Showing 24001 words to 27000 words out of 321579 words

Chapter 9 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

ya fuce.

Shaf shaf ya rage kayan jikin shi Ya shiga bathroom don ya yi wanka.

Bayan wani Lokaci ya fito daga part dinsa ya dauki wankan blue sky voile, sai kamshi ke tashi a jikin shi, walking magestically ya nufo down.

tun kafin ya ?araso takun tafiyarsa yaja hankulansu ga duban shi, a lokacin sun dawo falo suna jiran shi.

A hanzarce suka mimmi?e tsaye, kaitsaye ya nufi Dr Shureim, side hug ya yi masa tare da ruko hannunsa sukayi musabaha, Dr shurem ya Wan yi mamakin saukin kan Chief yadda ya tarbe shi kamar sun saba da juna.

With respect Aneelerh da Benazir suka gaishe da shi tare da yi mashi sannu da dawowa, fuskarsa da fara'a ya amsa masu.

Gaba Waya Ya lura da yanayin fuskokin su kamar ba walwala akai.

Sarah mashi Taj ya yi daga zaunen da ya ke bai motsa ba ya yi mashi sannu da dawowa, mayar masa da martanin sarawar ya yi kafin ya amsa gaisuwar da ya yi masa tare da mi?a masa hannu suka gaisa da juna.

Daga bisani ya zauna gefen Taj, ya kasance suna fuskantar su Dr shureim..

"A yi mini afwa, na barku kunata jirana." ?an murmushi suka yi gaba dayansu.

Dr shureim ya ce, "bakomai wlh, Allah yasa dai bamu katse maka aiki ba"

Fuskarshi a sake ya Wan jinjina kan shi,

Tunkafin ya tambayi wani abu Taj ya yi hanzarin daukar wayar Ana dake ajiye gefensa ya kunna masa videon tare da mi?a masa ya sa hannu ya kar6a tare da daura idanunsa akan Screen din wayar ya nutsu yana kallon videon, bayan ya gama kallo shiru ya yi yana Wan jinjina kan shi.

Lamarin ya Waure mashi kai tamau, kuma tunanin su ya zo Waya dana Taj.

Gyaran murya ya yi masu a hankali suka mayar da dubansu gare shi.
Tambayoyi ya fara yi ma Anila dangane da Ana da kuma Uncle din ta, bata boye masa komai ba duk abunda ya tambaya sai ta bashi amsa.

Bayan Ya kammala yi mata tambayoyin, Taj ya ce, "Benazir, ki yi masa bayanin abun da ke damun ki" cikin sanyin murya ta amsa mashi da toh,

A tsanake ta kwashe komai da ya faru da ita a gidan Uncle musa ta sanar da Chief, ta ?ara da cewa, "Ban sanar ma kowa ba, Yaya Shureim ne kaWai ya sani, bayan haka yanzu an Waga ?afa da kawo min harin."

Yanayin fuskar Chief ya nuna tsantsar ruWani da al'ajabi, kallon Dr Shureim ya yi wanda gaba daya hankalin sa baya akan su, duba da yadda ya sadda kan shi ?asa.

"Za ki iya suffanta mini mutumin da ya kawo maki hari a cikin toilet?"

Ta amsa da eh, kafin ta fara siffanta mashi mutumin.

Kallon kallo suka jefawa juna tsakanin shi da Taj, lamarin ya daure masu kai, saboda gaba Waya yadda Benazir ta suffanta mutumin, baida bambanci da giant Win kurkukun ?addara, amma abun tambayar anan meyasa ake son kashe ta? Zurfin tunani Chief ya shiga har na tsawon yan mintuna, kafin ya Wago ya dubi Benazir suka haWa ido cikin na juna.

"A lokacin baya, kafin ?addara ta rabaki da gidan mijin ki, babu wanda ki ka ta6a yi ma laifi kuka samu sa6ani a tsakanin ku har ta kai ya ci wani alwashi a kan ki?"

Girgiza kai ta yi,"Gaskiya ni ba wanda wani abu ya taba haWa ni da shi..."

Bata ?are maganar ba, ganin irin kallon da Taj ya yi mata, nan take ta fahimci me yake nufi wato yasan halinta ciki da bai.

