Showing 291001 words to 294000 words out of 321579 words

Chapter 98 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

Mommynsa ta gabatar masa da shi.


Har Lokacin da Prime minister Ya kira ta awaya ya bu?aci Ya na son ganin su a Nigeria, baisan tana a tare da Omair ba, bata faWa ma kowa ba, iya abun daya sani ta faWa masa suna da hidindimu a dubai na bikin Ya'yan Uncle din ta, kuma idan ta tafi zatayi sati uku acan, ita ta fara zuwa dubai daga bayane su Nazli suka biyo ta, shi kuma a lokacin ya tafi Nigeria domin ya halarci family Meeting, hakan na nufin ko su Nazli basu san komai game da Omair ba.


A lokacin ta shiga damuwar tayaya zata tafi tabar danta dake bukatar kulawarta duk da akwai maids dake kula mata da shi.

Badan taso ba, Ta dam?a musu amanar shi, taja kunnansu sosai akan su kula mata da shi! Ranar kamar kar su rabu, ya rurru?eta har bakin motarta da kyar ta shawo kan shi Yabarta ta tafi..

Daga guest house dinta ta wuce Zabeel palace the ruler's resident, kwana biyu tayi kafin su ka shirya tafowa Nigeria ita da Yazrin da Nazli.

Bayan da suka bar ?asar, cikin ma'aikatan gidanta, aka samu wani munafuki Yaje har fadar Emir ya kai masa tsegumin Yaron da Mujeedat ta ke boyo agidan ta, ta bayan fage, Emir Khalid Ya turo Royal guards don su Binciko masa wanene yaron da ta ke boye"?


Ranar da guards suka zo palm Jumeira cikin guest house Win mujeedat, guards dinta na ganin su suka basu iznin shiga saboda sunsan Emir ne ya turo su.

A lokacin Omair Yana a zaune kan dining Chair, Chefs sun kewaye shi, ga abinci sun jera mashi akan table, sunata lallashin shi don yaci abinci ya?i ci sun rasa gane meke damun shi, ko magana bai yi masu tun bayan da Shiekha ta tafi! basu san kewa bace ke damun shi..


Sa'ilin da Royal guards din suka shigo dining din

Wata razana su ka yi da ganin Omair, su ka ruWe saboda ganin kyakkyawan matashi mai kama da ji?ar Emir.

Cikin sauri Waya daga cikin guard Win ya Wauke shi hoto da wayarsa Ya tura ma Emir duk Fa Yana kallon su a lokacin baisan su wanene ba bai kuma san meya kawo su ba.

Ba'ajima da tura masa hoton ba sai ga kiransa bayan guard din ya yi picking Emir Ya Umarce su da su tabbatar sun tafo mashi da lu'u lu'un nan, Yana son ganin shi a cikin fadar shi"!


Bayan guard din Ya gama yin wayar da Emir, suka Umarci Omair daya taso su tafi fadar mai martaba Khalid Yana son ganin shi.

Rashin sani Yafi dare duhu, Omair baisan wanene mai martaba ba balle yayi musu biyayya ya bisu, hasalima ko kallo ba su ishe shi ba.

Tun suna bashi Umarni yana share su, har suka fara haWa baki gurin yi masa tsawa akan Ya taso su tafi, kai a karshe da su ka ga ya?iya sai suka kama lallashin shi..

da sukaga dagaske bazai bisu ba, sai suka fara ?o?arin Waukarsa ta tsiya, aikuwa Ya fara naWe hannuwan rigarsa zai yi dambe da su, wayaga Iliya Wan mai ?arfi.

Koda Chefs suka fahimci me Ya ke shirin yi cikin sauri Waya daga cikin su tayi masa magana cikin harshen turanci tace mashi royal guards ne daga ruler's resident na dubai, kuma mahaifin Sheikha Mujeedat ne sarkin su sannan shine Ya turo su, kada yayi faWa da su yayi musu biyayya su tafi ba cutar da shi zasuyi ba.

Kasa fahimtarta yayi har saida ta kira sheikha Mujeedat ta faWa mata abun da ke faruwa, tayi mamakin jin baban ta ya turo guards har guest house dinta don su tafi da Omair, amma bata damu ba nan take Ta umarce ta da ta bashi wayar suyi magana, bayan hadimar ta bashi wayar ya kar6a ya kara a kunnansa ta fayyace masa ala?arta da mahaifinta tace karyaji shakku aranshi, Yabisu su tafi zai fi samun kulawa agurin daddyn ta.

