Showing 9001 words to 12000 words out of 321579 words

Chapter 4 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

fitarta daga dakin a jikin bango ta Jingina bayanta, fuskarta sharkaf da hawaye taji takaicin rungumar da Uncle musa yayi mata, kamar ta hadiyi zuciya ta mutu ta ke ji, Ya dasa mata kiyayyarsa a cikin zuciyarta.

Tana cikin tafiya wani irin ciwon mara Ya turnuke ta, da sauri ta dafe cikinta da tafin hannunta, sam takasa cigaba da tafiya a nan ta durkushe tana faman fitar da huci...

Adai dai lokacin dr shureim Ya hauro Upstairs din domin amsa kiran da Uncle Musa yayi ma shi, Yana ganinta Jikinshi na rawa ya karaso gurinta Yana tambayarta meke damunta? muryarta na rawa ta furta"cikina yaya shureim ciwo yake min, ka taimaka ka maida ni gida" ganin halin da take a ciki yasa shi ruko hannunta, ya taimaka mata ta mi?e suka sauko down, A lokacin babu kowa a falon gaba daya sun Koma garden can inda akeyin shagalin.
Har suka fito harabar gidan basu ci karo da kowa ba.

Sai nishi takeyi tana jan numfashi, dr shureim sai sannu yakeyi mata har suka karaso Cikin Gidan Imam, Ya tambayeta tana da maganin ciwon cikinne ko yaje ya siyo mata ne? Dakyar ta bude baki tace mashi bata da shi ya kare" Cikin sauri Dr shureim Ya fita Ya nufi chemist din dake a kusa da su don ya siyo mata maganin, tausayinta duk ya kama shi..

Lokacin daya dawo gidan hannun shi ruke da leda ta maganin daya siyo mata, a bakin kofar falo yai ta ?wala sallama shiru bata amsa mashi ba, Kuma Yan aikin gidan duk basa a kusa, wayar sa ya zaro ya danna mata call tana fara ringing, tayi picking yanayin yadda yaji Muryarta ba karamin Waga masa hankali tayi ba.

Cikin shesshekar kuka take fadin"ya shureim mutuwa zanyi, ka taimaka min, " adabarbarce ya furta"Aisha kina ina ne? Ga maganin na kawo maki" shiru yaji bata amsa mashi ba, a rude Ya mike Ya soma neman bedroom dinta saboda bai taba shiga dakinta ba, duk zuwan da zaiyi gidan A falo ya ke tsayawa.

Dakyar ya gano bedroom dinta, saboda tsabar rudu ya afka Ciki, a kwance ya taras da ita tsakiyar gadonta, sai juyi takeyi tana murkususu, tafukan hannayenta adaddafe da mararta, sam babu abaya ajikinta zafin daya taso matane yasa ta cireta cikin fitar hayyaci batare da saninta ba, sai Camisole data rage a jikinta shara shara gaba daya surar jikinta ta bayyana muraran.

Bai kula ba saboda hankalinsa ba akwance yake ba burinsa kawai ya taimake ta, Aje maganin yai akan bedside drawer Ya fito da sauri jim kadan ya dawo hannun shi ruke da bottle water Ya zauna daga gefen gadon..

Sai da Ya ballo kwayar maganin Ya juyo don ya taimaka mata tasha, kwatsam Idanun shi suka sauka akan Santala santalan Cinyoyinta lokaci Waya tunanin shi ya gushe, ya fara jin wata irin matsananciyar sha'awa na taso mashi kamar ransa zai fita, Zuciyarshi ta dinga azalzalarshi kanshi ya fara juya mashi kamar hankalinshi na barin jikinshi, Bawan Allah a lokacin yaita kokari kaucewa sharrin shaidan amma abun Yaci tura saboda yadda surar ummi ke fusgarsa har baisan sa'adda Ya afka mata ba, ga zafin ciwo tana fama da shi a haka dr shureim ya keta mata haddi, taji radadin da bazai misaltu ba, cikin fitar hayyaci ta dinga Sakin kukan azaba, tana yi masa magiya akan ya kyale ta, kada ya kashe ta, kada ya rabata da mutuncinta, amma duk abanza saboda a lokacin shureim yayi nisan da baya jin kira. Ya Ilahi!




*Daga Al?alamin Boss Bature=?%?
'?*





*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*=?%?=؋?=؞? &?=ؔ?=؞?>???

