Showing 246001 words to 249000 words out of 321579 words

Chapter 83 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

baka shawarar ka aureta dadi nake ji, saboda ba karamin taimako zamu yi ma rayuwarta ba, ina jin tausayin rayuwarta, bata da kowa in ba Allah da mu ba"


idanunta ne suka cicciko da ?walla.


"Am so proud of you, bani da tamkarki turai, kin cika mata tagari, kyawawan halayanki sunfi komai jan hankalina, baki da son kai, da wata ce ba zata taba bari kawarta da take a cikin wani hali na rashi, ta auri mijinta ba, ke ta dabance..."

ya fada tare da rungumota, murmushin jin dadi ta saki"kaima ka cika miji nagari, Uban marayu, ina alfahari da kai"

yaji dadin kalamanta.

Peck ya manna mata a forehead dinta.

"Nagode sosai Ummu Naja'at, Allah yayi maki albarka, Allah ya saka maki da aljanna silar kyautatawar da kike mani"

"Ameen daddyn Azeezaty.." dariya suka sakarwa juna.


~________________________________
Lokacin da Hajjaty ta karaso murna ta cika su, batare da bata lokaci ba, ta kama hannayen Unaisah ta fara tsantsara mata ?unshi, both side na hands dinta da tafin hannunta dana kafarta, da yatsunta duka ta kawata su da maroon henna, sai da kowa ya raina kunshin shi saboda haduwar kunshin Unaisah, abunka ga fatar amarya taji gyara, duk da suma bridemaids din nasu yayi kyau.

Ko da Batool taga kunshin Unaisah nan fa ta haWe rai tace itama Hajjaty take so tayi mata kunshi kuma irin na Unaisah ta ke so komai da komai..

Hajjaty tace bazai yiwu ba, anfi son kunshin amarya ya banbanta dana bridemaids.


Kowa bai goyi bayan ayi mata irin kunshin Amarya ba, hakan yasa ranta ya 6aci, har tayi zuciya ta mike zata bar gurin
Unaisa tayi saurin dakatar da ita, cikin sanyin murya ta lallashe ta tace ta dawo ta zauna ayi mata irin kunshinta, dakyar ta shawo kanta ta koma ta zauna har suna tsonakarta da cewa copycat din amarya, komai amarya tayi sai tayi itama, bata ko kula su ba.

Abun daya Waurewa Unaisah kai, meyasa Batool ta ke son yin komai irin nata? Yanzu ta gane dalilin dayasa tun farko taki yarda ayi mata kunshi ashe jira takeyi ayi mata irin nata, ta rasa gane meyasa batool take kishi da ita? Meyasa take kwaikwayonta? tun bata fahimta har saida tafara ankara, daidai da spa idan sukaje komai akayi mata na gyaran jiki, batool sai tace ayi mata irin nata, komai da ake ma amarya itama sai anyi mata, ko kallonsu kayi ba zaka ga banbanci ba, kamar dukan sune amaren, kuma idan ta nuna tanaso ayi mata irin nata wani ya nuna rashin goyan bayanshi, ranta baci ya ke yi, har sai ta samu ta lallasheta, bawai bakin ciki take yi da hakan ba, ta yarda da Batool sai dai tarasa gane meyasa take yi mata haka?
Lokacin da lallen nasu ya bushe Hennah artists dinne suka wanke masu shi, su ka shafe masu zanan kunshin da mayuka masu kara fito da kyawun kunshi.

Bayan da suka kammala zaman kunshin, henna artists suka tafi bayan da aka hada masu sha tara na arziki, Hajjaty ce kadai bata kaiga tafiya ba.
ta kira Unaisah gefe daya ta fada mata tana son suyi magana.

Unaisah tace su shiga daga ciki.

A bedroom din ta suka shiga.
Ta daura Handbag dinta akan gadon Unaisah suka fuskanci juna..


"Unaisah ba sai da nace maki kyauta zanyi maki kunshin ba? ya akai naga alert na dubu dari uku kudin menene har haka"? arude Unaisah tace"bani na tura maki kudi ba, amma muga alert din" mi?a mata waya hajjaty tayi tasa hannu ta kar6a tare da duba reciept din.

Murmushine ya bayyana akan fuskarta"Aunty hajjaty, wannan alert din daga Chief ne, ni na fada masa ke zakiyi min kunshi amma bansan cewa shi zai biya ba"

Murmushi Hajjaty tayi"sunyi yawa Unaisah, sai kace ni nayiwa duka yan matan amarya kun shi?