Bayan da suka kammala wayar ne, ya bi Royal guards din suka buWe mashi mota Ya shiga ya zauna, suka tada motocin suka fuce daga guest house din ta..


~___________________________________=؋?

Fadar Zabeel hadaddiyar daular arzi?i ce dake a cikin daular larabawa, kuma Babban mazaunin Sheikh Khalid, mai Wumbin tarihi da ikon, tana a tsakiyar Dubai, katafariyar Palace din tana a kewaye da kyawawan lambuna, tafkuna, da maSuSSugan ruwa, ga dogayen bishiyin dabino, ta haWu karshen haWuwa, Alkamina bazai Iya misalta maku ?awatuwar Katafariyar daular ba, Aljannar duniya, abun sai wanda ya gani



Tun daga katafariyar main entrance zaka fara cin karo da Royal security Guards karfafa masu kirar Zakuna..

Bayan da Motocin suka karaso, a harabar ajiye motoci suka yi parking, lokacin da Danish ya fito daga Motar, ya ruWu da ganin haduwar ginin kamar a mafarki Ya ke jin kanshi..

Guards Win ne su ka yi escorting din sa zuwa ciki

tun shigowarsu Royal Guards suke ta Zare ido suna kallon shi, duk inda ya gifta idanun su akan shi haka da suka shiga ciki Hadimai da sauran jama'ar Fadar suka dinga binshi da kallo mai cike da tsantsar Al'jabi..

Har cikin Katafariyar Fadar Emir Khalid suka shiga da shiga, Fadawansa na ganin sa Suka zare idanun su cike da al'ajabi suke bin shi da kallo, Abunka ga wanda baisan takan Fadar Emir ba, maimaiko Ya zauna saiya Tsaya a tsaye ?i?am kamar gunki ko fara'a babu akan fuskarsa babu ladabi babu biyayya, Emir Khalid Yana zaune kan throne dinsa Cikin shigar sarakunan labarawa Na alfarma, Ya nutsu Yana kallon sa.

Cikin harshen larabci fadawan suka dinga umartar shi daya zu?unna Ya mi?a gaisuwa gurin Emir.

Ko kallo basu ishe shi ba, har saida Emir Ya mi?a masa hannu alamar Yazo gurinsa tukunna Ya nufesa ba tare da jin fargababa, da ya ke yaga kamanninsa da Gimbiya mujeedat kamar yayi kakin ta.

Ru?o hannunsa yayi a cikin nashi ya rungumosa Yana shafa bayansa..
Karo na farko daya fara ganin shi, duk da baisan wanene shi ba? Menene ala?arsa da Yarsa Mujeedat? Amma kamanceceniyarsa da surukinsa Hateem da jikarsa Nazli Ya sa ji aransa zaiyi wuya in ba yaron jikansa ba ne duk da yasan Mujeedat bata da Wa Namiji.

Bai ta6a jin tsantsar ?aunar bare farat Waya a kallo Waya makamancin yadda yaji akan Omair ba, Bashi ba Hatta fadawansa sun kamu da kaunarsa, Kyawunshi Ya ruWe su su da suke larabawa jinsin kyawawa, duk yadda suka kai ga Wokinsa da jan shi a jiki sai dai sun kasa yin magana da shi saboda Ya?i basu hadin kai, da Emir kaWai Ya yarda shima albarkacin mommynsa ya ci.

Daga Palace Emir Ya shiga da shi Cikin gidan, Zo kuga Yadda Royal Family mutane masu ?ima da daraja su Ke kallon Omair kamar zasu haWiyesa saboda ruWewar da su ka yi da kyansa da kuma kamanninsa da Nazli.

Kowa Saida Ya hallara Dangin su, tun daga kan Grandparents, parents, Uncles, aunts, elders, kowa da kowa, kyawawan labarawa wadanda suka gaji Sarauta da arzi?i na fitar shari'a..

Kowa Tambaya ya ke yi wanene kyakkyawan matashin saurayin nan? Wan wanene? daga Ina Ya ke? Wasu ma daga cikin su tambaya su ke yi mijin sheikha Mujeedat yana da wata matar ne da ta haifa masa Yaron ko kuwa Nephew dinsa ne (dan dan uwansa).