~<><><><><><><><><><><><><><>
'?~

~___________________________________~


Bata tashi farkawa ba, sai Bayan sallar Magrib, bakinta dauke da sunan Allah, tana kokarin motsawa don ta mi?e taji wani azababben zafi agabanta, ga wata kasala data baibaye sassan jikinta, tunani to soma yi meya faru da ita? A ina take"? jin iska na ratsa jikinta yasa tay saurin shafa jikin nata, lokaci daya gabanta Ya soma faduwa jin babu sutura a jikinta cikin sauri ta yunkura ta mi?e zaune, tana kallon kanta kafin ta yi saurin kallon gefenta, shureim ta gani a kwance kan gadon batare da sutura a jikin shi ba, sai dan bargon daya lullu6e ass dinsa, sam ta kasa tuna komai amma tabbas taji a jikinta raping Winta yayi Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un fashewa tayi da matsanancin kuka tamkar ana zare ranta, Koken da ta ke yi ne ya farkar da shi, a firgice ya bude idanun shi da suka kada jawur ya dube ta da su, baiyi aune ba yaji saukar zazzafan mari kan kuncinsa ta sha?e wuyanshi tana kuka ta furta"nashiga uku! yaya shureim ka kashe min rayuwata, ka gama dani! Ka wulakanta martabar jikina ka goga min ?azantar Zina, Allah Ya isa tsakanina da kai, bazan ta6a yafe maka ba..."


zafafan hawayene suka wanke fuskarshi kwata kwata baiji zafin marin da tayi mashi ba saboda ruWun da kwakwalwarsa ta shiga gaba daya yabi ya rikice yana kokarin tariyo abunda ya aikata mata, saboda baya a cikin hayyacinsa komai ya faru, wlh ko a mafarki bai ta6a sha'awar ya kusanci macen da ba muharramarsa ta aure ba, balle Aisha da yake yi mata kallon kanwarsa, tana kuka Yana kuka Yace"Aisha bayin kaina bane, ba halina bane aisha, ke shaidace akaina, wlh ni ba mazinaci bane..."

bai ?are maganarba ta Fasa tsawa tana huci tace "babu abunda zaka fada min ya shureim, wlh sai Allah yayi min sakayya, da kasan irin burin da nake dashi akanka da ba kai yi min haka ba, da tunfarko ka fadamin kana son Jikina, Ni mai iya aurenka ce don in dinga biya maka bukatarka saboda son da nake maka, amma ka rasa ta hanyar da zaka neme ni sai ta hanyar Zina"?

Tana magana Jikinta na kerma, Idanunta sun kada jawur kamar an watsa mata barkono.

Cikin disasshiyar murya tace "ka karyamin zuciyata yaya shureim, ka cuceni, ka zalunce ni, Inayi maka kallon mutun mai tsoron Allah, ashe kaima fasiki ne, kana daya daga cikin mazan da basa son mace don Allah sai don surar jikin ta, kaja mun aikata zunubi, Yanzu da wani ido kakeso In kalli Babana, da mutanan da sukeyi min kallon mutuniyar kirki! Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..." duk yadda yaso ya shawo kanta ya kasa, taki ta saurareshi balle ta fahimce shi, saukowa tayi daga kan gadon jikinta duk ba kwari dakyar ta mayar da rigarta da gudu ta shuge toilet tana kuka ta kulle kofar, tabar shureim a zaune kan gadonta yana ta kuka kamar karamin yaro, sau uku yana marin kanshi saboda bakin ciki da takaicin abunda ya aikata ma Aisha, Matar da yayi burin ya aura.

"Ya Allah ba halina bane, Kafi kowa sanin bawan nan naka, Ni maijin tsoronka ne mai gudun saba maka ne, kullum ina rokonka akan ka kareni daga sharrin zuciya da sharrin shedan amma meyasa Hakan ta faru dani? Meyasa na aikata ma Aisha haka"?...

Cikin shesshekar kuka yajiyo muryarta daga cikin toilet tana fadin"Yaya shureim ka tashi ka tafi tunkafin Aunty laura ta dawo"..

Jiki asanyaye Ya sauko daga kan gadon Cike da danasani Ya mayar da suturarsa, Wlh Yaji kunya mara misaltuwa, Yaji radadin da har yau In ya tuna sai yaji Waci aran shi.

