Showing 12001 words to 15000 words out of 321579 words

Chapter 5 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

zullumi da fargaban abunda zai biyo baya In sheikh Ya san Aisha tana da ciki, yasa Aunty Laura ta rame, kamar mai fama da zazzabi har saida sheikh Imam Ya lura da canjin da tayi, ko da ya tambayeta meke damunta sai tace mashi Ciwon aisha shine silar damuwarta, hakuri kawai yake ba.

Dubarace ta fado mata arai, ta sami Aisha da zancen su zubda Cikin kawai, Aisha tace bazata iya ba, bata son ta kuma aikata wani zunubin na kisan kai bayan wanda suka aikata, ita bazata iya kashe rai ba, laifin da shureim ya aikata mata bazai shafi abun dake a Cikin ta ba.

Aunty laura taita kokarin tunzurata don ta amince asamu arufawa kai asiri amma Aisha ta yi kunnan Uwar shegu da maganarta, ganin tasa kafiya yasa Aunty laura ta dinga zuba mata maganin zubar da ciki aboye take barbada mata shi cikin abinci ko cikin abun sha, sai dai wani Iko Na Allah tun da tasoma yunkurin 6arar mata da ciki Allah bai nufa ba, saima kara lafiya da ta ke yi.

Lokacin Da Cikin Yakai wata Biyar, Ya fara bayyana a jikinta, daga ka kalle ta zaka gane tana da ciki Amma sheikh Imam Ya kasa Yarda Ciki ne saima yace ture akai mata, Ajiyar Aljanu ce, haka ya dinga banka mata ruwan addu'o'i tana sha, In zataci abinci sai ya tofe shi da addu'a in zata kwanta bacci sai ya shigo har daki gaban gadonta yayi mata addu'a, Zuciyar Aisha ta karaya da ganin irin Yardar da mahaifinta yayi da ita, shiyasa ta kasa buWe baki ta furta mashi Ciki ne a jikin ta, sai dai in suna atare yanayi mata addu'a ko yana bata abinci abaki, tayi ta zubar da hawaye tana kallon shi, ya dinga lallashinta yana fadin mamana kiyi hakuri Allah yana tare da bayinsa masu Hakuri, ki jure ki cinye jarabawar nan, In sha Allah koma wanene yake nemanki da sharri kanshi zai koma, mutanene ba Allah aransu bakin ciki da hassada sunyi yawa azukatan mutane.

Wani sa'in in yanayi mata maganar sai ta dinga Yunkurin buWe baki don ta fada mashi gaskiya amma sai ta kasa, In Aunty laura na akusa taga tana kokarin fada masa sai tayi saurin janye hankalin shi da tunanin wani abun.

Saboda Lalurar Aisha Yasa Sheikh Imam Ya hana ta fita ko kofar falo bata le?awa, saboda baison wani yaga Aljiyar da aljanu sukayi mata a zargi ciki ne, duk wanda yazo nemanta gida sai dai suce mashi bata nan tayi Tafiya Sudan gidan Kawunta, babu wanda yasan Aisha tana agida har su Benazir.

Daliban Aisha na islamiya, Da abokananta malamai da duk wani mai sauraren wa'azinta sai da ya damu da rashin ganin Aisha, saboda Allah yayi ta da farin jinin mutane suna son Aisha.

A kwana a tashi ba wuya gurin Allah, Cikin Aisha Ya Cika wata tara Cuf, tashi dakyar zama dakyar haka ta ke fama, a daren wata ranar Juma'a ne nakuda ta kamata, Aunty Laura ta matsa akai ta Asibiti ganin yadda take shan wahala, amma Sheikh Imam Ya hana yace ciwonta bana asibiti bane, sai dai ya bata ruwan addu'a tasha, a lokacin Aunty Laura, har yunkurin fada mashi gaskiya tayi amma saboda tsoron Kada ya saketa Yasa taja baki tayi shiru, ta bar shi ya gani da idon shi.

A falo ya zauna yana jan cazbaha, Ya baro Aunty laura adakin Aisha.

Bayan wani Lokaci, Kukan Jariri Ya cika kunnen shi, Wani irin Bugu Zuciyar shi tayi tamkar zata fasa kirjin shi, Tsantsar tashin hankali da rudanine Ya bayyana akan fuskarshi, cikin sauri Ya mi?e Ya shiga dakin Aisha, dira kafarshi keda wuya ba zato ba tsammani idanun shi suka sauka akan Jinjirin da Aunty Laura ta ru?e a hannunta.