"Please karki damu, rabonki ne, yaji dadi kinyiwa amaryarsa lalle shiyasa shima ya baki tukuicinsa.."


annurin farin ciki ne ya bayyana akan fuskarta, Taji dadin yadda Unaisah take bata girma.


"Saboda za6ana da kikayi a matsayin wadda zata yi maki lalle, nima ga nawa gudummuwar .."


ta ?arashe maganar tare da buWe handbag dinta, Unaisah ta kura ido a kagare da son ganin menene ta kawo mata.

Set ta curo na kayan gyaran jikin amarya..

Dayawan su, Sudanese dilka, kabbasa spray, Hair bakhhoor diffuser, sandal sukkariya, dilka soap, turaren tsugunno da sauran su, saida ta gama jerasu agaban Unaisah tukunna ta soma yi mata bayanin yadda zatayi amfani da su, ta nutsu tana sauraron ta hadi da dan jinjina kan ta..



daga bisani ta Waura da yi mata nasiha

"sai fa an cire kunya da girman kai ake nunawa miji soyayya, ki zama karuwar mijinki, kullum ki kasance cikin gyara da tsafta, bana son tuna rayuwata ta baya amma zan fada maki sirrina saboda inaso kisan surrukan mallakar miji ba boka ba malam, wanda in har kika bisu nayi imanin mijinki ba zai ta6a gajiya da ke ba, zai kasance kullum cikin marmarin ki"


daWine ya lullu6e Unaisah ta kasa kunne tana sauraron sirrikan da Hajjaty ke faWa mata, ta bayyana mata komai batare da jin kunyarta ba, sai dai ita idan taji abun daya fi karfinta ta Wan sunnar da kanta ?asa ko ta rufe fuskarta da tafinta ko ta sanya pillow.

Amma fa taji dadin shawarwarin da hajjaty ta bata game da zamantakewar aure..


Unexpected ta dinga hango inuwar mutun jikin window din dakinta, ta wutsiyar idanun ta kamar akwai wanda ke yi masu la6e.

"Bansan da wasu kalmomi zanyi maki godiya ba aunty Hajjatyna, Allah ne kadai zai iya biyanki, ke ta dabance, Kina da kirki, kinason yar nan taki sosai.

Taji dadin maganar Unaisah"karki damu Unaisah, ni dai fatana ki zauna lafiya a gidan mijinki.. "

Ta fada tare da mikewa, itama Unaisah ta mike.
Wayar Unaisah ce tayi ringing da sauri ta juya ta dauko tayi picking tare da karawa a kunnanta.

"Mommy, har mun gama zaman kunshin, Naji shiru baku dawo nan ba"

On the other hand Muryar Benazir ta amsa da cewa"muna a part din Danejo, aikine ya ru?e mu, ba lallai mu shigo nan ba, zamu kwana anan"

"Am sorry mommy, mun barku da aiki"

"Karki damu, Ya zaman kunshin naku? Ina fata anyi maki mai kyau"?

"Eh mommy, Aunty hajjaty ce tayi min, yanzu haka muna a tare, baki ga alherin da tayi min ba, ta kuma bani shawarwarin da zasu amfaneni"


"Kai Amma naji daWi wallahi, idan tana a kusa ki bata wayar inyi mata godiya"

"Toh" ta fada tare da mikawa hajjaty wayar da fara'arta ta kar6a, Benazir ta dingi yi mata godiya.

A hankali Unaisah take dan satar kallon Window glass ta wutsiyar idanun ta, Tarasa gane wanene ke yi masu la6e, kuma yaki tafiya yana nan yana sauraronsu baisan tana ganin inuwar shi ba.

Bayan da hajjaty ta yi sallama da Benazir, ta mi?a mata wayar ta kar6a ta kara a kunne.

"Unaisah, Ki kula min da kanki"

"Toh mommy, kema haka"

Daga haka sukayi Sallama, bayan ta ajiye wayar, suka fito tare da hajjaty don tayi mata rakiya.

Gaba Waya ?awayen amarya agidan za su kwana saboda sunyi dare sosai, duk da babu nisa gidajen su amma akwai tazara kaWan.


Har bakin gate ta rakota, bayan sunyi sallama ta dawo gida.