______________________________________
'?

Lokacin da su Benazir suka lura babu malama Aysha a gurin partyn nanfa hankalinsu ya tashi suka dinga nemanta sako da lungu na gidan, har layin wayarta suka kira akashe.

Hankalin su atashe suka tuntu6i Aunty Laura da maganar, tace kada su damu, ta koma gida dama bada son ranta tazo ba, bayan Kammala partyn suka biyo Aunty Laura gidan don suga idan ta dawo, bayan sun shigo gidan suka Nufi dakinta, adatse suka iske kofar, Knocking su ka yi tare da ambaton sunanta, Tana jinsu tayi shiru bata amsa masu ba, har saida suka fara gajiya da bubbuga kofar su ka fara tunanin ko bata nan ne.

A lokacin da basuyi tsammani ba, sai ga kiran ta ya shigo layin Benazir, cikin sauri Benazir tayi picking up tana tambayar ina ta shiga ne? Suna ta neman ta.

Cikin raunanniyar murya Aysha tace kada su damu, tana acikin dakin, ta kwanta ne saboda bata jin dadin jikinta amma da sauki.

Cike da tausayinta Benazir tayi mata sannu da jiki kafin ta mika ma Anila itama tayi mata sannu.

Daga bisani su ka yi wa Aunty Laura sallama suka tafi, zuciyoyinsu cike fal da tunanin yanayin da sukaji Muryar Aisha.

Tun daga Ranar Aisha ta Wauke Kafa da zuwa gidan aminnanta, Babu wanda yasan abunda ya faru tsakaninta da dr shureim, ita kadai tayi ta nukunuku ta ki yarda Aunty laura ta gane halin da take a ciki, saboda bata son kowa ya sani ta fiso ta rufawa kanta asiri.


Tsawon kwana uku bata bude wayarta ba, baci ba sha, ba bacci, ta killace kanta adaki, wani irin depression ne Ya kamata ga ciwon rabin kai da take fama da shi, In ta fara kuka har sai hawayenta sun kafe tukunna take dakatawa, kusan kwana ta ke yi tana yin istigfari tare da kai kukanta gurin Allah.

Saboda tayi imanin shi kadai ne zai kawo mata mafita, Hankalin Aunty laura ba karamin tashi yayi ba, ganin Aisha na neman ta halaka kanta, Ta rasa gane meke damunta gaba daya ta hana kanta sukuni, ta rame tayi duhu, idanunta kullum a kumbure suke saboda kukan da take sha, ba irin magiyar da batayi mata ba akan ta faWa mata meke damunta amma taki sanar da ita, sai dai tace ta tayata da addu'a Allah ya yaye mata abunda ke damunta, tace toh In sha Allah zatayi mata addu'a.

Idan muka koma bangaren Dr shureim tun washe garin ranar da abun Ya faru, Yabar Kasar, Ya tafi Egypt saboda bazai Iya cigaba da jurar zama yana ganin Aisha da abun kunyar daya aikata mata ba.

Bayan makonni da afkuwar Lamarin, Sheikh Imam Ya dawo Nigeria, Bayan ya huce Gajiya a dakinsa, Aunty laura ta jera mashi abincin shi akan rug din dakinsa, Kasa cin abincin yayi saboda faduwar da gaban shi keyi, kuma yaji shiru Aisha bata leko ta yi mashi sannu da zuwa ba, kamar yadda ta saba yi mashi.

"Ina mamana? Ko taje islamiya ne, Aunty laura tace aa tana adaki Yace ta kira ma shi ita.

Fitowa tayi daga dakin ta shiga dakin Aisha, tayi mamakin ganinta a kudundune cikin bargo jikinta sai kerma yakeyi kamar wadda sanyi ya kama.

Hankali atashe Aunty Laura ta haye kan gadon tare da yaye bargon, gabanta ne ya fadi rass, ganin yadda idanun Aisha suka juye, tsabar zafin da jikinta ya dauka tamkar naman da aka gasa da wuta, arude Aunty laura ta zabga salati Ta watso aguje ta nufi dakin sheikh Imam Ta sanar da shi halin da Aisha take aciki, abincin da bai ci ba kenan, jikinshi na 6ari yabiyo bayan Aunty laura suka nufi dakin Aisha, Suna shiga suka taras da Amai na fita daga bakinta.