Lokaci daya yanayin fuskarshi ya sauya, A lokacin Ayshah tana a kudundune Cikin bargo Aunty laurace ta taimaka mata tayi wanka bayan ta kar6i haihuwarta.

Jikinshi na kakkarwa ya karasa shiga dakin a gaban Laura ya tsaya yana ?arewa Jinjirar kallo idanunshi azazzare.

Babyn Fara Sol da ita, Idanunta dara dara farare kamar an diga zaiba, ga wata yalwatacciyar sumar kai har gaban goshinta gashin ne a nannaWe, kallo daya zakai mata kagane Ba jinsin bakar fata bace.

A lokacin Jikin Aunty Laura kerma yake kamar mazari, Ga wani bugu da kirjinta keyi mata saboda tsoron Hukuncin da Shiekh Imam zai yanke mata.

Numfashi yaja tare da mi?a hannu Ya kar6i jinjirar daga Hannun Laura, Ya kura mata idanu Yana kallon ta.

Ya kasa yarda da abun da Zuciyarshi ke raya mashi, ya yi fatan ace mafarki ya ke yi ba gaskiya ba, wani kululun bakin cikine da takaici Ya tokare makoshin shi..

Muryarshi na rawa ya furta"Shegiya agidana? Gidan Alkali sheikh Imam? Sanannan malamin addinin islama! Me yi ma wasu fada da nasiha akan aikata Barna"? Yau agidana aka aikata barna? Ni sheikh? yata Aisha ce ta haifi Shegiya acikin gidana? Batare da Aure ba? inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..."

wani makokon bakin cikine ya mamaye zuciyarshi, hannayenshi na kerma Ya mika ma Laura yarinyar da sauri tasa hannu ta kar6a, jikinshi na kerma ya zauna Gefen gadon Aisha Cikin sanyin murya ta wanda ya karaya ya furta"mamana, tayaya kika samu Ciki? Wanene yayi maki aika aikar nan"?

Kunya da bakin cikine suka sa Aisha tagaza furta kalma, taki fitowa daga cikin bargon jikinta sai kerma ya ke yi.

Shurun da tayi ne ya bata masa rai, Ya doka mata tsawar data firgitar da su, Har Jaririyar saida ta fashe da kuka

Yana Huci Yace"Ba zaki bani amsar tambayar da nayi maki ba"?

Aunty laura tana kuka tace"Abien Aisha tsautsayine da kaddara..."

Bata kare maganar ba, Ya zabura ya mi?e ya nufe ta gadan gadan, batai aune ba Taji safkar maruka zafafa kan kuncinta, Har saida shatun hannayensa suka fito rudu rudu akan kuncin ta, gefen bakinta ya fashe jini ya fara WiWWiga.

"Allah Ya isa tsakanina dake Laura, Kin cuce ni kin cuci kanki kin kuma Cuci Aisha, sannan kin Cuci malama Batool! Kin ci amanata, nasan komai ya faru da Aisha kece Sila, kece kika ja komai, shashasha mara hankali"

Fashewa tayi da kuka Jinjirar hannunta sai kuka takeyi.

"Kunyi tunanin bansan komai bane? Duk abunda ke faru agidan nan an fada min, Kece Kika matsa ma Aisha kuka tafi partyn dana hanata zuwa, kina amfani da biyayyar da takeyi maki gurin Cutar da rayuwarta.."

Cikin shesshekar kuka tace"wallahi Allah shine shaidana, Ni ban ta6a Cutar da Aishaba, na ruke amanar da ka bani, Kai ka sani in ba ni ba wa kake tunanin zata kula maka da yarka kamar yadda na kula maka da ita"?

Bai kula ta ba, Ya koma ga Aisha Ya sanya Hannu Ya yaye bargon data lulluba da shi wata irin zabura tayi ta mike zaune jikinta na kerma ta dinga girgiza kai batare data iya furta kalma ba.

"Ki gaya min wani fasikin ne yayi maki ciki"?

Cikin rawar murya ta zayyana mashi komai daya faru.

"Dan Allah ka yafe min baba, Ba laifina bane, bayin kaina bane, Na rantse maka da wanda raina yake a hannunsa Bada son raina komai ya faru ba, dr shureim shine Ya yi min fyaWe, baba kayi hakuri kayi hakuri, nasan nakarya maka zuciya, Naji kunya baba, nayi abun kunya, har rokon Allah nayi ya dauki raina in huta saboda bakin cikin abunda yaya shureim yayi min..."

sambatu tadinyi yi mashi...
Bai san sa'adda hawaye suka cika idanun shi ba.

