Showing 135001 words to 138000 words out of 321579 words

Chapter 46 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

doc din dake kula da Omar, bayan ya daga cike da fargaba ya tambayi ya jikin Omar"?

Doc din yace"har yanzu bai farfaWo ba, amma muna ganin cigaba a lafiyarsa, kuma muna sa ran zai iya farfaWowa a kowani lokaci..."


da jin maganar da doc din ya faWa nan fa hankalinsu Ya ?ara tashi..

Jikin Taj ya hau yin kerma

"in kuwa hakane, Koma wanene ya Wauke su zai iya yiyu wa daga Elders ne, tun da har ya iya sauya kamannin shi, hakan na nufin matsafi ne, amma tayaya za'ay mu san wanene Ya Wauke su? chief ne ya jefa ma kanshi tambayar da bashi da amsarta.


Damuwace tsantsa akan fuskar taj "inna lillahi wa'inna ilaihirraji"un bana fata hakan Ya kasance saboda nasan ba zasu masu dakyau ba, da nasani ban tafi nabar su ba, laifina ne, da duk hakan bata faru, rashin sani yasa dukan mu bamu ga
kiran Unaisah ba, ni nasan????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?  tayi iyakar kokarinta donta same mu awaya, kuma inaji raina ba hakanan aka tafi da su ba, saboda Unaisah tana wayou dole akwai wani abu da akayi masu..."


zafafan hawaye ne suka wanke Fuskar shi, ga wani zazzabi da ya rufa sa.


Sum ma rasa ta ina zasu fara binciken wannan al'amari? Wanene Ya dauke su? Meyasa aka sace su? Da wata manufa akayi hakan? Me kuma zai biyo baya!.

Babu wani mai kwanciyar hankali a cikin su, sam sun manta da batun Ummi.


Taj Ne ya kawo shawarar Su jaraba Bin diddigin Layin Unaisah, yana tunanin Ta tafi da wayarta tun da basu ganta a dakin su ba.


A hanzar ce Chief Ya fara ?o?arin yin tricking din layin ta ta hanyar wayar sa, sai dai bai Iya gano komai ba duk ?warewar sa.


Har Number dinta Ya turama wasu Cyber Experts daga Cikin jami'an su, amma daga baya suka kira tare da sanar da shi sunyi iyakar bakin kokarinsu don ganin sunyi hacking layinta, amma sun kasa gano ta?amaimai location din da wayar ta ke, suna tunanin tana a gurin da babu network ko kuma an jefar da wayar wurin da baza a iya tracking ba.


bakin Ciki ne Ya cika Zuciyoyin su.


Daga shi har Taj an rasa me lallashin wani kowa Ya shiga damuwa.


Tunanin komawa Cikin gidan su ka yi don su kara bincikawa su tabbatar babu su din don jin abun su ke kamar ba gaske ba.


Babu inda basu duba ba, suma officers din gidan sun tayasu neman su, babu su babu alamar su, Kowan nan su sai da ya haWa gumi akan fuskarsa.


Falo suka koma su biyu shida Taj suka zauna saman Sofas kowan nan su ya zabga Uban tagumi kamar marasa galihu.


Unexpected suka tsinkayi sautin tafiya, kusan atare suka kalli Mai shigowa cike da sa ran su Unaisah ne.


Kamar mahaukaciya ta faWo Falon, Ko takalma babu a kafafunta, fuskarta jaga jaga da hawaye, idanunta sun kumbura suntum, gyalenta ma A hannu Ta ruke shi, har suna haWa baki gurin ambaton Sunanta UMMI..


Kusan atare suka mike suna Kallonta ganin Yadda ta sauya lokaci Waya kamar wadda tasha bugu.


Kaitsaye Ta nufi Chief Tana karasawa gaban shi, Ta zube kan gwiwowinta, kamar zata haukace masu, Cikin Kuka da wata irin raunanniyar murya ta furta"zai.. Zai kashe su! Shine Ya Wauke su! Suna a wurin shi, Kashe su zai yi..." gaba daya ta ruWar da su sun kasa gane kan maganarta.


Faduwar gaba suka ji, daram dararam, a razane suka kalli juna.


"Ummi ki yi mana bayani meke faruwa? Su wanene zai kashe? Kuma wanane kike magana akai"?


