Showing 141001 words to 144000 words out of 321579 words

Chapter 48 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

iya faruwa.



Da?yar ta jinjina mashi kai cikin raunanniyar murya ta ce, "Shine baba, uncle Musa, ya daWe yana ?ulla makirci atsakanin mu, ban ta6a ganin azzalumin mutun irinsa ba, ya karya mini zuciyata, ya ha'ince mu, wata shari'ar sai a lahira, amma ya cutar da rayuwar mu..."


kamar a mafarki suke sauraron maganar Aisha, gaba daya sun kasa tantance wani Musan take magana akan shi, Taj ne kaWai ya san komai, sai kuma Benazir da Anila.


Sauran da ke a falon sun ruWe sosai, sun rasa gane inda ta dosa.


"Aisha kada ki ji komai, ki fadamin kawai, bazan karaya ba, nasan zai aikata saboda ya kullace ni a ranshi, dama ni saida na yi zargin dasa hannunsa a cikin abun da ya faru, kawai don bani da hujjar da zan tuhume sa ne.."


ya faWa cikin karfin hali kamar zai iya jurewa.


?arasa shiga cikin falon suka yi, saboda su samu damar jin komai, a saman sofas kowan nan su ya samu wuri ya zauna suka nutsu suna kallon Aisha da baba Imam, kwata kwata basu san da zaman su ba, saboda hankalinsu ba akansu yake ba, basu san ma sun shigo falon ba.


Numfasawa tayi cikin karyayyar murya ta soma zayyana masa komai da Uncle Musa ya faWa mata, tiryan tiryan abu Waya da ta boye masa saboda gudun halin da zai shiga, shine karuwancin da ta yi a America da kuma haramtacciyar ala?arta da Musa tasan in ya ji wannan komai zai iya faruwa ita kuma ba ta so Musa yayi nasara akan mahaifinta, ta dai sakaya ta ce shi ya kaita America ya Wauki nauyin komai nata saboda ya kawar da tunaninta akan dawowa gida.


Tunkan ta ?arasa labarta mashi Hajiya Layla ta mi?e tsaye tana tafa hannayenta a kiWime take zabga salati, Alhaji Ubaid dake a zaune sai jinjina kansa ya ke yi yama kasa furta komai saboda ?uncin da zuciyarshi ta yi mashi, ina ga Dr shureim dake neman zaucewa saboda tashin hankalin da ya haifar masa da raWaWi mara misaltuwa a zuciyarsa, bai ta6a zaton Uncle musa zai iya yi masa haka ba, saboda yasan shi ya cutar da rayuwarshi shiyasa ya dawo da shi gidan shi da zama, haka lokacin da ya ke neman taimako yaita kiransa baya shiga ashe blocking Winsa ya yi, kowa dake falon sai da ya razana ba kaWan ba, Musa ya karya zuciyoyinsu, basu ta6a tunanin shine munafukin da ke ?ulla musu makirci ba.

Saboda bacin rai da fusata yasa shekh Imam zubda gumi akan fuskarsa, ba a ta6a cin galaba akanshi ba sai wannan karon, Musa ya cuce shi, wani laifi ya yi masa da yasa shi yanke masa mummunan hukuncin nan?"

Kawai saboda ya hana shi auran Aisha? Saboda ba?in zalunci da rashin imani ya shiga tsakaninta da shi, yayi mata kazafi bayan ya shiga tsakaninta da Shureim, abun da yafi bakanta ransa tsawon shekarun da ya raba shi da ?arshi, ashe yana a tare da ita, saboda zalunci irin na shi, yanzu ya gane komai da ya faru da Aisha shi ya ja mata, tun da akan shi yake Waukar fansa, bata ji ba bata gani ba. Ru?o hannayenta ya yi a cikin nashi, saboda kerma da jikinshi ke yi itama nata jikin ya kama kerma idanunsu a cikin na juna yana kuka tana kuka ya ce, "Allah Ya yi maki sakayya Aisha, Allah ya bi maki hakkin ki. Wlh bamu ya cuta ba kanshi ya cuta, la'ananne, In sha Allah sai rayuwarsa ta wula?anta tun a gidan duniya, na yi danasanin sanin shi a rayuwata, dama wasu mutanan Allah yana hadamu da su ne don ya jarabcemu da su, wasu kuma don su zama alkhairi a cikin rayuwarmu.."


kasa ?arasa maganar ya yi saboda kululun bakin cikin da ya tokare makoshin shi, ya ji zafi a ranshi, bakin ciki ya cika shi kamar zai haWiyi zuciya ya mutu.