Har lokacin bridemaids basu je sun kwanta ba, sun cika falon da haniyarsu.

Gyaran muryar da tayi masune yaja hankalin su ga kallonta.

"Kuje ku kwanta, Gobe akwai aiki agaban mu"

ba musu suka amsa mata da toh.

Bayan ta nunnuna masu Bedrooms din da zasu kwana a ciki, duk mutun uku daki daya.

A tare da Azeeza da Jemimah suka nufi Bedroom din ta.

Bayan sun shiga, ta Wauko masu rigunan baccinta taba su suka musanya dana jikin su, kafin su ka kwanta kan gado.

Kamar ance ta kalli kayan da Hajjaty ta kawo mata nan take gabanta ya fadi ganin babu wasu daga Cikin su, dayake komai kala biyu ta kawo mata, an Webi kala WaiWaya anbar mata sauran.

To fa! Ta fada da rudu akan fuskarta aranta ta ayyana wanene ya shigo dakinta ya sace mata kaya? Da sauri ta dubi window tunawa da inuwar mutumin data gani dazu yana yi masu labe, zato zunubi amma tana ji a ranta dakyar in ba Batool bace ta sace su tun da itace ke gasa da ita, In ba ita ba waya damu da kayan amarya.

Girgiza kai ta danyi tare da kallon su jemimah har sunyi nisa a baccin su.

Wayarta ta Wauko, Ta kira layin batool almost 3 times tana ringing batayi picking ba.

harta fidda rai sai ga kiran Batool ya shigo wayar
Da sauri ta yi picking"sis Ina kika shiga ne? Ba adakina zaki kwana ba"?

On the other Hand Batool tace"ai ni gani nan harna kwanta.."

"A wani daki ne Kuma ku nawa ne"?

"Mu ukune ni da Sajeeda da Zeenatu"

"Meyasa ba zaki dawo nan ba? Nafi son inji ki a kusa dani" ta fada kamar zata saka mata kuka.

"Kiyi hakuri Ukhtyna, na riga na kwanta, Kuma muna a down stairs, kinga dare yayi bazan iya fitowa ni kadai in dawo nan ba.."

kanta ne ya daure, Batool bata taba yi mata gaddama akan tayata kwana ba in ta bukata sai yau, nan take ta tabbatar da zargin da takeyi mata, wato tana jin tsoron tazo asirinta ya tonu ta gane itace ta daukar mata kayanta.."

cikin sanyin murya tace"karki damu sis, ki kulamin da kanki, sai Allah yakaimu"

"Kema haka.." bayan sunyi sallama, ta koma kan kujerar gaban study desk dinta ta zauna, table Lamp ta kunna nan take haske mai kyalkyali ya gauraye gurin.


Lumshe idanunta tayi tana shakar kamshin dake fita daga jikin ta.


Duk yadda taso ta hana zuciyarta kawo mata tunanin shi saida ta gagara..

Kalamansa ne suka soma dawo mata a cikin tunaninta..

_Unaisah my desire for you burns fiercely, taking your virginity has become my utmost dream, For what feels like an eternity, I've been tormented by my longing for you, I've concealed it for your sake, but my craving for you only intensifies_

_I'm patient, Unaisah, not wanting to rush or harm you, I yearn to make love to you with your trust, your consent, I don't mean to pressure you, I simply can't wait to be with you_

_When I return, grant me my heart's desire, Unaisah And let's create a memory that will last a lifetime..."_

siraran hawaye ne suka soma gangarowa ta cikin idanunta dake a rufe kaitsaye suke dira saman kuncin ta..


Cikin rawar murya ta furta"meyasa tun lokacin da kana araye bangane yadda kake azabtuwa da son kasancewa dani ba? bani da hankali Danish, ni sakarya ce"!


"Abun da kake ji nima inajin shi Danish, inama ana iya dawo da wanda ya mutu? Da ba abunda zai hana in dawo dakai don in cika mana burin mu.." da sauri ta toshe bakinta, gudun kada shesshekar kukanta ya farkar da masu yin bacci a Wakin..


"Allah ya jaddada rahamarsa a gare ka my Man"

_ta saba yi mashi addu'a duk da bata da tabbacin koya musulunta before ya mutu_

"ina fata nima Allah ya dauki raina saboda na kosa ayi tashin alkiyama kona sa ke ganinka"


Tana kuka ta fada. (Unaisah da wauta)


kamar mai tabin hankali ta dinga sambatu ita kadai, taki tashi taje ta kwanta, duk daren Allah Haka take fama.