Gyaran murya ta dan yi, "A lokacin baya nasan bana jin magana, idan nace ban taba samun sabani da wani ba to na yi ?arya, amma bana tunanin na yi laifin da har za'ayi yun?urin kashe ni"

"Bakya tunanin wanda ya yi maki kurciya shine yake nema ya kashe ki saboda ya ga kin dawo a raye, may be akwai wani abu da ya haWa ku ko sanin sirrin wani wanda baya son asirin shi ya tonu ta silar bayyanar ki shiyasa yake nema ya halaka ki..."

Maganar Chief tasa ta jin faduwar gaba, zurfin tunani ta shiga yayin da ?wa?walwarta ke kokarin tariyo mata abubuwan da suka faru a lokacin baya kafin ta gudu daga gidanta, sai dai ta kasa tuna komai kamar an wanke mata brain dinta.

"Ki yi kokari ki tuna Benazir, ba ?aramin taimako zaiyi mana ba"

Taj ne ya yi mata maganar cikin kwantar da murya, har kallon shi saida tayi kamar wani abu bai shiga tsakaninsu ba, Chief yana lura da duk wani motsin su haWi da karantar yanayinsu ta fuskarsu.

Cikin kunnanta ta tsinkayi muryar Aneelerh dake yi mata magana cikin raWa, "Please ki tuna Benazir, ni nasan baza a rasa wadanda kuka taba samun sabani da su ba, ko ya ya ne ki yi tunani pls"

Wani abu da Chief ya lura da shi shine satar kallon Dr shureim da take yi, hakan yasa shi zargin akwai abun da ta sani, kuma tana so ta fada sai dai bata son Dr Shureim ya ji shiyasa take satar kallon shi a fakaice.

Fahimtar hakan yasa shi cewa, "Kada ki damu, zan baki lokaci, bayan kin koma gida kiyi kokari ki tuna in ya so sai ki kira Taj a waya ki sanar da shi"

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke fuskarta da Win murmushi ta ce, "In sha Allah idan na tuna zan kira in sanar da ku"

Shiru suka dan yi na wani lokaci.

"Meke damun shi ne?" Chief ne ya fada idanunsa akan fuskar Dr Shureim ?an hawayen da suka cika idanun shi sai kokarin sauka kan kuncinsa suke yi.

Taj ya ce, "Yawwa Sir, namanta ban fada maka ba...." A hankali Chief ya mayar da hankalinsa akan Taj, komai da ya faru bayan fitowar Ummi Ya sanar da shi, jinjina kai ya yi tare da kallon su Anila, "Zan iya sanin menene ala?ar ku da ita?"?

Har suna haWa baki gurin furta eh saboda suna son ya taimaka masu tunda agidanshi take da zama.

"Yaya Shureim," Benazir ce ta kira sunan shi, cike da damuwa ya Wago ya kalle ta, a kunne ta yi masa raWa, "Suna son sanin menene alakar mu da Aisha, zan iya faWa masu komai da ya faru? tun da ka ga agurinsu take da zama may be idan su ka ji su taimaka mana"

Ya Wan ji nauyin maganar, amma a halin yanzu baida za6i,

Cikin sanyin murya ya ce, "Idan kina ganin zasu sama mana mafita, ki fada masu komai,"

Ajiyar zuciya ta sauke, kafin ta maida dubanta akan Taj da Chief.

Nan ta fara basu labarin rayuwarsu, da alakar su da Aisha, da kaddarar data raba su da juna, bata 6oye masu komai ba, da yake ta iya bada labari ko mistake bata yi.

Lokacin data ?arasa basu labarin idanunta cike tab da ?walla, yayin da su kuma tsantsar mamaki da al'jabine ya kamasu, A sanin su da Ummi tantiriyar Karuwace da ta yi ?aurin suna a America, ashe kaddara ce ta canza mata rayuwa, sun ji tausayinta sosai, har ta kai ga sun yi shiru jimm suna Wan jinjina heads din su, shi dama Taj ya daWe yana yi mata kallon sani, sai yanzu da Benazir ta bada labarinsu, Ya tabbatar ma kansa Bintu Imam ce.