Kwantar da kansa ya yi saman kafaWar Ummi, ya Waura hannayensa a saman bayanta.

Cikin sigar lallashi yake dan bubbuga bayan nata, tsananin tausayinta ne ya kama shi, saboda gaba daya rayuwarta a cikin jarabta ta ke, kowa dake a falon sai da ya tausaya masu, Hajiya Laila ta yi danasani, sai cizon yatsa take yi, gani take kamar hada laifinta komai ya faru, idan har Musa yana sarrafa Alhaji Ubaid da sihirinsa toh ita da hankalinta take yin komai.

A fakaice ta dinga share kwalla tana satar kallon Aisha da mahaifinta..

Cikin ruWu Alhaji Ubaid ya ce, "Har yanzu na kasa yarda da abunda kunnuwana suke jiye min! Dan Allah ku fahimtar da ni! Kaina ya Waure, Wani musan kuke nufi? ?anina musa ko wani musan ne daban?"



Hajiya Layla ta yi saurin cewa, "Wallahi zai aika! Fiye da haka ma, ai baida mutunci ko kaWan, mutun sai bakar zuciya kamar ta kafuran farko, na daWe ina zargin ba mutumin kirki bane Musa, kuma dukiyarsa bata Allah da Annabi ba ce, Ai ni bazan ma Musa ba..."..



Benazir ta kar6e da cewa, "Abun da Aisha ta faWa gaskiya ne daddy, na dade ina jiran wannan ranar da zan fadi ta cikina, ku yi hakuri da ban ta6a sanar da ku ba, na boye maku ne saboda nasan zai yi wuya ku yarda da ni a wannan lokacin, saboda ku kan ku sai yadda ya yi da ku...."


mayar da hankalinsu su ka yi akan Benazir..

A tsanake ta labarta masu komai da ya faru tun daga lokacin data ta kama shi yana yin waya agidan shi, har izuwa kan asirin da ya yi mata..

Daura hannu biyu Hajiya Layla ta yi akanta.

Mami ta zabga salati, Dr Shureim ya zabura ya mike a kidime jin ?arsa da ya binne Uncle Musa ne ya dauke ta, yama kasa magana sai zazzare idanunsa ya ke yi gaba Waya ya ruWe, nan ta ke ?wa?walwarsa ta fara tariyo masa abubuwan da suka faru a baya, lokacin da ya je ya tone ?abarinta ya ga ?asusuwa saida ya yi zargin wani abu, just in two weeks da ya binne ta har ta zama ?ashi, bayan haka ya daWe yana ji aranshi tana a raye saboda bai ta6a mafarki da ita a mace ba, Ya Ilahi! Yanzu ya gane komai.


Jirin tashin hankali ne ya Webesa yayi taga taga zai kife, Alhaji ubaid ya yi saurin mi?ewa ya tallabo shi, tare da rungume shi kan kirjinshi, kukan ba?in ciki ya fashe da shi kamar ranshi zai fita, tuni zazzabi da ciwon kai sun kama shi.


Sheikh Imam ya ?ara shiga damuwa daga shi har Aisha jin rashin imanin da Uncle musa yayi ma Benazir saboda kawai ta nemi ta tona masa asiri don ta ?watarwa Aisha hakkin ta.



Cikin shesshekar Kuka Hajiya layla ta dinga Wura mashi ashariya tana tsine masa albarka, dama da ?iyayyarsa aranta, bata ta6a son shi ba, kwata kwata baya burgeta saboda izzarshi, ta tsane shi ta tsani komai nasa.



?wallar bakin ciki ce ta cika idanun Alhaji Ubaid, cikin rawar murya yake ambaton duk wata addu'a da ta zo bakinsa don ya samu sassaucin radadin da zuciyar sa ke yi masa.

Abie da ke zaune a gefensa dafa kafadarsa ya yi batare da ya iya furta kalma ba, kowa ya razana da jin abun da Musa ya aika ta.

Babu wanda zuciyar sa bata karaya ba..