Unexpected kira ya shigo wayar ta, duba sunan me kira tayi ganin Angon nata ne yasa tayi picking call din tare da kara wayar a kunne..

Sexy Voice dinsa ce ta ratsa kunnanta"me kike yi har yanzu baki yi bacci ba"?

Lumshe idanunta tayi slowly tana ji kamar Danish ne ke yi mata magana..

"Tunaninka nakeyi..."

"Nima na kasa runtsawa saboda tunaninki, saura kwanaki kadan suka rage, i can't wait to see you on my bed"

kunya ce ta kamata har takasa furta kalma, ta rasa ya akai take jin muryarshi sak irin ta Danish ko dan ta sama ranta shi ?

Mayar da kiran yayi Video call

ga mamakinta sai taga duhu a screen din..

"Tabarakallahu Ahsanul khalikin, dagaske kece kika koma haka? kyawunki ya razana ni Unaisah"

"Why i can't see you honey, duhu screen din"!

"Dagangan na toshe camera din, baki tuna wani abu ba?..." ya tambaya.


tuntsirewa tayi da dariya tunawa da wannan ranar da bazata taba mantawa ba..

"Oh kaima ka kira ne don ka gaisa da mutanan duniya, shekararka nawa? Ina mai wayar?..

Ta fada da zolaya..
Sautin dariyar shi tajiyo ta cikin wayar.

Murmushi tayi tana jin wani irin nishadi da kwanciyar hankali na ratsa ta..

"Unaisah, Ina fata babu namijin da ke kalle min ke? In ba haka ba Kishi zai iya kashe ni"

dariya tayi har fararen hakoranta suka bayyana kamar gonar auduka tar da su.

Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ta soma jin yana saukewa mai haWe da fitar numfashin sa..

aruWe ta furta"hubby? Kana lafiya kuwa? Naji voice dinka ya sauya.

"Ke kika jefani a halin da nake ciki Unaisah, kallonki da nakeyi a yanzu ba karamin fusgana kike ba.."

gabanta ne ya faWi ta manta rigar bacci ce a jikinta time din daya kira picking kawai tayi ba tare data rufe jikinta ba, a rude ta soma dudduba jikinta duk fa yana kallonta da alama ta manta.


Mikewa tayi daga kan kujerar ta je ta dauko throw pillow da duvet, ta dauki wayar ta koma kan couch ta kwanta tare da rufe rabin jikinta da bargon, ta rungume pillown a kirjin ta.

Saida ta daidaita nutsuwarta tukunna ta saita fuskarta akan screen din wayar..

"Hello! Husband to be kana ji na"? Shiru taji bai tanka mata ba..

Tayi zaton matsalar network ne, batasan duk wani motsinta akan idanunsa.

Har ta fidda rai da sake jin muryar shi taji yace"Ina ma ace nine kika rungume kamar yadda kika rungume pillow din hannunki.."

runtse idanunta tayi tana jin wani irin yanayi mara misaltuwa, sometimes idan yana furta mata kalaman soyayya har tunani takeyi ina matarsa Nazli sarauniyar kyau? Ko itama yanayi mata irin haka? Ko da yake ita da take agida ai already tafi ta jin ire iren daWaWan kalamansa.

"Am sorry idan baki ji dadin maganata ba, bazan iya jurewa bane Unaisah, ni kadai nasan halin da nake shiga idan ina sauraron muryarki, kona kalli fuskarki shiyasa na haramtawa kaina ganinki har sai bayan an shafa fatihar auranmu, a lokacin dana tabbatawar kaina kin zama mallakina halak malak..."

nema ya ke ya kasheta da daWaWan kalamansa gashi yanzu baya kunyar gaya mata irin wadan nan kalaman, gaba daya ya haifar mata da jin kasala a jikin ta..

Cusa kanta tayi cikin pillow duk wani abu da ya ke ji itama tana jin shi sosai..