"Dan Allah ku taimaka mana, kada ku bari Aisha ta koma America, ku ruke mana ita har sai mun sansanta tsakaninta da mahaifinta da kuma mu, muna so ta koma kamar yadda take a da, sauyin da muka gani atare da ita ya tada mana hankali, wlh kallo Waya da nayi mata na fahimci ta canza rayuwarta"

Chief ne ya ce,"Na yi maku alkawari In sha Allah, Aisha ba zata koma America ba, zan cigaba da ruke ta anan har sai na cika maku burukan ku, saboda nima na damu da ita na tausayama rayuwarta sosai, na ji zafin abun da ya yi silar rabata da mahaifinta da kuma halin da ta jefa rayuwarta, wanda nayi imanin tsinuwar da mahaifinta ya yi mata ce ke bibiyarta, bayan haka Dr Shureim..."

Ya amsa mashi da na'am idanunsu acikin na juna.

"Kaima na tausaya maka sosai, labarinku ya ta6a zuciyata, kun bani tausayi, please ka cigaba da hakurin da ka saba yi, in sha Allah ni Chief na yi maka al?awarin Ummi won't leave this house until everything is settled"

Maganar Chief ta kwantar masa da hankalinsa, wani dadine ya ji ya lullu6e zuciyar shi, Anila Da Benazir basu san sa'adda suka saki murmushin jin dadi ba, har suna hada baki gurin yi mashi godiya.

"Ina fata mun gama magana, ko akwai sauran wani abu?" Cikin kulawa Chief Ya faWa yana duban su,

"Unaisah, ta ?i kula ni...." gaba daya ta fada mashi abunda ya faru tsakaninta da Unaisah, har cikin ranshi bai ji dadi ba, amma ya fahimci Unaisah, baiga laifinta ba, dole ne dama ta ?i accepting din ta saboda ta ?ullace ta aranta.

"Kada Ki damu, Ni zan yi mata bayanin da zata fahimta, In sha Allah"

Ita dai Anila tunaninta ya fara komawa gida fargabanta kada Junaid ya saki baki ya furta dodon da ya kashe Anah a gaban Uncle.

"Akwai gargadin da nake so na yi maku gaba dayanku, daga rana irin ta yau inaso ku dauki kanku a matsayin jami'an sirri, kada ku kuskura ku faWa ma wani damuwarku, sannan kada ku bari yanayin ku ya nuna! Duk wani abu da muka tattauna anan to mu binne shi anan!" Ya faWa yana nuna floor da index finger Winsa.

"Sirrinku a cikin zuciyarku, In zai yiwu ma, ku daina tunanin abun cos kuskure kaWan zai iya jefa rayuwar ku cikin hadari. Tun da har kun fada mana komai, from now on Case din yabar hannun ku, yanzu yana a hannunmu, kuma in sha Allah zamu cigaba da yin bincike akai"

Gaba Waya sun yi amanna da maganar shi, kuma sun daukar mashi al?awari zasu kiyaye.

"Yakamata mu tafi, na ga an kusa fara kiran Magrib" Aneelerh ce ta faWa tana duba wrist watch din hannunta.

Taj ya ce, "Zamu ru?e wayar Ana a hannun mu, har zuwa time da zamu kammala bincike. Mungode sosai, Allah ya maida ku gida Lafiya"

Atare suka hada baki gurin furta Ameen muna godiya muma da aka kar6e mu hannu bibbiyu tare da fatan nasara.

Dakyar Dr shureim ya mike fuskarsa sam ba walwala, ya so ace zai iya ganin Aisha kafin su tafi.

Da?yar ya iya furta,"Please zan iya samun phone number din Aisha?"

Taj ya ce, "Mi zai hana." ya Wauko wayarsa ya lalubo layin Ummi ya mika masa, yatsun hannunsa har kerma suke saboda zumudin ya kar6a, shaf shaf yayi copying dinta bayan ya gama ya mika ma Taj tare da yi mashi godiya.

Benazir dake kallon shi ta kasa gane me ya hana shi mikewa? A ganinta ko rakiya ne yakamata ya yi masu.

"Muje nayi maku rakiya" Chief ne ya fada tare da mikewa, ya ruko hannun Dr shureim a cikin nashi suka yi gaba, Aneelerh da Benazir suna a biye da bayan su.