Cikin raunanniyar Murya yace"Aishana, meyasa lokacin dana hanaki fita partyn bakiji maganata ba? Meyasa? Har ni zansa maki doka ki karya saboda Wannan shashashar ta tursasa maki" ya fada yana nuna Aunty laura da yatsa.

"Aishana baki taba yi min gardama ba, ban taba hanaki abu kika ?iyi ba sai akan Paryn nan! Kika bijiremin, Ni dama saida raina ya bani wani abu zai iya faruwa shiyasa Na hanaki zuwa, da ace kinbi maganata da duk hakan bata faru ba, Kinga illar Kin bin Umarnin Iyaye ko"?

jinjina mashi kai ta yi Jikinta nata kerma.

"Aisha, Kinbiyewa Son zuciyarki, Kin cuce ni Kin Cuci kanki, Kin kuma Cuci mutanan da suka yarda da mu, sannan Kin zubarmin da mutucina kema kuma Kin zubar da naki mutunci, kinja mana abun kunyar da shiga cikin mutane zai gagaremu, Kin karya alkawarin da kikayi min na kare mun mutuncina da kimata a idon duniya, masuyi maki kallon mutuniyar kirki da zarar sunsan abun kunyar da kika aikata zasu fara yi maki kallon fasika mai fuska biyu, da Ina alfahari dake amma A yanzu babu wannan Aishana, Kin lalata komai, farin Cikin da kika sama min tun ranar haihuwarki a yau kin bata shi, Kin dasa min bakin cikin da har abada bazan ta6a warkewa daga radadin da naji ba, Aisha Ina da makiya wadanda suke son ganin bayana, Idan har sukaji abun kunyar da kika aikata zasuyi min dariya, kuma zasu yi amfani da hakan gurin ganin raunina..."

fashewa tayi da kuka tana fadin"baba kadaina fadin maganganun nan bana jin dadi baba, Kaifa malamine, kafi ni sani baba, Abunda ya faru dani Kaddara ce, wata irin addu'ar neman tsari ce bakai min ba? Nima haka inayi ma kaina amma hakan bai hana kaddara ta afkamin ba, saboda Allah ya riga daya kaddara faruwar hakan, babu wanda Allah baya jarabta baba, Annabawan Allah sun fuskanci jarabobin rayuwa basu taba gazawa ba, ya kamata kaima kayi koyi da su, baba wannan ne karo na farko daka fara fuskantar jarabawa mafi muni arayuwarka sau Waya tak yarka tayi ciki batare da aure ba, Dan Allah baba Mu dauki Hakan amatsayin Kaddararmu, muyi hakuri mu jure, baba Kafi jin kunyar duniya akan ta lahira? Mutane bazasu amfane mu da komai ba saboda basune zasuyi mana hisabi ba"!

Maganganun Aisha sun karya Zuciyarshi, har ya gaza yanke mata hukuncin da yayi niyar yi mata.

Mikewa yayi da sauri Ya fuce daga dakin, Yana fita Aunty laura ta mika mata Jinjirar dake ta kuka"ki bata nono Tasha yunwa take ji" Kar6ar jinjirar Aisha tayi, ta fara shayar da ita idanunta akan fuskar Jinjirar yayin da take tsotsar nono sai kallon fuskar mamanta takeyi, hawayen Aisha dake gangarowa ta cikin idanunta kaitsaye yake sauka saman fuskarta, tayi azan In ta haifi yarinyar zataji tsanar ta saboda bata sameta ta hanyar aure ba, amma sai ta ji tsantsar kaunar yarinyar fiye da komai na duniyar nan.

Aunty laura ta kara lallashin Aisha har saida ta kwantar mata da hankali.

"Aisha nayi danasani da nayita kokarin zubda maki Ciki saboda inajiye maki bakin mutane da kuma abunda zai biyo baya idan mahaifinki Yaji, wlh yanzu da kika tunasar damu sai naji jikina yayi sanyi, da na kashe yarinyar nan da nayi danasani na har abada, baiwar Allah gata kyakkyawa kamanninta sak dana Ubanta, Allah ya raya mana ke bisa tafarkin addinin islam, Allah yasa ki gaji Kyawawan halayan Mamanki"

aisha na murmushi ta amsa mata da ameen.