Cikin shasshake murya tace"U..U..Unaisah, da Bab.. Ba tool, Ya faWa min komai, Ya cuce ni, ya yaudare ni, shiya rabani da mahaifina Ya kuma rabani da kowa nawa, Batool diya ta ce, Ita ce babyn dana bari, bata mutu ba, tana araye, shiya sadaukar da su yanzu kuma Ya kara Wauke su ....."


Tsantsar tashin hankali ne ?arara akan fuskokin su, Sun riga da sun gane wanene Ya Wauki su Unaisah, dama sunata hasashen zasu kawo masu farmakin bazata, ba zasu ta6a kawo ma ransu ta kansu Unaisah zasu biyo ba, Wlh sun shammace su, ga kuma Mamakin kasantuwar Batool diyarta.

"Ummi Ki natsu ki fada mana komai da kuka tattauna da shi, watakin mu samu ta hanyar da zamu iya ceto rayuwar su, mu kan mu bamusan tayaya akai suka dauke su ba, saboda ba mu a cikin gidan"


Dakyar ta iya fayyace masu komai da Alhaji Musa ya faWa mata.

Ba su yi mamaki ba saboda sun riga da sun san komai itace bata sani ba, abun da yafi bakanta ransu ta yadda ya bayyana mata komai da yayi mata batare da tunanin wani hali zata shiga ba.


Kwata kwata basu tambayeta meyasa tayi gangancin daya gano ta ba, duba da halin da take a ciki ba.


HaWuwa sukayi atare suna Lallashinta tare da yi mata alkawarin zasu yi iyakar bakin ?o?arin su don ganin sun Ceto rayuwar su.


Dakyar suka shawo kanta, Taj Yace Ta shiga ta kwanta, ta huta.


Tace mashi ita da hutu Har abada, bata tunanin zata iya rayuwa batare da Yar ta ba, don basu san me take ji a cikin zuciyarta ba.


Tsananin tausayinta ne Ya kamasu, kamar zasu zubda mata ?walla.


Tace ma Taj ya ara mata wayar shi, Tana son tayi kira.
Ya tambayeta wa zata kira?
Tace Ya shureim tana son Ta fada masa komai.

chief Yace tayi hakuri ka da ta daga mashi hankali, Ta bari su fara samun mafita tukunna

Kuka tasaka masu tare dayi masu magiya tana rokonsu akan su bata ta kira shureim tana son ganin shi tana son ta nemi yafiyar shi, sannan tana so ta faWa mashi game da babyn su.

?in amincewa su kayi, gaba daya ta rikice masu kamar ta fara fita hayyacinta sai sambatu ta ke yi masu, can Kuma data galabaita wani matsanancin ciwon 6arin kai Ya taso mata, ta fara ganin jiri jiri tun tana karanta addu'o'i harta kasa, ta fada masu kanta ciwo yake mata, kirjinta zafi, numfashinta zai Wauke.


da sauri chief ya juya yaje medical room din gidansa ya Wauko mata sedative, ya dawo falon tare da Glass of water a hannunsa ya mika ma Taj ya kar6a tare da mi?a mata maganin hannunta na kerma ta kar6a ta tura abaki, ya kanga mata ruwan ta sha, har saida takusa ?warewa kamar za ta yi amai ta kama kakari.


sun bata maganin da nufin ta samu tayi bacci amma sai ya zamana kamar sun ?ara ninka mata azabar radadin da take ji, baiwar Allah kamar ?aramar yarinya ta dinga rusa masu kuka tana ambaton sunan Baba imam, shureim, Babynta.


Har tambayar ta su ka yi ta fada masu address din Guest house din sa, tace bata sani ba, sau biyu ta ta6a zuwa, kuma duk zuwan da zatayi shi ya ke zuwa Waukarta da motar shi, baya bari drivern daya Waukota ya karasa da ita, ba zata iya gane komai ba, ko sunan anguwar bata sani ba.


Gudun kada ta hadiyi Zuciya ta mutu Yasa suka yanke shawarar bata wayar donta kira su, bayan Taj Ya nuna mata Contact din su a wayarta yace ta kira su ta ce su zo amma kada ta fada masu meke faruwa ta bari sai sun zo.


dama Suna da burin Su sasanta tsakaninta da Mahaifinta, kuma a wannan ga6ar tana bukatar su saboda su kadai ne zasu lallasheta taji don wlh gab ta ke da ta zare.