Bin su da kallo ya yi har saida suka 6ace ma ganinsa, lumshe idanun shi yayi a hankali yake tariyo komai da ya faru tun farkon zuwan su Benazir.

Unexpectedly ya ji an sumbaci forehead dinsa, a firgice ya buWe idanun shi, har saida gaban shi ya fadi da ya yi tozali da Benazir ta sunkuyo da kanta saitin fuskarshi, nan da nan ya haWe rai,

"Baki tafi ba?"

"Taya zan tafi kana fushi dani" ?aure mata fuska ya yi.

"Pls abunda ya faru Wazu ka yafe mini, raina ne ya 6aci," Ta fada tana kashe mashi murya.

"Na ji, ya wuce."

"Yaushe zaka maida ni ne? Na gaji da jira." Wani kallo ya yi mata mai kama da harara ya ce, "Toh rasa kunya 6eran tanka, ke baki ji kunyar furta in maida ki ba? Hauka nake da zan dauki macen da take ru?e kwalar rigana kamar zata doke ni!"

Ya fada babu wasa akan fuskarsa.

Marairaice fuska ta yi kamar zata fashe da kuka ta ce, "Pls ay na baka hakuri, wlh na gane kuskure na, don Allah ka daina wahalar da ni mana, nafa san kana sona har yanzu." ta faWa tana yi mashi farfari da idanunta.

Hakan da tayi ba ?aramin sace zuciyar shi ta yi ba.

"Ka yi shiru bakace komai ba," Ta fada da yar shagwa6arta.

?agowa ya yi suka hada ido cikin na juna wani kallon so da kauna suke jefawa junan su, bakomai take tuna mashi ba face Unaisah.

"Wallahi wannan karon idan ka mayar dani, zan yi maka biyayya sau da ?afa, zan tarairayeka kamar jinjiri, yanzu fa na canza ba Benazir din da ka sani ada bace, ka ga yanzu na iya girki, na iya gyara gado, na iya wanki, wlh har wanka zan dinga yi maka...."

Duk yadda ya kai ga hana kanshi sakar mata fuska baisan sa'adda ya tuntsire da dariya ba, saboda kalamanta sun bashi dariya, kuma dagaske take fada masa babu wasa akan fuskarta.

"Oh, kina nufin yanzu kin gane an halicci hannayenki don ki girka ma ?ato abinci?" Ya fada tare da Wage mata gira, dariya ta saki har dimples dinta ya lotsa.

"Bama iya girki ba, komai zanyi masa." Tabe bakinsa ya dan yi.

"Yakamata ki tafi suna jiranki." ?an bubbuga kafafunta ta yi kan floor, "Taya zan tafi baka bani amsa na ba?"

"Zamu yi magana a waya" Ba don ta so ba tace, "ka yi mini al?awari?" Jinjina mata kai ya yi.

"Okay, ka rama min kiss da na yi maka." Zare idon shi ya Wan yi bata jira amsar shi ba ta manna mashi peck ta juya tana dariya ta nufi Kofa, bin bayanta ya yi da kallo har ta bace ma ganin shi.


________________________________________
'?


Around ?arfe tara na dare, Benazir ta fito daga bedroom dinsu, hannunta a ru?e da wayarta, har ta sanya kayan bacci a jikin ta, sai dai baccin ya ?auracewa idanunta, a hankali take tafiya yayin da zuciyarta ke ta azalzalarta akan ta kira Taj ta faWa masa abunda ta kasa sanar da su Wazu, sai dai tana matu?ar jin shakkar ta fitar da sirrin gani take kamar zai koma masa ne, amma in ta tuna halin da Aisha ta shiga, da irin u?ubar da Dr Shureim Ya sha akan yarinyar sai kawai ta ji ?wara ta fada kawai ko da hakan zai yi silar rasa rayuwarta ne, ta ma san ko bata fada ba, hakan bazai hana a cigaba da yun?urin kashe ta ba.

