Showing 213001 words to 216000 words out of 321579 words

Chapter 72 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

shi daWe, meyasa tun yanzu zaka razana? Ba zaka bari mu shiga kotu ba.."

Ya faWa tare da juya masa Screen Win Ipad Win hannunsa, wai ashe tun zaman shi live video ya ke Wauka.

Alhaji Musa ji ya yi kamar ya haka ?asa ya binne kansa saboda wutar bakin cikin dake azabtar da zuciyarsa, Owais ya gama da shi, ya kashe shi da ranshi, ya ruguza duk wani mutuncinsa a idon duniya, yanzu kowa ya ga mummunar suffarsa da halin da ya ke a ciki.


"Da zaka ga sharhin da mutane suke yi akan ka, sai ka ji ka tsani kanka, tsinuwa ce da la'anta ta ko'ina, sai kuma dariya da yi maka Allah shi ?ara."


buga kansa ya yi jikin bango da ?arfi.


So yake ya mutu sai dai ba halin mutuwa, da biyu suka Waure mashi ?afarshi da Wayan hannunsa marar ciwon, don sun san zai iya amfani da su gurin kashe kan shi, ga zuciyar tashi da ke ta ?onuwa da bakin ciki ta ?i bugawa bare ya ware, lokacinsa bai yi ba. Tun a duniya ya fara ganin sakamakon zunuban da ya aikata, da ya ke jaki ne yafi jin kunyar duniya baisan tun awurin zare ransa zai gane kuskuren sa.



"Unaisah ta yi maka ta'asa Musa, ka ga kuwa mummunar halittar jikinka? Kamar gwaggon biri, so ta yi ta kashe ka, amma mahaifinta ya hana abata damar da za ta yi hakan saboda ba ya son ?arsa ta zama silar mutuwar wani, bayan haka mun fi so ka fara gir6ar abun da ka shuka anan kafin ka ba?unci ?abarinka.


zufa ta wanke fuskarsa, sai faman gurnani ya ke yi da nishi.



"Na ga duk abubuwan da nake so na gani a tare da kai, amma banga nadama ba, sai dai itama nadamar za ta zo maka ne a yayin da ka ga wannan..."



Ya ?arashe yin maganar tare da zura hannunsa cikin aljihun wandonsa ya zaro wasika,


"Ka nemi duniya ido rufe, ka bi???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?yewa son zuciyarka, ka dinga yima mata ciki suna haifa maka ?a'?a, ba kai tunanin iyayen ya'yan da su kansu yaran wani hali zasu shiga ba idan su ka ji irin cin amanar da ka yi masu, ka kasance me son kai Musa, burinka ka faranta ranka, ka nakasa waninka in har zaka samu abun da kake so, nasan Unaisah ta faWa maka game da wasikar da ?arka Unaizah ta bada a baka, to gata nan ta bani in baka, ya rage naka, in ma ka karantata ko ka ketata, matsalarka ce, amma zai fi ka karantata, ita ta rubuta da kanta.."

a hankali ya Waura masa wasi?ar daga gabansa.



Tun kafin ma ya buWe wasi?ar ya karanta abun da ke a cikinta, wasu tagwayen hawaye suka fara zarya kan kuncinsa.


Har Owais ya fuce daga cell din bai lura ba, ya kafe idanunsa akan wasikar da ya gaza buWewa, yana jin fargaban ya ga me Unaizah ta rubuta masa!



Lokaci Waya ya fara tariyo komai nata, gaba Waya ?a'?ansa da ya sadaukar bai ta6a yi ma wani son da ya yi ma twins Winsa mata ba, Zeenatu da Unaizah kuma su kaWai ne ya samu ta hanyar Aure cikin waWanda ya sadaukar, son duniya ne da ya rufe masa ido ya ja ya sadaukar da su gashi nan yanzu ya ja dukan su basa a raye saboda zaluncin shi.



Da yatsun hannunsa mai ciwon ya samu ya buWe wasi?ar da ?yar, yana ganin handwritting Winta ya shaida ita ta rubutata, ta yi rubutunne cikin harshen da ta fi ji british english, da ?yar ya samu nutsuwar karantata.



~________________________________________>?z?