Chief bai ga ta zama ba, yace ma Taj Ya kula da ummi, shi zai tafi tare da jami'ai su nemo su, Taj yace bazai iya zama ba, ?wara su tafi a tare, saboda Hankalinsa ba akwance yake ba, in har ba dawo da su Unaisah akayi ba.

Chief yace ya kwantar da hankalinsa in sha Allah ba abun da zai faru da su, amma ba yadda za'ay su tafi da shi saboda har yanzu ?afarsa bata daidaita ba, kuma gurine mai hadari zasu je, Taj yana sharar kwalla yace"bazai gane ba, tayaya ma zai iya kwantar da hankalinsa bayan yaransu suna a hannun fasi?in mutumin da babu imani a zuciyarsa? Wa yasan me zai yi musu? Dakyar Chief ya lalla6a shi harya amince zai zauna badan yaso ba.



*Dr. Shureim=ؔ?*


Bayan ya kammala Yin Nafila Ya buWe kur'ani yana karantawa, wayarsa ce ta soma yin ringing, saida yakai aya, Ya dubi wall Clock Karfe shabiyu, Aransa ya ayyana wanene ke nemansa a irin wannan Lokacin? Ko dai na cikin gida ne"? Mikewa yayi daga kan prayer mat din, Ya nufi wayar dake aje kan gadon nasa.

Daukar wayar yayi da rudu Yake kallon bakuwar Number din da aka kirasa da ita.

Baisan wanene ba, Kuma ba ya jin zai iya picking call at this time duk da wani sashe na zuciyarsa yana shawartarsa dayabi bayan kiran.

Har zai aje wayar wani Kiran ya kuma shigowa.

Picking Yai tare da kara wayar Yana kokarin Yin sallama, kunnuwansa suka jiyo masa sheshshekar kukan mace ta cikin wayar, gabansa ne ya fadi

Bai gane wacece ba, addu'ar neman tsari Ya karanta a cikin zuciyarsa kafin Ya yi sallama tare da tambayar wacece?

"Ya shureim ni ce, Aishatu bintu imam ce.."


sa'ilin da muryarta ta ratsa dodon Kunnansa wani sanyi mai haWe da dadi yaji a cikin Zuciyar shi, kamar wanda akayiwa albishir da gidan Aljanna

Adabarbarce Ya furta"Aisha dagaske kece? Ba mafarki nake ba? Ke da kanki kika kira ni"?


"Ni ce Ya shureim, Ba mafarki bane..." bai karasa jin zancen nata ba Ya zube kan gwiwowinsa Ya fuskanci alkibla yayi sujudusshukr..

Time din da ya dago Hawaye farin ciki ne a kwance saman fuskarsa ga wani tsantsar annurin farin Ciki daya bayyana a tare da shi.

"Aisha, har yanzu Ina kokwanto.."

"Ya shureim, Inason ganinka! pls ka zo, idan ba kazo ba zan iya rasa raina, kai kawai nake son gani.."

muryarsa da zumuWi ya firta"basai kin rokeni ba, Zanzo yanzu, Karki damu, ki kwantar da hankalin ki.."

Katse kiran yayi, jikinsa na 6ari Ya dauki Car key nasa, cike da zumuWi ya fito Jikinsa na bari cikin sauri Ya nufi Hanyar fita daga Main falo..

Kafin Ya ?arasa Ya tsinkayi Muryar Benazir a cikin kunnansa.

"Ya shureim!..." ba dan Benazir ce ta kirasa ba da ba abun da zai hana Yaki waiwayonta..

Juyowa yayi fuskarsa da fara'a ya ke duban ta, sanye take da kayan bacci riga da wando maroon tayi rolling headscarf, sai da ta matso kusa da shi Ya lura da wayar dake a hannunta, Fuskarta duk a yamutse.

Car key din hannunsa Ta kalla"ya shureim Ina za ka je da daren nan? Ka duba lokaci kuwa?

Murmushi ya yi"Ki taya ni Murna Ukhtyna, Aisha ta kira ni yanzun nan awaya, tace tana son ganina, Inzo gidan dg"


aruWe ta furta"Aisha kuma? Ya shureim yaushe aisha ta sauko daga kan dokin zuciyar da ta hau da har zata kira ka? Ka kuwa duba kaga ita dince ta kira ka dagaske?


"Bakuwar Number ce amma Tabbas Aisha ne, Ni naji muryarta.."