Tana ?o?arin juyawa ta koma Waki ta ji motsin shigowar mutun Falon, da sauri ta kai idanunta ga duban shi, Alhaji Musa ne ya shigo cikin takun nan nasa na izza yake tafiya fuskarsa ba annuri, ya zuba hannayensa cikin aljihun wandon shaddar Jikin shi, hakanan ta tsinci kanta da jin faduwar gaba, cikin sauri ta juya da sauri ta faWa bedroom din ta, kamar munafuka ta dinga le?en shi, waro ido ta yi ganin ya dan dakata da yin tafiyar, alamun ya ji ajikin shi ana kallon shi, jikinta na kerma ta datse kofar Wakin.

A hankali yake bin ko'ina da kallo, ganin ba abunda ya yi zata bane yasa shi gyaWa kai ya cigaba da tafiya Ya nufi part dinsa.

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tare da hadiyar yawu, tunani ta soma yi a ina yakamata tayi wayar cos bata so wani ya ji koda kalma Waya da zata furta ne.

?aura idanunta ta yi akan Zeenatu da ke a kwance kan bedmatress tayi nisa acikin baccin ta, Cikin tafiyar sanWa ta nufi gadon ta janyo duvet ta lullu6e mata jikinta gaba daya.

har ta nufi toilet zata shiga sai kuma ta fasa, tunawa da babu kyau yin magana acikin toilet.

Gaba daya kanta ya Waure, tsoro take ji, ga shi abun ya dameta so take kawai ta fallasa sirrin da ta daWe da shi a cikin zuciyarta, ba zata iya jira gobe ta yi ba.

Akan Mirror Chair ta zauna, ta fara danna wayar ta kira layin Taj ta kurawa screen din wayar idanunta tana jiran ya yi picking.


Lokacin da kiran ya shigo layin Taj, yana a kwance kan gadonsa har ya fara bacci kiran ya katse shi.

Kasantuwar ya aje wayar a kusa da kunnansa, ransa a Wan 6aci ya janyo wayar ko da ganin kiran Benazir cikin sauri ya daidaita nutsuwar shi.

Bayan yayi picking ya kara wayar a kunnansa.

Ko sallama bata yi mashi ba ta ce, "shine ko ka kira ka tambayi mun isa lafiya ko?"

Cikin disasshiyar muryarshi ta wanda bacci bai ishe shi ba yace, "I'm sorry Ummu Unaisah, wlh kuna araina, tun dazu nake ta zucci zuccin in kira ku.."

Da shagwa6a ta ce, "Hankalinka kwance ma bacci kake yi, Ni gani nan damuwar rashin ka a kusa dani ta hanani runtsawa sai faman tunanin ka nake yi" Har cikin ranshi ya ji dadin kalamanta, murmushi ya yi, "Waya fada maki ni ban damu dake ba? Nima kin tafi kin barni da tunanin ki, da zarar na rufe idanuna ke nake gani,"

Sautin dariyarta ne ya cika kunnan shi.

( Allah sarki tsohuwar Zuma=?? har wani ?ara kankame pillow yake yi a kirjin shi, da alama Benazir tayi winning heart din Taj.)


"Ina babynmu?"

"Tana a bedroom din su, may be ta yi bacci"


"Okay," shiru su ka dan yi jimm har saida ya furta, "Akwai wani abu da kike son fada mini ne?"


Cikin sauri ta ce, "Eh dama dazu akwai tambayar da ku ka yi mini ban samu na amsa maku ba, saboda Yaya Shureim yana a wurin bana so yaji..."

Cike da zumudi Taj ya ce,"Okay, Ina sauraron ki Ummu Unaisah"

Calmly Ta soma ba shi labari.

"Kafin dawowar mu Jos, A lokacin ina a gidan Uncle Musa, ban kai ga sanin komai da ya faru tsakanin Yaya Shureim da Aisha ba, na ta6a kama Uncle yana yin wata waya ta sirri, wuraren karfe Waya na dare ban runtsa ba, dama dabi'atace idan ina yin Chatting bana yin bacci da wuri, to adaren ranar na fito daga Wakina dake a cikin gidan sa, hannuna ruke da wayata ina tafiya ina yin chat da niyyar daukko ruwa, gaba daya na shagala har na sauko down batare dana ankara ba, Na shiga zagaye falon gidan kafin na nufi walkway din da zai sadani da backyard din gidan na tsaya, kwatsam kunnuwana suka soma jiyo mun muryar mutum yanayin waya ?asa kasa kamar baya son wani


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login