Showing 312001 words to 315000 words out of 321579 words

Chapter 105 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

hawa da sauka ba karamin jan hankalin shi su ka yi ba, bakomai ya ke tunawa ba face time din da babu albarkatu a kirjinta, kamar na namiji saboda shafewar su, bai ta6a tunanin wannan ranar zatazo ba, kamar zaiyi murmushi ya dan ta6e red lips dinta.

Fuskarta Yabi da kallo tana bacci kamar jinjira.

Ya gaza yarda Ya mallaki Unaisah, Yanzu tashi ce ita, matar shi, uwar ya'yanshi masu zuwa, ta zama a karkashin ikon shi, Nauyin komai nata na akan shi, Allah ne kadai Yasan farin cikin da ya ke ji.

a cikin zuciyarshi ya karanta addu'ar tashi daga bacci, A tsanake Yake sake bin eye lashes dinta da kallo, a hankali Ya Daura yatsunsa asaman sumar kanta Yana dan shafa mata ita kamar jinjira, kwata kwata bai lura da lokaci ba, saboda shagalar da yayi gurin kallonta.

Kamar ance Ya dubi agogo, arude Ya zare eyes dinsa ganin karfe goma na safe, Bacci Ya shagalar da su har asuba ta wuce ba su yi Ibada ba.

Tunani ya somayi tayaya zai tayar da ita daga bacci batare daya takura mata ba! Badan sallah ba da ba abun da zaisa ya farkar da ita.

Saitin kunnanta ya kai labbansa cikin muryar raWa ya furta

"ya rouhi, Tashi muje muyi sallah, mun makara"


shiru bata farka ba.
Sau uku yanayi mata raWa kamar wanda zai tayar da jinjira.
Yasan ta da nauyin bacci wani lokaci,balle jiya data jigata.


Qira'ar Alqur'ani ya soma yi mata cikin nutsatstsiyar muryarsa, Unexpected cikin bacci ta tsinkayi ?ira'arsa mai dadin sauraro irin ta Larabawa.

Tana buWe idanunta kaitsaye suka shiga cikin nashi, ta ?ura mashi idanu tana kallon yadda ya ke motsa labbansa yana qira'a tayi mamaki sosai, jin surar da yake Karanta mata da kai batare daya duba al'qur'ani ba, Saida ya kai aya tukunna ya dakata yana lumshe idanun shi yace"barka da safiya ya malak albi, kin tashi lafiya" lumshe idanunta tayi tana jin ta awata duniyar nishaWi.

Saida ta fara karanta addu'ar tashi daga bacci duk yana kallon ta daga bisani tace

"My man In har zaka dinga tada ni daga bacci irin haka zanfi kowa more tashi daga bacci, zanji dadi idan ka zama mutun na farko da zan fara yin tozali da shi a duk lokacin dana farka daga bacci.

Murmushi yayi wanda bai wuci fatar labbansa ba.

"Mun makara bamuyi sallah ba"

da sauri ta dubi agogo, zare idanu tayi, tare da yin saurin mi?ewa, Batai aune ba, Taji Ya cuccu6eta ya sauko da ita daga kan gadon, A saman kafadarshi Ya sa6e ta, Babu alamun Yana jin nauyinta, Ji ya ke kamar ya Wauki jinjira, Toilet Ya shige da ita.

Bayan sunyi alwala, suka fito Coset room suka shige don su shirya kan su, jim kaWan suka fito cikin shigar larabawa hannunsu ruke cikin na juna suka nufi prayer room wanda komai na cikinsa na yin ibada ne.

Asaman wata dankareriyar prayer mat, suka tsaya tana gaba Yana abayanta, Shi yaja su sallar, dakyar ta samu nutsuwar daina kallon bayan shi ta maida natsuwarta kan sallar da suke..

A tsanake suka yi sallar, Bayan da suka kammala, suka zauna ya mika hannu Ya janyo prayer beads Biyu Ya mika mata daya ta kar6i, ya ru?e Waya a hannun sa, suka soma yin tasbihi, tsawon mintina, ganin yayi mata nisa yasa ta ja jiki ta dawo gefen shi don taji dadin kallon shi.

