Showing 273001 words to 276000 words out of 321579 words

Chapter 92 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

DEMON AS YOU THINK, I'M NOT DEAD, I'M ALIVE, I'M YOUR DANISH! YOUR SHIELD, I KNOW IT WILL BE HARD FOR YOU TO BELIEVE ME"!*_


(UNAISAH NI BA FATALWA BA NE! BA KUMA ALJANI BANE KAMAR YADDA KIKA ZATA, NI BAN MUTU BA, INA ARAYE, NI NE DANISH DINKI! GARKUWAR KI, NASAN ZAI YI WUYA KI YARDA DANI..... " )


bai kai ?arshen maganar tashi ba ganin yadda ta fisge jikin ta daga nashi, ta sanya runannun idanunta a cikin kyawawan idanun shi farare tass kamar an Wiga zaiba, Reddish iris dinsa Ya ciza launinsa kyau iya kyau, cikin ruWu da razana ta ke girgiza kanta, yayin da hawaye ke cigaba da yin sintiri kan kuncin ta..

La66anta na kerma tace"Ba zai ta6a yiwuwa ba, sai dai idan mafarki na ke yi, amma wanda ya mutu baya dawowa, ka riga da ka mutu, fatalwarka ce"


tana ?arashe maganar, tabi ta gefen shi da gudun ceton rai ta nufi door room din tana ?arasawa gaban ?ofar Unfortunately tayi locking kanta..

Bugun ?ofar ta din ga yi tana ture ta da dukkan ?arfinta kamar zata 6alle ta, cikin shesshe?ar murya take ambaton


"Mommy! Daddy!! Hubby !! Aunty Danejo!! Batool ... " don su kawo mata Wau?i Dan ba karamar firgita tayi ba.

Duk yana atsaye yana kallon ta, phone dinsa data jefar kan floor ya dauko, Walking slowly ya nufi ?ofar, kwata kwata bata ji motsin tafowarsa sa ba, har ya ?araso daga bayanta ya tsaya tare da yi mata rumfa da faffaWan ?irjinsa hannayenta da take bugun ?ofar da su Ya ru?o a cikin nashi Ya manna su jikin ?ofar, gaba Waya ya kashe mata sauran kuzarin daya rage a jikin ta ya haifar mata da jin matsananciyar kasala, tuni ta nemi shesshekar kukan da takeyi ta rasa wata nutsuwa ta soma ratsa ta..


sosai yayi tighting dinta ta yadda zai samu damar fahimtar da ita, da ya ke yasan halin kayansa da wuyar sha'ani ga kafiya.


"Ki bani dama In yi maki bayanin da zaki fahimta! Ko da ba zaki yarda da ni ba... " kasa buWe baki tayi don tayi magana..

Hakan Ya bashi karfin gwiwar cigaba dayin maganarsa..

"Ba ki shaida mutuwa na ba Unaisah! Baki ga gawata ba ido da ido! tayaya ba zaki yarda cewa ni ne ban mutu ba"?


Da?yar ta iya furta"saboda Danish ba zai iya rayuwa batare dani ba, in har yana araye bazai iya rayuwa nesa dani ba, ko inda babu ni, amma Yau kusan shekaru da mutuwarsa, tayaya zan yarda cewa yana araye"?



Kwata kwata bata iya ganinsa cos Ya manne jikinta da glass din ?ofar, amma shi yana iya hangen fuskarta, wallah shi kadai yasan me ya ke ji, almost years rabonsa da muradin ransa..


Bata ?are maganar ba Ya katse ta"ki faWa min me zanyi maki wanda zaisa ki yarda da magana ta?

"Babu, abunda zaka faWamin In yarda, Kawai kabarni in tafi, ko ka 6ace ka koma ?abarin ka, in ba haka ba daddyna yana akan hanyar zuwa gidan nan, tare da sheikh imam malik zai zo, Zaiyi maka ru?iya ya ?onaka da ayar Allah..."

maganarta taso bashi dariya, tausasan la66anta Yabi da kallo sun ji?u da hawayen ta...

"Okay, bari na kira daddyn naki, may be Idan shi yayi maki bayani ki yarda.." faduwar gaba taji


A hankali Ya zame hannunsa daga kan nata, Ya zaro wayar daya saka a aljihu Ya daddannata

Unexpected taji Muryar Taj yana yin sallama ta cikin wayarsa..