Emir ne ya fayyace masu abun daya sani game da Omair, Ya daura da cewa su yi hakuri zuwa lokacin da sheikha Mujeedat zata dawo daga Nigeria, zata fada musu wanene shi, amma Yanzu Yana so kowan nan su Ya ja shi ajiki, su bashi kulawa kamar yadda suke kula da sauran ya'yan sheikha Mujeedat saboda yana ji aranshi da akwai wani abu game da yaron tun da har take 6oyen shi a guest house din ta.!

kunsan larabawa da girman kai musamman ga bare amma dayake Omair ya kwanta musu arai sun ganshi da abubuwan ban al'ajabi atare da shi shiyasa su ka yi saurin amince ma shi.

Omair bai ta6a sanin Yana da babban Family na hamsha?an masu kuWi ba kuma kyawawan gaske sai da Ya tsinci kanshi a cikin ruler's resident na dubai, ashe shi din Wan dangine, Ya fito daga tsatson mashahuran larabawa.

Kowa Wokinsa Ya ke yi, amma Rashin sabo ya hana shi sakin jiki da su.

musamman Emir Ya ware masa katafaren Bedroom dinsa tare da Hadiman da zasu dinga yi ma sa hidima, in a short time Emir Ya siye zuciyar Omair, shine mutun na farko daya fara sakin jiki da shi, saboda kyautatawar da ya ke yi masa, Har takaiga dare kaWai ke raba su, ya zama kamar Wan Cikin sa, In zai shiga Palace a tare suke zuwa, su ci abinci atare da shi da iyalansa su fita yawon sha?atawa, Hadiman Gidan sun sanya mashi ido sosai, kunsan ba'a raba hadimai da tsegumi burinsu kawai su ji wanene shi"?


Daga bisani Lokacin da Asirin kurkukun ?addara Ya Tonu duniya Taji, sa'ilin da labarin Ya ris?i Familyn Mujeedat, sun razana sun kuma shiga tashin hankali da jin wanene surukin su Obinna, Ransu ya 6aci matu?a, Baba Obie Ya Karya musu Zuciya, Ya ci amanar yardar da su ka yi ma shi, sun kuma fusata sosai, sai da su ka yi dana sanin ?ulla ala?a da shi saboda basu son abun da zai ta6a mutuncin su duk min ?an?antar shi, suna girmama mutuncin su fiye da komai.


dama tunfil azal basu so sheikha ta auri bare ba kuma ba?ar fata Wan Nigeria saboda su a ?a'ida basu fiye auran bare wanda ba jinsin su ba, abaya lokacin da Mujeedat tazo da Hateem amatsayin wanda takeso ba karamin rikici akayi a family din ba, duk da matsayinsa da arzi?insa Yasha wahala kafin su bashi auranta, saboda ta rantse ta maya bata da miji a duniyar nan daya wuce Hateem, mahaifinta ne mutun na farko daya fara goyon bayan ta auri za6inta saboda tsantsar son da yake mata fiye da sauran ya'yansa ita kaWai ce mace kuma autar sa, mahaifiyarta ma ta goyi bayanta, daga bayane kuma bayan sunyi aure Dangin nata suka Fara son Hateem saboda yadda Al'umma su ke yabon kyawawan halayansa.


saboda fallasuwar asirin Obie Har Family meeting su ka yi game da Yanke ala?arsu da surukinsu, Mafi rinjayen su wadanda su ka fi fusata, sun goyi bayan a kira Hateem Ya saki sheikha Mujeedat, KaWanne basu goyi bayan yin hakan ba, daga ciki hada Mahaifinta da kawunta da kuma yayanta sun ce sai dai A kira Mujeedat tazo Nigeria suji ra'ayinta in har ta nuna tana son taci gaba da zama da mijinta babu abun da zaisa su raba su.

Haka wasu daga cikin fadawan Emir Khalid sun shawarce shi da ya yanke ala?arsa da obinna saboda gudun surutun mutane amma Ya tsawatar ma kowa akan shi bazai Raba Mujeedat da mijinta ba, In har ba itace ta nuna tana son rabuwa da shi ba


Komai da ke faruwa a family dinsu gimbiya Mujeedat bata sani ba, Ta kashe wayarta saboda rashin kwanciyar hankali da damuwa.