_Idan wani ya zalunci yaro, iyayensa ne na farko da yake fara kai kukansa wajen su, amma idan iyayen nasa ne suka zalunce sa, wurin wa zai kai kukansa? Ni da bansan akwai wanda ya halicce ni ba? Laifin me na yi maka daddy? Me na yi maka dana cancanci wannan hukuncin daga gare ka? Ka sani kokwanton anya kai ubana ne? Anya kana da zuciya a ?irjin ka? Uba koda azzalumi ne shi zaka same shi da son ya'yan shi sai dai ya zalunci na wasu, me na yi maka? Yanzu na gane dalilin da yasa ka hana in san kowa naka, ka 6oye min real identity Winka, ni ina kokwanton ma zai yi wuya idan ba sato ni ka yi ba. Ka yaudare ni, ka ci amanata, ka ha'ince ni, ashe wasan da kake yi min da dariya da gatancin da kake bani duk kana yi ne saboda ka riga da ka sadaukar da ni saboda biyan bu?atarka, ina farin ciki daddyna yana sona, yana gatanta ni, baya son 6acin rai na, ya fi sona fiye da komai ashe na yi kuskure, ka ci amanar yardar da na yi maka, baka ta6a sona ba, ka karya zuciyata. Daddy na rasa wani zunubi na yi maka! Ubangijin da ya halicce ni ma ka hana in san shi, ka yi min ?aryar babu wani addini, idan na ga kana yin sallah sai ka ce motsa jiki kake yi, kawai saboda ba ka son in ra6i rahamar ubangiji na, ka hanani duniyata ka kuma hana in nemi lahirata daddy, kun haWu kai da mommy kun gur6ata rayuwata, ka yaudare ni, ka ce korean school zaka kaini, ashe gidan matsafa ka sadaukar da ni. Burinka ya cika, sun wula?anta ni, kamar karya suka maida ni, mutun shidda a kaina, manya waWanda suka fi ?arfin shekaruna, ni Waya, shekarata sha shidda, ka fi kowa sani. Abun da suka yi min ban ji zafinsa ba fiye da yadda na ji zafin cin amanar da ubana ya yi min, meyasa baka kashe ni ba tun farko? Wallahi na yi danasanin kasantuwarka ubana, mugu, azzalumi, mara imani, alade mai kwanciya da ?ar cikinsa. In sha Allah sai rayuwarka ta wula?anta, kukan ba?in ciki da na yi sai ka yi ninkin baninkinsa, radadin azabar da na ji sai ka ji mafiyinsa. Na tsanake! Na tsanake ka!! Ka kawo ni kurkukun ?addara don matsafa su amfana, nima na amfana, addinin daka hana in sani, ka ke boyemin don kar Allah ya tuhume ka, ?ar uwata Unaisah ta fayyace min komai, ita ce ta ganar da ni wanene mahaliccina, bayan haka silar zuwa na kurkukun kaddara, Allah ya haWa ni da yan uwa masu sona tsakani da Allah, sun bani tarbiyar da baku bani ba, sun bani kulawar da baku bani ba, ku kuma ku je ku da Allah, ga duniyar nan, ita da kuke nema Allah ya bar ku da ita daddy, ku ga idan zata amfane ku, kuma duk min daran daWewa kuma zaku zo inda nake. Allah ya isa ban yafe maka ba! Allah ya saka min cutarwar da ka yi min_.


Bai ?are karanta wasikar ba ya fashe da kukan ba?in ciki, wani irin ?unci mara misaltuwa ne ya baibaye zuciyar sa, kuka har da majina, ya jibge guri guda kamar bijimin sa, ha?i?a kalaman Unaizah sun karya zuciyar shi, sun sa shi jin raWaWin da ba zai misaltu ba, gaba Waya ya rasa meke masa daWi, cikin shesshekar kuka ya ke ambaton sunanta Unaizah Unaizah, kwatsam! Ta soma yi masa gizau a cikin idanunsa, ya zama kamar mahaukacin kare, ya dinga haushi yana kai hannu zai kamo ta sai dai ya ji ya cafki iska..