"Har yanzu baku fayyace mana komai ba, Ina so in san wace irin sadaukarwa ce Musa ya yi da yarinyar Shureim da kuma yarinyar Benazir? suna a raye ko sun mutu?"



Cike da fargaba Abie ya yi tambayar, saboda yana son yasan in duk a tare suke da Wan Iya.


Shiru su ka yi saboda basu da amsar tambayar da zasu ba Abie.


_Taj Ka faWa masu komai, yanzu lokaci ne da kowa yakamata yasan gaskiya, Illa iyaka kowa ya yi hakuri da abun da zai ji_

Zuciyarsa ce ta raya ma shi.


Gyaran murya ya yi hankalin kowa ya dawo kan shi.

falon yayi tsit kamar mutuwa ta gifta, baka jin sautin komai sai na muyar Taj dake basu labari..

Ya fara ne daga kan labarin le?en asirin da suka yi wa matsafa shi da Uzair, rabuwarsa da Unaisah da hannun da kowan nan su ya faWa, Alherin da Chief Owais ya yi masa da kuma haWuwarsa da ?arsa bayan shekaru..

Lokacin da ya fara basu labarin gidan kurkukun ?addara, saida suka yi danasanin jin labarin shi, saboda matsanancin tashin hankalin da suka shiga, sun ruWe sosai, sun razana, zuciyarsu ta tsinke da jin irin azabtarwar da ake yi wa yaran da basu ji ba basu gani ba. Babu wanda bai share ?walla ba acikin su, kuka ne ya kubcewa Benazir da Anila kamar ransu zai fita, Hatta Hajiya Layla da Mami saida suka yi kuka na fitar hayyaci, shi Alhaji Ubaid ma kukan zuciya mai radadi ya kama yi, shi da Abie, musamman da ya zo kan labarin Unaizah abin ya ta6a zuciyoyin su.

Jin abun suke kamar ba a gaske ya ke faruwa ba saboda ruWun da suka shiga.


Bayan ya ?arasa basu labarin, ya juya ya nufi sitting room din Chief ya Wauko diary din Unaizah wanda tun shekaran jiya da ya shiga Wakin ya gan shi akan table.


Bayan da ya dawo hannunsa ru?e da diary din, ya Mi?a masu ya ce yana so kowan nan su ya dubi hotunan dake a cikin diary din da kyau.

Alhaji Ubaid ya fara mika mawa hannunsa na kerma ya kar6a tare da bude shafin farko, wata zabura ya yi ya mike a firgice yake tambayar diary din wanene? Mai ya kawo hoton Musa da na ?arsa Zeenatu a cikinsa.." Da jin wannan maganar yasa Benazir ta mike cike da rashin kuzari ta nufe shi, hajiya Layla ma tuni ta mike tana le?a hoton ta furta, "Kai! Ai Zeenatu ce wannan! Da Musan! Me ya kawo hotunansu anan? Wace ce kuma wannan baturiyar?" Ta tambaya a ruWe.

Kowa sai da ya duba hotunan, bayan da suka gama kallo, Taj ya fayyace masu komai game da diary din, ya ce yarinyar da suka gani ba Zeenatu bace sunan ta Unaizah, twin sister din yarinyar wurinsa ce da ya sadaukar tun tana jaririya ya rabata da mamanta ya kaita England gurin karuwarsa ta raine ta.


A bayanin da Taj ya yi masu suka fahimci yarinyar da yake yin magana akai itace ta kurkukun nan wadda ubanta ya yaudare ta.


Kansu ya daure tamau, lamarin ya girmi tunanin su!



Hajiya layla ta ce, "Anya Musa mutunne ba shaiWan ba?" Ta ce ta na kokwanto, saboda rashin imaninsa ya yi over, kamar babu zuciya a kirjinsa, abun da ya fi basu takaici cin amanar da yayi ma hajiya Sarah, baiwar Allah batasan twins ne ta haifa ba, Har yar cikinsa bai bari ba, ya zata ji idan ta ji abin da ya yi ma ?arta?



"Kakan Chief Owais Shine shugaban Kurkukun ?addara, Kamar yadda Musa ya ha'ince ku, shima haka kakansu ya ha'ince su, ya dade yana sadaukar da jikokin family dinsu agidan kurkuku batare da sanin su ba. Musa Yana Waya daga cikin Elders na kurkukun ?addara, Shine Jan wuya, kawun Anila shima yana Waya daga cikin Elders..."