Cikin harshen turanci ya daura da cewa

"A wannan lokacinne zan bayyana maki irin kaunar da nake maki kamar raina, zan gatantaki Unaisah, zan baki dukkan kulawata da soyayyata, zan mantar dake duk wani bakin ciki da kika taba dandana a cikin zuciyarki, zaki zama sarauniya a masarautar gidana, zan zama hadiminki me yi maki hidima, zan kuma zama sojanki mai baki kariya, in kuma zama likitan da zai dinga ceto rayuwarki a kowani hali na ciwo, na maki alkawari a dare Waya zan canza maki rayuwa.."

bitting lower lip din ta tashiga yi tsigar jikinta na Wan tashi
Cikin rawar murya ta furta"yaya Owais, bacci nake ji, sai Allah yakaimu, ka kulamin da kanka.."

tana karashe maganar bata jira amsarshi ba tayi rejecting call din.

Fashewa tayi da matsanancin kuka mai tsuma zuciya, gaba daya ya tuna mata yanayin da su ke shiga ita da Danish idan suna a tare, da?yar bacci 6arawo ya yi awon gaba da ita.


=إ?=ث?


Allah yayi dare gari ya waye, Da sassafe Amarya da ?awayen suka farka daga bacci kowaccen su ta shiga toilet tayo wanka, suka shirya kan su cikin abaya, Already an tanadar masu abinci mai rai da lafiya na breakfast din su a dining area..

Bayan da suka zauna yin beakfast, kowa Ya ci ya koshi, In ka cire Unaisah data kasa ci dayawa, kalaman chief owais ne keta dawo mata a cikin tunaninta, duk ta rasa sukununta, da tunanin shi ta farka daga bacci, batason ganin komai in ba shi ba, gashi ya haramtawa kanshi zuwa zance har sai bayan an shafa fatihar auransu.

Around ?arfe shabiyu na rana, Benazir ta kira Unaisah awaya ta ce tana son ganinta tare da ?awayenta, su hadu a part din Danejo...

Bayan ta sanar da su, gaba Waya suka dunguma izuwa Sashen Aunty Danejo, suna shiga main falo suka fara hango haWaWWun Invitation bags a saman rug, daga jikin kowace jaka an rubuta will you be my Bridemaid? tare da sunan mamallakin jakar.

Nan take suka gane nasu ne za'a basu, farin Ciki Ya cika su kamar su zuba ruwa kasa su sha.

Anan suka taras da Benazir da Ummi tare da Danejo, with respect suka gaishe da su, Unaisah ta zagaya ta bangaren mommynta tayi hugging din ta bayan sun gaisa tayi hugging din Danejo dake ta sakar mata murmushi.

Batool tuni ta yi gurin mommynta, su kayi hugging din juna.

Bayan sun gama gaggaisawa da ?an matan amarya..

Benazir tace"gaba daya munayi maku barka da zuwa, jiya bamu samu zama ba, shirye shiryen biki ya hana mu leko gurin ku, shiyasa bamu samu zuwa munyi maku barka da zuwa ba, amma kuna aranmu, munji dadin zuwan ku..." Ummi ta Waura da cewa"muna fata kunyi bacci lafiya kun tashi lafiya, Ya kuma gajiyar zaman ?un shi"

atare suka hada baki gurin furta"Alhamdulillah, Mun tashi lafiya, muma munyi farin ciki da kuka gayyace mu, kuma in sha Allah da mu za'a kare bikin nan"

murmushi suka saki gaba dayansu sunji dadin maganar su.

Danejo tace"wadannan invitation bags din da kuka gani, musamman saboda ku ango ya bada akayi maku daga Company, ba wai iya jakar bace, hada kyaututtuka na musamman a cikin su, Kun shirya gani?.."

Ihun Farin Ciki suka sanya tare da shewa Yeehhhhhh..

Ummi tace"yawwa my ladies, ku jera layi, duk wadda muka kira sunanta sai tazo ta kar6i nata"

cikin sauri suka shiga layi suka yi shiru cike da zakuwa suke jira abasu don su ga menene a ciki..


Ummi da Danejo ne ke daukar bags din idan suka duba sukaga sunan dake a jiki sai su kira su ba mai ita..

"Sadeeja, Zeenatu, kuzo ku kar6i naku" Benazir ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ce ta kira sunansu atare.

Bayan da sukazo ta damka masu bags din a hannayensu kafin ta manna masu peck a forehead dinsu"yan matana, Allah ya nuna min naku da raina da lafiyata..."

ta fada tana shafa kafadarsu cike da jin dadi suka amsa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login