A ranar da Isod agents suka zo tafiya da baba Obie, kowa da kowa na family dinsa saida Ya hallara a babban falon gidan sa, tun daga kan ?a'?ansa, jikokinsa, hada Sheikh Imam malik shima ya zo, momma ma tana nan, jiya jiya aka sallame ta daga asibiti, ta samu lafiya, memory Win ta ya dawo.

family din matayensa da suke a tare da su duk suna anan, wasu suna a zaune kasa suna jimami, wasu suna a zaune kan kujera sun zagba tagumi, wasu ma kasa zaman su kayi, kowa ya shiga tashin hankali da damuwa.


A gaban Kofar dakinsa Agents din suka tsaitsaya Chief Owais ne agaba, dama Ya faWa masa idan suka kammala binciken su suka kama Elders zai buWe ?ofar, bayan da yayi knocking ?ofar cikin karyayyar Murya yace"baba mun zo mu tafi da kai headquarter din mu, jibi za'ayi zaman shari'ar ku"


kowa Jiran fitowarsa ya ke yi wasu Allah Allah suke Ya mutu adakin karya fito da ransa.

Lokacin da suka fara jiyo alamun zai buWe ?ofar dakin, Hajiya saratu tayi kukan kura ta dira agaban kofar dakin, Ta daddafeta da hannayenta, tana kuka ta dinga rokonsa tana fadin baba dan Allah kada ka fito, baba na roke ka, baba ka 6ace ka tafi wani guri kayi rayuwarku, in ba haka ba zasu azabtar da kai, su kashe mana kai, dan Allah baba ka taimaki rayuwana, banason ka tozarta a idon duniya, bana son su ta6a lafiyar jikin ka, .... "


lokacin da ta ke yin wannan maganar a cikin harshen Igbo tayi, Bakowa ya fahimci me take cewa ba, Yayyenta ne kadai suke jin harshen mahaifin na su.

Kowa dake agurin saida ya tausaya mata, baiwar Allah duk tabi ta haukace ta dinga kuka kamar karamar yarinya babu wanda bai zubda mata kwalla ba.


?iri ?iri ta?i bari ya fito, ta?i kaucewa taba Agents din hanyar da zasu kama shi.


A lokacin yana sauraron maganganunta acikin kunnansa, harya buWe ?ofar, ya kasa motsawa saboda yaji saratu ta daddafeta ta hanasa ya karasa fitowa, kuma kowa ya kasa kawar da ita saboda karya masu zuciya da ta yi.

Ya yi kukan zuci mai radadi, Ya kara jin danasani fiye dana ranar da asirin shi ya tonu, ganin irin halin daya jefa ya'yan shi, kuma still basu daina jin shi a amtsayin Ubansu ba, saratu ta bashi tausayi ta karya mashi zuciya.

Dakyar Sharafudden da sir mubarak suka rabata da kofar dakinsa, tana turjewa suna janta, ta dinga kokarin ?wacewa.


Lokacin daya fito babu wanda gabansa bai fadi ba, sun razana da ganin yadda ya sauya cikin ?an?anin lokaci, Ya rame sosai, tsufansa ya fito, dakyar yake iya Waga kafarsa, bakar jallabiya ce a jikinsa mai hula, Ya rufe rabin fuskarsa da takunkumi, saboda kunyar hada ido da su yasa bai iya dagowa ya dubi kowan nan su ba, har saida suka hada baki gurin furta Baba.

Tukunna a hankali ya Wan dinga satar kallon fuskokin su Waya bayan daya tun daga kan ya'yan shi ya fara, har izuwa kan jikokinsa, akan fuskar kowan nan su ya karancin halin da suke a ciki, bai taba jin kunyar kansa irin na yau ba, jikinsa yadinga kerma kamar mazari, kukan saratu Ya cika kunnansa akan idon shi yaga Sir mubarak da Sharafudeen sun nufi daki da ita, tana ta kiran sunan shi tana fada masa ya 6ace kada ya bari su tafi da shi, a karshe ma hada zagi tadinga hada masa baba tana cewa ya 6ace, wallahi in ka bari suka tafi dakai Allah ya isa ban ya fe maka ba.

Bai ?ara tabbatar da raunin mace da tausayinta ba sai yau, Duk irin abun da yayi wa saratu ya aura mata mijin da shi yasan ba son ta ya ke yi ba, Ya kuma gur6ata shi, amma ahaka take nema ta cece shi saboda bata son ataba lafiyarsa.