"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un" arude Sheikh Imam Ya furta, baiyi wata wata ba, Ya sungumi Aisha Ya fuce da ita da gudu Laura tabi bayanshi, Suka shiga mota.

Kaitsaye Suka Nufi Asibiti da ita, aranar saida aka kwantar da ita saboda jikinta yayi tsauri.

A asibitin suka kwana, Sheikh Imam bai runtsa ba, Yadda Ya ga rana haka yaga dare, har fada saida yayi ma Aunty Laura akan sakacinta na rashin kula da Aisha, gaya nan har ciwo yakamata batare da ita ta sani ba, Aunty laura dai sai hakuri take bashi tace ba laifin ta bane, nan ta fayyace masa halin da Aisha ta shiga bayan tafiyarsa, ta kara da cewa ba irin magiyar da banyi mata ba akan ta fadamin meke damunta amma takiya sai dai tace Intaya da addu'a, Sheikh Imam ya damu sosai, Babban abunda ya kara daga masa hankali ramewar da tayi, kamar ba Aisharsa ba.


Basu sanar da kowa game da ciwonta ba, a duk lokacin da su Benazir suka kira Aunty Laura su kai mata korafin sun kira layin Aisha basa samu sai tace masu su yi hakuri ayyuka ne su ka yi mata yawa, kwanansu Waya a asibitin baci ba sha saboda damuwar Halin da Aisha take a ciki, Bayan dr din dake kula da Aisha ta gama bincikenta akan lafiyarta, ta kira Sheikh imam don suyi magana acikin Office din ta.

Bayan sun shigane Dr din Ta dube shi dakyau fuskarta da damuwa tace"Sheikh, naji dadi da Ya kasance Ni Ce amintacciyar Likitar dake duba Iyalanka, Saboda kai malamina ne, ni kuma dalibarka ce, ni me rufa maka asiri ce don kare martabarka" Cike da gamsuwa sheikh Imam Ya jinjina mata kai da alamun rudu akan fuskarsa.

Takardar dake a hannunta ta mi?a masa jiki asanyaye ya kar6a har zai buWe muryar Dr din ta katse shi.

"Sakamakon gwajin da mukayi ma Aisha ne"

A hankali Ya soma karanta sakamakon, abun mamaki sai taga yana dariya maimakon taga tashin hankali akan Fuskarshi don ta san muddin Ya karanta sai Hankalinsa ya tashi ba kadan ba.

"Sheikh Lafiya naga kana dariya" mika mata takardar yayi"Ki duba dakyau, wannan sakamakon bana Aisha bane, watakil kunyi mistake ne, Aisha da bata da aure, Ina ita Ina ciki"? Ya fada da murmushi akan fuskarta, Idanun Dr dinne suka cicciko tab da kwalla saboda tsananin tausayin shi daya kamata.


"Dan Allah, Ki bani na Aishana inaso in san meke damunta, wannan kuma ku nemo mai shi ku bata, kada asamu matsala..."

girgiza kai Dr din tayi cikin rauni na murya tace"Kayi hakuri Sheikh, kai malamine nasan kayi imani da Allah ka kuma yi imani da kaddara, wlh result din Aisha ne, Tana dauke da juna biyu, Nima dana ga sakamakon saida na karyata kaina saboda nasan Aisha bata da aure, sannan Aisha kamilar macace, amma dana zurfafa bincike na sai na gano dagaske Cikine a jikin ta...."

bata ?are maganarba sakamakon Tsawar da Sheikh Imam Ya doka mata tamkar zai fasa dodon kunnanta, Tuni tasha jinin jikin ta.

Yana Huci Ya furta"Kin bani mamaki dr Husaina, kin kuma ji kunya wlh, baki taba yi min karya ba sai yau, wannan sakamakon da kika nuna min bana Aishana bane, mamana bazata taba aikata zina Ba, ?ata kamila ce, mai jin tsoron Allah bazata taba aikata abunda zai sabawa Mahaliccin ta ba, Na yarda da ?ata Aisha bazata ta6a ruke koda hannun Namijin daba muharraminta bane, don haka ki gaggauta janye kazafin da kike kokarin yi mata, watakil biyanki akayi don kiyi mata ?azafi, dama akwai masu jin haushin daukakar da Allah yayi mata watakil kema kina daga cikin su...'

kwata kwata Dr husaina bataji haushin kalaman Shiekh Imam ba, sai ma tausayin shi daya ?ara kamata.