"Bari naje na shirya maki Abinci nasan kina jin yunwa"

"Aunty Laura, Baki gaji ba? Naga kin raunata" murmushi tayi kada ki damu Aisha, duk raunin da zan ji bai kai wanda kika ji ba.

Ta fada tare da fucewa ta shiga kitchen da kanta Ta hada mata farfesu bayan ta gama ta kawo mata adaki.

A bangaren Sheikh Imam bayan daya Koma dakinsa safa da marwa ya cigaba dayi, Zuciyarshi cike fal da tunanin ta yadda zai bullowa lamarin saboda bayason asirin abun da ya faru da yarshi aisha ya tonu a idon duniya, yana jiye masu tsoron tozarcin da zasu fuskanta agurin mutane..

A bangaren Dr shureim tun bayan daya Koma Egypt gurin aminsa, Bai kara samun kwanciyar hankali ba, saboda damuwar abunda yayi ma Aisha, Sai da ya shafe sati daya cur bai runtsa ba, abinci sai anyi dakyar ake samu yaci, ya yi duhu ya rame saboda tunanin A wani hali aisha take aciki, ga wani irin azababben sonta daya kara nunkuwa acikin Zuciyar shi, har takaiga baya iya bacci batare da yayi mafarkinta ba, Sometimes sai yayi tunaninta ya ke samun nutsuwa a cikin zuciyar shi, kusan kwana yakeyi akan darduma yana istigfar tare dayi ma Aisha addu'ar Allah yaye mata damuwarta ya kawo mata sauki acikin rayuwarta, saboda yasan zunubin daya aikata mata bazai barta ta zauna lafiya ba, dole su fuskanci kalubale ita da Mahaifinta.


tun yana boye abunda ke damunshi har amminsu ta lura da rashin walwalar shi ta dinga tambayarshi meke damunshi yaki fada mata, ta kasa jurewa ta kira iyayen shi ta sanar da su halin da Dan su ke a ciki, da jin hakan Hajiya layla ta bashi Umarnin ya dawo Nigeria, saboda ammi tace ta rasa gane kanshi, baya bacci baya son cin abinci, wanka ma saita matsa mashi ya ke yi kamar karamin yaro.

Bayan ya dawo Nigeria, Iyayenshi suka tasa shi agaba da tambayar meke damunshi? ya?i ya sanar dasu, Ba irin lallashin da basuyi mashi ba amma duk abanza.

Saida Ya samu nutsuwa ya kira Benazir a dakinsa ta same shi ya tambayeta Ina Aisha? Tace mashi rabon ta da Aisha kusan wata tara da kwanaki, Aunty Laura tace masu ta tafi sudan gurin kawunta, Ko sun kira layinta basa samu kuma koda zata tafi ba ta yi masu sallama ba"

Hankalin shi ba karamin tashi yayi ba, Zuciyarshi ta karaya sosai.

Ana haka saiga kiran Sheikh Imam Ya shigo wayar shi, wata irin kunyace ta kama shi kamar bazai daga kiran ba sai kuma Ya daga, Ko sallamar shi sheikh Imam bai amsa ba Yace shureim Inason ganinka, Ka same ni agidana, Ya amsa mashi da toh.

Bai bata Lokaci ba, Ya shirya kanshi cikin shadda Ya nufi gidan Sheikh Imam A garden Ya taras da shi zaune kan kujera fuskarshi babu walwala kamar bai taba dariya ba, tuni Shureim Yasha Jinin jikin shi.

Bayan daya zauna kan kujerar dake fuskantar sheikh Imam Malik Ya yi shiru Yana sauraron shi..

Kallo Waya sheikh Imam yayi mashi Ya lura da irin ramar da yayi daga gani yana acikin damuwa.

"Akwai wata rana, dana farka tsakar dare, na fito daga daki Ina zagaye Gidana, dama Ina yawan yin hakan sometimes bana iya bacci batare dana tofe ko'ina da addu'a ba, ina gab da zan gifta dakin aisha Najiyo shesshekar kukan ta, Kasan me naji tana fadi"? ya tambaya da tsantsar bacin rai Yana kallon fuskar Shureim daya gama rudewa, Girgiza kai yayi"aa baba'

"Addu'a takeyi Allah ya cika mata burinta na ganin ta auri yaron makwabtana data mutu akan kaunarsa batare da sanin shi ba.."

wata irin karaya Zuciyar dr shureim tayi.