Tana jan Cazbaha tana satar kallon red lips dinsa, Dadi takeji Man dinta ya Musulunta Ya iya karatun al'qur'ani da komai ma,komai sabo yake zo mata a tare dashi tabbas wannan omair ne ba danish din da ba sauyin rayuwa ta ko ina,ransa ne ya bashi tana kallon shi, da zarar yayi kamar zai juyo sai tayi saurin sadda kanta kasa taci gaba da jan casbaha.

Murmushin gefen fuska ya saki, shi kanshi yasan dole Unaisah ta susuce akan shi.

Qur'ani ya buWe masu akan wooden qur'anic stand.

Muraja'a suka yi atare idan ta karanta aya sai ya karanta ayar gaba, Sura Uku suka karanta kafin Ya rufe al'qur'anin.

A lokacin da bata zata ba, Taji Ya janyo hannayenta a cikin nashi ya shiga murza ziraran yatsunta yana kallon zanan kunshin ta.

ta Wago da farare idanunta ta dube shi.

Yayin da ya saka idanunsa a cikin nata.

"Jiya bayan Waurin aurenmu, daddynki Ya kira ni gefe daya ya faWa mun wasu maganganu da suka karya zuciyata... " gabanta ne ya fadi aruWe take duban shi.

Numfasawa yadanyi before ya daura da cewa"ya yarda dani dari bisa dari, kuma yasan cewa babu namijin da zai iya sarrafaki bayan shi sai kuma Ni saboda ya shaida tsantsar son da kike min, Ya bani amanarki, rukon ki ya dawo gurina, da dukkan dawainiyarki, ya bani ke badan ya gaji dake ba, sai don yana son kema ki raya sunnar Manzon Allah SAW kamar Yarda kowani uba nagari yake fatan yayanshi sukasance sunyi koyi da wannan sunna, ya kuma rokeni akan na kula masa dake kamar yadda ya kula dake tun kina jinjira har ya labarta min zaman da kukayi ya kara da cewa yasan wani lokaci baki jin magana kina da saurin fushi amma inyi hakuri da ke, idan kikai min badaidai ba, kada in ?waurace maki, in zaunar dake inyi maki nasiha, zaki gyara, saboda ni kadaine kusa dake, ayanzu zanfisu sanin me kike a ciki, idan na juya maki baya zaki kuntata, kuma bai yarda son da muke wa juna ya rufe mana ido mu kasa ganin laifin junan mu ba, mu ji tsoron Allah mu tafiyar da rayuwar aurenmu bisa tafarkin addininmu, mu kuma yi koyi da rayuwar manzon Allah da matayensa, lokacin daya ke fada min maganganun nan abun dayafi karya min zuciyata, dayace yasan bazai hana ki fuskanci jarabawar rayuwar aure ba da kowace mace take fuskanta agidan ta, amma koda nan gaba naji kin fita araina kada in tsangwameki, In dawo mashi da ke bazai taba gajiya da yar sa ba kuma bazai ji haushi na ba, Unaisah yana magana hada kwalla ya zubar min wai ni... " ya faWa tamkar zai fashe da kuka saboda abun ya ta6a zuciyar shi.

tunkan ya karashe labarta ma, Idanunta suka cuccuko tab da ?walla, a hankali zafafan hawaye suka soma gangarowa saman kuncin ta, ta ?arajin kaunar daddynta da tausayin shi yana sonta fiye da komai na duniyar nan tun tana kankanuwarta ta??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ke azabtar da shi daidai da rana daya bawan Allahn nan bai ta6a tsanarta ba, hasalima sai dai Yaja ta a jiki in ta yi badaidai ba..

Batasan sa'adda ta fashe mashi da kuka ba kamar jinjira, da sauri Ya janyota jikin shi Ya rungumeta a kirjinshi, Ya daura hannayensa bayanta Yana lallashin ta dakyar ya samu ta dakata tana shessheka.

"Ni ban fada maki don na sanya ki kuka ba, sai dan Inaso ki taimaka min Unaisah ki bani hadin kai, mu zauna lafiya da juna, inajin tsoron na gaza ruke amanarki yadda ya kamata, amma nasan son da nake maki bazai bari ni in cutar da ke ba ko da ni zan cutu, a shirye nake dana baki dukkan kulawata da soyayyata, da lokacina"!