Kekketa Takardar yayi, Tare da watsa pieces din saman table din gabanta, Ya juya afusa ce Yabar Office.


Yana tafiya Visitors dake zarya acikin asibitin sai kallon shi sukeyi ganin Sheikh Imam wasu har gaishe da shi sukeyi amma bai kula su ba, Yana shiga dakin da aka kwantar da ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Aisha Ya iske Aunty laura zaune kan kujerar dake a gefen gadon ta zabga uban tagumi..

Tana jin motsin shigowarshi ta mike tana tambayarshi me dr tace.

Rai a6ace yace"ba zamu cigaba da zama acikin asibitin nan ba, Gida zamu tafi inyaso sai muyi jinyarta acan"

"Amma ba'a sallame mu ba, kuma jikin nata har yanzu da sauranshi..."

bata ?are maganar ba, Ya daka Mata tsawa"Ki ruko Aisha mu tafi" jikinta na bari ta taimaka ma Aisha ta mike baiwar Allah ko tafiya bata iyayi sai layi take kamar zata kife ?asa a haka suka shiga mota da ita.

Bayan sun dawo gida Aunty Laura Ta matsa mashi akan ya faWa mata me doc Husaina tace akan ciwon Aisha Nan ya kwashe komai da suka tattauna ya sanar da ita, itama a lokacin biye mashi tayi suka karyata maganar Dr husaina.

Cikin da laulayi ya zo ma Aisha, bakar wahala take sha, wani sa'in tana a kwance kan gado take fara kwarara amai ta sauko da gudu ta fada toilet ta karasa shi acan.

Gashi kullum Cikin yin zazzabi takeyi, daga bayane Aunty Laura ta gano Ciki ne da ita, Bazan Iya misalta tashin hankalin da Aunty Laura ta shiga ba, a daki ta same ta kwance kan gado tace taji tsoron Allah ta fada mata gaskiya! Akwai ciki jikinta ko babu? saboda ta fara kokwanto akan yanayin ta, Kafin ta sanar da ita saida ta fara rokonta akan karta fada ma baba Imam tabarshi a matsayin sirri atsakaninsu duk da tasan watarana dole ne Yaji, Aunty laura tace tayi mata alkawarin bazai taba ji abakinta ba.

Anan ta labarta mata komai daya faru tsakaninta da shureim, a lokacin Aunty Laura ta zabga salati tana sallallami, Jikinta Ya kama bari Saboda razanar da tayi, ta girgiza ba kadan ba, musamman dataji cewa Shureim ne yayi mata aika aikar, Babban tashin hankalinta Idan Sheikh Imam Ya gano Cikin ne dagaske, to fa itace mutun tafarko da zai fara tuhuma saboda ita ta matsa ma Aisha akan suje Partyn.

Aunty Laura tayi kuka kamar ranta zai fita, saboda tausayin Aisha daya kamata, Yarinya Kamila da ita an zubar mata da mutuncin ta, dr shureim Yasha tsinuwa agurin Aunty laura, tace dan iska munafuki mai fuska biyu, kamar Na Allah, In sha Allahu sai yaga sakayyar abunda yayi mata, daga bisani ta lallashi Aisha taja ta ajiki sosai, ta dinga bata hakuri hadi dayi mata nasiha har hakuri ta bata akan Tursasa matan da tayi akan taje, gani take ma kamar itace Silar komai daya faru da Aisha.

A haka aka cigaba da rayuwa, Har Ila Yau sheikh Imam yaki yarda cewa Aisha ciki gare ta, wani'sa'in agaban shi zatayi amai amma ko kadan bai yarda ya zargeta da ciki ba, Iya bakin gwargwado tana samun kyakkyawar kulawa agurin Baba Imam, baya barinta cikin damuwa, Ya hana a kaita asibiti kuma Ya hana dr Husaina zuwa agidan, Ko tazo da niyar duba Aisha tun daga bakin gate security Officers ke korarta.

lamarin ya daure mata kai, ita burinta kawai ta taimaka ma sheikh Imam su nemi mafita gudun kada kimarshi ta zube sai dai Yaki bata damar ganawa da shi, Har court taje ta same shi a office dinshi Amma Yaki sauraronta, badan taso ba tahakura da bibiyar shi.

Saboda


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login