"Nayi mamaki a wannan lokacin, saboda Aisha bata taba bude baki ta fadamin ga wanda takeso ba, amma a lokacin danaji tayi addu'ar nan ni kuma sai nayi alkawarin zan aura mata yaron nan da take so saboda in cika mata burin ta.."

zafafan hawayene suka wanke fuskar Dr shureim.

"Yarinyar da tayi dakon soyayyarka acikin zuciyarta na tsawon shekaru, ta hana idonta bacci don ta roki Allah ya mallaka mata kai ita ka wulakanta rayuwarta Shureim? Ya faWa rai abace.

"Inayi maka kallon mutumin kirki kamili, mai jin tsoron Allah, ashe na yaudari kaina! shureim ka sani ka take sani? Da yata ka aikata zina? Sannan baka taba waiwayonta ba, Ka haura kafa kabar kasar, Sai jiya na samu labarin ka dawo! Baka damu da halin da ka jefata ba shureim! Har yabonka nakeyi saboda na yaba da kyawawan halayenka amma ka tashi ka watsa min kasa a ido"

Fashewa da kuka dr shureim yayi kamar karamun yaro, shima sheikh Imam din hawaye ne ke zarya kan kuncinsa.

Cikin karyayyar murya mai tattare da danasani dr shureim Shureim Ya soma bashi hakuri Yace ya amsa laifinsa amma wlh baisan Ya akaita ba, Allah shine shaidarshi bai ta6a kusantar zina ba, bai ta6a sha'awar Ya kusanci Aisha batare da aure ba, Amma ya karbi laifinsa kuma Yana neman alfarmar ya bashi aurenta saboda su rufawa kansu asiri.

Sheikh Imam yace yaji amma yana so yaje gida Ya fada ma iyayensa abunda Ya aikata sannan Ya sanar da su zai auri Aisha, Duk abunda su ka ce Yazo ya sanar da shi, Jikinshi na 6ari ya mike har tambayar sheikh yai Aisha tana nan cikin gidan? Yace mashi eh, ya sake cewa zai iya ganinta? Imam Yace aa bai amince Yaganta ba, har sai bayan an daura auransu.

Bayan komawar Dr shureim gida ya kira Alhaji ubaid da Hajiya layla a falo Benazir ce kadai ke babu a cikinsu.

Bayan sun nutsu, Dr shureim Ya fayyace masu komai daya faru tsakanin shi da Aisha Sannan Yace Ya yanke shawarar zai aureta..

Tunkan Ya kare maganar Hajiya layla ta fara zazzaga masifa tana fadin wallahi bada yawunta ba, bai isa Ya bata masu suna agari ba, sai dayaga zabe ya kusa zai zo masu da wannan maganar mara dadin ji? Salon yaja masu zagi agurin Jama'a? ta inda take shiga bata nan take shiga ba.

Da farko Alhaji Ubaid yaso Ya fahimci dr shureim Har fada yayi masa akan abunda yayi ma Aisha, sannan yace ya amince masa zaije suyi maganar aurensu da sheikh Imam din, Shureim Yaji dadin maganar Mahaifinsa hajiya layla sai banbamin bala'i takeyi, Ita damuwarta ba akan abun kunyar da shureim yayi ma aisha bane, face Takarar da Alhaji ubaid Ya tsaya ga zabe ya kusa In har abokan adawarsu suka Ji abun nan zasu nemi bata masu sunane, a karshe su rasa kujerar da suke nema.


Bayan kwana daya da afkuwar Lamarin, Alhaji Ubaid Ya canza magana, ya kira shureim Ya fada masa yayi hakuri amma gaskiya bazai bari ya auri Aisha ba, saboda yayi bincike ya gano aisha ba mutuniyar kirki bace, dama can ta saba bin maza, har videos dinta na batsa wanda tayi tare da maza an tura masa awaya, sannan abun da ya faru tsakanin shi da ita ya yarda bayin kanshi bane, laifin Aishar ne itace shaidaniyar dataja Hankalin shi donta biya bukatar kanta.

Hankalin dr shureim ba karamin tashi yayi ba, ya dinga salati Yana karanto duk wata addu'a da zata sanyaya zuciyarshi, ranshi ya 6aci matuka da jin kazafin da mahaifinsa yayi ma Aisha, Yace wlh daddy karyane, wannan maganar ba gaskiya bace, kaji tsoron Allah, kaji tsoron ranar da zaka koma gare shi, Aisha ba fasika bace, mutuniyar kirkice ita, abunda aka fada maka akanta karyane, kai kasan wacece aisha tuntana karamarta kamilar macace mai kamun kai,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login