A daki suka sanya saratu, tare da twins din ta, suka umarce su da su zauna tare da ita, gudun kada ta lahanta kanta, daga bisani su ka kulle dakin, ta yadda ba zata iya fitowa ba.

Tadinga bubbuga kofar, twins suna rurruketa tana bangaje su, su fadi ahaka zasu mike su cigaba da ru?e ta.

Babu wanda ya ?ara furta kalma, tun bayan da suka ambaci sunan shi.

Ko handcuff agents din basu sanya ma shi ba, saboda nauyin yin hakan agaban Dg sukeji.

Lokacin da ya ke tafiya agents din na biye da shi, yayin da yake kallon kowa dake a kewaye da shi, karaf idanunsa suka sauka akan Jazz dake ta kuka kamar ransa zai fita, mommynsa turai ta rungume kansa a kirjinta, ita ta hana ya motsa da ba abun da zai hana yayi irin haukan da saratu ta yi, saboda kaunar da ya ke ma baba Obie, bakomai ne ya fado masa aranshi ba face maganganun da suka ta6a shi da baba Obie.


_baba, Bana jin daWin yadda wasu suke guduna saboda rashin asalina, meyasa sauran mutane ba kamar kai da daddy mubarak suke ba_

_Na tsani kaina baba, Rashin asalina Yana neman Yaja min na rasa abunda nakeso, kowa ya buWi baki sai yace ni Wan mai aikine bani da asali, Har shege ake kirana baba_

_Kamar yadda nasaba fadamaka,Yau ma zan maimaita maka, Ni dai inason family Winka, Ina alfahari daku, nayi fatan ace nima ina Waya daga cikin jikokin ka sai dai Allah bai nufa_

A cikin ransa yake tariyo komai yayin da yake kallon Jazz, at same time jazz daya ga irin kallon da baba obie yake masa shima saiya tuna da ranar da sukayi maganar..

_ Toh toh ya isa ka yi shiru, Bana son Kana sanya damuwa aranka, Kukan Ya isa haka, kowani Wan adam da ka gani a duniyar nan da irin tashi ?addarar, babu wanda Allah baya jarabta, inaso ka rungumi wannan amatsayin ?addararka, Kada ka ta6a bari wani Yasa ka canza tunaninka, Allah Shi yake son ganin rayuwarka haka, Kuma shine zai nema maka mafita"

_Jazz baka Wauke ni kamar yadda na dauke ka ba, ko da yake ba laifinka bane, laifin wadanda suke yi maka gorine, sune sukasa kake jin kanka bare afamily dina, amma inaso kasani, baba obie baya yi maka kallon bare, inasonka jazz kamar yadda nakeson jikokina, Kamar yadda kake fatan ka zama daya daga zuri'ata nima haka nake fatan ka kasance_

Fashe wa ya kuma yi da wani kukan Aransa ya shiga furta inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Baba meyasa ka kasance azzalumi? baba me yaja maka? Meyasa ka sauya daga yadda nasanka? Ka karya zuciyata baba..."


Aransa yayi maganar, adaidai lokacin baba obie ya Wauke idanunsa da daga kan Jazz, ya dan girgiza kan shi, hawaye na sauka kan kuncinsa..

Sau Waya ya haWa idanunsa dana Momma ya yi saurin kawar da su gefe cike da jin kunyar ta data kamashi, itama ta zubda kwalla kamar ruwan hawayen ta za su ?are.


Bayan da suka fito gaba Wayan su, Chief Owais ya buWe mashi backseat na Motar shi..
Bai kaiga shiga ba, Sai ga Mota ta kunno kai cikin estate din kaitsaye ta nufo gurinsu da matsakaicin gudu tana gab da zata karaso gudunta ya ragu slowly tayi parking a gefen su.


Gaba Waya suka ?ura idanunsu akan Motar suna jiran ganin wanene zai fito.


Amininsa ne Jan kunne Ya fito daga motar, fuskarsa jaga jaga da hawaye, kayan jikinsa sun yi squeezing kamar mahaukaci, ko takalma babu a kafarsa.

