin ba har suka gani ai da tuni ta jima da mutuwa."

Chief Owais da sauran matasan dake agurin sunyi shiru suna sauraron su.

Deen ya sake cewa, "Baku zargin faWa ne ya haWa ta da hajjatyn har tayi mata bugun kawo wu?a?"

Girgiza kai Abdul razak yayi. "Bana tunanin hajjaty zata iya cutar da Saratu, tsawon shekaru bata ta6a cutar da wanin mu ba, bawai don na yarda da ita ba, ni yanzu na yi hankali, mugu bashi da kama, kowa zai iya rayuwa da kai da fuska biyu na tsawon lokaci yana kyautata maka saboda wata muguwar manufa ta shi, tun da har mahaifinmu ya ci amanar mu balle ita da take bare, kawai abun ya Waure min kai ne na rasa wa zan zarga..." Ya ?are maganar fuskarsa a yamutse.

"Zato zunubi ne koda ya kasance gaskiya, kada mu yi saurin yanke ma hajjaty hukunci saboda ganin hajiya Saratu da aka yi adakinta, ba dole ya kasance ita ne ta cutar da ita ba..."

Sharafuddeen da ya Wauko maganar bai kaiga direta ba, Sir mubarak ya dan yi gyaran murya, gaba Waya suka maida dubansu a gare shi, tun da suka fara magana bai saka baki ba sai yanzu.

"Tun Wazu da ku ka ga na yi shiru, nazari nake yi akan abubuwan da suka faru abaya, maganar gaskiya bana zargin hajjaty ce ta cutar da auta, sai dai idan Pravin ne ya yi mata hakan.."

Da Wan ruWu akan fuskarsu suke kallon shi, sam sun shafa'a sun manta da Pravin basu lura ma babu shi agidan ba.

"Meyasa ka ce haka?" Deen ya tambaya.

"Abun da yasa nake zargin pravin, Idan ba zaku manta ba aranar dinner din Hateem, Pravin ya yi wani abu da ya ja hankulan mutanan dake agurin, a bainar jama'a ya dam?i hannun Hajjaty ya tursasa mata akan tabar hall din, tun anan na sanya masu alamar tambaya..."

Da yayi wannan maganar nan take suka tunano lokacin da abun ya faru babu wanda bai zargi akwai boyayyiyar alaka a tsakaninsu ba, a lokacin har mataki suka ce zasu Wauka akan shi, amma daga bisani suka yi watsi da maganar.

Sir mubarak ya Waura da cewa, "May be sun daWe suna kulla makirci a bayan idon mu, bayan haka komi ya faru da Saratu baba ne ya ja mata, lokacin da ta zo da shi daga ?asar India ta nuna shi take so ta aura gaba Wayan mu babu wanda ya amince saboda bai kwanta mana a rai ba, saida muka musa akan mu bamu yarda Saratu ta auri bare wanda ba jinsin mu ba, mutumin da ko asali baida shi, ba mu san kowa nashi ba in ba ita ?ar uwar ta shi ba da ya zo da ita daga baya, amma Saratu ta ?i sauraron mu saboda baba ya goya mata bayan ta auri za6in ranta" ya faWa ransa a matu?ar 6ace.

"Bayan haka ina zargin baba shine ya janyo pravin cikin harkar tsafinsa, watakil sunyi yarjejeniyar zai bashi auranta idan ya amince zai yi masa abun da yake so shi kuma da ya ke dama kwaWayin dukiyar Saratu ce ta ruWe sa shiyasa ya biyo ta don ya kwashi rabon shi, shine ya amince zai masa biyayya..."

Maganar Sir Mubarak ta Waga hankulansu saboda suma sun hasaso abun da ya ke zargin.

Hateem ya ce, "In kuwa hakane Baba ya zalunci Saratu, ni dama na yi mamakin yadda ya yi saurin amince ma auranta da shi, saboda kwata kwata ba ajinta bane, a matsayinsa na mutun mai girmama darajarsa da ?imarsa amma ya rufe ido ya nace akan abar Saratu ta auri za6in ta, abun ya tsaya min araina, a lokacin har kwatanta masa muka yi ya rufa mana asiri kada ya zubar mana da mutuncinmu Saratu ta fi karfin Pravin, ba sa'an aurenta bane, mutane zasu yi mana surutu amma duk bai duba wannan ba, thats mean dama can da wata a ?asa a tsakanin su..."

Chief Owais dake sauraronsu zuciyarshi ta zo wuya saboda tsabar 6acin rai da tsanar hali irin na grandpa dinsa da kuma haushin Pravin.


Jikinsu Ziyad ya yi sanyi lakwas, jin abun suke kamar a mafarki saboda al'ajabi.

"Lokacin da momma ta fara tona masu asiri, munafukin batare da sanin mu ba ya zame jiki ya fuce daga falon, ina tunanin a lokacin da zai gudu Auta ta gan shi, shine ta bishi don ta tuhume shi akan abunda momma ta faWa, watakil ta riske shi a Wakin hajjaty suna kokarin guduwa shine su ka yi mata haka don kada ta tona masu asirin abun da suke kokarin yi..."