"Nayi kokarin na fahimtar da Unaisah cewa nine ban mutu ba ta?i yarda dani..."

"Idan tana a kusa ka bata wayar"

Kara mata wayar ya yi a kunnanta..

Arude tace "wallahi Ba daddy na bane, Wan uwanka aljani ka kira don ka ruWani"

sautin dariyar Taj ce ta cika kunnanta, arude ta ke dan zazzare idanun ta akan glass din ?ofar..

"Unaisah, ki kwantar da hankalinki, ki nutsu ki saurareni! Daddyn ki ne, muna waya Wazu ta katse, ban samu damar da zan fayyace maki komai ba, bawan Allahn dake a tare dake Ba aljani bane, ba kuma fatalwarsa ba ce, Danish Winki ne ya dawo araye kuma a matsayin mijin ki... "


maganarsa ta kara rikirkita tunanin ta, kokarin fahimtarsa ta ke yi sai dai tarasa nutsuwar yin hakan..

Mayar da wayar yayi kan kunnansa"bansan ya zanyi da ita ba, ta?i ta saurareni"


Taj yace"ta ruWene amma ka yi kokarin fahimtar da ita ta yadda zata yarda..."

"Okay shukran... " sallama su kayi, ya mayar da dubansa kan Unaisah data haWa uban gumi kan fuskarta..

Kafin ya furta kalma ta katse masa hanzarin sa


_"Idan har dagaske kaine tayaya akai ka rayu bayan ka faWa cikin rijiya? A ina ka ke yin rayuwa tsawon shekaru batare da sanin mu ba? Kayi loosing memory Winka ne? ko kuwa doguwar suma ka yi ne"?_

"Zanyi maki bayani, mu koma mu zauna" make kafadarta tayi"ba zan matsa daga inda na ke ba! Har saika bani amsar tambayana"! Yadda tayi maganar ya tabbatar masa da cewa ta fara yarda shi Win ne.


~_______=?%?______???_______~


~_______=?%?______???_______~




*_FLASH BACK, WAIWAYE ADON TAFIYA, BARI MU KOMA BAYA MUJI LABARIN TAYAYA AKAI DANISH YA RAYU? TAYAYA GABRIELLAH TA KU6UTA DAGA CIKIN TAFKIN JINI? KUMA TAYAYA AKAI KHALA TA KU6UTA DAGA TARKON MUTUWAR DA ELDER YA ?ANA MATA?_*





"Ku fara kokarin ceto rayukan fursinonin dake a ciki kafin su ankara da shigowarku, Danish da Salsabeel kuyi masu jagora zuwa da?unan da fursinoni suke." suka amsa mata da toh.


Ta ?ara da cewa, "Duk yaran da kuka taimaka, ku kawosu nan, zan taimaka masu su fita daga kurkukun..." Bayan tafiyarsu zullumi da fargaba Ya cika Zuciyar Tsohuwa Khala, ta kasa tsaye ta kasa zaune saboda tsoron kada su kasa yin nasara akan Giant da Elders tasan muddin suka san dasa hannun ta, Na lahira sai ya fita Jin dadi, bayan tafiyar su da mintuna, Allah Allah take su fara kawo mata firsinonin da suka ku6utar donta taimaka masu su fita daga kurkukun kafin Elders su Ankara.



A lokacin da batai tsammani ba taji motsin mutane a kofar dakin ta, cikin sauri taje gaban kofar, da faduwar gaba ta tambayi su wanene"?

Daga waje tajiyo murya mutun

"Isod Soldiers ne, Chief ne ya umarce mu da mu kawo maki Fursinonin da muka ku6utar..."

ajiyar zuciya ta sauke, jikinta na kerma ta cire sakatar ?ofar, ta le?a kanta, Sojoji biyar ne tare da matasan Fursinonin da suka fara ku6utarwa dukansu jikinsu kerma ya ke yi bayin Allah..

"ku tsaya a bakin kofar dakina, Ni zan tafi da wadannan furnonin, Idan wasu sojojin sun sake ku6utar da wasu fursinonin ku ce masu su kawo su gurin da ku ka shigo kurkukun" amsa mata sukayi da toh, a hanzarce ta dubi fursinonin ku biyo ni"

Cikin sa'a suka karaso wurin a lokacin sauran sojojin da suka karaso suna ta durowa ta cikin tagogin ta ko'ina sune sun cika wurin.

suna ganin khala suka gane itace tsohuwar da danish ya fada musu zata basu hadin kai idan suka karaso..