Ya Wan dakata da yin maganar kafin ya daura da cewa..


"jiya bayan daurin aurenmu naji dadin da bazan iya misalta shi ba, saboda farin cikin kin zama tawa, zaki rayu agidana a karkashin ikona da kulawata, gaba daya dawainiyarki ta dawo kaina, komai ni zanyi maki Unaisah, Ina da halin da zan tafiyar da rayuwarmu harma data ya'yan mu batare dana gaza ba.. " yayin da ta ke sauraron daWaWan kalamansa wani sanyi da daWi ne ke ratsa zuciyarta..

"Nasan dole wata rana mu samu sa6ani a rayuwar auran mu, amma in har muka yarda da junanmu, muka zama masu hakuri da juriya, mu ka kuma ru?e addu'a, batare da sonkai ko son zuciya ba, In sha Allah zamu zauna lafiya, Aure yana bukatar fahimtar juna da soyayya, uwa uba hakuri shine jigon zaman aure gaba daya ma, kuma ni nayi imanin akwai fahimta a tsakanin mu... "

ya faWa yana duban fuskarta, kanta na akan kafadardarsa bata motsa ba, hawayen dake tsiyayowa ta cikin idanunta ya bi da kallon ji yayi bazai juri kallon su ba, tana kokarin buWe idanunta Batai auneba taji ya sanya red tongue dinsa akan fuskarta a hankali ya shiga lashe hawayen ta.


A lokaci Waya ta dinga jin wutar kaunar shi na ruruwa a cikin zuciyarta, fiye dana kowani lokaci.

?aura idanunsa yayi acikin nata suka ?urawa juna ido kamar yau ne rana ta farko da suka fara ganin juna, tun fil azal Allah ya jarabce su da kaunar juna, yadda kasan tushen soyayyar su a jikin ransu take saboda yadda su ke mutuwar son kansu.

sunkuyar da kanta ?asa tayi cikin sanyin murya ta soma magana yayi shiru yana sauraron ta.

"In sha Allah zanyi iya kokarina gurin taimaka maka na ganin ka sauke nauyin dake akanka, zan dage da tayamu addu'a Allah ya tayaka ru?ona My man, Nima ka tayani da addu'a Allah Ya bani ikon sauke hakkinka da ke akaina, Allah ya bani ikon yi maka biyayya sau da kafa... "

har cikin ranshi yaji dadin maganarta, a hankali yake amsawa da ameen yana kallon lips din ta still kanta na kallon kasa.

"Allah ya bamu hakuri da juriyar da zamu rayu cikin farin cike da jin dadi batare da mun samu sa6ani ba, kuma koda zamu samu sa6anin in dai mun kasance munayi wa juna addu'a in sha Allahu shaidan ko zuciya ba zasu rinjaye mu ba balle wani, sai dai mu mu rinjaye su,sai kaga cikin kankanin lokaci mun shirya kanmu..."

dakatawa ta danyi tana kallon Yatsunsu dake harWe cikin na juna..

"My man, ji nake kamar nafi kowace mace a duniya, bazan iya godewa ni'imar da Allah yayi min ba, daya za6eni cikin matayen duniya ya mallaka min kai a matsayin mijina, kai din burin kowace ya mace ne, son kowa kin wadda ta rasa, namiji mai tsada da wuyar samu afadin duniya, Allah ya kar6i koken da nake masa Ya dawo min dakai, Tun da na mallake ka ji nake babu abun daya rage ban mallaka aduniya ba, Allah ya gama min komai atanan saura fatan cikawa da kyau da imani..."

baisan sa'a murmushi ya subuce masa ba Yabon Unaisah agaresa kamar an masa albishir da gidan Aljanna ne.

"Ina matu?ar alfahari da ke! Nima bazan iya godewa ni'imar da yayi minba Daya mallakamin mace mai tsada mai wuyar samu a duniyar nan ni daya ya zabeni ciki mazan duniya, Kinfiye min komai Unaisah, in babu ke babu ni, kece ni Unaisah, Inason ki, Ina son mu rayu har karshen nunfashinmu..



daWaWan kalamai suke ta gayawa junan su.


Daga bisani Suka Waga hannayen su sama suna yiwa kan su addu'oi cikin harshen larabci.