Duk da sanyin A.c din dake falon hakan bai hana su fitar da gumi ba, saboda tsantsar tashin hankalin da suke a ciki, gaba daya sun razana da jin maganarsa, rudu yasa suka shiga tambayar shi wani Owais din yake nufi kuma wani kakan nasa?"

"Obinna," ya faWa masu ne saboda su kwantar da hankalinsu, su san cewa basu kaWai ta shafa ba, hakika sun razana fiye da yadda suka razana da jin munanan laifukan da Musa ke aikatawa, kamar an kashe masu bakunansu gaba daya suka yi shiru kamar masu zaman makoki.


Abie ya ce, "Inama ace mafarki ne komai ke faruwa? Wannan wace irin musiba ce ta kunno mana kai? Wani irin neman duniya ne wannan da zaisa ka dinga azabtar da rayuwar bayin Allah waWanda ba su ji ba ba su gani ba? ka manta da lahirar ka, Ka dauki rai ba a bakin komai ba? Hakanan bawa ya jefa kansa cikin bala'e ya kuma jefa ahalinsa, ina amfanin irin wannan rayuwar da suka Waukarwa kansu? Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..." Ya fada yayin da hawaye ke zarya kan kuncinsa.

Jikina ya yi sanyi wai an jefi kaza da gishiri, wlh komai na duniyar nan ya sire min, Wan adam ba abun yarda bane, In har uba zai iya kwanciya da ?ar cikinsa meye kuwa bazai faru ba? Da yawa wasu fitintinun da ke faruwa da mu daga laifukanmu ne, bawa shi ke ja ma kanshi, tayaya zamu ga daidai bayan irin zunubban da muke aikatawa, tayaya zamu zauna lafiya bayan irin fasadin da ake aikatawa a doron kasa? A kashe wanda bai ji ba bai gani ba, ko a azabtar da shi, A tauye masa hakkinsa na rayuwa! Meyasa wasu basa tunawa da cewa kamar yadda suka kashe wata rana suma mutuwar zata riske su kuma basu isa su dakatar da ita ba?Ina zaka je da hakkin rayukan dake akanka? A ranar daka farka ka ganka a cikin ?abari batare da komai na duniya da kake ta?ama da shi ba ya za ka yi? kafin ka aikata ba daidai ba ka fara tunanin menene makomarka? Bakasan ranar mutuwarka ba, a wace rana, a wani lokaci? Don haka mu ji tsoron Allah!


Duk a wannan zaman Taj ya faWa masu game da sace su Unaisah da Musa ya yi, kuma ya bayyana masu Wiyar Shureim ita ce Batool yarinyar nan dake a tare da Unaisah. Sun shiga damuwa sosai, duk da halin da sheikh Imam ya ke a ciki saida ya taimaka da yi masu nasiha ganin yadda su Benazir suke kuka, ya ce su daina kuka bazai ta6a yi masu maganin damuwarsu ba, in har sun dogara da Allah, kuma sun yi imanin shi kadai ne zai iya nema masu mafita toh su tashi a cikin daren su yi nafilfili In sha Allah babu abun da zai same su, Bi'iznillah...


Sun ji daWin shawarar da Baba Imam ya basu.

Ba tare da 6ata lokaci ba, Taj Ya nuna masu Wakunan da zasu shiga su yi alwala..


kafin su gama yin alwalar Taj ya yi ma ma'aikatan gidan magana suka shimfiWa masu prayer mats a nan main falo, darduma ce mai faWi da tsawo, Ummi ce ta Wauko hijabs taba Benazir da Anila.

Sheikh Imam Malik ne ya ja su sallar da kyakkyawar niyyarsu, mazan suna a sahun gaba, yayin da matan su ke a sahun karshe na bayansu gwanin ban sha'awa kamar a masallaci

Yadda suka ga rana haka suka ga dare, nafilfili suka dinga yi batare da gajiyawa ba, har saida kafafunsu suka fara zogi tukunna suka kammala sallar, kowan nan su ya Waga hannayensa sama, Sheikh Imam ya dinga karanto addu'oi cikin harshen larabci suna amsa mashi da Ameen Ameen.