"Muga number din" ta fada tare da mika masa hannu bayan Ya bata wayar ta dubi contact din nan take ta gane Number Taj ce.


"Yanzu Can zan tafi, tana jira na"


"Yaya shureim dagaske Aisha ce, number data kiraka da ita, ta Daddyn Unaisah ne amma meyasa take son ganinka a irin wannan lokacin? Ta faWa da rudu akan fuskarta.

"Kada ki tsayar Dani Benazir, ki bani kawai in tafi.." ya fada yana mika mata hannu..

Tana kokarin mika masa wayar, suka tsinkayi Muryar Mami a cikin kunnuwan su..

"Su wanene nan"? Ta fada tana nufo su, atare suka dube ta, Damuwace ta bayyana akan fuskar Shureim har saida Ya harari Benazir ganin taja masa har mami tagansu yasan ba lallai tabar shi Ya fita ba.

?arasowa tayi daga gaban su ta tsaya"meya ke faruwane? Ina kuma zuwa? Ta fada tana nuna key din hannun dr shureim..

Kamar marasa gaskiya sukayi shiru suna kallon kallon atsakanin su..

Hakan Yasa ta fahimci da akwai wani abu dake faruwa kuma basa son sanar da ita..

Har ta buWe baki zata kuma yin magana phone ringing din Dr shureim Ya katse mata hanzarin ta, ganin number da Aisha ta kira ne yasa shi saurin yin picking..

"Ya shureim ka taimaka min ka zo, naji komai daya faru, bayin kanka ba ne, akwai abun da nakeso in fada maka dan Allah kazo, magana ce mai muhimmanci"

Waro idanu waje su ka yi gaba Wayan su sun ruWe sosai, daga mamin har Benazir din sunji komai, basu karasa jin ?arashen zancen ba kiran ya katse..

Arude Mami Ta kar6e wayar shureim tadinga kiran layin ba'a dagawa, kallon su tayi cikin rudani tace"ku fadamin wacece wannan Win? Meyasa take neman ka? Akan me take yin magana? nasan kun sani, kada ku 6oye min ku fada mun kawai in ba haka ba zan sa6a maku.."

Ta karashe maganar kamar zata doke su..

Ran mami Ya 6aci jin sunyi shiru basu Bata amsa yasa ta daka masu tsawa"wai don ubanku ba zaku bani amsar tambayar da nayi maku ba? So kuke ku haukatani ne..." cikin rawar murya Benazir ta ce"aisha ce mami, kiyi hakuri mun boye maki, amma Aisha ce, tana agidan Dg, Kuma Yarinyar nan Azeezaty, bakowa bace face Unaisah ?ata Angel, mahaifinta kuma shine Taj mijina...."


wani faduwar gaba Mami taji, sai zare idanu takeyi saboda al'ajabi..

Ru?e Hannunta Benazir tayi"mami zanyi maki bayanin komai, mu ma bada son ranmu muka 6oye maki ba, Dg ne yayi mana warning akan karmu sanar da kowa game da su saboda Rayuwarsu tana acikin hadari, bazai yiwu a yanzu in fayyace maki komai ba, amma dan Allah mami kuzo mu tafi can gidan, zaifi mu hadu mu duka kowa yaji komai dake faruwa, Saboda Inaji araina Akwai wani abu dake faruwa shiyasa Aisha takira shureim ta nemi da ya je, kuma dama suna bincike akan case din daya shafe mu da kuma shi Taj din..."


Cike da zumuWi Mami Tace toh, bari in Wauko hijabi
Cikin sauri Ta nufi daki, tana shiga ta taras da Alhaji Ubaid Yana kokarin fitowa daga toilet, koda ya tambayi daga ina take? Tace mashi Ya biyota kawai su tafi, akwai wani babban al'amari"

Badajimawa ba, sai gasu sun fito tare da Alhaji Ubaid din, sai tambayarta yake ina za su je cikin daren nan? tace mashi Yabi su kawai in sunje zai gani, da yaga Benazir da shureim Hankalinsa Sai ya kara tashi, bai dai tambaye su ba, yabi bayan su Suka fito daga Falon, Cikin sauri suka nufi Parking space, gaba dayansu a motar Dr shureim suka zauna, Hajiya Layla da Alhaji Ubaid suna a backseat, Benazir tana a front seats tare da Dr shureim.