Atakaice Cikin kwanakin nan sha?uwa mai karfi da zazzafar soyayyace a tsakanin ma'auratan nan, zan iya cewa ban ta6a ganin masoyan da suke masifar son juna da zuciya Waya irin su ba, tsantsar kulawa suke bawa junansu, tattalin juna sukeyi da tarairaya, sallah kadai ke fitar da shi daga gidansa kasantuwar bai fara zuwa Office ba,dayake a nan Nigeria ya zabi zaiyi aiki, hutunsa Yake sha agidansa tare da hurul aininsa, Basa gajiya da faranta ran junansu, kullum suna a manne da juna, Wanka atare suke yin shi, sanya sutura a tare, Cin abincin a tare, bacci a rungume da juna, su yi gym a tare, su yi karatun al'qur'ani a tare, ranar da zata fara yin girki a tare su ka yi shi, Musamman saboda ita Ya ko yi girki agurin mommynsa, shi ya ke zama Ya gyara mata sumar kanta idan Ya hargitsa mata ita gurin kwanciya, idan ya gama itama ta gyara mashi tashi sumar, a tare suke zagaye bangarorin sha?atawar dake a cikin gidan, duk idan zasuyi fira saita tambaye shi ya bata labarin rayuwarsa agidan iyayensa baya gajiya da labarta mata, dadi takeji idan yana faWa mata irin rayuwar da yayi tare da iyayensa da yayyansa, itama takan bashi labarin rayuwar da tayi bayan babu shi, abu mafi kayatarwa a tare da su yadda suke kokarin sauke hakkin junan su.

Duk in ya rigata tashi daga bacci da karatun alqur'ani ya ke farkar da ita, sometimes da kissing yake tashin ta har saita farka, saboda dadin da takeji Yasa itama ta dinga tashin shi ta yadda shima ya ke tashin ta cikin salon soyayya..

rayuwar farin ciki da jin daWi su ke yi, sun sangarta junan su, gatanta kansu su ke yi kamar ran su, One week sun kulle kansu a cikin kurkukun masoya ba shige ba fuce, abun da ba zata ta6a mantawa da shi ba arayuwar arayuwarsu shine daren daya kar6i budurcin ta, da kuma kyautar bazatan da yayi mata a washe garin ranar, saboda yaji dadin faranta masa rai da ta yi ne yasa ya bata kyautar Black card with A brand new Mercedes-Benz S-Class and A brand new BMW X5, ita kadai, Aranar kukan farin ciki ta dinga yi masa, sai da takai ga shi ya koma yana lallashin ta.



Tun ranar da Taj Ya hana Benazir zuwa gidan Unaisah lokacin da ta kira su a daren auren ta, Ya fayyace mata komai game da wanda Unaisah ta aura, tsantsar al'ajabi ya kamata, tayi murna Har kukan farin ciki sai da tayi saboda murnar Unaisah ta auri za6inta, mutumin da take ta hauka akanshi ya rayu, da tana ta jin fargaban Kada Owais Yaga zanan tattoo dinta amma da taji cewar mamallakin sunan ne ta aura sai taji hankalinta ya kwanta bata da sauran damuwa.



A bangaren Batool, Sai da ya rage saura Kwana biyu dinner din auran su, aranar abi dinta da mommynta suka kirata a falo suka zauna tare da fayyace mata game da bayyanar dan uwansu Danish da kuma auran shi da Unaisah harma da Auranta da aka daura tare da Owais, Tsabar rudani da al'ajabine yasa ta kasa furta kalma, ta razana da jin Danish yana araye tsawon lokacin nan yana tare da Iyayen sa, kuma ta ruWe da jin cewa Yaya Owais mijinta ne, farin ciki biyu a lokaci Waya, jin abun tayi kamar a mafarki wai ta zama matar dg Owais, nan Ta ke ta fashe da kukan farin ciki, ta dur?ushe kan floor ta yi sujudusshukur.