Daga baya ne Emir Ya tuntubi Prime minister awaya, Ya umarce shi dayazo Yana son ganinsa, Idan masu karatu ba su mantaba akwai wani kira da Emir yayiwa Hateem Har yaji shakkar zuwa saboda zullumin kada Su raba shi da matar shi, to abun daya faru bayan ya amsa kiran, suka yi tafiyar sirri zuwa dubai tare da Iyalinsa.

Bayan sun isa Airport Royal Guards suka zo Daukarsu a motoci, kaitsaye suka garzaya da su zuwa Ruler's resident, a lokacin Hateem Bashi da nutsuwa, zullumi da fargaba sun cika zuciyarshi Ya damu da fargaban meyasa Surukinsa ke nemansa? yasan Sun riga da sun ji komai a news, kuma yana da tabbatacin kiran da ya yi masa yana da ala?a da Abun da ke faruwa a family din su..

~______________________________~


Kwata kwata Hateem baisan Danish Yana a tare da dangin mujeedat ba, saboda a lokacin baida kwanciyar hankalin da zai iya tunawa da shi, bai kuma san komai game da kasantuwar sa Wan shi ba.

Bayan da suka ?arasa hateem bai samu tarbar daya saba samu agurin wasu daga cikin danginta ba.

hakan ya ?ara haifar masa da matsananciyar damuwa, ta inda ya ji sanyi aransa Emir da Kawun mujeedat da Yayanta da ma wasu daga cikin su sunyi mashi kyakkyawar tarba, a bangaren Sheikha Mujeedat da ke a cikin gidan suka fara huce gajiyarsu, bayan hadimai sunyi masu hidimar kawo abinci daga bisani bayan sun huta sosai, sai ga kiran Emir ya shigo wayar Mujeedat bayan ta Waga yace su shigo ciki yana son ganin su.


Gaba Waya suka Wunguma izuwa Private Living room, A nan suka Iske Kowa na familyn sun hallara suna jiran su.



A lokacin ba Hateem kadai Ya shiga damuwa ba, hada Mujeedat da Su Nazli, saboda sun san mawuyacin abune su ?yale Hateem batare da sun raba ala?ar su ba.


Cikin zullumi da fargaba suka zazzauna suna fuskantar Emir khalid da sauran family members din.


Falon yayi shiru babu mai magana, Hateem Ya sadda Kan shi ?asa cike da jin kunyar hada idanu da su, gimbiya Mujeedat ce ke Wan tausarshi Tana matsa yatsun hannunsa dake a cikin nata duk dan ta kwantar masa da hankali.


Gyaran murya Emir yayi, Hankalin kowa Ya dawo kan shi, cikin nutsuwa ya ce sunji komai da mahaifinsa Ya aikata, basu ji dadi ba, Ya karya musu zuciya, ya kuma ja masu abun kunya a idon duniya, amma ba zasu ala?anta shi da laifin da mahaifinsa Ya aikata ba, hakika sun tausaya masu sun kuma jajanta musu, sai dai ya sani bazasu lamunci abin da zai taba martabar family din su ba..."

Lokacin da Hateem ke sauraronsa Hankalinsa Idan yayi dubu toh Ya tashi.

Emir Yana ?are maganarsa, Khal din Mujeedat Ya daura da cewa"don haka, yayi hakuri da hukuncin da zasu Yanke! Sakamakon Mafi rinjayen family dinsu sun fusata sun nuna rashin goyan bayan alakar sa da mujeedat..."

khal bai ?are maganar tasa ba, Mujeedat ta fashe da kuka Hankalinsu Ya tashi saboda sun daWe basu ga zubar hawayenta ba, Cikin karyayyar murya tace kada su rabata da Hateem! Bazata iya rayuwa batare da shi ba, tayayama zata iya barin shi a mawuyacin halin da ya ke a ciki? Dame zaiji? Su dubi girman Allah kodan darajar ya'yan dake a tsakaninta da Hateem kar su rabata da shi, zata iya rasa ranta su tausaya mashi!"

duk yadda Nazli takaiga izza saida ta sanya baki ita da Yazrin suka taya mommynsu rokon danginta akan kada su raba su da mahaifinsu, ba laifinsa bane, ko Allah baya kama mutun da laifin da bashi ya aikata ba, su tausaya masu! In kuma har suka raba mommynsu da daddynsu suma zasu yanke alaka da su, saboda bazasu taba rabuwa da daddyn su ba.

maganar Su Nazli ta Waga hankulan su, saboda suna son su kamar ran su amma still basu canza ra'ayin su ba..