Tsantsar tashin hankali da damuwa ne akan fuskarsa.


Sunyi mamakin ganin shi, bayan yasan neman shi akeyi don a kama shi, Owais ne kaWai yasan da maganar zuwan shi, saboda tuntuni baba Obie ya faWa masa ya ce zai mika wuya saboda baba Obie kuma ya cika alkawarinsa ya kawo kan shi, don a hukunta su a tare..


Gaba Waya haushin shi da tsanar shi su ke ji, gani suke kamar shine ya jefa mahaifinsu a halin da ya ke a ciki, Ko arzikin kallon mutunci bai samu agurin su ba, kwata kwata baya a cikin nutsuwar shi, kamar ya fara samun tabin hankali.


tun da ya fito bai nufi kowa ba sai baba Obie, Bai kaiga karasowa ba, Ya'yan baba Obie Suka kare ubansu cikin fushi suka daka mashi tsawa, su ka ce babu shi babu ubansu, tsakanin su sai dai hange daga nesa, amma ya gama kusantar inda mahaifin su ya ke.


Baba Obie Yana kallon aminin nasa da ke ta ambaton sunan shi yana ro?on su akan su bar shi ya gana da amininsa shi kaWaine zai iya kwantar masa da hankali.


Baba Obie yaso su barshi suyi magana amma suka ki basu dama.


Akan idon shi, agents suka sanya mashi handcuff a hannayenshi, suka tura shi cikin motar su.

Owais Yace ya shiga daga ciki, cikin sanyi jiki ya shiga ya zauna, ya rufe masa cardoor din.

Ta gilashin motar yake ta kallon ya'yansa da jikokinsa dake ta kuka kamar ransu zai fita.

Chief owais da kan shi yayi driving din baba Obie.

Duk suna atsaitsaye motocin suka fuce daga Obie estate, gaba da bayan su motocin sojoji ne dana yan sanda saboda su ba su tsaro..



Lokacin da ya ke yin driving dinsa yana satar kallonsa ta mirror, zuciyarsa ta karaya da ganin yadda baba Obie ke ta kuka hada magina a hancin sa.


Cikin shesshekar murya yaji yana fadin kaicona, na zalunce kaina, na zalunci ya'yana da jikokina, na zubda mutuncina, na kashe rayuwar ya'yana da kaina, na kashe rayuwata, bani da hankali, dabbane ni, bazan taba yafewa kaina ba

ya dinga zagin kansa yana aibata kansa.


Kasa magana Owais yayi saboda baida abun da zai iya furta masa, amma daya tuna taimakon da yayi masu sai yaji zai iya masa wani abu.


"Baba bani da abun da zan iyayi maka, ka riga da katabka babban kuskure, shawara Waya da zan baka shine, Ka tuba ka musulunta ka komama Allah kafin mutuwarka, ko dan ka samu sassauci" ya faWa ne kawai don ya kwantar masa da hankali amma shi kanshi yasan ina!


"Owais, Allah ba zai ta6a kar6ar tubana ba, koda na kar6i musulunci, babu abun da zai sauya Owais, ayyukana gaba daya irin na yan wuta ne, tun a duniya owais nasan menene makoma ta, duk wanda ya aikata mai kyau ya sani owais, na aika zunubbai masu yawa munana, hakkin rayukan dake akaina basu kirguwa, ina jin kunyar mahaliccina, ina jin fargaban ranar da zan farka in ganni a cikin ?abarina daga ni sai mugun halina Owais, wallahi na kasa kashe kaina ne saboda tsoron abun da zan taras a cikin ?abarina, wallahi na zalunci kaina saboda neman duniyar da zamu mutu mu barta, gayanan naja ma kaina da ahlina.

maganganunsa sun jefa chief owais a hali na damuwa.


"Duk da haka baba, ka musulunta in har dagaske ka tuba, kuma ka ji tsoron haWuwarka da Allah, bansan hukuncin da kotu zata yanke maku ba, amma nasan zaku yi zaman gidan yari, kaga in hasashe na ya tabbata zaku samu sauran lokacin da yarage maku a duniya, hakan na nufin kana da sauran damar da za kayi ta yin istigfari",


Girgiza kai yayi cikin kunci yace"owais, koda Allah


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login