Sam bakinta kasa rufuwa yayi saboda zunzurutun farin cikin daya cika zuciyarta, kamar wadda akayima albishir da gidan Aljanna, Ummi da Shureim sun ji dadi da ganin yadda ta nuna farin cikin ta, dama burinsu ne su faranta mata rai, sai da takaiga su ne suka dinga lallashinta don tayi shiru ta daina kukan, Ummi ta soma zolayarta da cewa yanzu sai hankali ya kwanta, tun da ta auri muradin ranta, qiyamul laili tayi aiki, yanzu sai ta daina kishi da yar uwarta, tun da bata aurar mata miji ba kowa da nasa.

ko da jin wannan maganar ta Umminta tana kuka ta zarce da dariya, suma suka kama yin dariya, sham ta shafa'a ta daka tsallan farin ciki, da taga sun saki baki sototo suna kallon ta da murmushi akan fuskokinsu saita watsa da gudu ta nufi bedroom dinta, tana shiga ta faWa kan gado cike da farin ciki take tariyo abin daya faru a tsakanin da chief, dama saida tayi mamakin nemanta da tayi saboda tasan shi din mutunne mai tsoran Allah ba zai iya aikata abin da zai sa6ama mahaliccinsa ba, yanzu tagane jarabata yayi saboda yasan matarsa ce ita, cikin sanyin murya ta furta Am sorry My husband duk da ko a lokacin banyi maka mummunan zato ba, bansan kana sona ba Ya Owais, meyasa ka boye mi ni, ka barni da ciwon sonka! ka hanani bacci ka hana zuciyana sukuni, amma tun da ka aure ni bani da sauran damuwa, naji dadi da Allah ya amsa addu'ar dana daWe inayi akan ka, In sha Allah zan zama mata tagari a gare ka, zan yi maka biyayya sau da ?afa... "



ita ka Wai ta dinga sambatu cikin nishaWi da annushuwa.


A yammacin ranar da ana saura kwana Waya ayi dinner..

Batool tana saman darduma ta kudundune kanta a cikin hijab Winta, daga sallame sallar La'asar bacci mai Wan karan daWi yayi awon gaba da ita,tun dazu take ta sharar bacci cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, sautin ringing din wayartane yayi silar farkawarta ba dan tagaji da baccin ba, mikewa tayi zaune tana mi?a da hamma cike da kasala ta tashi Tsaye ta dauko wayar idanunta biji biji take kallon screen Win ko da ganin sunan Heartbeat nan take ta wartsake, jikinta na 6ari tayi picking call din ta kara a kunne kamar tana agabasan, ta nutsu ta zauna daga gefen gadon ta..

"Assalamu alaikum, yaya Owais barka da marece, ya kake? Ina wuni? Ya Aunty Nazli"

On the Other hand taji ya furta"wa'alaikissalam my baby girl,Alhamdulillah, muna lafiya, ina fata kema haka"

"Eh," ta bashi amsa a takaice..

"Inason ganin ki, zanzo after magrib.. " zare idanu tayi cike da zumudi tace"toh, shikenan sai kazo" bayan ya katse kiran, ta mi?e tana rawar murna ta tube hijab din jikinta ta jefar kan gado,jallabiyane a jikinta da sauri ta shige toilet, mintuna ?alilan ta fito ta nufi dressing mirror, ta shafe jikinta da lotion din ta, saida ta gama shafe shafenta sannan ta dauko Atampa riga da skirt ta saka a jikinta tana gama sawa ana Kiran sallah magrib, hijab dinta ta mayar tare da kabbara sallah bayan ta gama taci gaba da shiryawa,tana cikin daura kallabi ya kira yace gayanan a waje ya iso da sauri ta qarasa daure kanta da dankwalin, gyalen ma a kafada ta yarfa shi, bayan ta saka high heels a kafarta, ta koma gaban mirror ta shafe jikinta da humra mai ?amshin gaske..

Cike da rawar jiki ta fito daga dakin, ganin babu kowa a falon yasa ta nufi bedroom din abie dinta don ta fada masu game da zuwan yaya Owais, har takusa isa ta dakata tunawa da basu nan, abi dinta tun da ya fita office bai dawo ba, Ummi kuma ta tafi gidan Aneelerh, kuma shi zai biya su dawo tare..

Tunawa da cewa mijintane Yazo ba wani ba, yasa ta yanke shawarar fita tasan ko su ba zasu hana ta je gurinsa ba, duk da hakan saida ta turama ummi sako ta waya..

DG OWAIS

Yana a zaune a driver seat na


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login