Key ya yi ma motar, tare dayin riverse Ya nufi Gate, sam Sun manta da Security Officers, aikuwa suna hango motarsu suka Tunkareta gadan gadan..
Hajiya layla tace karya kuskura ya tsayar da motar zasu 6ata masu lokaci ?arshe su hanasu fita, tun da gate din a buWe yake da alama wasu ne suka fita aka bude ba a kaiga rufewa ba ya fuce da su kawai.

Alhaji ubaid yace kada ay haka su bi komai a sannu.

Dr shureim dayafi su zumudi ya kure speed din Motar, Gadan gadan Ya nufi Security Officers din kiris Ya rage Yabi takansu da mota Hakan yasa suka dare tare da bashi hanya, Ya ba motarshi Wuta Ya kara gaba.


Wasu daga Cikin Security Officers din Har bin Motar shi su ka yi sai dai tuni sunyi musu nisa.

Sai da ya tabbatar da sun 6ace masu sannan Ya rage gudun Motar.

Wayar Benazir ce ta soma ruri cikin sauri Ta duba Mai kira ganin Anila yasa ta yi picking tare da kara wayar a kunne

Tana niyar yi mata sallama kukan Anila Ya katse ta,
Arude Ta furta"Anila? Meya faru? Meyasa kike kuka"?


Maganar da tayi ne ta karkato da hankulan su Hajiya layla ga kallon su.


da wata irin raunanniyar Murya ta furta"Benazir, Muna cikin tashin hankali, Uncle Ya kashe ta, mun ga gawarta, yanzu haka da na ke yi maki magana gidan mu a kewaye ya ke da sojoji"

Dafe kirji Benazir tayi"Inna Lillahi wa'inna ilaihirraji"un..."

"Menene? Meya faru? Benazir meke damun ta ne? Me ta fada maki"? Su mami ne Suke ta tambayarta Cikin rudu..

"Bani kadai bace Anila, Ina atare da su mami, Yanzu haka Muna akan hanyar zuwa gidan Dg, Aisha ce ta kira ya shureim tana kuka ta bukaci tana son ganin shi ina tunanin wani abu yana faruwa acan, in ba damuwa mu haWe acan.."


Ta amsa mata da toh
Bayan tayi rejecting Call din ta dubi Dr shureim da ke kallon ta kafin ta mayar da dubanta ga su mami da ke abaya.

"Anila ce, ta fada min wani abu ya faru agidansu, bana iya jin me take cewa kamar kuka takeyi, Amma nace mata mu hadu a gidan Dj nasan zata zo"


Cike da fargaba suka amsa mata da toh kowa da abunda ya ke sa?awa A cikin ran su..

Lokacin da motar su ta haura kan Titin Obie Estate, Cikin sauri Benazir ta kira layin taj, bayan yayi picking ta fada mashi game da zuwan su, tace ya taimaka yayi masu hanyar da zasu shigo cikin sauki, ya ce mata kada su biyo ta gate din gaba, su shigo ta gate din baya na estate din, zai sanar da securies din.

sallama su ka yi da shi, bayan ta fada ma dr shureim abun da ya ce, Ta yi shiru zuciyarta cike fal da fargaba, Muryar Taj da taji ta daga hankalinta kamar baya a cikin nutsuwar shi.

ta gate din baya suka shiga Estate din basu sha wahala ba, saboda already Taj Ya sanar da securities din game da zuwansu..


A parking Space dr shurem ya yi Parking din Motarsa.

Bayan sun fito, Hajiya layla ta dinga jinjina kanta, ganin haduwar tamfatsetsan Gidan dg, tayi zaton daga gidan Alhaji musa an gama Gini mai kyau a Abuja sai yau da Allah Ya kawota gidan Chief.


Shi Kanshi Alhaji Ubaid Ya jinjinama haduwar Villa din..
dr shureim ne ya fara yin gaba jikinsa sai tsuma yakeyi saboda zumuWi, da sauri suka Bi bayan shi.


Basu kaiga ?arasawa ga Kofar Ba, Horn din mota Ya katse masu hanzarin su, sunyi tunanin su Anila ne Hakan Yasa suka dakata tare da juyawa suna kallon Motar da ke shigowa da matsakaicin gudu ta nufo Entry Hall sai da takusa ?arasowa inda suke suka ga gudun nata Ya ragu slowly ta yi Parking daga


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login