"Kun gama shigowa Ko akwai wasu sojojin" ta tambaya tana dubansu, sukace sun gama shigowa sauran sojojin da suka rage awaje, matukan jiragensu ne dana motocin su..

Jinjina kai tayi tare da kallon Sojojin da suka rage a bakin tagogin rufin suna ta kokarin Waure igiyoyi masu gwa6i da tsawo jikin tagogin saboda idan zasu koma da su za su yi amfani gurin haurawa sama su fuce.

Hakan ba karamin dadi yayi mata ba, batare da bata lokaci ba, suna gama daure igiyoyin suka zuro da su kasa har kan ground floor din gurin tace ma fursinonin su kama igiyoyin su haura sama idan sun isa suyi rarrafe akwai kofar da zata 6ular da su, wani Soja yace mata daga sun fita zasu iske sauran sojojin da ke a waje, already sun shirya komai.

Bayin Allah sun kasa bin igiyoyin saboda basu iyaba, sai da sojojin suka taimaka masu gurin kwatanta masu yadda zasu bi igiyar, cikin ikon Allah sai gashi sun kama igiyoyin a hankali har suka haura sama, tun suna hawa daya bayan daya har suka koma suna hawa uku uku..

Suna kammala hayewa, sai ga wasu fursinonin gungu guda sojoji sun tafo da su, a gaggauce suka koya masu yadda za su bi igiyoyin.

Na karshe da sojoji suka kawo sune wadanda su Danish suka ku6utar a dakin FiWa, hada mata masu ciki, yawanci ba koshin lafiya gare su ba, dama da taimakon sihirin Danish suka mi?e akan kafafun su har suka iya tafiya, dakyar suke bin igiyar, wasu ma daga cikin masu juna biyun hada kukansu saboda radadin da suke ji, tsananin tausayinsu ya kama sojojin da khala, sai dai ba yadda zasu yi da su, a haka suka haura saman rufin gaba Wayan su, masu juna biyun sunfi shan ba?ar azaba, saboda kuntatar da cikin su yayi, suna nishi da haki ga yanar data cika rufin da kananun kwari masu harbi da suka addabesu da kyar da sidin goshi suka karasa bakin Kofar da sojoji ke gadin ta, sai da suka taimaka ma kowani prisoner gurin mikewa saboda sagewar da gwiwowin su sukayi yasa basu iya mikewa, kaitsaye sojojin suka dinga shigar da su cikin jiragensu da motocin su, nan ma saida suka koya masu yadda zasu shiga, saboda basu san komai ba, hasalima tsoron jiragen su ke yi da motocin, bayan sun shigar da su duka, matukan suka tada jiragen da motocin ba 6ata lokaci suka basu wuta, da gudun gaske kamar zasu tashi suka nufi hanyar barin dajin da su gudun kada akawo masu farmaki ta bayan fage, tun acikin motocin sojojin suka rarraba musu ruwan sha, masu rauni a cikinsu kuma suka fara basu taimakon gaggawa dama suna da emergency box din su mai dauke da kayan agaji saboda tsaro.


Idan muka koma cikin kurkukun bayan sojojin da ke kawo yaran sun tabbatarwa khala da sun kammala kwashe fursinonin da ke a ciki.

Hankalinta ba karamin tashi yayi ba, ganin bata ga yarinyar data kwallafa rai akan son ta taimake ta ba, arude tace ma sojojin su sake dubawa dakyau saboda ita tasan adadin fursinonin da suka rage a cikin kurkukun akwai wadanda babu"

sojojin suka ce"Danish da Salsabeel sun tabbatar masu da babu sauran fursinoni,"

da ta matsa lamba akan su sake dubawa suka ce mata akwai bakwainin da suka gani a wani daki cikin containers kuma ba zasu iya jigilar daukarsu ba, saboda suna a cikin hadari basu da isasshen lokaci.."

jikinta ne yayi sanyi lakwas taso duka acece su saidai bazai yiwu ba kamar yadda suka fada, cikin sanyin murya tace"akwai Allah, yana atare da su, shiyasan yadda zaiyi da rayuwarsu, duk da haka bayan bakwainin da kuka ce kun bari, akwai yarinya daya da babu a cikin fursinonin Ni banganta ba, kuma nasan ta, na ta6a taimakon ta, ni zanje na nemota da kaina"

tana faWa ta 6ace ma ganinsu, bata dira a ko'ina ba sai cikin Wakunan fursinoni ta dinga bi tana dubawa sako da lungu, batare data bari wani yaganta ba, sai dai ita tana ganin yadda Giant da sojoji suke faWa

Ko'ina ta duba ban da ground floor da Hall din da ake bada horon zama giant saboda tasan zuwanta zai iya haifar mata da matsala.