Da ruWu akan fuskokin su suke kallon shi, gaba daya sun yarda da maganar shi.

"Mayaudaran banza, na dade banga mugun miji irin pravin ba, tsawon shekara da shekaru yana auran Saratu ashe bada zuciya Waya yake tare da ita ba, ni takaici na ?a'yan dake atsakanin su, ya za su ji idan su ka ji mugun halin uban su? Da kuma abun da ya aikata, dama ya lafiyar gwiwa! Suma ba hankaline ya ishe su ba, uban nasu ya 6ata su, badan mun tsaya masu tsayin daka ba akan tarbiyarsu, da Allah kadai yasan lalacewar da zasu yi...." Senate Lateef ne ya faWa cikin fushi.

"Kuma wallahi na rantse da wanda raina yake a hannunsa, Waya daga cikinsu ba zai sha ba, ko da zasu gudu daga ?asar nan ne su tafi birnin sin saina sa an kamo min su an dawo dasu nan, dole su gir6i abun da suka shuka..."

Ya faWa tare da kai hannu ya daki hand sofa.

"Dole Saratu ta shiga mawuyacin hali, nafi jin tausayinta, ba ta yi dacen uba ba, ba kuma ta yi dacen miji ba.." a cewar Deen

"Owais, su wanene sauran Elders din?" Ajiyar zuciya ya Wan sauke tare da duban daddyn nasa, "Elders goma sha biyu ne, shidda suna jagorantar kurkukun ?addara, sauran shiddan ba a ?asar nan suke da zama ba, mutun huWu da momma ta fada su kaWai muka sani a cikin su, amma akwai mutun biyu da muke zargin suma elders ne, anan Abuja suke da zama, nan bada jimawa ba zamu kammala bincike akan su, na tambayi baba amma ya ki ya sanar da ni..."

ya faWa cikin raunannan murya.

Har suna haWa baki gurin furta, "ka yi magana da baba? Yaushe?"

Numfasawa yayi kafin ya zayyana masu komai da suka tattauna tare da baba Obie.

Gaba Waya basu ji dadin ?in faWa masan da bai yi ba, duk da sun riga da sun san halin uban nasu, duk da mugun halinsa yana da amana da kuma rukon alkawari, tun da har ya ?i sanar da shi to kuwa bazai ta6a faWa ba.

Kwantar masa da hankali su ka yi, su ka ce kada ya damu tun da har ya ce ya nemi taimakon Allah, toh ya dage da addu'a suma zasu taya shi da addu'a, kada ya kuskura ya bari maganar baban ta sagar ma shi da gwiwa, in sha Allah babu abun da zai gagare shi, su basu ma so ya nemi taimakon sa ba, da ya yi shawara da su da ba zasu bari ba, saboda haushin shi da suke ji, kuma suna so ya sani a yanzu binciken bana hukumarsu bane kaWai suma sun shiga ciki, zasu taya shi faWan har zuwa lokacin da zasu kawo ?arshen su, sannan komai ake ciki ya sanar da su, zasu taimaka mashi da iyakar iyawarsu, su kuma wadanda momma ta fadi sunayen su a cikin elders din za su yi kokarin kama su don ba zasu bari a ci gaba da aikata fasadi a doron kasa ba...."

Maganganunsu sun karfafa zuciyar Chief, musamman da suka bashi shawarwarin da zasu amfane shi akan binciken shi, sun bashi goyan bayansu dari bisa dari, prime minister ya ce zai ?ara mashi da Canadian Police, Sir mubarak ma ya ce zai bada gudummuwar sojoji, kwata kwata basu yi magana akan inmates ba, ba don basu damu da su ba, sai don sun fi so su fara kawo karshen elders amma abun yana aran su, suna son suga duka inmates watakil su samu sauran yaransu da ke a raye=?%?

Har maganar Jan kunne suka yi sir Mubarak ya ce, "Abun haushi abun takaici wai aure! haba ni dama abun na daure min kai, amintarsu ta jima tana burgeni, basu taba samun sabani ba, basu gajiya da ziyartar juna, musamman shi jan kunnan, ashe akwai wata a ?asa, wama yasan me suke aikatawa idan suka shige Waki, bamu taba kawo komai a ranmu ba, saboda yardar da mu ka yi da su, munafuki shiyasa ya ?i ajiye iyali ashe yasan me ya taka, wato uban namu ne iyalinsa ko..."

Maganar shi ta so basu dariya ba don halin da suke a ciki ba.



Lokacin da marece ya kunno kai, gaba daya suka shirya tafiya Villa, Chief ne kadai bai bi su ba saboda ya damu da ya dawo gidansa, a cikin motocin security details din Sharafuddeen su ka tafi, ba zan iya misalta maku haduwar presidential resident ba, abun sai wanda ya gani.




Daya bayan daya motocin suka shiga cikin Villa, da matsakaicin gudu suka nufi presidencial medical center, a gaban hospital din suka yi parking, a hanzarce security officers din dake tsaron asibitin suka yi hanzarin karasowa tare da buWe masu cardoors din, suna fitowa suka fara sara masu..

Cikin sauri suka shiga cikin katafaren asibitin duk inda suka gifta jiki na


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login