Khalar Mujeedat tace ba zasu taba canza ra'ayin su ba, dole Sheikha ta za6a, ko dai Ta rabu da Hateem ta rayu da danginta, ko kuma taja ma kanta itama su Yanke alaka da ita.

Hateem baisan sa,adda hawayen bakin Ciki suka wanke fuskarsa ba, sam Ya kasa magana sai dai jinjina kansa da ya ke yi.

Da?yar ya iya buWe baki, cikin girmama yace baiga laifinsu ba, bai kuma ji zafin hukuncin da su ke so su Yanke mashi ba, mahaifin shi ne yaja ma shi! amma bai ta6a zaton jin hakan daga gare su ba, a matsayinsu na musulmai masu ilmin musulunci, sun san komai ya faru da shi mukaddarine daga Allah, bai kamata su juya mashi baya don mummunar kaddara ta same shi abun da ya faru da shi zai iya faruwa da kowa haka Allah ke jarabtar bawansa ta inda bai zata ba! amma kafin su fara yanke hukuncin raba shi da matar shi, yana neman alfarmar su akan su ba mujeedat za6i tun da tana da ?an ci, ta faWi ra'ayinta akan ala?arsu, saboda bazai ta6a sakin ta ba, kuma bazai rabu da ita ba, In har ba ita da kanta ta nemi ya sake ta ba, idan kuma su ka ce zasu tilasta masu, zai sanya lauyoyinsa a ciki.

lokacin da ya yi maganar zuciyarsa a wuya ta ke, yana jin zai iya komai akan Mujeedat..

Gaba Waya sun kunna masu wuta babu wani sassauci so su ke kawai su raba su.

A Lokacin da Hateem Ya sare da rokonsu akan su janye maganar raba su, Cikin fushi da 6acin rai ya mi?e cike da rashin kuzari Ya juya da niyar yabar falon harya fara tafiya, Unexpected Ya tsinkayi Muryar mutum a kunnanshi Yana kiran shi da sunan daddy minister...

A sukwane ya dakata da yin tafiyar, Ya kasa motsawa, cikin ruWu ?wa?walwarsa ke kokarin tariyo masa muryar wanene Yaji a cikin kunnansa? Wanene me irin muryarsa? Wa kuma ya ke kira..."?

Bai ?arashe zancen zucin nashi ba Ya kuma tsinkayar muryarsa a karo na biyu yace"daddy minister, it's me Danish.. "

Gabansa ne Ya faWi a ruWe Ya juya ya fuskanci inda Yake jin muryarsa kaitsaye idanunsa suka sauka akan Danish dake a tsaye sanye cikin shigar larabawa, kasa yarda yayi da abun da idanunsa ke nuna masa, ganinsa ya ke kamar a mafarki, Ya soma murza idanunsa da yatsunsa don ya tabbatarwa kansa daidai yake gani.


Nazli da Yazin Tun fitowarsa suka hango shi, A rude suka mi?e tsaye kan kafafunsu suna bin shi da kallo mai cike da al'ajabi, ganin matashin saurayin da suka ta6a gani a farewall dinner din daddynsu, ba zasu taba mantawa da fuskarsa ba, musamman Nazli, cos a farko data fara ganinsa Taji kishi sosai saboda arayuwarta batason mutum me kama da ita, batason ace wani nada wani abu irin nata, saboda tsabar izzar ta, a lokacin abun daya Waure masu kai tayaya akai Yaron da yake a Nigeria ya zo dubai? kuma har cikin gidan family din su? Tayaya hakan zai yiwu? Wama ya kawo sa? Menene alakarshi da su?

Sheikha mujeedat ce kaWai bata motsa daga inda take ba, saboda tasan komai game da zamansa a gidan su.

_Gaba Waya babu wanda yasan da zaman shi a falon, amma tun farkon da suka fara tattaunawa ya fito daga dakinsa da niyar ya tafi fadar Emir yana shigowa falon idanunsa suka hango mashi Mommynsa da Prime minister wani iko na Allah kallo Waya da yayi masa nan take ya tuna da komai daya manta, hakan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login