Damuwa ce ta cika zuciyarta, Hankalinta Ya tashi matuka, aranta ta furta"ina kika shiga Gabriella? Ga taimako kun samu, bana so damar nan ta wuce ki, Inaso na cika maki alkawarin dana daukar maki! Ko dai sun kashe ki ne"?


abun da take jima fargaba kada ace sun haWu da tsohuwa inno don tasan kuwa muddin suka hadu sai Ta cutar da ita, ba karamar wahala tsohuwa khala tasha ba gurin neman Gabriella, saida ta haWa uban gumi akan fuskar ta.



A karshe ta buga sandar hannunta a ?asa tayi shiri donta samu damar ganin abun daya faru da Gabriela bayan giants sun fito da ita daga dakin ta, sai dai kash bata ga komai ba a inda ta buga sandar sai dai taga kasan gurin yayi jajir kamar jini ya 6are..

Abun ka ga mai ilmin matsafa, zukunnawa tayi gaban gurin tayi dogon nazari akan ma'anar launin jan, nan take ta gano me hakan ke nufi.

6acewa tayi 6att daga gurin.

Lokacin da ta shigo ke6a66en wurin da tafkin jinin nan yake, bata iya ganin komai ba saboda idanunta basu cika gani ba idan babu wadataccen haske.

kware murya tayi da karfi ta shiga kwala mata kira Gabriel! Gabriel! Gabriel, Kina ina? Kina jin murya ta, ni ce khala! Idan kina jina kiyi min alamar da zan gane a ina kike"!

Saboda yadda take kware murya tana magana makoshin ta har zafi ya ke mata.

ranta ne ya bata ko bata anan ne? Watakil tayi kuskure a duban da tayi, juyawa tayi har ta daga kafa da niyar ta fuce Unexpected kunnuwanta suka soma jiyo mata sautin wani azababben nishi mai hade da gurnani daga ji koma wanene keyin nishin yana a cikin mawuyacin hali, kuma yana fama da karancin iska da zai sha?a.."

saboda tsabar zumudin taga wanene, ta juya tana lalube da sandarta harta cimma bakin tafkin.

batai aune ba taji safkar hannun mutun akan kafarta kamar laluban hanya ya ke yi.

cikin duhun nan ta dam?i hannun da iya karfinta na karshe ta janyo da ita aikuwa gaba daya suka kife ?asa, lokacin da khala ta mi?e tana laluba jikin mutumin data tsamo daga cikin jinin, Hankalinta ya tashi saboda ta gane Gabriella ce, taji tausayin halin da take a ciki, ganin yadda jini ya wanke jikinta, baka iya ganin komai nata, kuma tayi mamakin yadda har ta kai wannan lokacin a cikin tafkin jinin batare data suma kota mutu ba, ta jure ?arni da Woyin jinin data sha?a, ko magana bata iya yi sai nishi ta ke yi, kofofin hancin ta da bakin ta sai malalar da jini su ke yi.



Idan har ta ce zata tsaya ta bata taimakon gaggawa anan za'a iya riskarsu, hakan yasa batai wata wata ba, ta dafe bayan gabriella da ke a kwance ?asa, tayi masu sihiri suka 6ace daga gurin gaba Waya.