Sun yi ma su Unaisah addu'o'in tsari da kariyar Ubangiji, suka yi ma su Chief addu'o'in nasara da kariya, sun kuma la'anci su Musa da sauran Elders na kurkukun ?addara..


Akan kunnuwansu aka fara kiraye kirayen sallar asubahi, nan ma suka kuma mi?ewa su ka yi Salatul fajri.

babu wani mai kwanciyar hankali a cikin su, sun damu sosai, zukatansu sun cika fal da fargaban a wani hali yaransu suke a ciki? Suna a raye ko ya kashe su?"



Meya faru bayan tafiyar Chief Owais?



Tun a daren ranar ya kira CI ya sanar da shi abunda ke faruwa ya kuma umarce shi da ya tattara Senior Agents dinsu da Isod soldiers dukansu Su bazama neman Alhaji Musa, ya kuma Kira Commender James ya Fada masa akwai matsala, Yana son ganin shi tare da sauran yan team Winsa.


Daga bisani ya kira Taj ya ce ya ba Alhaji Ubaid waya yana son yin magana da shi, bayan Taj ya ba Alhaji Ubaid wayar, chief ya yi masa tambayoyi game da wuraren da yasan Alhaji Musa yana yawan zuwa.

Alhaji Ubaid ya bayyana masa guest houses dinsa da location din da suke, Cos yana yawan zuwa da shi wasu lokutta in zai yi baki daga kasar waje.

godiya chief ya yi masa daga bisani su ka yi sallama.


Cikin ?an?anin lokaci jiniyar motocin jami'ai ta karaWe ilahirin birnin Abuja, wiwi wiwi, ga sautin bikes din Isod soldiers dake sintiri kan titituna, duk wani rai da ke bacci saida ta girgiza saboda yadda ?arar jiniyar ta cika kunnuwan mutane kamar za'a tada garin, sa?o da lungu na garin da kowani titi ma?il yake da sojoji harma da ?an sanda.


Hankulan jama'an gari ya tashi haikam, ganin yadda Jami'ae ke sintiri, Kowa so Yake ya ji meke faruwa? Musamman ?an jarida tun safe suke ta sintiri jami'ai sun hana su yi aikin su, ko kusa da su basu isa su ?araso ba.


Ba a ta6a fuskantar tsaro irin na yau ba a garin, kan al'umma ya Waure tamau, ko ina zancen ake yi, wasu ma ?an jaridan har sun fara buga labaran ?arya suna yaWawa don su karkato hankalin al'umma.


Idan muka koma Isod Headquater, wasu gungun cyber expert ne masu fikra a cikin katafaren Surveillance room din su, na'urorine ?an bala'i cike da Wakin, Kowani agent ya tasa computer dinsa a gaba sun baza basirar su da ?warewar su gurin yin binciken su.


Ta cikin na'urorinsu suna kallon komai dake wakana a cikin garin abuja, sun sanya ido sosai akan motsin komai da ke gudana.


Agent Ethan Kim ne yake jagorantar su, a bisa Umarnin Chief Owais, duk bayan ?an mintuna sai ya le?o Wakin ya duba su don ya ga in ana samun cigaba.


Duk bayanin da suka bashi batare da bata lokaci ba yake kiran Dg a waya ya sanar da shi halin da ake a ciki.




~_________________________________


Shin Meke Faruwa A gidan Alhaji MusaS'




Sakamakon jiniyar da ta karaWe cikin gidan ne ya yi silar farkawar wadanda ke bacci.


Da gudu Zeenatu ta fito daga bedroom dinta hannayenta rungume da pillow, hada duvet Winta da ya nannaWe jikinta, tsabar rudu ne yasa ta rikice ta rasa ina zata dosa.


"Mommy! Daddy! Ya Shureim! Aunty Benazir! Mommy Layla! Uncle! wai kuna ina ne? Babu mai jina ne?"


Da sauri maids din gidan suka fito daga part dinsu daga gani bacci bai ishe su ba, hankulansu a tashe jin Jiniya.


"Meke faruwa ne? Su wanene ke shigowa gidan? Daga Ina nake jin jiniyar nan? Kai jama'a kamar za'a fasa dodon kunnan mutane? Wannan ?ara haka ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login