Basu dira a ko'ina ba, sai cikin dakin Khala, kamar an wurgo su daga sama, suka faWo kasa.


wannan jinin da su Chief owais suka gani malale a kasan dakin Khala, ba jinin kowa bane face jinin da Gabriellah ta amayar, da hannu khala ta dinga buga mata dunduna, ta dinga sakin aman jini har saida ta fitar da jinin da ta sha.


mi?ewa khala tayi da sauri ta nufi daya daga cikin tulunan dakinta mai dauke da ruwa mai sanyi, ta kinkimo tulun ruwan da hannunta daya, yayin da dayan hannun ke a ruke da sandarta, ta dawo gaban Gabriella ta ?warara mata ruwan a jikinta.

sai lokacin ta fara dawowa hayyacin ta, aje tulun kasa khala tayi, ta zukunna tare da kwalfar ruwa a tafin hannunta ta wanke mata fuskarta, ta kwafa mata bakin tulun abaki ta shiga kuskure bakin ta, duk wannan abun da khala tayi mata bata san wacece akanta ba, saida tasha ruwa sanyi ya ratsa makoshinta, tana dagowa da rinannun idanunta suka shiga cikin na khala, fashewa tayi da kuka tamkar ranta zai fita, cikin sauri khala ta rungumeta a kirjinta, ta shiga lallashinta, tasan ta da zuciya, cikin shesshekar kuka ta zayyana ma khala abun daya faru tsakanin ta da tsohuwa inno, tace mata tayi hakuri ta jure, ta manta da komai, yanzu ga taimako sun samu, sojoji sunzo har ma sun ku6utar da fursinonin kurkukun gaba daya, a lokacin wani ihun farin ciki ta saki, arude tace mata ina dan uwanta gabriel? Shima sun fita da shi"? Khala tace mata eh, sune ma na farko da aka tafi da su" ta faWa mata hakanne don ta samu ta shawo kanta tabi su su tafi.


Cikin sauri Khala ta nufi bookshelves din dakinta ta zaro kundi biyu Waya na tarihin kurkukun ?addara Wayan kuma littafin rijistar fursinoni ne ta rungumesu a hannunta ta nufi wata tsohuwar jakar fata dake makale jikin bango ta curota ta zazzage kayan cikinta, ta zura kundaddakin a ciki, Gabriella duk tana kallon ta bayan data gama ta mi?a mata Jakar tace ta ruke ta da kyau, suna da mahimmanci, Idan ta fita daga kurkukun ta bama sojojin, tace mata toh.

Batare da bata lokaci ba, Ta janyo hannunta, suka fito daga dakin, lokacin da suka karasa gaban sojojin dake tsaron tagogin rufin ta damka masu gabriela tace su tafi da ita, cike da tashin hankali tace ma khala tazo su tafi tare, khala tace a'a su fara tafiya zatazo daga baya, idan sojojin sun kammala ya?in zata biyo su, fashewa da kuka Gabriella tayi, ta sanya musu rigima akan bazata tafi ba in har khala ba zatazo su tafi atare ba, bata son ta tafi tabarta, gani take kamar zata mutu ne..

ganin zata 6ata musu lokaci yasa sojojin suka tasa ?eyarta, tana ji tana gani suka rabata da khala, har ta fara bin igiyar bata daina waiwayen Khala ba, tana atsaye tana kallonta, fuskarta dauke da murmushi tace karta damu, tayi mata alkawarin indai da rai da lafiya zata zo inda su ke, sannan idan ta hadu da dan uwanta Gabriel ta gaishe mata da shi.


itama tana kuka tace ta kula mata da kanta, duk runtsi duk wuya karta bari ta mutu, tana son ta.." bayan Gabriela ta dura ta rufin, ta rarrafa ita kadai tana kuka tabi hanyar da zata 6ular da ita...

Saida sojojin dake tsaron gurin su ka ce ma khala tabi ta su tafi tace masu a'a, bazata iya tafiya batare da ta ga karshen fadan ba, saboda akwai burin da take da shi, tana son taga nasarar su akan idanunta, in har ta tafi zullumi da fargaban a wani hali suke a ciki bazai bari ta zauna lafiya ba.."


badan sun so ba suka ?yale ta.


Idanun ta cike tab da kwalla, ta juya ta nufi hanyar komawa dakinta, zuciyarta a cike fal da kewar Gabriella, tana son yarinyar ta shaku da ita, tana son su sake haduwa sai dai tana ji aranta da wuya ta rayu, bayan irin 6arnar da tayiwa Elder bayan ta shiga dakin kasa zama tayi saboda zullumin awani hali su Danish suke a ciki..



Ta yi zurfi a tunaninta kwatsam tajiyo takun tafiyar mutun abayanta, juyowar da za tayi keda wuya idanunta suka sauka akan Elder Obinna daya faWo a fujajen jikinshi sai tsuma ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login